Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 4/1 pp. 19-24
  • Ka Saurara Ga Kalmomin Annabci Na Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Saurara Ga Kalmomin Annabci Na Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sāke Kamani Ya Gina Bangaskiya
  • Yadda Tauraro na Assubahi Ya Fito
  • “Haske Ya Shigo Cikin Duniya”
  • Annabcin Mulkin Allah Ya Tabbata
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Darussa Daga Wasiƙun Yaƙub da Bitrus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 4/1 pp. 19-24

Ka Saurara Ga Kalmomin Annabci Na Allah

“Muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatasda ita; wadda ya yi maku kyau ku lura da ita.”—2 BITRUS 1:19.

1, 2. Waɗanne misalai na almasihan ƙarya za ka iya bayarwa?

CIKIN ƙarnuka, almasihan ƙarya sun yi ƙoƙarin annabta abin da zai faru a nan gaba. A ƙarni na biyar A.Z., wani mutum da ya kira kansa Musa ya huɗubantar da Yahudawa a tsibirin Karita cewa shi ne almasihu kuma zai cece su daga zalunci. A ranar da aka ajiye na ’yanci, sun bi shi kan tudu suna kallon Bahar Maliya. Ya ce abin da ya rage kawai, sai su faɗa cikin teku, zai rabu. Mutane da yawa da suka faɗa sun sha ruwa sun mutu, sai almasihun ƙarya ya ɓace da gani.

2 A ƙarni na 12, wani “almasihu” ya taso a Yamal. Halifa, ko kuma sarki, ya ce ya nuna alamar cewa shi almasihu ne. Wannan “almasihun” ya ce halifan ya sa a yanke masa kai. Ya annabta cewa tashinsa zuwa rai nan da nan zai zama alama. Halifan ya yarda da hakan—kuma wannan ne ya zama ƙarshen “almasihun.”

3. Wanene Almasihu na gaskiya, kuma menene hidimarsa ta tabbatar?

3 Almasihan ƙarya da annabce-annabcensu ba su kai labari ba, amma sauraron kalmomin annabci na Allah ba zai kai ga yin nadama ba. Almasihu na gaske Yesu Kristi, shi ya cika annabce-annabce da yawa na Littafi Mai-Tsarki. Alal misali, marubucin Lingila, Matta, da ya ɗauko daga annabcin Ishaya ya rubuta: “Ƙasar Zabuluna da ƙasar Naftalima, hanyar teku, ƙetaren Urdun, Galili na Al’ummai, mutane waɗanda su ke zaune cikin dufu suka ga haske mai-girma, mazauna cikin wurin mutuwa da inuwatta, a garesu haske ya ɓullo. Daga lokacin nan Yesu ya soma wa’azi, ya ce, Ku tuba; gama mulkin sama ya kusa.” (Matta 4:15-17; Ishaya 9:1, 2) Yesu shi ne “haske mai-girma” ɗin, kuma hidimarsa ta tabbatar da cewa shi ne Annabin da Musa ya annabta. Za a halaka waɗanda suka ƙi su saurari Yesu.—Kubawar Shari’a 18:18, 19; Ayukan Manzanni 3:22, 23.

4. Ta yaya Yesu ya cika Ishaya 53:12?

4 Yesu har wa yau, ya cika kalmomin annabci na Ishaya 53:12: “Ya tsiyaye ransa har ga mutuwa, aka lissafta shi wurin masu-laifi: duk da haka ya ɗauki zunubi na mutane dayawa, ya kuma yi roƙo sabili da masu-laifi.” Da sanin cewa ba da jimawa ba zai ba da ransa na bil’Adam don fansa, Yesu ya ƙarfafa bangaskiyar almajiransa. (Markus 10:45) Ya yi wannan a hanya ta musamman, ta sāke kamani.

Sāke Kamani Ya Gina Bangaskiya

5. Da naka kalmomi, yaya za ka kwatanta sāke kamanin?

5 Sāke kamani wani aukuwa ne na annabci. Yesu ya ce: “Ɗan mutum za ya zo cikin darajar Ubansa tare da mala’ikunsa . . . Hakika ina ce maku, Akwai waɗansu a cikin na tsaye a wurin nan, da ba za su ɗanɗana mutuwa ba daɗai, har sun ga Ɗan mutum yana zuwa cikin mulkinsa.” (Matta 16:27, 28) Wasu manzanni sun ga Yesu yana zuwa cikin Mulkinsa kuwa da gaske? Matta sura ta 17:1-7 ya ce: “Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yaƙub, da Yohanna ɗan’uwansa, ya kai su bisa cikin wani dutse mai-tsawo a kaɗaice: kamassa ta sāke a gabansu.” Lallai abu ne na ban mamaki! “Fuskatasa tana ta haskakawa kamar rana, tufafinsa kuma suka zama farare kamar haske. Sai ga Musa da Iliya suka bayana garesu, suna zance da shi.” Kuma, “girgije mai-haske ya inuwantadda su,” sai suka ji muryar Allah tana cewa: “Wannan Ɗana ne ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai; ku ji shi. Sa’anda almajiran suka ji, suka fāɗi bisa fuskassu, suna jin tsoro ƙwarai. Yesu kuwa ya zo, ya taɓa su, ya ce, Ku tashi, kada ku ji tsoro.”

6. (a) Me ya sa Yesu ya kira sāke kamanin, wahayi? (b) Menene sāke kamanin ya nuna?

6 Wannan aukuwa na ban mamaki ƙila ya auku ne a kan Dutsen Hermon, inda Yesu da manzanninsa uku suka kwana. Babu shakka, sāke kamanin ya auku ne da daddare, shi ya sa ya fita sarai. Dalili ɗaya da ya sa Yesu ya kira shi wahayi shi ne, domin Musa da Iliya da suka mutu da daɗewa ba sa wurin a zahiri. Kristi ne kawai yake wurin da gaske. (Matta 17:8, 9) Irin wannan aukuwa da ya bayyana sarai ya nuna wa Bitrus, Yaƙub, da kuma Yohanna alama ta gaba na bayanuwar Yesu cikin darajar ikon Mulki. Musa da Iliya suna nuna daidai hoton shafaffun magāda tare da Yesu, kuma wahayin cikin iko ya ƙarfafa shaidarsa game da Mulki da sarautarsa ta gaba.

7. Ta yaya muka san cewa Bitrus ya tuna da sāke kamanin nan sarai?

7 Sāke kamanin ya taimaka wajen ƙarfafa bangaskiyar manzanni ukun waɗanda za su yi aikin ja-gora a cikin ikklisiyar Kirista. Walƙiyar fuskar Kristi, tufafinsa farare fat, da kuma muryar Allah kansa da ke cewa Yesu Ɗansa, ƙaunatacce ne da ya kamata su saurare shi—dukan waɗannan sun cika aikinsu da kyau. Amma manzannin ba za su faɗa wa kowa wahayin nan ba, sai Yesu ya tashi daga matattu. Shekara 32 daga baya, wannan wahayi na sāke kamani ya kasance sarai cikin zuciyar Bitrus. Da yake magana game da shi da kuma muhimmancinsa, ya rubuta: “Gama mu, lokacinda muka sanashe ku ikon Ubangijinmu Yesu Kristi da zuwansa, ba tatsuniyoyi sāmammu daga wayon mutane muka bi ba, amma shaidun ido mu ke na ɗaukakarsa. Gama ya karɓi girma da ɗaukaka daga wurin Allah Uba, sa’anda aka kawo masa daga cikin mafificiyar ɗaukaka wannan irin murya, Wannan ƙaunatacen Ɗana ne, wanda ni ke jin daɗinsa sarai: wannan murya kuwa mu da kanmu muka ji daga sama ta kawo, sa’anda muna tare da shi cikin dutse mai-tsarki.”—2 Bitrus 1:16-18.

8. (a) Sanarwar Allah game da Ɗansa ya mai da hankali bisa menene? (b) Menene girgije da ya bayyana a sāke kamanin yake nufi?

8 Mafi muhimmanci ita ce sanarwa da Allah ya yi: “Wannan ƙaunatacen Ɗana ne, wanda ni ke jin daɗinsa sarai; ku ji shi.” Wannan sanarwar tana jawo hankali ga cewa Yesu, Sarki ne da Allah ya naɗa, wanda tilas ne dukan halitta su yi biyayya sosai gareshi. Girgije da ya rufa manzanni uku waɗanda suke wurin ya nuna cewa cikar wannan wahayi mara ganuwa ne. Waɗanda suke da fahimi a “alamar” bayanuwa mara ganuwa na Yesu cikin ikon Mulki ne kawai za su gane. (Matta 24:3) Hakika, yadda Yesu ya gargaɗe su kada su gaya wa kowa wahayin nan har sai ya tashi daga matattu ya nuna cewa ɗaukakarsa da kuma daraja za su zo ne bayan tashinsa daga matattu.

9. Me ya sa ya kamata sāke kamanin ya ƙarfafa bangaskiyarmu?

9 Bayan ya yi magana game da sāke kamanin, Bitrus ya ce: “Muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatasda ita; wadda ya yi maku kyau ku lura da ita, kamar da fitila mai-haskakawa cikin wuri mai-dufu, har gari ya waye, tauraro na assubahi kuma ya fito cikin zukatanku: kuna fa sanin wannan dafari, babu annabci na Littattafai wanda fasarassa ke daga hankalin kan kowa. Gama ba a taɓa kawo kowane annabci bisa ga nufin mutum ba: amma mutane suka yi magana daga wurin Allah, Ruhu Mai-tsarki ne yana motsa su.” (2 Bitrus 1:19-21) Sāke kamanin ya nanata tabbacin kalmomin annabci na Allah. Tilas ne mu saurara ga kalmomin ba “tatsuniyoyi sāmammu,” waɗanda ba su da goyon baya daga wurin Allah ba. Bangaskiyarmu ga kalmomin annabci ya kamata ya ƙarfafa ta sāke kamanin domin wannan wahayi da ya nuna Yesu a darajarsa ta Mulki da kuma iko ya zama gaskiya. I, muna da tabbaci da ba za a iya ƙaryatawa ba, cewa Kristi yana nan a yau Sarki ne mai iko a sama.

Yadda Tauraro na Assubahi Ya Fito

10. Wanene ko kuma menene “tauraro na assubahi” da Bitrus ya ambata, kuma me ya sa ka faɗi haka?

10 Bitrus ya rubuta: “Ya yi maku kyau ku lura da [kalmomin annabci], kamar da fitila mai-haskakawa cikin wuri mai-dufu, har gari ya waye, “tauraro na assubahi kuma ya fito.” Wanene ko kuma menene “tauraro na assubahi” ɗin nan? Furcin nan “tauraro na assubahi” ya bayyana sau uku ne kawai cikin Littafi Mai-Tsarki, kuma yana da ma’ana da ke kama da ta “tauraro na rana,” bisa ga (NW ). Ru’ya ta Yohanna 22:16 ya kira Yesu Kristi “tauraro na assubahi, mai-haske.” A wasu lokutta cikin shekara, irin waɗannan taurari suna fitowa a ƙarshe a gabashin duniya. Suna fitowa ne kafin rana ta fito, da haka, suna shelar wayewar gari. Bitrus ya yi amfani da kalmar nan “tauraro na Assubahi” ya nuna Yesu bayan Ya karɓi ikon Mulki. A wannan lokacin, Yesu ya fito a sararin samaniya, har da duniyarmu ma! Kamar Almasihu Tauraro na Assubahi, ya yi shelar wayewar gari, ko kuma sabuwar zamani, ga mutane masu biyayya.

11. (a) Me ya sa 2 Bitrus 1:19 ba ya nufin cewa “tauraro na assubahi” ya fito daga ainihin zuciyar mutum? (b) Ta yaya za ka yi bayani game da 2 Bitrus 1:19?

11 Masu fassarar Littafi Mai-Tsarki da yawa suna gabatar da ra’ayin cewa kalmomin Bitrus da ya rubuta a 2 Bitrus 1:19 yana nufin zuciyar mutum ta zahiri ne. Nauyin zuciyar babban mutum ozoji 9 zuwa 11 ne kawai. Ta yaya ne Yesu Kristi—wanda yanzu halitta ne na ruhu mara mutuwa a sama—zai fito cikin wannan ƙaramin ɓārin mutum? (1 Timothawus 6:16) Hakika, wannan ya shafi zukatanmu ne ta alama, domin da su, muke mai da hankali ga kalmomin annabci na Allah. Amma ka duba 2 Bitrus 1:19 da hankali, za ka gani cewa New World Translation ya yi amfani da waƙafi bayan furcin nan “har gari ya waye, tauraro na Assubahi ya fito,” ya ware su daga kalmomin fari na ayar da kuma furcin nan “cikin zukatanku.” Wannan ayar za a iya furta ta haka: ‘Muna kuwa da maganar annabci wadda an fi tabbatasda ita; wadda ya yi maku kyau ku lura da ita, kamar fitila mai-haskakawa cikin wuri mai-duhu, watau, cikin zukatanku, har gari ya waye, tauraro na rana kuma ya fito.’

12. Yaya zukatan dukan mutane yake, amma menene gaskiya game da Kiristoci na ƙwarai?

12 Yaya zukata ta alama na mutane masu zunubi yake gabaɗaya? Hakika, zukatansu yana cikin duhu na ruhaniya! Amma dai, idan Kiristoci na gaske ne mu, yana kamar muna da fitila da take haskakawa cikin zukatanmu, wanda idan ba haka ba, da ta yi duhu. Kamar yadda kalmomin Bitrus suka nuna, sai ta wurin saurarawa ga kalmomin haskakawa na annabcin Allah Kiristoci na ƙwarai za su zauna babu barci kuma a haskaka ga wayewar sabuwar rana. Za su san cewa Tauraro na Assubahi ya fito, ba a cikin zukatan zahiri na mutane ba, amma a gaban dukan halitta.

13. (a) Me ya sa za mu tabbata cewa Tauraron Assubahi ya riga ya fito? (b) Me ya sa Kiristoci za su jimre wa yanayi masu wuya da Yesu ya annabta don kwanakinmu?

13 Tauraron Assubahi ya riga ya fito! Za mu tabbata da wannan ta wurin saurarawa ga annabci mai girma na Yesu game da bayyanarsa. A yau, muna ganin cikan waɗannan a aukuwa kamar su yaƙe-yaƙe da babu irinsu, yunwa, girgizan ƙasa, da kuma wa’azin bishara a dukan duniya. (Matta 24:3-14) Ko da yake yanayi masu wuya da Yesu ya annabta suna shafan mu Kiristoci ma, mu jimre cikin salama da kuma farin zuciya. Me ya sa? Domin muna sauraran kalmomin annabci na Allah kuma muna da bangaskiya ga abubuwan da ya yi alkawarinsu na nan gaba. Mun san cewa muna kusa da lokaci mafi kyau domin mun yi nisa sosai cikin “kwanakin ƙarshe”! (Daniel 12:4) Duniya tana cikin yanayi mai tsanani da aka annabta a Ishaya 60:2: “Duba, duhu za ya rufe duniya, baƙin duhu kuma za ya rufe al’ummai.” Ta yaya wani zai iya samun hanyar fita daga cikin wannan duhu? Dole ne mutum ya saurara ga kalmomin annabci na Allah yanzu kafin ya makara. Ya kamata mutane masu zuciyar kirki su juya zuwa wurin Jehovah Allah, Tushen rai da haske. (Zabura 36:9; Ayukan Manzanni 17:28) Ta wurin yin wannan ne kaɗai mutum zai sami wayewa ta gaske da kuma bege na more abin mamaki da Allah ya nufa ya yi wa mutane masu biyayya a nan gaba.—Ru’ya ta Yohanna 21:1-5.

“Haske Ya Shigo Cikin Duniya”

14. Dole ne mu yi menene domin mu ga cikan annabce-annabce masu ban mamaki na Littafi Mai-Tsarki?

14 Nassosi sun nuna sarai cewa Yesu Kristi yana Sarauta yanzu. Domin ya hau mulki a 1914, dukan sauran annabce-annabce na ban mamaki za su cika. Don mu ga cikansu, muna bukatar tabbatar da kanmu cewa mu masu tawali’u ne waɗanda suke nuna bangaskiya ga Yesu Kristi, muna tuba daga ayyuka na zunubi da kuma laifofi da muka yi cikin rashin sani. Hakika, waɗanda suke ƙaunar duhu ba za su sami rai na har abada ba. Yesu ya ce: “Shari’a fa ke nan, haske ya zo cikin duniya, amma mutane suka fi son duhu da haske; domin ayukansu miyagu ne. Gama kowanene wanda ya ke aika mugunta ƙin haske ya ke yi, kuma ba shi zuwa wurin haske, domin kada ayukansa su tonu. Amma wanda ya ke aikin gaskiya yana zuwa wurin haske, domin a bayyana ayukansa, a cikin Allah an yi su.”—Yohanna 3:19-21.

15. Me zai faru idan muka yi banza da ceto da Allah ya shirya ta wurin Ɗansa?

15 Hasken ruhaniya ya shigo duniya ta wurin Yesu, kuma sauraronsa yana da muhimmanci. Bulus ya rubuta: “Allah, da ya yi ma ubanni magana a zamanin dā ta wurin annabawa da rabo dabam dabam, da hanya dabam dabam kuma, a ƙarshen waɗannan kwanaki ya yi mana magana cikin Ɗansa, wanda ya sanya magajin abu duka.” (Ibraniyawa 1:1, 2) Menene zai faru idan mun yi banza da wannan ceton da Allah ya shirya ta wurin Ɗansa? Bulus ya ci gaba da cewa: “Gama idan magana wadda aka faɗi ta bakin mala’iku ta tsaya tabbataciya, dukan takar shari’a da ƙin ji magana kuma suka sha sakamako mai-dacewa; ƙaƙa za mu tsira mu, idan mun ƙyale ceto mai-girma haka? wanda aka fara faɗinsa ta wurin Ubangiji, kāna aka ƙarfafa shaidassa a garemu ta bakin waɗanda suka ji; Allah kuma yana ba da shaida tare da su, ta wurin alamu da al’ajibai, da ikoki iri iri dabam dabam, da baye-baye na Ruhu Mai-tsarki, bisa ga nufi nasa.” (Ibraniyawa 2:2-4) I, Yesu shi ne cibiya a yin shelar kalmomin annabci.—Ru’ya ta Yohanna 19:10.

16. Me ya sa ya kamata mu ba da gaskiya sosai ga dukan annabce-annabce na Jehovah Allah?

16 Kamar yadda muka lura, Bitrus ya ce: “Ba a taɓa kawo kowane annabci bisa ga nufin mutum ba.” Mutane kawai ba za su iya annabci na gaskiya ba, amma za mu iya kasance da bangaskiya sosai ga dukan annabce-annabce na Allah. Waɗannan asalinsu daga Jehovah ne Allah kansa. Ta ruhu mai-tsarki, ya sa bayinsa su fahimci yadda annabce-annabcen Littafi Mai-Tsarki suke cika. Hakika, mun yi godiya ga Jehovah domin mun ga cikan annabce-annabcen irin waɗannan da yawa tun daga shekara ta 1914. Mun tabbata sarai cewa sauran annabce-annabcensa game da ƙarshe na wannan mugun tsarin abubuwa duk za su cika. Yana da muhimmanci mu ci gaba da sauraron abin da Allah ya ce zai faru nan gaba yayin da muke barin haskenmu ya haskaka. (Matta 5:16) Muna godiya ga Jehovah da yake sa ‘haske ya haskaka cikin baƙin duhu’ da ya lulluɓe duniya a yau!—Ishaya 58:10.

17. Me ya sa muke bukatar haske na ruhaniya daga wurin Allah?

17 Haske na zahiri yana sa muna gani. Yana kuma sa shuke-shuke da suke ba mu abinci iri iri su yi girma. Ba za mu rayu na lokaci mai tsawo ba idan babu haske na zahiri. Hasken ruhaniya fa? Yana yi mana ja-gora kuma yana nuna mana abin da zai faru nan gaba kamar yadda aka annabta a cikin Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki. (Zabura 119:105) Cikin ƙauna Jehovah Allah ya ‘aika mana da haskensa da kuma gaskiya.’ (Zabura 43:3) Babu shakka, ya kamata mu nuna godiyarmu ga irin waɗannan tanadodi. Saboda haka, bari mu yi iyakacin ƙoƙarinmu mu tsosi haske na “sanin darajar Allah” don ya haskaka zukatanmu ta alama.—2 Korinthiyawa 4:6; Afisawa 1:18.

18. Menene Tauraron Assubahi na Jehovah yake shirye ya yi yanzu?

18 Lallai mun albarkatu da muka san cewa a shekara ta 1914, Yesu Kristi, Tauraro na Assubahi, ya bayyana cikin dukan sararin samaniya kuma ya fara cika wahayin sāke kamani! Tauraro na Assubahi na Jehovah a yanzu yana bayyane, a shirye yake ya fara cika ƙudurin Allah a ƙarin cika na sāke kamanin—“yaƙin babbar rana na Allah Mai-iko duka.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Bayan an share wannan tsohon tsari, Jehovah zai cika alkawarinsa na “sababbin sammai da sabuwar duniya,” inda za mu yabe shi kuma ɗaukaka shi har abada shi Ubangiji Mai-Ikon Mallaka na sararin samaniya kuma Allah na annabcin gaskiya. (2 Bitrus 3:13) Kafin wannan babbar ranar, bari mu ci gaba da tafiya cikin hasken Allah ta saurarawa ga kalmomin annabci na Allah.

Ta Yaya Za Ka Amsa?

• Yaya za ka kwatanta sāke kamani na Yesu?

• Ta yaya sāke kamanin yake gina bangaskiya?

• Waye ko kuma menene Tauraron Assubahi na Jehovah, kuma yaushe ya fito?

• Me ya sa ya kamata mu saurara ga kalmomin Annabci na Allah?

[Hoto a shafi na 20]

Za ka yi bayani game da muhimmancin sāke kamani?

[Hoto a shafi na 22]

Tauraron Assubahi ya riga ya fito. Ka san ko yaushe kuma ta yaya?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba