Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 5/1 pp. 4-7
  • Yaƙi da Rashawa da Takobi na Ruhu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yaƙi da Rashawa da Takobi na Ruhu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ta Yaya Za a Magance Rashawa?
  • Littafi Mai-Tsarki Ya Haramta Rashawa
  • Cin Nasara a Yaƙi da Rashawa da Gaskiyar Littafi Mai-Tsarki
  • “Wanda Ya Ƙi Cin Hanci Zai Rayu”
  • Me Ya Sa Rashawa ta Yi Yawa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Mulkin Allah​—⁠Gwamnatin da Babu Cin Hanci da Rashawa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Matsalar Cin Hanci da Rashawa a Gwamnati
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Gabatarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 5/1 pp. 4-7

Yaƙi da Rashawa da Takobi na Ruhu

“Ku yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.”—Afisawa 4:24.

AƊAUKAKARTA, Daular Roma ita ce tsarin mulki na ’yan Adam da ta fi girma da duniya ta taɓa gani. Dokar Roma tana da ƙarfi sosai da har ila ita ce tushen tsarin dokoki na ƙasashe da yawa. Amma, duk da abin da Roma suka cim ma, rundunarta ba su iya kawar da wani magabcinsu ba: rashawa. Daga bisani, rashawa ta sa Roma ta faɗi da sauri.

Manzo Bulus yana ɗaya daga cikin waɗanda suka sha wahala a ƙarƙashin lalatattun ma’aikatan Roma. Filikus, gwamna na Roma ya yi masa tambaya sosai kuma babu shakka ya gane sarai cewa Bulus ba shi da laifi. Amma Filikus, ɗaya daga cikin lalatattun gwamnonin lokacinsa, ya yi jinkiri a yi wa Bulus shari’a, yana zaton Bulus zai ba shi kuɗi don ya sake shi.—Ayukan Manzanni 24:22-26.

Maimakon ya ba Filikus cin hanci, Bulus ya gaya masa a fili game da “adalci, da kamewa.” Filikus bai canja hanyoyinsa ba, Bulus kuma ya zauna cikin fursuna maimakon ya yi ƙoƙari ya kawar da hanyar doka da cin hanci. Ya yi wa’azin saƙon gaskiya da sahihanci, kuma ya yi rayuwa daidai bisa haka. Ya rubuta wa Kiristoci Yahudawa: “Mun kawarda shakka muna da kyakkyawan lamiri, muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.”—Ibraniyawa 13:18.

Irin wannan kasancewa dabam ya saɓa sosai da ɗabi’u na lokacin. Pallas ɗan’uwan Filikus yana ɗaya daga cikin waɗanda suka fi arziki a duniya ta dā, kuma arzikinsa—da aka lissafta dala miliyan 45—ya tara kusan duka ta wurin cin hanci da ƙwace. Amma, arzikinsa kaɗan ne in an gwada da biliyoyin daloli da wasu lalatattun masu sarauta na ƙarni na 20 suka ɓoye a bankuna. Babu shakka, sai dai wawa ne kawai zai yarda cewa gwamnati a yau sun yi nasara a yaƙi da rashawa.

Tun da yake rashawa ta kasance da ƙarfi haka na lokaci mai tsawo, sai mu ɗauka cewa ɓangare ne na halin mutane? Ko kuma za a iya yin wani abu don a magance rashawa?

Ta Yaya Za a Magance Rashawa?

Mataki na farko da ya fita sarai na magance rashawa shi ne a fahimci cewa rashawa tana yin ɓarna kuma ba ta da kyau, tun da tana amfanan marasa ɗabi’a ne ta yi ɓarna ga wasu. Babu shakka an sami ci gaba a wannan wuri. James Foley, mataimakin sakatare na jiha ta United States, ya ce: “Mun gane cewa abin da rashawa take kawowa yana da yawa. Cin hanci yana ɓata gwamnati, yana ɓata tattalin arziki da bunƙasa na ƙasa, murguɗe kasuwanci, kuma ya sa ’yan ƙasa a dukan duniya su wahala.” Mutane da yawa za su yarda da abin da ya ce. A 17 ga Disamba, 1997, sanannun ƙasashe sun sa hannu a “yarjejeniyar cin hanci” da aka shirya “don a yi yaƙi da rashawa a dukan duniya.” Yarjejeniyar “ta sa ya zama laifi a bayar, yi alkawari ko kuma ba da cin hanci ga ma’aikacin wata ƙasa don a sami ko kuma a ci gaba da kasuwanci na ƙasashen waje.”

Ba da cin hanci don a sami kwangila a wasu ƙasashe, sashe ne ƙarami kawai na rashawa. Kawar da rashawa yana bukatar mataki na biyu da ya fi wuya: canja zuciya ko kuma canjin zukatan mutane da yawa. Dole ne mutane a ko’ina su koyi ƙyamar cin hanci da rashawa. Sa’annan ne kawai maguɗi zai ɓace. Don a yi haka, jaridar Newsweek ta ce wai wasu suna jin cewa ya kamata gwamnati ta “ƙarfafa ɗabi’a mai kyau.” Haka ma, wani rukuni da suke aiki na wakilai a yaƙi da rashawa a dukan duniya, sun ba da shawara cewa masu goyon bayansu su “shuka ‘yin gaskiya’ ” a wurin aiki.

Yaƙi da rashawa na hali ne, ba wanda za a ci, ta kafa doka ba ne kaɗai ko kuma a ba da “takobin” horo ba. (Romawa 13:4, 5) Dole ne a shuka ɗabi’u masu kyau da yin gaskiya a zukatan mutane. Za a fi cim ma wannan ta yin amfani da abin da manzo Bulus ya kira “takobin Ruhu,” Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki.—Afisawa 6:17.

Littafi Mai-Tsarki Ya Haramta Rashawa

Me ya sa Bulus ya ƙi yin na’am da rashawa? Domin yana son ya yi nufin Allah, “wanda ba ya tara, ba ya kuwa karɓan rashawa ba.” (Kubawar Shari’a 10:17) Ban da haka ma, babu shakka Bulus ya tuna da gargaɗi da ke a cikin Dokar Musa: “Ba kuwa za ka yi tara ba: ba kuwa za ka karɓi rashawa ba; gama rashawa ta kan makantar da idanun masu-hikima, ta kan karkatarda zancen mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 16:19) Sarki Dauda ma ya fahimci cewa Jehovah ba ya son rashawa, kuma ya yi roƙo cewa kada Allah ya kirga shi cikin masu zunubi waɗanda, “hannunsu na dama cike ya ke da karɓan rashawa.”—Zabura 26:10.

Waɗanda suke bauta wa Allah da gaske suna da ƙarin dalilai na ƙin rashawa. Sulemanu ya rubuta: “Ta yin gaskiya sarki ya kan tabbatar da ƙasa, amma wanda yake da kwaɗayin cin hanci ya kan rushe ta.” (Misalai 29:4, juyin New International Version) Idan aka yi gaskiya—musamman daga manyan ma’aikata zuwa ƙananan—zai tabbatar da ƙasa, yayin nan kuma rashawa tana talauta ƙasa. Newsweek ya ce: “A tsari inda kowa yana son ya samu nasa riba daga rashawa kuma ya san yadda zai samu, tattalin arzikin zai faɗi.”

Ko ma arziki bai fāɗi ba gabaɗaya, masu ƙaunar gaskiya suna baƙin ciki yayin da rashawa tana ci gaba ba a yi kome ba. (Zabura 73:3, 13) An ɓata wa Mahaliccinmu, wanda ya ba mu sha’awar yin gaskiya. A can dā, Jehovah ya sa hannu ya kawar da tsananin rashawa. Alal misali, ya gaya wa mazaunan Urushalima a fili abin da ya sa zai yasar da su ga magabtansu.

Ta wurin annabinsa Mikah, Allah ya ce: “Ku ji wannan, ina roƙonku, ku shugabannai na gidan Yaƙub, ku mahukumta na gidan Isra’ila, ku da ku ke ƙin shari’a, kuna ɓata dukan gaskiya. Manyanta suna shari’a domin toshi, [firistoci, NW ] nata suna koyarwa domin ijara, annabawanta kuma suna duba domin kuɗi . . . Domin wannan, saboda aikinku za a huɗe Sihiyona kamar gona, Urushalima kuma za ta zama tuddai, dutsen gidan Ubangiji kuma za ya zama kamar tuddan kurmi.” Rashawa ta yi ɓarna ga jama’ar Isra’ila, yadda ta halaka Roma ƙarnuka daga baya. Da gaske ga kashedi da Allah ya yi, kamar ƙarni guda bayan Mikah ya rubuta waɗannan kalmomi, Urushalima ta halaka kuma aka yasar da ita.—Mikah 3:9, 11, 12.

Ko yaya, ba mutum ko al’umma da ya kamata ya lalace. Allah ya ƙarfafa migayu su bar hanyar rayuwansu kuma su canja hanyar tunaninsu. (Ishaya 55:7) Yana son kowanne cikinmu ya canja haɗama zuwa rashin son kai rashawa kuma zuwa adalci. Jehovah ya tunatar mana: “Wanda ya zalunci fakirai ya jawo ma Mahalicinsa zargi: Amma wanda ya nuna jinƙai ga masu-mayata yana girmama shi.”—Misalai 14:31.

Cin Nasara a Yaƙi da Rashawa da Gaskiyar Littafi Mai-Tsarki

Me zai motsa mutum ya yi canji? Irin ikon nan da ya motsa Bulus ya ƙi rayuwar Bafarisi ya zama mabiyin Yesu Kristi mai gabagaɗi. Ya rubuta, “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” (Ibraniyawa 4:12) Yau, gaskiya ta Nassi tana ɗaukaka adalci, har ma a tsakanin waɗanda suka yi nisa ƙwarai cikin lalata. Ga misali.

Ba da daɗewa ba bayan ya gama aikin soja, Iskandari, da ya fito daga Gabashin Turai, ya bi rukuni da suke samun kuɗi ta ƙeta, ƙwace, da kuma cin hanci.a “Aikina shi ne na tilasta wa ’yan kasuwa masu arziki na karɓi kuɗi, wai ina tsarewa,” in ji shi. “Yayin da ɗan kasuwan ya amince da ni, sai waɗanda suke cikin rukuninmu su yi masa barazana. Sai na ce zan yi maganin abin—a kan kuɗi mai yawa. ‘Abokan cinikina’ sai su gode mini wai don na taimake su magance matsalolinsu, ba su san ni ne ainihin tushen matsalolin ba. Ko da abin mamaki ne, abin da ni ke so ke nan cikin wannan aiki.

“Na kuma more kuɗi da jin daɗi da wannan yayin rayuwa ya ba ni. Ina tuƙa mota mai tsada, ina zama a gida mai kyau, kuma ina da kuɗin sayan dukan abin da na ke so. Mutane suna tsoro na, wannan yana ba ni ƙarfi. Ina jin cewa ba wanda zai iya yi mini kome kuma na fi ƙarfin doka. Za a iya warware kowace matsala da ’yan sanda ta ƙwarerren lauya, wanda ya san hanyar guje wa yin shari’a, ko kuma ta ba da cin hanci ga mutumin da ya dace.

“Amma, babu aminci tsakanin waɗanda rayuwarsu ta dangana bisa rashawa. Da wani cikin rukuninmu ya tsane ni, na ga ba a so na kuma. Farat ɗaya, na yi hasarar motata, kuɗina, budurwata mai son kaya masu tsada. Har na sha mugun bugu. Wannan juyawar rayuwa ta sa ni na yi tunani sosai game da manufar rayuwa.

“Watanni kaɗan da suka shige, uwata ta zama ɗaya cikin Shaidun Jehovah, kuma na soma karanta littattafan su. Kalmomi da ke Misalai 4:14, 15 ya sa na yi tunani: ‘Kada ka shiga hanyar miyagu, kada ka yi tafiya cikin tafarkin mutane masu-mugunta. Ka kauce masa, kada ka gilma wurin: Ka kawarda kai, ka wuce.’ Ayoyi kamar wannan ya huɗubantar da ni cewa waɗanda suke bin rayuwa na aika laifi ba za su sami rayuwa mai kyau ba a nan gaba. Na soma yi wa Jehovah addu’a, na gaya masa ya bishe ni a hanya da ke daidai. Na yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah, kuma daga baya na keɓe raina ga Allah. Tun lokacin ina rayuwa cikin gaskiya.

“Babu shakka, rayuwa cikin mizanan gaskiya ya sa ina samun kuɗi kaɗan. Amma yanzu ina ji ina da abin da zan zama a nan gaba, rayuwata tana da ma’ana na ainihi. Na gane cewa yayin rayuwata ta dā tare da abubuwanta masu tsada tana kama da ginin kati da zai faɗi a kowane lokaci. Dā lamirina yana da tauri. Yanzu, godiya ga nazari na na Littafi Mai-Tsarki, kowane lokaci da na shiga jaraba na yi rashin gaskiya yana suka na—ko a ƙaramin al’amari. Ina ƙoƙari na rayu cikin jituwa da Zabura 37:3, wanda ya ce: ‘Ka dogara ga Ubangiji, ka yi aikin nagarta; ka zauna a cikin ƙasan, ka lizimci aminci.’ ”

“Wanda Ya Ƙi Cin Hanci Zai Rayu”

Kamar yadda Iskandari ya gane, gaskiyar Littafi Mai-Tsarki za ta iya motsa mutum ya sha kan rashawa. Ya yi canje-canje cikin jituwa da abin da manzo Bulus ya ce a wasiƙarsa ga Afisawa: “Ku tuɓe, ga zancen irin zamanku na dā, tsohon mutum, wanda yana ƙara lalacewa bisa ga sha’awoyin yaudara; ku sabonta kuma cikin ruhun azancinku, ku yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya. Domin wannan fa sai ku faɗi gaskiya kowanne game da ɗan’uwansa, kuna kawarda ƙarya: gama mu gaɓaɓuwa ne na junanmu. Mai-yin sata kada shi ƙara yin sata: amma gwamma shi yi aiki, da hannuwansa yana aika abin da ya ke da kyau, domin shi kasance da abin da za shi ɗiba shi bayar ga wanda ya rasa.” (Afisawa 4:22-25, 28) Rayuwa mai kyau a nan gaba na mutane ya dangana a irin wannan sabontawa ce.

Idan ba a kawar da su ba, haɗama da rashawa za su ɓata duniya, yadda suka ɓata Daular Roma. Amma abin farin ciki, Mahaliccin mutane bai bar irin al’amuran nan ga zarafi ba. Ya ƙuduri aniya ya “halaka waɗanda ke halaka duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 11:18) Kuma Jehovah ya yi wa waɗanda suke son duniya da ba ta da rashawa cewa jim kaɗan “sabbabin sammai da sabuwar duniya, inda adalci ya ke zaune” za su zo.—2 Bitrus 3:13.

Gaskiya, ba shi da sauƙi a kasance da mizanan gaskiya a yau. Duk da haka, Jehovah ya tabbatar mana cewa daga baya, “mai haɗama yana kawo wahala ga iyalinsa, amma wanda ya ƙi karɓan cin hanci zai rayu.”b (Misalai 15:27, NIV) Ta wajen ƙin rashawa yanzu, muna nuna gaskiyarmu lokacin da muke addu’a ga Allah: “Mulkinka shi zo. Abin da ka ke so, a yi shi, cikin duniya, kamar yadda a ke yinsa cikin sama.”—Matta 6:10.

Yayin da muke jira wannan Mulki ya aiwatar, kowannenmu zai iya ‘shuka cikin adalci’ ta ƙin yarda da rashawa ko kuma yin ta. (Hosea 10:12) Idan mun yi haka, rayuwarmu ma za ta ba da shaida ga ikon Kalmar Allah da aka hure. Takobin ruhu zai kawar da rashawa.

[Hasiya]

a An canja sunansa.

b Babu shakka, akwai bambanci tsakanin cin hanci da ba da kyauta. Yayin da ana ba da cin hanci don a juya gaskiya ko don wasu abubuwa na rashin gaskiya, kyauta nuna godiya ce ga aiki da aka yi maka. An bayyana wannan a cikin “Tambayoyi Daga Masu Karatu” cikin Hasumiyar Tsaro ta (Turanci) fitar 1 ga Oktoba, 1986 .

[Hoto a shafi na 7]

Da taimakon Littafi Mai-Tsarki, za mu gina “sabon mutum” kuma mu guji rashawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba