Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w05 2/1 pp. 3-7
  • Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yesu Kansa Ya Ba da Tabbaci
  • Wahayi ya Ƙarfafa Su
  • Ƙarin Haske ga Amintattun Allah
  • An Kāre Su Cikin Duhu da Wahala
  • Wanene Yesu Kristi?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Wane ne Yesu Kristi?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
  • Ta Hanyar Almasihu Ne Allah Zai Kawo Ceto
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Amsoshin Tambayoyinmu Game da Yesu Kristi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2005
w05 2/1 pp. 3-7

Domin Kristi Aka Yi Annabce-annabce

“Gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon yin annabci.”—Wahayin Yahaya 19:10.

1, 2. (a) Wane zaɓi ne Isra’ilawa suka fuskanta farawa da shekara ta 29 A.Z.? (b) Menene za a tattauna a cikin wannan talifin?

ASHEKARA ta 29 A.Z. Isra’ila ta cika da maganar Almasihu da aka yi alkawarinsa. Hidimar Yahaya Mai Yin Baftisma ta ƙarfafa sa rai da mutane suka yi. (Luka 3:15) Yahaya ya ce ba shi ne Kristi ba. Maimakon haka, sai ya nuna Yesu Banazare, ya ce: “Na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.” (Yahaya 1:20, 34) Ba da daɗewa ba, taron jama’a suka bi Yesu domin su saurari koyarwarsa kuma don ya warkar da su.

2 A watanni da suka biyo baya, Jehobah ya ba da shaida sau da yawa game da Ɗansa. Waɗanda suka yi nazarin Nassosi kuma suka kiyaye ayyukan Yesu suna da dalili mai ƙarfi na ba da gaskiya a gare shi. Amma, galibin mutanen alkawari na Allah ba su ba da gaskiya a gare shi ba. Kaɗan ne kawai daga cikinsu suka yarda cewa Yesu shi ne Kristi, Ɗan Allah. (Yahaya 6:60-69) Menene za ka yi da a ce kana raye a lokacin? Da za ka amince cewa Yesu shi ne Almasihu kuma ka zama mabiyinsa mai aminci? Ka yi la’akari da tabbacin tarihinsa da Yesu kansa ya bayar, sa’ad da aka zarge shi da cewa bai kiyaye Assabaci ba, kuma ka lura da tabbaci da ya bayar daga baya domin ya ƙarfafa bangaskiyar almajiransa masu aminci.

Yesu Kansa Ya Ba da Tabbaci

3. Wane yanayi ne ya motsa Yesu ya ba da tabbaci game da kansa?

3 A lokacin Idin Ƙetarewa na shekara ta 31 A.Z. Yesu yana Urushalima. Bai daɗe da warkar da wani mutumin da ya yi shekaru 38 yana rashin lafiya ba. Yahudawa kuwa suka tsananta wa Yesu domin ya warkar da mutum a ranar Assabaci. Suka zarge shi da saɓo domin ya kira Allah Ubansa kuma suka so su kashe shi. (Yahaya 5:1-9, 16-18) Amsoshin da Yesu ya bayar da kansa sun ba da muhimman hujjoji guda uku da za su tabbatar wa kowane Bayahude mai zuciyar kirki kowanene Yesu.

4, 5. Mecece manufar hidimar Yahaya, kuma yaya ya cika ta?

4 Da farko, Yesu ya yi amfani da shaidar wanda ya share masa fage, Yahaya Mai Baftisma, yana cewa: “Kun aika wajen Yahaya, shi kuma ya shaidi gaskiya. Yahaya fitila ne mai ci, mai haske kuma, kun kuwa yarda ku yi farin ciki matuƙa da haskensa ɗan lokaci kaɗan.”—Yahaya 5:33, 35.

5 Yahaya Mai Yin Baftisma shi ne ‘fitila mai ci’ domin kafin Hirudus ya ɗaure shi ba dalili, ya cika umurnin da Allah ya ba shi na share wa Almasihu fage. Yahaya ya ce: “Domin a bayyana shi [Almasihu] ga Isra’ila ne na zo, nake baftisma da ruwa. . . . Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma zama a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”a (Yahaya 1:26-37) Yahaya musamman ya ambaci cewa Yesu shi ne Ɗan Allah—Almasihun da aka yi alkawarinsa. Shaidar da Yahaya ya ba da ta tabbata, har ta sa watanni takwas bayan mutuwar Yahaya, Yahudawa masu zuciyar kirki suka ce: “Duk abin da [Yahaya] ya faɗa game da mutumin nan gaskiya ne.”—Yahaya 10:41, 42.

6. Me ya sa ayyukan da Yesu ya yi ya kamata su tabbatar wa mutane cewa yana da goyon bayan Allah?

6 Bayan haka, Yesu ya sake ba da wani dalilin da ya ba da tabbacin cewa shi ne Almasihu. Ya nuna ayyukan da ya yi masu kyau da suka tabbatar yana da goyon bayan Allah. “Shaidar da ni nake da ita ta fi ta Yahaya ƙarfi,” ya ce, “domin ayyukan da Uba ya ba ni in gama, su ainihin ayyukan nan da nake yi, ai, su ne shaidata a kan cewa Uba ne ya aiko ni.” (Yahaya 5:36) Har ma maƙiyan Yesu ba su musanta wannan tabbacin ba, waɗanda suka haɗa da mu’ujizai masu yawa da ya yi. Wasu ma cikinsu suka yi tambaya, “Shin, me muke yi ne, har mutumin nan yake ta yin mu’ujizai da yawa haka?” (Yahaya 11:47) Wasu suka saurare shi kuma suka ce: “Sa’ad da Almasihu ya zo, zai yi mu’ujizai fiye da na mutumin nan?” (Yahaya 7:31) Waɗanda suka saurari Yesu sun kasance ne a yanayi da ya dace na ganin halayen Uba a Ɗansa.—Yahaya 14:9.

7. Ta yaya ne Nassosin Ibrananci suka ba da shaida game da Yesu?

7 A ƙarshe, Yesu ya jawo hankalinsu ga wata shaidar da ba su iya ƙaryatawa ba. Ya ce: “Littattafai . . . su ne ke shaidata.” Ya ƙara da cewa: “Da dai kun gaskata Musa, da kun gaskata ni, domin labarina ya rubuta.” (Yahaya 5:39, 46) Hakika, Musa yana ɗaya daga cikin shaidu masu yawa da suka yi rubutu game da Kristi kafin lokacin Kiristoci. Abubuwan da suka rubuta sun haɗa zuriyarsa da ɗarurruwan annabce-annabce game da Almasihun. (Luka 3:23-38; 24:44-46; Ayyukan Manzanni 10:43) Dokar Musa kuma fa? Manzo Bulus ya rubuta: “Shari’a ta zama uwargijiyarmu da ta kai mu ga Almasihu.” (Galatiyawa 3:24) Hakika, “gaskiyar da Yesu ya bayyana ita ce ta ba da ikon [ko kuma ma’ana da dalilin] yin annabci.”—Wahayin Yahaya 19:10.

8. Me ya sa yawancin Yahudawa suka ƙi su ba da gaskiya ga Almasihu?

8 Bai kamata a ce shaidar da Yahaya ya ba da, da ayyuka masu ban al’ajabi da Yesu ya yi, da halaye na ibada da ya nuna, da kuma tabbaci mai yawa da Nassosi suka ba da, sun gamsar da kai cewa Yesu ne Almasihu ba? Duk wanda yake da tabbataciyar ƙauna ga Allah da kuma Kalmarsa, zai gane wannan kuma zai ba da gaskiya cewa Yesu shi ne Almasihun da aka yi alkawarinsa. Babu irin wannan ƙaunar a Isra’ila. Ga masu adawa da shi, Yesu ya ce: “Na san ku, ba ku da ƙaunar Allah a zuci.” (Yahaya 5:42) ‘Suna karɓan girma a junansu,’ amma “girman da ke daga Allah Makaɗaici kuwa, ba [sa] nemansa.” Shi ya sa suka ƙi su karɓi Yesu, wanda kamar Ubansa, ya ƙi irin tunaninsu!—Yahaya 5:43, 44; Ayyukan Manzanni 12:21-23.

Wahayi ya Ƙarfafa Su

9, 10. (a) Me ya sa lokacin da aka ba da alama ga almajiran Yesu yake da muhimmanci? (b) Wane alkawari na ban mamaki ne Yesu ya yi wa almajiransa?

9 Shekara ɗaya ta riga ta wuce tun da Yesu ya ba da tabbaci da aka ambata da suka nuna cewa shi ne Almasihu. Idin Ƙetarewa na shekara ta 32 A.Z., ya riga ya wuce. Yawanci da suka gaskata da shi sun daina bin sa, wataƙila domin tsanani, ko don son abin duniya, ko kuma don alhini na rayuwa. Wataƙila wasu sun rikice ko sun yi sanyin gwiwa domin Yesu ya ƙi ƙoƙarce-ƙoƙarcen da mutane suke yi su naɗa shi sarki. Sa’ad da shugabannin addinai na Yahudawa suka tuhume shi, ya ƙi ya nuna musu alama daga sama domin ya ɗaukaka kansa. (Matiyu 12:38, 39) Wataƙila ƙi da ya yi ya ba wasu mamaki. Bugu da ƙari, Yesu ya fara yi wa almajiransa bayanin wani abu da ba su fahimta ba cewa—“lalle ne ya tafi Urushalima, ya sha wuya iri iri a hannun shugabanni da manyan firistoci da malaman Attaura, har a kashe shi.”—Matiyu 16:21-23.

10 “Yesu ya san lokacinsa ya yi da zai tashi daga wannan duniya ya koma wurin Uba,” a cikin watanni tara ko goma masu zuwa. (Yahaya 13:1) Domin ya damu sosai game da almajiransa masu aminci, Yesu ya yi wa wasu a cikin su alkawarin alama daga sama—abar da ya hana Yahudawa marasa-bangaskiya. “Hakika, ina gaya maku,” Yesu ya ce, “akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Ɗan Mutum na zuwa cikin Mulkinsa.” (Matiyu 16:28) Yesu ba ya nufin cewa akwai wasu a cikin almajiransa da za su kasance a raye har lokacin da za a kafa Mulkin Almasihu a shekara ta 1914 ba. Abin da Yesu yake nufi shi ne zai bai wa uku cikin almajiransa da suka fi shaƙuwa alamar bayyanarsa a cikin darajar Mulki. Ana kiran wannan wahayin sake kamani.

11. Ka kwatanta wahayi na sake kamani.

11 Bayan kwana shida, Yesu ya ɗauki Bitrus, Yakubu, da Yahaya zuwa kan wani dutse mai tsawo—ƙila a kan wasu tuddai na Dutsen Harmon. A wurin “sai kamanninsa ya sāke a gabansu, fuska tasa ta yi annuri kamar hasken rana, tufafinsa kuma suka yi fari fat suna haske.” Sai annabi Musa da annabi Iliya suka bayyana, suna zance da Yesu. Ƙila wannan aukuwa na ban mamaki ya faru ne daddare yadda almajiran za su iya gani sosai. Hakika, wannan ya kasance da gaske har da Bitrus ya ce zai kafa bukkoki guda uku—guda na Yesu, guda na Musa, guda kuma na Iliya. Bitrus yana cikin magana ke nan, sai gajimare mai haske ya kewaye su sai kuma suka ji murya daga cikin gajimaren yana cewa: “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”—Matiyu 17:1-6.

12, 13. Ta yaya ne wahayin sake kamani ya shafi almajiran Yesu, kuma menene ya sa?

12 Hakika, Bitrus ya riga ya faɗa cewa Yesu shi ne “Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.” (Matiyu 16:16) Amma, ka yi tunanin jin muryar Allah da kansa, yana ba da tabbaci game da shafaffen Ɗansa da kuma matsayinsa! Babu shakka, wannan wahayi na sake kamani ya ƙarfafa Bitrus, Yakubu, da Yahaya! Domin an ƙarfafa bangaskiyarsu, suna shirye don lokatai masu wuya da suke zuwa a nan gaba da kuma muhimman ayyukan da za su yi a ikilisiya a nan gaba.

13 Sake kamanin ya motsa zuciyar almajiran. Bayan shekara 30, Bitrus ya rubuta: “Allah Uba ya girmama shi [Yesu], ya kuma ɗaukaka shi, sai murya ta zo masa daga mafificiyar ɗaukaka cewa, ‘Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena wanda nake farin ciki da shi ƙwarai,” mu ne muka ji muryan nan da aka sauko daga Sama, don muna tare da shi a kan tsattsarkan Dutsen nan.” (2 Bitrus 1:17, 18) Aukuwar ma ta motsa Yahaya. Bayan shekara 60 da aukuwar, ya yi waɗannan kalaman: “Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.” (Yahaya 1:14) Duk da haka, sake kamani ba shi ne wahayi na ƙarshe da mabiyan Yesu suka gani ba.

Ƙarin Haske ga Amintattun Allah

14, 15. A wane azanci ne manzo Yahaya zai kasance a raye har sai Yesu ya zo?

14 Bayan ya tashi daga matattu, Yesu ya bayyana ga almajiransa a Tekun Galili. A wurin ya gaya wa Bitrus: “In na nufe shi [Yahaya] da wanzuwa har in zo, menene naka a ciki?” (Yahaya 21:1, 20-22, 24) Wannan yana nufin cewa manzo Yahaya zai sami tsawon rai ne fiye da sauran manzannin? Kamar haka ne, domin ya sāke bauta wa Jehobah da aminci na kusan wasu shekaru 70. Amma kalmar Yesu tana ɗauke da muhimman abubuwa fiye da wannan.

15 Furcin nan “har in zo” ya tuna mana abin da Yesu ya ce: “Ɗan Mutum na zuwa cikin Mulkinsa.” (Matiyu 16:28) Yahaya na raye sa’ad da Yesu ya zo, domin daga baya an ba shi wahayi game da zuwan Yesu cikin ikon Mulki. Kusan ƙarshen rayuwar Yahaya, sa’ad da yake bauta a tsibirin Batamusa, ya ga Wahayi masu ban mamaki na abubuwan da za su auku “a ranar Ubangiji.” Wahayin da aka nuna wa Yahaya ya motsa shi sosai, da Yesu ya ce: “Ina zuwa da wuri.” Sai Yahaya ya ce: “Amin. Zo, ya Ubangiji Yesu.”—Wahayin Yahaya 1:1, 10; 22:20.

16. Me ya sa yake da muhimmanci mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu?

16 Mutane masu zukatan kirki da suke raye a ƙarni na farko sun yarda cewa Yesu ne Almasihu, kuma sun ba da gaskiya a gare shi. Waɗanda suka zama masu bi suna bukatan a ƙarfafa su domin rashin bangaskiya da ya kewaye su, aikin da za su yi, da kuma gwajin da ke zuwa a nan gaba. Yesu ya ba da tabbaci masu yawa da suka nuna cewa shi ne Almasihu kuma ya ba da wahayi domin ya ƙarfafa mabiyansa masu aminci. A yau, muna zaune ne “a ranar Ubangiji.” Nan ba da daɗewa ba, Kristi zai halaka dukan mugun zamanin Shaiɗan kuma zai ceci mutanen Allah. Dole ne mu ƙarfafa bangaskiyarmu ta yin amfani da dukan tanadodi na Jehobah domin lafiyarmu ta ruhaniya.

An Kāre Su Cikin Duhu da Wahala

17, 18. Wane bambanci ne ke tsakanin mabiyan Yesu da kuma waɗanda suke hamayya da manufar Allah a ƙarni na farko, kuma yaya abubuwa suka kasance wa kowane rukuni?

17 Bayan mutuwar Yesu, almajiransa sun bi umurninsa da gaba gaɗi na yin shaidarsa a “Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) Duk da yawan tsanani, Jehobah ya albarkaci sabuwar ikilisiyar Kirista ta lokacin da wayewa ta ruhaniya da kuma sababbin almajirai masu yawa.—Ayyukan Manzanni 2:47; 4:1-31; 8:1-8.

18 A wani ɓangare kuma, aniyar waɗanda suke hamayya da bishara sai ƙara duhu take yi. “Hanyar mugaye kuwa duhu ne baƙi ƙirin, kamar ɗuhun dare,” in ji Karin Magana 4:19. “Sukan fāɗi, amma ba su san abin da ya sa suka yi tuntuɓe ba.” “Duhun” ya ƙaru a shekara ta 66 A.Z., sa’ad da sojojin Roma suka zagaye Urushalima. Bayan sun janye na ɗan lokaci ba dalili, sojojin Roma suka sake dawowa a shekara ta 70 A.Z., suka halaka birnin. In ji ɗan tarihin Yahudawa Josephus, fiye da Yahudawa miliyan ɗaya ne suka halaka. Kiristoci masu aminci kuwa sun tsira. Me ya sa? Domin sa’ad da sojojin suka janye da farko, sun yi biyayya ga umurnin Yesu na su gudu.—Luka 21:20-22.

19, 20. (a) Me ya sa mutanen Allah ba su da dalilin jin tsoro yayin da ƙarshen zamanin nan ya yi kusa? (b) Wane fahimi ne Jehobah ya ba mutanensa kafin shekara ta 1914?

19 Yanayinmu kusan ɗaya ne. Matsananciyar wahala da ke tafe, za ta kawo ƙarshen mugun zamani na Shaiɗan. Mutanen Allah ba sa bukatan su ji tsoro, domin Yesu ya yi alkawari: “Ga shi, ni kuma kullum ina tare da ku har matuƙar zamani.” (Matiyu 28:20) Domin ya gina bangaskiyar almajiransa na farko kuma don ya shirya su domin abin da ke zuwa a nan gaba, Yesu ya ba su alamar ɗaukakarsa na samaniya a matsayin Sarki Almasihu. Yau kuma fa? A shekara ta 1914 wannan alamar ta zama gaskiya. Kuma ta ƙarfafa bangaskiyar mutanen Allah! Tana ɗauke ne da alkawarin na nan gaba mai ban sha’awa, kuma bayin Jehobah sun sami fahimi game da wannan tabbacin. A cikin duniya ta yau mai duhu, “hanyar da adalai ke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.”—Karin Magana 4:18.

20 Kafin shekara ta 1914, ƙaramar rukunin shafaffun Kiristoci sun soma fahimtar gaskiya game da dawowar Ubangiji. Alal misali, sun gane cewa dawowarsa ba wanda za a gani da ido ba ne, kamar yadda mala’iku guda biyu da suka bayyana a shekara ta 33 A.Z., ga almajiran sa’ad da Yesu ya haura sama suka faɗa. Bayan an ɗauke Yesu zuwa sama kuma almajiransa suka daina ganinsa, sai mala’ikun suka ce: ‘Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa Sama.’—Ayyukan Manzanni 1:9-11.

21. Menene za mu tattauna a talifi na gaba?

21 Manzaninsa masu aminci ne kawai suka ga lokacin da Yesu ya haura sama. Kamar yadda ya kasance da sake kamani, ba dukan jama’a ba ne suka gan shi. Hakan zai kasance game da dawowar Kristi cikin ikon Mulki. (Yahaya 14:19) Almajiransa shafaffu masu aminci ne kaɗai za su gane bayyanuwarsa na sarauta. A cikin talifinmu na gaba, za mu ga yadda wannan fahimtar za ta shafe su, wadda za ta kai ga tattara miliyoyin da za su zama talakawan Yesu a duniya.—Wahayin Yahaya 7:9, 14.

[Hasiya]

a Babu shakka, Yahaya ne kaɗai ya ji muryar Allah a lokacin baftismar Yesu. Yahudawan da Yesu ya yi wa magana ba su “taɓa jin muryarsa [Allah] ba, ko ganin kama tasa.”—Yahaya 5:37.

Ka Tuna?

• Sa’ad da aka tuhumi Yesu cewa bai kiyaye Assabaci ba da kuma yin saɓo, wane tabbaci ne ya ba da domin ya nuna cewa shi ne Almasihu?

• Ta yaya ne almajiran Yesu suka amfana daga sake kamani?

• Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya ce Yahaya zai kasance a raye har sai ya zo?

• Wace alama ce ta zama gaskiya a shekara ta 1914?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba