Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 2/1 pp. 8-12
  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ya Kamata ne Mu Ji Tsoron Iblis?
  • Me ya sa Shaiɗan ke Tsananta Mana?
  • “Ka Cece Mu Daga Mugun”
  • Kada Ka Yarda Iblis ya Ribace Ka
  • Makaman Allah na Kāre Mu
  • Ka yi Tsayayya da Iblis, Kuma zai Guje Ka
  • “Ku Yi Tsayayya Da Shaiɗan” Yadda Yesu Ya Yi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • “Ku Yi Tsayayya Da Iblis”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Wane ne ko kuma mene ne Iblis?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2016
  • Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 2/1 pp. 8-12

Ka Yi Tsayayya Da Shaiɗan, Kuma Zai Guje ka!

“Ku zama . . . masu-biyayya ga Allah, amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje maku.”—YAƘUB 4:7.

1, 2. (a) Wane halin Iblis ne ya bayyana a kalaman da ke rubuce a Ishaya sura 14? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

IBLIS shi ne babban mai girman kai. Fahariyarsa ta bayyana a cikin kalaman da annabin Allah, Ishaya ya rubuta. Fiye da ƙarni guda kafin Babila ta zama mai iko da duniya, an nuna mutanen Jehobah suna cewa game da “sarkin Babila”: “Cikin zuciyarka ka ce, har sama zan hau, zan ɗaukaka kursiyina bisa tamrarin Allah [wato, zuriyar Dauda da suka yi sarauta]: . . . In maida kaina kamar Mai-iko duka.” (Ishaya 14:3, 4, 12-15; Litafin Lissafi 24:17) Fahariyar “sarkin Babila” ta yi daidai da halin Shaiɗan, wanda shi ne “allah na wannan zamani.” (2 Korinthiyawa 4:4) Amma girmankai na Shaiɗan zai ja masa halaka, kamar yadda ƙarshen sarakunan Babila ya zama abin kunya.

2 Muddin Iblis na raye, muna iya damuwa da tambayoyi kamar su: Ya kamata ne mu ji tsoron Shaiɗan? Menene ya sa Shaiɗan yake sa mutane su tsananta wa Kiristoci? Ta yaya za mu guji faɗawa hannun Iblis?

Ya Kamata ne Mu Ji Tsoron Iblis?

3, 4. Me ya sa amintattun Kiristoci shafaffu da abokansu ba sa jin tsoron Iblis?

3 Waɗannan kalaman na Yesu Kristi sun ƙarfafa Kiristoci shafaffu: “Kada ka ji tsoron wahala da za ka sha: ga shi, Shaiɗan yana shiri ya jefa waɗansu daga cikinku a kurkuku, domin a gwada ku; kwana goma kuwa za ku sha ƙunci. Ka yi aminci har mutuwa, ni ma in ba ka rawanin rai.” (Ru’ya ta Yohanna 2:10) Shafaffu da abokanansu masu begen zama a duniya ba sa jin tsoron Iblis. Wannan rashin tsoron ba don gaba gaɗin da aka haife su da ita ba ne. Ta wanzu ne domin suna tsoron Allah kuma ‘suna samun mafaka ƙalƙashin inuwar fukafukansa.’—Zabura 34:9; 36:7.

4 Mabiyan Yesu Kristi na farko masu gaba gaɗi sun kasance da aminci har mutuwa duk da wahalar da suka sha. Ba su ji tsoron abin da Shaiɗan Iblis zai yi ba, domin sun san cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da waɗanda suka kasance da aminci gareshi ba. Haka nan ma, sa’ad da suke fuskantar tsanani sosai, kiristoci shafaffu da abokanansu da suka keɓe kansu sun kuduri aniya za su ci gaba da amincinsu ga Allah. Amma, manzo Bulus ya bayyana cewa Iblis yana iya jawo mutuwa. Bai kamata hakan ya ba mu tsoro ba?

5. Menene muka koya daga Ibraniyawa 2:14, 15?

5 Bulus ya ce Yesu ya zama mutum “domin ta wurin mutuwa shi wofinta wanda yake da ikon mutuwa, watau Shaiɗan; shi kuma sake dukan waɗanda ke ƙarƙashin bauta muddar ransu saboda tsoron mutuwa.” (Ibraniyawa 2:14, 15) Domin yana da “ikon [jawo] mutuwa,” Shaiɗan ya rinjayi Yahuza Iskariyoti, bayan haka ya sa shugabannin Yahudawa da kuma Romawa suka kashe Yesu. (Luka 22:3; Yohanna 13:26, 27) Ta mutuwarsa ta hadaya, Yesu ya ’yanta ’yan adam masu zunubi daga hannun Shaiɗan kuma ya sa mun sami damar samun rai na dindindin.—Yohanna 3:16.

6, 7. Yaya yawan ikon da Iblis ke da shi na jawo mutuwa?

6 Yaya yawan ikon da Iblis ke da shi na jawo mutuwa? Tun daga farkon aikinsa na mugunta, ƙaryarsa da ja-gorarsa sun jawo wa mutane mutuwa. Hakan ya faru domin Adamu ya yi zunubi, ta haka, ya yaɗa zunubi da mutuwa ga mutane. (Romawa 5:12) Bugu da ƙari, bayin Shaiɗan da suke duniya sun tsananta wa masu bauta wa Jehobah, a wasu lokatai ma har kashe su suke yi kamar yadda suka yi wa Yesu Kristi.

7 Duk da haka, kada mu yi tunanin cewa Iblis zai iya jawo mutuwar duk mutumin da yake son ya kashe. Allah na kāre waɗanda ke na sa, kuma ba zai taɓa ƙyale Shaiɗan ya kawar da dukan masu bauta ta gaskiya a duniya ba. (Romawa 14:8) Hakika, Jehobah yana ƙyale a tsananta wa mutanensa, kuma yana ƙyale wasun mu su mutu a sakamakon harin Iblis. Duk da haka, Nassosi sun ba da bege na tashin matattu ga waɗanda suke cikin “littafin tunawa” na Allah, kuma Iblis ba zai iya hana hakan ba!—Malachi 3:16; Yohanna 5:28, 29; Ayukan Manzanni 24:15.

Me ya sa Shaiɗan ke Tsananta Mana?

8. Me ya sa Iblis ke sa a tsananta wa bayin Allah?

8 Idan mu bayin Allah ne masu aminci, akwai wani muhimmin dalilin da ya sa Iblis yake tsananta mana. Manufarsa ita ce, yana so mu bar bangaskiyarmu. Muna da dangantaka mai tamani da Ubanmu na sama, kuma Shaiɗan yana son ya lalata ta. Kada haka ya zama abin mamaki. A Aidan, Jehobah ya annabta cewa ƙiyayya za ta kasance tsakanin “macen” ta alama da “macijin” da kuma ‘zuriyarsu.’ (Farawa 3:14, 15) Nassosi sun kira Iblis “tsohon macijin” kuma sun bayyana cewa yana da gajeren lokaci kuma yana nuna hasala mai girma. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 12) Yayin da ƙiyayya ta ci gaba tsakanin ‘zuriyoyin’ biyu, waɗanda suke bauta wa Jehobah cikin aminci za su fuskanci tsanani. (2 Timothawus 3:12) Ka san ainihin dalilin da ya sa Shaiɗan ke tsananta mana?

9, 10. Wane batu ne Iblis ya tayar, kuma ta yaya hakan ya shafi halin mutane?

9 Iblis ya ta da batun ikon mallaka na sararin samaniya. A batun, ya tuhumi amincin mutane ga Mahaliccinsu. Shaiɗan ya tsananta wa mutumin nan mai aminci Ayuba. Me ya sa? Domin yana so ya karya amincin Ayuba ga Jehobah. Matar Ayuba da kuma abokansa uku “masu-ta’aziya na ban takaici” sun cika manufar Iblis a wannan lokacin. Kamar yadda aka nuna a littafin Ayuba, Iblis ya tuhumi Allah, ya faɗi cewa babu mutumin da zai kasance da aminci ga Allah idan aka ƙyale Shaiɗan ya jarabce shi. Ayuba ya riƙe amincinsa, da haka, ya nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. (Ayuba 1:8–2:9; 16:2; 27:5; 31:6) A yau, Iblis yana tsananta wa Shaidun Jehobah domin ya karya amincinsu kuma ya tabbatar da cewa tuhumarsa gaskiya ne.

10 Sanin cewa Iblis yana tsananta mana ne domin yana son mu karya amincinmu ga Allah, hakan zai taimaka mana mu kasance da gaba gaɗi da kuma ƙarfi. (Kubawar Shari’a 31:6) Allahnmu shi ne Mamallakin Duka, kuma zai taimaka mana mu riƙe amincinmu. Bari a kowane lokaci mu faranta wa Jehobah zuciya ta wajen kasancewa da aminci, domin ya iya mayar da magana ga babban mai zargi, Shaiɗan Iblis.—Misalai 27:11.

“Ka Cece Mu Daga Mugun”

11. Menene wannan roƙon ke nufi, “Kada ka kai mu cikin jaraba”?

11 Kasancewa mai aminci ba batu ba ne mai sauƙi, yana bukatar addu’a sosai. Kalaman da ke cikin addu’ar misali za su taimaka sosai. Kaɗan daga abin da Yesu ya ce shi ne: “Kada ka kai mu cikin jaraba, amma ka cece mu daga mugun.” (Matta 6:13) Jehobah ba ya jaraba mu da zunubi. (Yaƙub 1:13) A wasu lokatai Nassosi sukan ce ya yi ko kuwa ya jawo wasu abubuwa, amma, ya ƙyale hakan ya faru ne kawai. (Ruth 1:20, 21) Ta wajen yin addu’a kamar yadda Yesu ya nuna, muna roƙon Jehobah ne cewa kada ya ƙyale mu mu faɗa cikin jaraba. Kuma zai ji roƙonmu, domin muna da wannan tabbacin daga cikin Nassi: “Allah mai-aminci ne, da ba za ya bari a yi maku jaraba wadda ta fi ƙarfinku ba; amma tare da jaraba za ya yi maku hanyar tsira, da za ku iya jimrewa.”—1 Korinthiyawa 10:13.

12. Me ya sa muke yin addu’a: “Ka cece mu daga mugun”?

12 Bayan ya ambata jaraba a cikin addu’arsa na misali, Yesu ya sake cewa: “Ka cece mu daga mugun.” Wani fassara na Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka kāre mu daga mugun.” (Contemporary English Version) Amma, a cikin Nassosi, furcin nan “cece mu daga” na nufin wani, kuma Linjilar Matta ta kira Iblis “mai-jaraba.” (Matta 4:3, 11) Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi addu’a a cece mu daga “mugun,” Shaiɗan Iblis. Yana ƙoƙarin ya juya mu mu yi wa Allah zunubi. (1 Tassalunikawa 3:5) Sa’ad da muka yi wannan roƙo, “Ka cece mu daga mugun,” muna roƙon Ubanmu na samaniya ya kāre mu kuma ya taimaka mana domin kada Iblis ya ribace mu.

Kada Ka Yarda Iblis ya Ribace Ka

13, 14. Me ya sa Korantiyawa suke bukatar su daidaita yadda suka bi da wani mutum a cikin ikilisiya wanda malalaci ne?

13 Sa’ad da Bulus yake umurtar Kiristocin da ke Koranti su dinga yafe wa juna, ya rubuta: “Amma wanda ku ke gafarta masa komi, ni kuma haka: gama abin da na gafarta kuma, in dai na yi gafarar komi, sabili da ku na yi, a gaban Kristi; domin kada Shaiɗan ya ci ribar kome a bisanmu: gama ba mu cikin rashin sanin makiɗansa ba.” (2 Korantiyawa 2:10, 11) Iblis yana iya ribatarmu a hanyoyi dabam dabam, amma me ya sa Bulus ya yi kalaman nan da aka yi ƙaulinsu?

14 Bulus ya tsauta wa Korantiyawa domin sun ƙyale wani mutum malalaci ya ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya. Hakan ya faranta wa Shaiɗan rai, domin taƙaici ya faɗa a kan ikilisiyar don sun ƙyale “irin fasikanci ma da ba a iske shi ko wurin al’ummai.” Bayan haka, an yi wa mutumin yankan zumunci. (1 Korinthiyawa 5:1-5, 11-13) Daga baya mutumin ya tuba. Idan Korantiyawan suka ƙi su gafarta masa kuma su maido shi, Iblis zai ribace su a wata hanya. Ta yaya? Za su zama matsananta kuma marasa tausayi kamar Shaiɗan. Idan mutumin da ya tuba ya “dulmaya domin yawan baƙincikinsa” kuma ya daina bauta wa Allah gaba ɗaya, to, dattawa suna da hakkin wannan a gaban Jehobah Allah mai jinkai. (2 Korinthiyawa 2:7; Yaƙub 2:13; 3:1) Hakika, babu Kirista na gaskiya da zai so ya bi halin Shaiɗan ta wajen zama marar tausayi, da kuma matsananci.

Makaman Allah na Kāre Mu

15. Wane yaƙi ne muke yi, kuma samun nasararmu ya dangana ne a kan me?

15 Idan muna so mu tsira daga hannun Iblis, dole ne mu yi yaƙi na ruhaniya da miyagun ruhohi. Za mu sami nasara a wajen yaƙi da waɗannan miyagun ruhohi masu ƙarfi ne kawai idan muka yafa “dukan makamai na Allah.” (Afisawa 6:11-18) Wannan makamin ya haɗa da “sulke na adalci.” (Afisawa 6:14) Sarki Saul na Isra’ila ta dā ya yi rashin biyayya ga Allah kuma ya yi rashin ruhu mai tsarki. (1 Samuila 15:22, 23) Amma idan muka aikata adalci kuma muka kāre kanmu da makami na ruhaniya, za mu sami ruhu mai tsarki na Allah da kuma isashen kāriya don Shaiɗan da miyagun mala’ikunsa, aljanu.—Misalai 18:10.

16. Ta yaya za mu ci gaba da samun kāriya na tsayayya wa miyagun ruhohi?

16 Domin mu ci gaba da samun kāriya na tsayayya wa miyagun ruhohi, muna bukatar mu karanta kuma mu yi nazarin Kalmar Allah a kai a kai, kuma mu yi amfani da littattafai da “wakili mai-aminci” ke tanadinsu. (Luka 12:42) Da haka, za mu cika zuciyarmu da abubuwa na ruhaniya, kuma hakan ya jitu da shawarar Bulus: “ ’Yan’uwa, iyakar abin da ke mai-gaskiya, iyakar abin da ya isa bangirma, iyakar abin da ke mai-adalci, iyakar abin da ke mai-tsabta, iyakar abin da ke jawo ƙauna, iyakar abin da ke da kyakkyawan ambato; idan akwai kirki, idan akwai yabo, ku maida hankali ga waɗannan.”—Filibiyawa 4:8.

17. Menene zai taimaka mana mu zama ƙwararrun masu shelar bishara?

17 Jehobah ya sa mun ‘ɗaura wa sawayenmu shirin bishara ta salama.’ (Afisawa 6:15) Halartan taron Kirista a kai a kai na shirya mu mu sanar da bishara ta Mulkin Allah. Muna farin ciki sosai sa’ad da muka taimaka wa wasu su koyi gaskiya game da Allah kuma su sami ’yanci ta ruhaniya! (Yohanna 8:32) “Takobin ruhu, watau maganar Allah” yana da muhimmanci wajen watsar da koyarwan ƙarya da kuma “rushe wurare masu-ƙarfi.” (Afisawa 6:17; 2 Korinthiyawa 10:4, 5) Yin amfani da rubutacciyar Kalmar Allah Littafi Mai Tsarki da kyau, na taimaka mana mu koyar da gaskiya kuma yana kāre mu daga faɗawa cikin tarkon Iblis.

18. Ta yaya za mu “yi tsayayya da dabarun Shaiɗan”?

18 Bulus ya soma jawabinsa game da makaminmu na ruhaniya ne da: “Ku ƙarfafa cikin Ubangiji, cikin ƙarfin ikonsa kuma. Ku yafa dukan makamai na Allah, domin ku sami ikon da za ku yi tsayayya da dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:10, 11) Kalmar Helenanci da aka fassara “ku yi tsayayya” na nuni ne ga sojan da ke shirye. Muna tsaye da ƙarfi a wannan yaƙi na ruhaniya, duk da cewa Shaiɗan yana amfani da dabaru dabam dabam don ya lalata haɗin kanmu, ya gurɓatar da koyarwarmu, ko kuwa ya karya amincinmu ga Allah. Amma, har yanzu Iblis bai yi nasara ba a farmakinsa, kuma ba zai taɓa yi ba!a

Ka yi Tsayayya da Iblis, Kuma zai Guje Ka

19. Ta wace hanya ce za mu iya yin tsayayya da Iblis?

19 Za mu iya yin nasara a yaƙinmu na ruhaniya da Iblis da kuma miyagun ruhohin da suke ƙarƙashin ikonsa. Babu wani dalilin jin tsoron Shaiɗan, domin almajiri Yakubu ya rubuta: “Ku zama fa masu-biyayya ga Allah, amma ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje maku.” (Yaƙub 4:7) Hanya guda na ci gaba da yin tsayayya da Shaiɗan da kuma miyagun halittun ruhohi da ke tattare da shi, shi ne ta ƙin ƙungiya ta asiri, sihiri, da masu aikata su. Nassosi sun bayyana sarai cewa dole ne bayin Jehobah su ƙi ishara, ilimin taurari, duba, da sihiri. Idan muka kasance da ƙwazo da kuma ƙarfi a ruhaniya, ba za mu ji tsoron cewa wani zai yi mana asiri ba.—Lissafi 23:23; Kubawar Shari’a 18:10-12; Ishaya 47:12-15; Ayukan Manzanni 19:18-20.

20. Ta yaya za mu iya yin tsayayya da Iblis?

20 Muna “tsayayya da Shaiɗan” ta wajen manne wa mizanai da kuma gaskiyar Littafi Mai Tsarki, da kuma tsayawa da ƙarfi a gāba da shi. Duniya ta jitu da Shaiɗan domin shi ne allahnta. (2 Korinthiyawa 4:4) Saboda haka, mun ƙi halaye na duniya kamar su, fahariya, sonkai, lalata, mugunta, da son abin duniya. Mun sani cewa Iblis ya gudu sa’ad da Yesu ya ƙi harinsa na gwaji a cikin jeji ta wajen yin amfani da Nassosi. (Matta 4:4, 7, 10, 11) Hakazalika, Shaiɗan zai ‘guje mu’ idan muka yi biyayya sosai ga Jehobah kuma muka dogara a gare shi cikin addu’a. (Afisawa 6:18) Da taimakon Jehobah Allah da kuma ƙaunataccen Ɗansa, babu wanda zai iya yi mana lahani na har abada, ko Iblis ma bai isa ba!—Zabura 91:9-11.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da makamai na ruhaniya daga Allah, ka dubi Hasumiyar Tsaro, 15 ga Mayu, 1992, shafuffuka na 21-23 na Turanci.

Menene Amsarka?

• Ya kamata ne mu ji tsoron Shaiɗan Iblis?

• Me ya sa Shaiɗan ke sa a tsananta wa Kiristoci?

• Me ya sa muke addu’ar samun kāriya daga “mugun”?

• Ta yaya za mu yi nasara a yaƙinmu na ruhaniya?

[Hoto a shafi na 8]

Mabiyan Kristi masu gaba gaɗi a ƙarni na farko sun kasance da aminci har mutuwa

[Hoto a shafi na 9]

Iblis ba zai iya hana waɗanda Jehobah ya tuna da su tashi daga matattu ba

[Hoto a shafi na 10]

Kana addu’ar samun kāriya daga “mugun”?

[Hoto a shafi na 11]

Kana sanye da “dukan makamai na Allah”?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba