Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • lvs babi na 16 pp. 213-225
  • Kada Ka Ba Shaidan Dama

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Ba Shaidan Dama
  • Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Karanta a “Ƙaunar Allah”
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • “KAMAR ZAKI MAI JIN YUNWA”
  • MUNA DA “KOKAWA”
  • KA GUJI SHA’ANI DA ALJANU
  • SHAIƊAN YANA SO YA MANA WAYO
  • SHAIƊAN YANA AMFANI DA ABUBUWAN DA MUKE SO
  • LABARAN ALJANU
  • Gaskiya Game da Mala’iku da Kuma Aljanu
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Su Waye Ne Abokan Gāban Allah?
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Dubi Ƙari
Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
lvs babi na 16 pp. 213-225
Wani dan’uwa yana wa’azi don ya yi tsayayya da Shaidan

BABI NA 16

Kada Ka Ba Shaiɗan Dama

“Kada ku ba Shaiɗan dama, shi kuwa zai guje muku.”​—YAƘUB 4:7.

1, 2. Me muke bukatar mu sani game da Shaiɗan da kuma aljanu?

RAYUWA a sabuwar duniya za ta yi daɗi ba kaɗan ba. A lokacin, za mu yi irin rayuwar da Allah yake so mu yi. Amma a yanzu muna rayuwa a duniya wadda Shaiɗan da aljanu ne suke iko da ita. (2 Korintiyawa 4:4) Ko da yake ba za mu iya ganinsu ba, amma suna nan kuma suna da iko.

2 A wannan babin, za mu tattauna yadda za mu yi kusa da Allah kuma mu guji ba wa Shaiɗan dama. Jehobah ya yi mana alkawari cewa zai taimaka mana. Amma muna bukatar mu san dabarun da Shaiɗan yake amfani da su don ya ruɗe mu ko kuma ya kawo mana hari.

“KAMAR ZAKI MAI JIN YUNWA”

3. Mene ne Shaiɗan yake so ya yi?

3 Shaiɗan ya ce ba da zuciya ɗaya ’yan Adam suke bauta wa Allah ba kuma idan suka shiga damuwa, za su daina bauta masa. (Karanta Ayuba 2:​4, 5.) Shi ya sa idan wani yana so ya bauta wa Jehobah, Shaiɗan da aljanu suna ganin hakan kuma za su yi ƙoƙarin hana shi. Idan mutum ya yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ya yi baftisma, sukan yi baƙin ciki. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Shaiɗan da “zaki mai jin yunwa,” kuma yake “neman wanda zai cinye.” (1 Bitrus 5:8) Shaiɗan yana so ya ɓata dangantakarmu da Jehobah.​—Zabura 7:​1, 2; 2 Timoti 3:12.

Wani dan’uwa yana wa’azi don ya yi tsayayya da Shaidan

Shaiɗan yana fushi sa’ad da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah

4, 5. (a) Wane abu ne Shaiɗan ba zai iya yi ba? (b) Ta yaya za mu guji “ba Shaiɗan dama”?

4 Amma bai kamata mu riƙa tsoron Shaiɗan da aljanu ba. Jehobah ya rage abubuwan da za su iya yi mana. Jehobah ya yi alkawari cewa “babban taro” na Kiristocin gaskiya za su tsira “daga azabar nan mai zafi.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 14) Ba abin da Shaiɗan zai yi da zai hana hakan faruwa, domin Jehobah yana kāre mutanensa.

5 Idan muka yi kusa da Allah, Shaiɗan ba zai iya ɓata dangantakarmu da Allah ba. Kalmarsa ta ba mu wannan tabbaci cewa: “Yahweh yana tare da ku muddin ku kuna tare da shi.” (2 Tarihi 15:2; karanta 1 Korintiyawa 10:13.) Da yawa daga cikin bayin Allah na dā, kamar su Habila da Enok da Nuhu da Saratu da kuma Musa, sun yi kusa da Allah kuma hakan ya sa ba su ba Shaiɗan dama ba. (Ibraniyawa 11:​4-40) Mu ma za mu iya yin hakan. Kalmar Allah ta ce: “Kada ku ba Shaiɗan dama, shi kuwa zai guje muku.”​—Yaƙub 4:7.

MUNA DA “KOKAWA”

6. Ta yaya Shaiɗan yake kawo mana hari?

6 Duk da cewa Jehobah ya rage abubuwan da Shaiɗan zai iya yi mana, Shaiɗan zai yi iya ƙoƙarinsa don ya ɓata dangantakarmu da Allah. A yau Shaiɗan yana amfani da dabaru dabam-dabam, kuma yana amfani da wasu dabaru da ya yi amfani da su shekaru da yawa. Waɗanne dabaru ke nan?

7. Me ya sa Shaiɗan yake kai ma bayin Allah hari?

7 Manzo Yohanna ya rubuta cewa: “Duniya duka tana a hannun mugun nan.” (1 Yohanna 5:19) Shaiɗan ne yake iko da wannan duniyar kuma zai so ya yi iko a kan bayin Allah ma. (Mika 4:1; Yohanna 15:19; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​12, 17) Ya san cewa lokacinsa ya kusan ƙarewa, shi ya sa yake matsa ma bayin Allah don su yi ma Allah rashin biyayya. A wasu lokuta yakan kawo mana hari, a wasu lokuta kuma yakan yi amfani da wayo don ya rinjaye mu.

8. Me ya kamata kowanne Kirista ya sani?

8 Littafin Afisawa 6:​12, ta ce: ‘Muna kokawa . . . da mugayen ruhohi na sammai.’ Kowanne Kirista yana faɗa da Shaiɗan da kuma aljanu. Muna bukatar mu san cewa duk waɗanda suka yi alkawarin bauta wa Allah suna cikin wannan faɗan. A wasiƙar da Manzo Bulus ya rubuta wa Afisawa, ya ƙarfafa Kiristocin har sau uku su ‘dāge.’​—Afisawa 6:​11, 13, 14, Littafi Mai Tsarki.

9. Mene ne Shaiɗan da aljanu suke ƙoƙarin yi mana?

9 Shaiɗan da aljanu suna so su yaudare mu ta hanyoyi da yawa. Idan mun yi nasara a kan dabarar da Shaiɗan ya yi amfani da ita, zai sake amfani da wata hanya dabam don ya yaudare mu. Shaiɗan yakan yi ƙoƙari ya san kasawarmu don ya san hanyar da zai bi ya yaudare mu. Amma za mu iya yin nasara a kan sa, domin Littafi Mai Tsarki ya gaya mana dabarun da Shaiɗan yake amfani da su. (2 Korintiyawa 2:11; ka duba Ƙarin Bayani na 31.) Ɗaya daga cikin dabarun da Shaiɗan yake amfani da su shi ne sha’ani da aljanu.

KA GUJI SHA’ANI DA ALJANU

10. (a) Mene ne sha’ani da aljanu ya ƙunsa? (b) Mene ne ra’ayin Jehobah game da sha’ani da aljanu?

10 Sha’ani da aljanu ya ƙunshi abubuwan dabo kamar su duba da maitanci da kuma ƙoƙarin yin magana da matattu. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa sha’ani da aljanu abin “ƙyama ne,” kuma ba za mu iya bauta ma Jehobah da kuma yin sha’ani da aljanu ba. (Maimaitawar Shari’a 18:​10-12; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:8) Shi ya sa Kiristoci suke bukatar su guji kowanne irin abu da ya shafi aljanu.​—Romawa 12:9.

11. Me zai iya faruwa da mu idan muna marmarin abubuwan dabo ko tsafi?

11 Shaiɗan ya san cewa idan muna son abubuwan dabo ko tsafi, zai masa sauƙi ya sa mu soma sha’ani da aljanu. Duk wani abin da yake da alaƙa da aljanu zai ɓata dangantakarmu da Allah.

SHAIƊAN YANA SO YA MANA WAYO

12. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin ɓata tunaninmu?

12 Shaiɗan yana ƙoƙarin rikitar da mutane. A hankali yakan sa mutane shakka, har su “ce mugunta ita ce nagarta, nagarta kuwa mugunta.” (Ishaya 5:​20, LMT) Shaiɗan yana yaɗa ƙarya cewa shawarar Littafi Mai Tsarki ba ta da amfani kuma za mu yi farin ciki idan muka ƙi yin biyayya ga Allah.

13. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin sa mutane shakka?

13 Sa mutane shakka yana cikin dabarun da Shaiɗan yake yawan amfani da su. Ya jima yana amfani da wannan dabarar. A lambun Adnin, ya sa Hauwa’u shakka sa’ad da ya yi mata wannan tambayar: ‘Allah ya ce, lallai ba za ku ci daga kowane itacen da yake a gonar ba?’ (Farawa 3:1) Daga baya, a zamanin Ayuba ma, Shaiɗan ya gaya ma Jehobah a gaban mala’iku cewa: ‘A’i, ba a banza ne Ayuba yake jin tsoron Allah ba!’ (Ayuba 1:9) Bayan Yesu ya yi baftisma, Shaiɗan ya ce masa: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka umarci duwatsun nan su zama burodi.’​—Matiyu 4:3.

14. Ta yaya Shaiɗan yake sa mutane tunanin cewa sha’ani da aljanu ba shi da haɗari?

14 Har a yau ma, Shaiɗan yana ƙoƙarin sa mutane shakka. Yana sa mutane su soma tunanin cewa sha’ani da aljanu bai da wani haɗari. Har wasu Kiristoci ma suna ruɗin kansu da hakan. (2 Korintiyawa 11:3) To me za mu yi don mu kāre kanmu? Ta yaya za mu guji faɗawa cikin tarkon Shaiɗan? Bari mu yi la’akari da hanyoyi biyu da Shaiɗan zai iya yaudarar mu, wato nishaɗi da kuma neman lafiya.

SHAIƊAN YANA AMFANI DA ABUBUWAN DA MUKE SO

15. Ta yaya za mu iya soma sha’ani da aljanu ta wurin nishaɗinmu?

15 A yau, yawancin bidiyo da shirye-shiryen telibijin da wasannin kwamfuta da shafuffukan intane suna ɗauke da aljanu da dabo da kuma tsafi. Mutane da yawa suna ganin abubuwan nan ba su da wani haɗari, a maimako haka, suna ɗaukan su a matsayin abubuwan shakatawa. Mutum zai soma sha’ani da aljanu ta wajen zuwa wurin boka yin magani. Shaiɗan yana ƙoƙarin ɓoye illarsu kuma ya sa mu soma gani kamar ba za mu iya fahimtar su ba kuma suna da gwanin sha’awa. Mutum zai iya yin tunani cewa kallon fina-finan da ke nuna aljanu ba laifi ba ne tun da yake ba ya sha’ani da su. Me ya sa wannan tunanin bai dace ba?​—1 Korintiyawa 10:12.

16. Me ya sa ya kamata mu guje wa fina-finai ko waƙoƙin da ke da alaƙa da aljanu?

16 Shaiɗan da aljanunsa ba za su iya sanin abin da yake zuciyarmu ba. Amma za su iya sanin abin da muke so ta wajen lura da zaɓin da muke yi wa kanmu da iyalinmu, kuma hakan ya ƙunshi nishaɗin da muke zaɓa. Idan muna son kallon fina-finai ko saurarar waƙoƙin da akwai maita ko tsafi ko aljanu da dai sauransu, Shaiɗan da aljanunsa za su san cewa muna so mu san game da su. Don haka, za su yi ƙoƙari su sa mu soma sha’ani da aljanu.​​—Karanta Galatiyawa 6:7.

17. Ta yaya Shaiɗan zai iya amfani da bukatarmu ta ƙoshin lafiya?

17 Shaiɗan ya san cewa muna so mu kasance da ƙoshin lafiya kuma zai iya amfani da hakan don ya yaudare mu. Mutane suna fama da rashin lafiya a yau. Mutum zai iya yin jinya iri-iri amma bai sami sauƙi ba. (Markus 5:​25, 26) Hakan zai iya sa shi damuwa kuma zai yarda ya yi kome don ya sami sauƙi. Amma mu Kiristoci ya kamata mu yi hankali don kada mu karɓi magani ko wata jinya da ke da alaƙa da aljanu ko bokanci.​—Littafin Firistoci 19:31.

Wani dan’uwa yana addu’a tare da matarsa da ke kan gado a asibiti

Ka dogara ga Jehobah sa’ad da kake rashin lafiya

18. Wace irin jinya ce ya kamata Kirista ya guje ma?

18 A zamanin Isra’ilawa na dā, wasunsu sun yi sha’ani da aljanu. Shi ya sa Jehobah ya ce musu: “Idan kuka miƙa hannuwanku sama, zan ɓoye fuskata daga gare ku. Ko da ma kun yi ta addu’o’i, ba zan ji ba.” (Ishaya 1:15) Ka lura cewa Jehobah ya ƙi jin addu’o’insu! Ba ma so mu yi abin da zai ɓata dangantakarmu da Allah kuma ya hana shi taimaka mana musamman ma sa’ad da muke rashin lafiya. (Zabura 41:3) Shi ya sa ya kamata mu bincika don mu san ko jinyar da muke so mu yi tana da alaƙa da aljanu ko bokanci. (Matiyu 6:13) Idan mun lura cewa tana da alaƙa da aljanu, dole ne mu guji jinyar!​—Ka duba Ƙarin Bayani na 32.

LABARAN ALJANU

19. Me ya sa wasu mutane suke tsoron Shaiɗan?

19 Wasu ba su gaskata cewa akwai Shaiɗan da aljanu ba, wasu kuma sun san cewa suna wanzuwa domin sun taɓa sha’ani da su. Mutane da yawa suna yawan tsoron aljanu kuma sun gaskata da camfi. Wasu kuma sukan yaɗa jita-jita game da lahanin da aljanu suke yi. Mutane sukan ji daɗin irin waɗannan labaran kuma su ma sai su ba da labarin ga wasu. Irin waɗannan labaran sukan sa mutane tsoron Shaiɗan.

20. Ta yaya za mu iya yaɗa ƙaryar Shaiɗan?

20 Ka lura cewa Shaiɗan yana so mutane su riƙa tsoron sa. (2 Tasalonikawa 2:​9, 10) Shi maƙaryaci ne kuma yakan yi iko da mutanen da suke sha’ani da aljanu, kuma ya sa su gaskata abin da ba gaskiya ba. Irin waɗannan mutanen za su riƙa yaɗa labaran abubuwan da suka gani kuma suka ji. Yayin da suka ci gaba da yaɗa labaran, za a ci gaba da ƙara gishiri a labaran. Ba ma so mu taimaka ma Shaiɗan ya sa mutane tsoronsa ta wurin yaɗa irin waɗannan labaran.​—Yohanna 8:44; 2 Timoti 2:16.

21. A maimakon yaɗa labarai game da aljanu, mene ne za mu iya tattaunawa da mutane?

21 Idan wani Mashaidin Jehobah ya taɓa sha’ani da aljanu a dā, bai kamata ya riƙa yaɗawa ba. Ba ma bukatar mu riƙa jin tsoron abubuwan da Shaiɗan da aljanunsa suke da ikon yi. A maimakon haka, mu mai da hankali ga Yesu da kuma ikon da Jehobah ya ba shi. (Ibraniyawa 12:2) Yesu bai cika almajiransa da labaran aljanu ba. Ya mai da hankali ga wa’azin Mulkin Allah da kuma “abubuwan da Allah ya yi” masu ban al’ajabi.​—Ayyukan Manzanni 2:11; Luka 8:1; Romawa 1:​11, 12.

22. Mene ne ka ƙuduri aniyar yi?

22 Kada mu manta cewa Shaiɗan yana so ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Zai yi iya ƙoƙarinsa don ya yi hakan. Amma mun san dabarun Shaiɗan kuma mun ƙudurta mu guji sha’ani da aljanu. Ba za mu taɓa “ba Shaiɗan wata dama” ya sa mu yi wa Jehobah rashin biyayya ba. (Karanta Afisawa 4:27.) Hakika, idan mun ƙi ba Shaiɗan dama, Jehobah zai kāre mu daga tarkonsa.​​—Afisawa 6:11.

ƘA’IDODIN LITTAFI MAI TSARKI

1 SHAIƊAN NE YAKE IKO DA DUNIYA

“Duniya duka tana a hannun mugun nan.”​​—1 Yohanna 5:19

Mene ne Shaiɗan yake so ya yi?

  • 1 Bitrus 5:8

    Shaiɗan yana so ya ɓata dangantakarmu da Jehobah.

  • Ayuba 2:​4, 5

    Yakan yi fushi idan ya ga mutane suna koyan abubuwa game da Jehobah kuma suna ƙaunar sa.

2 KADA KA JI TSORON SHAIƊAN

“Domin haka sai ku miƙa kanku ɗungum ga Allah. Kada ku ba Shaiɗan dama, shi kuwa zai guje muku.”​—Yaƙub 4:7

Ta yaya muka sani cewa zai yiwu mu ƙi ba Shaiɗan dama?

  • Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:​9, 14

    Jehobah ya rage abubuwan da Shaiɗan zai iya yi mana. Allah ya yi alkawari cewa mutane da yawa za su tsira kuma su shiga sabuwar duniya.

  • 2 Tarihi 15:2

    Idan muka yi kusa da Allah, Shaiɗan ba zai iya ɓata dangantakarmu da shi ba.

  • 1 Korintiyawa 10:13; Ibraniyawa 11:​4-40

    Jehobah ya yi alkawarin taimaka mana mu jimre, kamar yadda ya taimaka ma bayinsa da yawa a dā.

3 KA YI HANKALI DA DABARUN SHAIƊAN

“Mun san dabarunsa sarai.”​—2 Korintiyawa 2:11

Waɗanne irin dabaru ne Shaiɗan yake amfani da su?

  • Yohanna 15:19; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​12, 17

    Shaiɗan ne yake iko da duniya, amma bai da iko a kan bayin Jehobah, shi ya sa yakan kai musu hari.

  • Farawa 3:1; Galatiyawa 5:​19-21; Afisawa 6:12

    Shaiɗan yakan yi ƙoƙari ya san kasawarmu domin ya yi amfani da su ya rinjaye mu.

  • Littafin Firistoci 19:26; Littafin Firistoci 19:31; Markus 5:​25, 26

    Mu yi hankali sa’ad da muke zaɓan irin jinyar da za mu yi. Mutum zai iya fama da rashin lafiya har ya yarda a yi masa jinya da ke da alaƙa da dabo ko tsafi.

  • Maimaitawar Shari’a 18:​10-12; Ayyukan Manzanni 19:19; Galatiyawa 6:7; Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:8

    Idan aljanu sun lura cewa muna son abubuwan dabo ko tsafi, za su iya amfani da hakan su cuce mu. Idan muka yi sha’ani da aljanu, mun yi rashin biyayya ke nan ga Jehobah.

4 KADA KA YAƊA ƘARYAR SHAIƊAN

“[Shaiɗan] mai ƙarya ne, uban ƙarya kuma.”​—Yohanna 8:44

Ta yaya za mu iya yaɗa ƙaryar Shaiɗan?

  • Romawa 1:​11, 12; 2 Timoti 2:16

    Mutane sukan yaɗa jita-jita game da Shaiɗan da kuma aljanu. Kuma suna ƙara gishiri a kan abubuwan da Shaiɗan da aljanu za su iya yi. A maimakon mu riƙa yaɗa jita-jita da zai sa mutane tsoro, mu tattauna abubuwan da za su ƙarfafa su.

  • Afisawa 6:11

    Sanin dabarun Shaiɗan zai taimaka mana mu ƙi ba shi dama kuma mu yi kusa da Jehobah.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba