WAƘA TA 144
Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!
Hoto
	- 1. A aljanna a duniyar nan, - Allah za ya cire duk cuta. - Waƙar yara, murna, salama, - Duk za su cika ko’ina, - Kuma za a ta da matattu - Domin su zauna har abada. - (AMSHI) - Allah zai yi abubuwan nan, - In muna ɗokin ladan nan. 
- 2. A aljanna dukan dabbobi - Za su kasance da mutane. - Ƙaramin yaro zai bi da su, - Duk za su bi umurninsa. - Jin tsoro da kuma mutuwa, - Za su daina damun mutane. - (AMSHI) - Allah zai yi abubuwan nan, - In muna ɗokin ladan nan. 
(Ka kuma duba Isha. 11:6-9; 35:5-7; Yoh. 11:24.)