AMSOSHIN TAMBAYOYI DAGA LITTAFI MAI TSARKI
Wane ne ya halicci Iblis?
Allah bai halicci Iblis ba. Maimakon haka, Allah ya halicce mala’ika wanda daga baya ya zama Iblis ko kuma Shaiɗan. Yesu ya bayyana cewa a dā wannan mala’ika yana da gaskiya kuma marar aibi ne. Saboda haka, a farko, Iblis mala’ika ne mai adalci.—Ka karanta Yohanna 8:44.
Ta yaya wani mala’ika ya zama Iblis?
Mala’ikan da ya zama Iblis ya yi hakan ne sa’ad da ya yi tsayayya da Allah kuma ya yaudari Adamu da Hawwa’u su yi wa Allah tawaye. Ta hakan ne ya mai da kansa Shaiɗan, wato, “Mai Tsayayya.”—Ka karanta Farawa 3:1-5; Ru’ya ta Yohanna 12:9.
Wannan mala’ikan da ya zama Iblis yana da ’yanci ya zaɓi ko zai yi nagarta ko kuma mugunta, amma sai ya fara sha’awar bautar da ake yi wa Jehobah. Wannan sha’awar ta mamaye zuciyarsa kuma ya daina ƙaunar Jehobah.—Ka karanta Matta 4:8, 9; Yaƙub 1:13, 14.
Ta yaya Iblis ya ci gaba da rinjayar ’yan Adam? Ya kamata ka ji tsoron shi ne? Za ka sami amsoshin waɗannan tambayoyin a cikin Littafi Mai Tsarki.