Nawa Ne Yawan Lokaci Da Ya Rage Ma Miyagu?
“Don minene . . . [Jehovah] kana yin shuru sa’anda mugu ya kan haɗiye mutum wanda ya fi shi adilci?”—HABAKKUK 1:13.
1. Yaushe ne duniya za ta cika sosai da sanin darajar Jehovah?
ALLAH zai taɓa hallaka miyagu kuwa? Idan zai hallaka su, har yaushe za mu jira? Mutane a dukan duniya suna yin irin waɗannan tambayoyi. A ina ne za mu sami amsoshin? Za mu iya samun amsoshin a cikin kalmomin annabci na Allah da aka hure game da ayanannen lokaci na Allah. Sun tabbatar mana cewa Jehovah bada jimawa ba zai zartar da hukunci bisa dukan miyagu. Sa’annan ne duniya za ta “cika da sanin darajar Ubangiji, kamar yadda ruwaye sun rufe teku.” Wannan shine alkawari na annabci da ke cikin Tsarkaken Kalmar Allah a Habakkuk 2:14.
2. Littafin Habakkuk ya ƙunshi waɗanne zartar da hukunci guda uku ne na Allah?
2 Littafin Habakkuk da aka rubuta misalin shekara ta 628 K.Z., ya ƙunshi zartar da hukunci guda uku daga Jehovah Allah. An riga an tafiyar da biyu cikin hukuncin nan. Na farko shine hukuncin Jehovah bisa al’ummar Yahuda ta dā, mai tawaye. Na biyu kuma fa? Hukunci da Allah ya zartar ne akan Babila mai zalunci. Saboda haka, lallai muna da dalilin gabagaɗi cewa na ukun waɗannan hukunci daga wurin Allah zai auku. Hakika, za mu zaci cikarsa bada daɗewa ba. Domin albarkacin masu adalci na waɗannan kwanaki na ƙarshe, Allah zai hallaka dukan miyagun mutane. Na ƙarshe cikinsu zai mutu cikin “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka,” da ke zuwa da sauri sauri.—Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16.
3. Menene lallai zai faɗā ma miyagu a lokacinmu?
3 Yaƙin babbar rana na Allah yana matsowa kurkusa fiye da dā. Kuma zartar da hukuncin Allah bisa miyagu cikin lokacinmu tabbas ne kamar cikar hukuncin Jehovah bisa Yahuda da Babila. Amma, a yanzu haka, bari mu yi tsammanin cewa muna cikin Yahuda a lokacin Habakkuk, ko yaya? Mu ga menene ke faruwa cikin ƙasar?
Wata Ƙasa Cikin Hayaniya
4. Wane labari mai baƙanta rai ne Habakkuk ya ji?
4 Ka hangi annabin Jehovah yana zaune bisa deben jinkan gidansa, yana shan iska mai sanyi na maraice. Kusa da shi akwai garaya. (Habakkuk 1:1; 3:19, rubutu na samansa a NW ) Amma Habakkuk ya ji labari mai baƙanta rai. Sarkin Yahuda Jehoiakim ya kashe Urijah kuma ya jefa gawar annabin nan cikin makabartan matalauta. (Irmiya 26:23) Hakika, Urijah bai ci gaba da dogararsa ga Jehovah ba, ya tsorata kuma ya tsere zuwa Masar. Duk da haka, Habakkuk ya san cewa muguntar Jehoiakim ba don yana son ya gabatar da ɗaukaka ta Jehovah ba ne. An ga hakan daga rena dokar Allah ga sarkin da kuma ƙiyayyarsa ga annabi Irmiya da wasu da suke bauta ma Jehovah.
5. Menene yanayin abubuwa a ruhaniya a Yahuda, kuma yaya Habakkuk ya yi?
5 Habakkuk ya ga hayaƙin turare na tasowa daga jinkan gidaje na kusa. Mutanen suna ƙone turaren wuta ba na bautar Jehovah ba. Sun shagala cikin ayyukan addinan ƙarya wanda mugun Sarki Jehoiakim na Yahuda ya gabatar. Sun yi abin kunya! Idanun Habakkuk sun cika da hawaye, sai ya yi roƙo: “Ya Ubangiji, har yaushe zan yi kira, kai kuwa ba ka yarda ka ji ba? Ina tada murya gareka saboda zafin mugunta, kai kuwa ka ƙi yin ceto. Don me ka ke nuna mani saɓo, ka sa ni duba shiririta kuma? gama ɓarna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso. Domin wannan shari’a ta yi sanyi, hukunci kuma ba shi aikawa; gama miyagu sun kewaye masu-adilci; domin wannan hukunci ya kan fita a karkace.”—Habakkuk 1:2-4.
6. Menene ya faru da doka da hukunci a cikin Yahuda?
6 I, ɓarna da mugunta sun yalwata. Duk inda Habakkuk ya juya, yana ganin damuwa, husuma, da jayayya. “Shari’a ta yi sanyi,” ba ta da ƙarfi. Yin gaskiya kuma fa? Lallai, ba “shi aikawa” da nasara! Bai taɓa cin gari ba. Maimako, “miyagu sun kewaye masu-adilci,” sun birkita doka da aka shirya don kāre mara laifi. Lallai kuwa, “hukunci ya kan fita a karkace.” An ɓata shi. Hakika, yanayin abubuwa sun lalace!
7. Menene Habakkuk ya ƙuduri aniya ya yi?
7 Habakkuk ya ɗan dakata, ya yi tunani game da yanayin. Zai fid da zuciya ne? A’a! Bayan ya sake bincika dukan tsananta ma amintattun bayin Allah da aka yi, wannan mutum mai aminci ya ƙara ƙarfafa ƙudurinsa ya tsaya da ƙarfi sosai, a yadda yake annabin Jehovah. Habakkuk zai ci gaba da yin shelar saƙon Allah—ko idan yin haka yana nufi mutuwa ma.
Jehovah Yana Tafiyar da “Aiki” Mai Wuyan Gaskatawa
8, 9. Wane “aiki” mai wuyan gaskatawa ne Jehovah yake tafiyar da shi?
8 Cikin wahayi, Habakkuk ya gan ’yan addinan ƙarya, waɗanda ba su daraja Allah ba. Ka saurari abin da Jehovah ya gaya masu: “Ku duba, ku da ke cikin al’ummai, ku lura, ku yi mamaki ƙwarai da gaske.” Mai-yiwuwa, Habakkuk ya yi mamakin abin da ya sa Allah yake magana da miyagun mutanen nan a wannan hanyar. Sai ya ji Jehovah ya gaya masu: “Ku yi mamaki ƙwarai da gaske; gama ina aika wani aiki a cikin kwanakinku, wanda ba za ku gaskata ba ko da na faɗa maku.” (Habakkuk 1:5) Hakika, Jehovah ne kansa ke tafiyar da wannan aiki wanda ba za su gaskata ba. Amma menene wannan aikin?
9 Habakkuk ya saurara sosai ga kalmomin Allah na gaba, da ke rubuce a Habakkuk 1:6-11. Wannan saƙon Jehovah ne—kuma babu allah na ƙarya ko gunki mara rai da zai iya hana shi cikawa: “Gama, ga shi, ina tada Chaldiyawa, wannan al’umma mai-zafin rai, mai-garaje; waɗanda suna tafiya suna ratsa ratar duniya, domin su gāji mazaunan da ba nasu ba ne. Masu-ban razana ne, da ban tsoro; shari’arsu da darajassu daga kansu su ke fitowa. Dawakansu sun fi damisa zafin tafiya, sun fi kerketan dare zafin rai; mahayansu su kan yi taƙama; i, mahayansu daga nesa su ke fitowa; su kan tashi kamar gaggafa mai-garajen cinyewa. Su dukansu su kan zo da nufin ƙwace; fuskokinsu suna kafe zuwa gaɓas da anniya; su kan tattara bayi kamar yashi. I, su kan yi ma sarakuna ba’a, ’yan sarakuna kuma abin reni ne a garesu; a garesu kowace kagara abin reni ne; gama ya kan tula turɓaya ya ci wurin. Sa’annan kamar iska za ya huce, za ya shuɗe kuma, ya zama mai-laifi; shi wanda ikonsa allahnsa ne.”
10. Wanene Jehovah zai tada?
10 Dubi irin gargaɗi na annabcin nan daga Maɗaukaki Duka! Jehovah zai tada Chaldiyawa, al’ummar Babila mara-hankali. Akan tafiyarta cikin ‘ratar duniya’ fa, za ta yi nasara bisa mazauna da yawa, da yawa kuwa. Lallai kuwa da ban tsoro yake! Yawan Chaldiyawan abin “ban razana ne, da ban tsoro,” mugu ne ƙwarai, mara-kyau. Sun kafa nasu doka mai-ƙarfi. ‘Shari’arsu daga kansu suke fitowa.’
11. Yaya za ka kwatanta zuwan sojojin Babila akan Yahuda?
11 Dawakan Babila sun fi damisa saurin tafiya. Mahayansu sun fi kerketan dare zafin rai. Cikin saurin tafiya, ‘ƙafafunsa suna shiga cikin ƙasa’ don rashin haƙuri. Daga Babila da ke da nisa sun nufi Yahuda. Suna tashi kamar gaggafa da ya ga abinci mai armashi, bada daɗewa ba Chaldiyawa za su fāɗa ma magabtansu. Wannan farmaki ne kawai, na kai hari da sojoji kalilan? A’a ha! “Dukansu su kan zo da nufin ƙwace,” kamar babban taron jama’a da ke hallakar da wuri. Fuskokinsu sai farinciki suke yi, suna tafiya ta yammancin Yahuda da Urushalima, suna tafiya da sauri kamar iskar gabas. Sojojin Babila sun ‘tattara bayi kamar yashi’ fursunoni da yawa da suka kama.
12. Wane hali Babiloniyawa su ke da shi, kuma game da menene babban magabcin zai “zama da laifi”?
12 Rundunar sojojin Chaldiyawa suna yi wa sarakuna ba’a kuma suna rena ’ya’yan sarakuna, waɗanda dukansu kuwa ba su da ƙarfi su dakatar da wulaƙancin nan. Sun ‘rena kowace kagara,’ gama an ci kowace mafaka lokacin da mutanen Babila suka ‘tara turɓaya,’ ta wurin gina babban garun ƙasa daga inda za su iya faɗā ma ta. A ayanannen lokaci na Jehovah, babban magabci “kamar iska za ya huce.” A faɗā ma Yahuda da Urushalima, za ta “zama da laifi,” a yi ma mutanen Allah rauni. Bayan babbar nasara, ƙila babban soja na Chaldiyawa ya yi fahariya cewa: ‘Ikon nan don allahnmu ne.’ Amma bai san kome ba!
Tushe Mai Kyau na Bege
13. Me ya sa Habakkuk yake da cikakkiyar bege da gabagaɗi?
13 Tare da ƙarin fahimtar nufin Jehovah, bege yana ƙaruwa cikin zuciyar Habakkuk. Tare da cikakkiyar gabagaɗi, ya yi magana cikin ɗaukaka ga Jehovah. Kamar yadda muka lura a Habakkuk 1:12, (NW ), annabin ya ce: “Ba tun fil’azal ka ke ba, ya Ubangiji Allahna, Mai-tsarkina? Ba za ka mutu ba.” Hakika, Jehovah shine Allah “tun fil’azal”—har abada.—Zabura 90:1, 2.
14. Wane tafarki ne ’yan ridda na Yahuda suka bi?
14 Da yake tunani game da wahayin da Allah ya ba shi da kuma farincikin fahimta da wannan ya tanadar, annabin ya ci gaba da cewa: “Ya Ubangiji, ka ƙadara shi ga hukunci; kai kuwa, ya Dutse, ka tsayasda shi domin horo.” Allah ya hukunta ’yan ridda na Yahuda sosai, kuma za su samu horo sosai, daga wurin Jehovah. Ya kamata su dogara gareshi kamar Dutsensu, ƙarfafa na gaske, mafaka, da kuma Tushen ceto. (Zabura 62:7; 94:22; 95:1) Duk da haka, shugabanne ’yan ridda na Yahuda ba su matso kusa da Allah ba, kuma sun ci gaba da cin zalin masu sujadar Jehovah marasa ɓarna.
15. A wane azanci ne Jehovah yake da ‘tsarki a idanu sosai da zai ga mugunta’?
15 Wannan yanayin ya ɓata ma annabin Jehovah rai sosai. Saboda haka ya ce: “Kai wanda tsarkin idonka ya fi gaban duban mugunta, ba ka iya kallon shiririta ba.” (Habakkuk 1:13) I, Jehovah yana da ‘tsarkin idanu sosai da zai ga mugunta,’ watau, ya ƙyale yin mugunta.
16. Ta yaya za ka taƙaita abin da aka rubuta a Habakkuk 1:13-17?
16 Saboda haka Habakkuk yana da wasu tambayoyi masu-taɓa zuciya. Ya yi tambaya: “Don menene ka ke zuba ido a kan masu-cin amana, kana yin shuru sa’anda mugu ya kan haɗiye mutum wanda ya fi shi adilci; kana kuwa maida mutane kamar kifayen teku, kamar masu-rarrafe waɗanda ba su da mai-mulkinsu? Ya kan same su duk da ƙugiya, ya kama su cikin ƙallinsa, ya tattara su cikin tarunsa; domin wannan ya kan yi murna da farinciki. Domin wannan ya kan yi ma ƙallinsa hadaya; ya, ƙona turare ga tarunsa; domin ta wurinsu rabonsa mai-romo ne, abincinsa kuma da yalwa. Za ya fa zazzage ƙallinsa, ba za ya dena hallakan al’ummai kullayaumi ba?”—Habakkuk 1:13-17.
17. (a) A kai ma Yahuda da Urushalima farmaki, ta yaya mutanen Babila suka aikata nufin Allah? (b) Menene Jehovah zai bayana ma Habakkuk?
17 Ta wurin farmaki da mutanen Babila suka kai wa Yahuda da babban birninta, Urushalima, sun aikata daidai da nasu buri. Ba za su sani cewa suna yin aiki a hanyar da Allah zai zartar da hukuncinsa na adilci bisa mutane marasa-aminci ba ne. Yana da sauƙi a ga abin da ya sa Habakkuk ya iske shi da wuya ya fahimci cewa Allah zai yi amfani da miyagun mutane na Babila don ya zartar da Hukuncinsa. Waɗancan Chaldiyawa marasa-juyayi ba masu sujada ga Jehovah ba ne. Suna ganin mutane kamar ‘kifaye da abubuwa masu-rarrafe’ da za a kama a mallake su. Amma ruɗewa da Habakkuk ya yi akan wannan al’amarin ba zai daɗe ba. Bada daɗewa ba Jehovah zai bayyana ma annabinsa cewa mutanen Babila za su sha horo don haɗamarsu na lalaci da kuma yawan zub da jini da suka yi.—Habakkuk 2:8.
A Shirye don Kalmomin Jehovah na Gaba
18. Menene za mu iya koya daga halin Habakkuk, yadda aka nuna a Habakkuk 2:1?
18 Amma kuma, a yanzu haka, Habakkuk yana jira ya ji kalmomin Jehovah na gaba gareshi. Annabin ya ƙuduri aniyar cewa: “Zan tsaya wurin tsarona, in tsaya a bisa hasumiya, in duba, in ga abin da za ya faɗa mani, da abin da zan amsa masa a kan ƙarata.” (Habakkuk 2:1) Tun da yake Habakkuk annabi ne, yana marmari sosai ya san abin da Allah zai faɗa ta wurinsa. Bangaskiyarsa cewa Jehovah wanda Allah ne da ba ya ƙyale mugunta, ya sa shi ya damu game da dalilin da ya sa mugunta ke cin gaba, amma a shirye yake ya gyara tunaninsa. To, mu kuma fa? Yayin da muka damu game da dalilin da ya sa wasu miyagun abubuwa ke faruwa, ya kamata gabagaɗinmu cikin adilci na Jehovah Allah ya taimake mu mu daidaita tsayawarmu kuma mu jira shi.—Zabura 42:5, 11.
19. Menene ya faru ma Yahudawa masu tawaye da ya nuna gaskiyar kalmar Allah ga Habakkuk?
19 Daidai bisa ga abin da ya faɗa ma Habakkuk fa, Allah ya zartar da hukunci bisa al’ummar Yahudawa masu-tawaye ta wurin ƙyale Babiloniyawa su ci Yahuda. Cikin shekara ta 607 K.Z., sun hallaka Urushalima da kuma haikalin, sun kashe tsofaffi da yara duka, kuma sun kama mutane da yawa zuwa bauta. (2 Labarbaru 36:17-20) Bayan hijira ta doguwar lokaci a Babila, ringin Yahudawa masu-aminci sun komo ƙasar haihuwarsu kuma daga baya suka sake gina haikalin. Amma kuma, bayan haka, Yahudawan sun sake yin rashin aminci ga Jehovah—musamman ma lokacin da suka ƙi Yesu akan shine Almasihu.
20. Yaya Bulus ya yi amfani da Habakkuk 1:5 game da ƙin Yesu da aka yi?
20 Bisa ga Ayukan Manzanni 13:38-41, manzo Bulus ya nuna ma Yahudawa a Antakiya abin da ƙin Yesu zai nufa, yana nufin yin banza da fansar hadayarsa. Da yake faɗin abin da ke Habakkuk 1:5 daga juyin Septuagint na Hellenanci, Bulus ya yi gargaɗi haka: “Ku maida hankali fa, kada wannan shi auko maku da aka faɗi a cikin annabawa; Ku duba, ku masu-renako, ku yi mamaki, ku lalace; gama ina aika wani aiki a cikin kwanakinku, aikin da ba za ku gaskata ba daɗai, ko da wani ya faɗa maku shi.” Cikin jituwa da abin da Bulus ya faɗa fa, cika ta biyu na Habakkuk 1:5 ya auku lokacin da sojojin Roma suka hallaka Urushalima da haikalinta a shekara ta 70 A.Z.
21. Yaya Yahudawa na kwanakin Habakkuk suka ɗauka “aiki” da Allah ya sa Babiloniyawa su hallaka Urushalima?
21 Ga Yahudawa na kwanakin Habakkuk, “aiki” da Allah ya sa Babiloniyawa su hallaka Urushalima ba daidai ba ne domin birnin ne cibiyar sujada ta Jehovah da kuma wurin da aka shafa sarkinsa da ya naɗa. (Zabura 132:11-18) Domin haka, ba a taɓa hallaka Urushalima ba. Ba a taɓa ƙone haikalinta ba. Ba a taɓa ƙwace sarauta na gidan Dawuda ba. Da wuya a gaskata cewa Jehovah zai ƙyale abubuwa irin haka su faru. Amma ta wurin Habakkuk, Allah ya bada isashen gargaɗi cewa waɗannan aukuwa masu ban mamaki za su faru. Kuma tarihi ya nuna cewa sun auku kamar yadda aka annabta.
“Aiki” na Allah Mai Wuyan Gaskatawa Cikin Kwanakinmu
22. Menene “aiki” na Jehovah mai wuyan gaskatawa a kwanakinmu ya ƙunsa?
22 Jehovah zai yi wani “aiki” mai wuyan gaskatawa cikin kwanakinmu? Ka tabbata cewa zai yi, ko da shike waɗanda suke yin shakka suna gani kamar wannan ba zai yiwu ba. A wannan lokaci, aiki mai wuyan gaskatawa na Jehovah shine hallaka Kiristendom. Kamar Yahuda ta dā, tana da’awar bauta ma Allah amma kuma tana da ɓatanci sosai. Jehovah zai tabbata cewa an share duk wani alamar tsarin addinan Kiristendom, kamar yadda za a yi da dukan “Babila Babba,” daular duniya ta addinin ƙarya.—Ru’ya ta Yohanna 18:1-24.
23. Menene ruhun Allah ya motsa Habakkuk ya yi ?
23 Jehovah yana da ƙarin aiki da Habakkuk ya yi kafin ya hallaka Urushalima a 607 K.Z. Menene Allah zai gaya ma annabinsa kuma? I, Habakkuk zai ji abubuwan da za su motsa shi ya ɗauki garayarsa ya rera waƙar baƙinciki ga Jehovah cikin addu’a. Amma dai, da farko, ruhun Allah zai motsa annabin ya yi shelar bala’in da zai auku. Babu shakka za mu ji daɗin samun sanin zurfafan ma’anar irin kalmomin annabcin nan don ayanannen lokaci na Allah. Saboda haka bari mu ƙara mai da hankali ga annabcin Habakkuk.
Ka Tuna?
• Wane yanayi ne ya wanzu a Yahuda cikin kwanakin Habakkuk?
• Jehovah ya tafiyar da wane “aiki” mai wuyan gaskatawa ne cikin kwanakin Habakkuk?
• Wane dalilin bege ne Habakkuk yake da shi?
• Wane “aiki” mai wuyan gaskatawa ne Allah zai tafiyar da shi a kwanakinmu?
[Hoto a shafi na 15]
Habakkuk ya damu da abin da ya sa Allah ya ƙyale mugunta ta kasance. Kai ma haka ne?
[Hoto a shafi na 16]
Habakkuk ya annabta bala’i ga ƙasar Yahuda a hannun Babiloniyawa
[Hoto a shafi na 16]
Kangayen tone-tonan ’yan tonan ƙasa na Urushalima, wanda aka hallaka a 607 K.Z.