Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 5/1 pp. 3-4
  • Me Ya Sa Rashawa ta Yi Yawa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Rashawa ta Yi Yawa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Menene Ke Haddasa Rashawa?
  • Yaƙi da Rashawa da Takobi na Ruhu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Mulkin Allah​—⁠Gwamnatin da Babu Cin Hanci da Rashawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Matsalar Cin Hanci da Rashawa a Gwamnati
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 5/1 pp. 3-4

Me Ya Sa Rashawa ta Yi Yawa?

“Kada ka amshi toshiya, domin toshiya tana makanta waɗanda suke gani kuma ta murɗe kalmomin masu adalci.”—Fitowa 23:8.

SHEKARA 3,500 da suka shige, Dokar Musa ta haramta cin hanci. A duk cikin ƙarnuka tun lokacin, dokokin yaƙi da rashawa sun ƙaru da gaggawa. Duk da haka, kafa doka bai magance rashawa ba. Kowace rana ana ba da miliyoyin cin hanci, kuma biliyoyin mutane suna shan wahalar sanadin haka.

Rashawa ta yaɗu ko’ina kuma ta zama da wuyan ganewa a duniya da har tana barazanar raunana tarayyar jama’a. A wasu ƙasashe kusan komi ba ya yiwuwa sai an ba da cin hanci. Ba da cin hanci ga wanda ya kamata zai sa mutum ya ci jarabawa, ya sami lasin direba, ya sami aiki, ko kuma ya ci shari’a a kotu. Wani lauya, Arnaud Montebourg a Paris ya furta baƙin ciki da cewa: “Rashawa tana kama da gurɓacewa da ta yi nauyi cikin halayen mutane.”

Cin hanci ya fi yawa musamman ma a ɓangaren kasuwanci. Wasu kamfanoni suna ba da kashi uku na dukan riba da suke samu don kawai su biya lalatattun ma’aikatan gwamnati. Jaridar Britaniya The Economist ta ce, kashi 10 bisa ɗari na dalla biliyan 25 da ake kashewa kowace shekara a sayar da makamai a dukan duniya ana kashewa ne wajen ba da cin hanci ga waɗanda ƙila za su zama ’yan ciniki. Yayin da wannan rashawa ta ƙaru, abin da take haddasawa ya zama bala’i. Cikin shekara goma na baya bayan nan, “aboki na kurkusa” jari hujja—maguɗi cikin kasuwancin da yake amfane kalilan waɗanda suke da hurɗan kasuwanci mai kyau—an ce sun lalata tattalin arzikin dukan ƙasashe.

Waɗanda suka fi shan wuya daga Rashawa da ɓarnanta na tattalin arziki da yawa sune matalauta, abin da babu makawa—waɗanda ba su da shi balle su ba wani cin hanci. Kamar yadda The Economist ya faɗa, “rashawa hanya ɗaya ce ta zalunci.” Za a iya a sha kan irin wannan zalunci, ko kuma dai rashawa da ba ta da makawa? Don a amsa wannan tambayar, dole ne mu gane da farko wasu muhimman dalilai da ke haddasa rashawa.

Menene Ke Haddasa Rashawa?

Me ya sa mutane suke zaɓa su lalace maimako suna yin gaskiya? Ga wasu mutane, lalata ita ce hanyar da ta fi sauƙi—ko kuma ita ce hanya kawai—na samun abin da suke so. A wasu lokutta, ba da cin hanci zai zama hanya ce mai sauƙi na guje wa horo. Mutane da yawa da sun lura cewa ’yan siyasa, ’yan sanda, da alƙalai sun ƙyale rashawa ko kuma ma su kansu suna yin hakanan sai kawai su bi sawunsu.

Yayin da rashawa ta ƙaru sosai, sai ta zama aba da aka amince da ita, a ƙarshe sai ta zama hanyar rayuwa. Ba yadda mutane da suke karɓan ƙaramin albashi za su yi. Dole su karɓi cin hanci idan suna son rayuwa madaidaiciya. Kuma yayin da ba abin da ya sami waɗanda suke karɓan cin hanci ko kuma waɗanda suke bayarwa don su sami moriya, mutane kaɗan ne suka rage da suke so su yaƙi ɗabi’ar. Sarki Sulemanu ya lura: “Saboda ba a aika shari’a da aka hukunta a bisa mugunta da sauri ba, shi ya sa zuciyar ’yan adam ta kan ji ƙarfin aika mugunta.”—Mai-Wa’azi 8:11.

Abubuwa biyu masu ƙarfi suke ci gaba da motsa rashawa: son kai da haɗama. Saboda son kai, mutane da suka lalace suna rufe idanunsu ga wuya da lalatarsu ke kawo wa wasu, kuma suna ganin ta dace domin suna amfana. Da zarar masu karɓan rashawa sun tara abin duniya, sai haɗamarsu ta ƙaru. Sulemanu ya lura cewa: “Wanda ya ke ƙaunar azurfa ba za ya ƙoshi da azurfa ba; wanda ya ke neman yalwa kuma ba za ya ƙoshi da ƙaruwa ba.” (Mai-Wa’azi 5:10) Hakika, haɗama wataƙila za ta yi kyau wajen neman kuɗi, amma tana rufe idanunta ga rashawa da taka doka.

Wani abu da bai kamata a yin banza da shi ba shi ne matsayin mai sarauta mara ganuwa na wannan duniya, wanda Littafi Mai-Tsarki ya nuna Shaiɗan Iblis ne. (1 Yohanna 5:19; Ru’ya ta Yohanna 12:9) Shaiɗan yana ɗaukaka lalata sosai. Cin hanci da ya fi girma da aka rubuta shi ne wanda Shaiɗan ya ba Kristi. ‘Zan ba ka dukan mulkokin duniya idan ka faɗi ka yi mani sujada.’—Matta 4:8, 9.

Amma, Yesu ba shi da lalata, kuma ya koya wa mabiyansa kada su yi hakanan. Koyarwar Kristi za ta zama abu mai amfani na yin yaƙi da rashawa ne a yau? Talifi na biye zai bincika wannan tambayar.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba