WAƘA TA 149
Waƙar Nasara
Hoto
(Fitowa 15:1)
1. Mu yabi Allah, mu ɗaukaka sunan Jehobah.
Ya hallaka Fir’auna da duk mayaƙansa.
Mu yabi Allah,
Babu wani Allah kamar sa.
Jehobah na da iko
A kan maƙiyansa.
(AMSHI)
Jehobah Allah Maɗaukaki,
Ba za ka canja ba har abada.
Za ka hallaka duk maƙiyanka
Don ka ɗaukaka sunanka.
2. Allah Jehobah, zai kunyatar da duk al’umma,
Don suna yin tsayayya
Da Mulkinsa sosai.
Yesu Ɗan Allah,
Zai cire su da Armageddon,
Jama’a za su ɗaukaka
Sunan Jehobah.
(AMSHI)
Jehobah Allah Maɗaukaki,
Ba za ka canja ba har abada.
Za ka hallaka duk maƙiyanka
Don ka ɗaukaka sunanka.
(Ka kuma duba Zab. 2:2, 9; 92:8; Mal. 3:6; R. Yoh. 16:16.)