Ku Girmama Waɗanda Suke Da Iko Bisa Kanku
“Ku girmama dukan mutane. Ku ƙaunaci ’yan’uwanci. Ku yi tsoron Allah. Ku girmama sarki.”—1 BITRUS 2:17.
1, 2. Yaya mutane suke ɗaukan iko a yau? Me ya sa?
“YARA ba su da dama. Ba sa ma ba wa iyaye daraja,” in ji wata uwa da baƙin ciki. “Tuhumi Masu Mulki” in ji wata sitikar motoci. Waɗannan misalai ne biyu na yanayi da ka sani ya kasance a yau. Rashin ba wa iyaye, malamai, shugabannan aiki, da ma’aikatan gwamnati daraja ya cika ko’ina cikin duniya.
2 Wasu za su iya tada kafaɗansu su ce, ‘Haba, waɗanda suke da matsayi ba su cancanci in ba su daraja ba.’ A wasu lokatai, wannan gaskiya ne. Ko da yaushe muna jin labarai game da lalatattun ma’aikatan gwamnati, shugabannan aiki masu haɗama, malamai da ba su ƙware ba, da iyaye masu cin zali. Abin farin ciki, Kiristoci kaɗan ne suke ɗaukan waɗanda suke da iko cikin ikklisiya hakan nan.—Matta 24:45-47.
3, 4. Me ya sa ya kamata Kiristoci su yi biyayya ga waɗanda suke da matsayi?
3 “Ya wajaba” mu Kiristoci mu yi zaman biyayya da masu mulki. Manzo Bulus ya gargaɗi Kiristoci su “yi zaman biyayya da ikon masu mulki: gama babu wani iko sai na Allah; ikokin da ke akwai kuma sanyayyu ne na Allah.” (Romawa 13:1, 2, 5; 1 Bitrus 2:13-15) Bulus ya ba da dalili mai kyau na yin biyayya ga iko cikin iyali: ‘Ku mata, ku yi zaman biyayya da maza naku, abin da ya kamata ke nan cikin Ubangiji. Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da iyayenku cikin kowane abu, gama wannan abin yarda ne cikin Ubangiji.” (Kolossiyawa 3:18, 20) Dattiɓan ikklisiya sun cancanci mu ba su daraja domin ‘ruhu mai-tsarki ya sanya su masu kula, su yi kiwon ikklisiyar Allah.’ (Ayukan Manzanni 20:28) Domin darajar Jehovah shi ya sa muke girmama mutane masu mulki. Lallai, daraja ikon Jehovah shi ne farko ko da yaushe a rayuwarmu.—Ayukan Manzanni 5:29.
4 Sa maɗaukakin ikon Jehovah a zuci, bari mu bincika misalai na wasu da ba su yi biyayya ba ga waɗanda suke da matsayi da kuma waɗanda suka yi biyayya.
Raini Yana Kai wa ga Rashin Amincewa
5. Wane halin raini ne Michal ta nuna wa Dauda, kuma ga menene wannan ya kai?
5 Daga tarihin Sarki Dauda, za mu gan yadda Jehovah yake ɗaukan waɗanda suke raina matsayin da Allah ya bayar. Lokacin da Dauda ya kawo sunduƙi na alkawari zuwa Urushalima, matarsa Michal “ta ga Dauda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji; ta kuwa raina shi a zuciyarta.” Ya kamata da Michal ta gane cewa Dauda ba maigidanta ba ne kawai amma kuma sarki ne na ƙasar. Duk da haka, ta faɗi yadda take ji cikin raini: “Ina misalin darajar sarkin Isra’ila yau, da ya buɗe asirinsa yau a idanun kuyangin bayinsa, kamar yadda su ashararu su kan buɗe asirinsu babu kunya!” A sakamakon haka Michal ba ta haifi ’ya’ya ba.—2 Samuila 6:14-23.
6. Yaya Jehovah ya ɗauki raini na Korah ga waɗanda ya naɗa?
6 Misali da ya fi muni na rashin daraja shugabanci da Allah ya tsara shi ne na Korah. Da shi ke shi Koriya ne, ya more gatar yin hidima a mazaunin yin sujada na Jehovah! Duk da haka, ya ga laifin Musa da Haruna, shugabanne da Allah ya naɗa na Isra’ilawa. Korah ya haɗa kai da wasu hakimai na Isra’ila suka ce wa Musa da Haruna babu kunya babu tsoron Allah: “Dukan jama’a masu-tsarki ne, kowane ɗayansu, Ubangiji kuma yana tare da su; don menene fa ku ke ɗaukaka kanku gaba da taron jama’ar Ubangiji?” Yaya Jehovah ya ɗauki halin Korah da masu goyon bayansa? Da halinsu, ba su daraja Jehovah kansa ba. Bayan sun ga yadda ƙasa ta buɗe baki ta haɗiye dukan waɗanda suka goyi bayansu, wuta daga wurin Jehovah ta halaka Korah da hakimai 250.—Litafin Lissafi 16:1-3, 28-35.
7. “Mafifitan manzanni” suna da wani dalili ne su zargi ikon Bulus?
7 A cikin ikklisiyar Kiristoci a ƙarni na farko, akwai waɗanda suka raina ikon Allah. “Mafifitan manzanni” cikin ikklisiyar Korinthos sun raina Bulus. Sun zargi iya maganarsa, cewa: “Ainihin jikinsa rarrauna ne, bakinsa kuwa ba wani abu ba ne.” (2 Korinthiyawa 10:10; 11:5) Ko Bulus ya yi magana ƙwarai ko a’a, ya cancanci a ba shi daraja tun da shi ke manzo ne. Amma maganar Bulus ba wani abu ba ne da gaske? Jawabinsa ga jama’a da ke rubuce cikin Littafi Mai-Tsarki ya ba da tabbaci yadda maganarsa ke huɗubantar da mutane. Shi ya sa, a sakamakon gajeriyar magana da ya yi da Hirudus Agaribas na II, “masani ne . . . da matsaloli duka waɗanda su ke wurin Yahudawa,” Bulus ya sa sarkin har ya ce: “Da ƙanƙanuwar rinjayarwa kana so ka maishe ni Kirista”! (Ayukan Manzanni 13:15-43; 17:22-34; 26:1-28) Duk da haka, mafifitan manzanni a Korinthos sun zarge shi wai maganarsa ba wani abu ba ne! Yaya Jehovah ya ɗauki halinsu? A wani saƙo ga masu kula da ikklisiyar Afisus, Yesu Kristi ya yi magana mai kyau game da waɗanda suka ƙi waɗanda ‘ke ce da kansu manzanni, ba kuwa haka su ke ba,’ su ja hankalinsu.—Ru’ya ta Yohanna 2:2.
Girmamawa Duk da Ajizanci
8. Ta yaya Dauda ya nuna cewa ya daraja iko da Jehovah ya ba wa Saul?
8 Akwai misalai da yawa na waɗanda suka daraja waɗanda suke da iko cikin Littafi Mai-Tsarki, ko ma waɗannan ba su yi amfani mai kyau ba da matsayinsu. Dauda misali ne mai kyau na irin wannan. Sarki Saul wanda ya yi hidima ƙarƙashinsa ya yi kishin abin da Dauda ya cim ma kuma ya yi ƙoƙari ya kashe shi. (1 Samuila 18:8-12; 19:9-11; 23:26) Duk da haka, da ya sami zarafi ya kashe Saul, Dauda ya ce: “Shafaffe na Ubangiji ne kuwa, har da zan miƙa hannu a kansa, da shi ke shafaffe na Ubangiji ne shi.” (1 Samuila 24:3-6; 26:7-13) Dauda ya san cewa Saul yana da laifi, amma ya bar wa Jehovah ya yi masa hukunci. (1 Samuila 24:12, 15; 26:22-24) Bai yi baƙar magana ba game da ko kuma ga Saul.
9. (a) Yaya Dauda ya ji lokacin da Saul yake wulaƙanta shi? (b) Yaya muka sani cewa daraja da Dauda ya ba Saul ta gaskiya ce?
9 Dauda ya yi baƙin ciki ne yayin da ake wulaƙanta shi? “Gama . . . azzalumai kuma sun nemi raina,” Dauda ya yi kuka ga Jehovah. (Zabura 54:3) Ya gaya wa Jehovah zuciyarsa: “Ka cece ni daga hannun maƙiyana, ya Allahna . . . Masu-iko sun taru a bisa kaina: Ba domin kuskurena ba, ba kuwa domin zunubina ba, ya Ubangiji. Su kan yi gudu su shirya kansu ba domin laifina ba: Ka farka garin taimakona, ka duba kuma.” (Zabura 59:1-4) Ka taɓa jin hakanan—ba ka yi wa wanda yake da iko kome ba, duk da haka yana ba ka wahala? Dauda ya ci gaba da yi wa Saul biyayya. Da Saul ya mutu, maimakon yana farin ciki, Dauda ya shirya waƙar makoki: “Saul da Jonathan abin ƙauna ne abin ƙawa suna da rai, . . . suka fi gaggafa sauri, suka fi zaki ƙarfi. Ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka bisa Saul.” (2 Samuila 1:23, 24) Wannan misali ne mai kyau na tabbataciyar daraja game da shafaffe na Jehovah, ko da Saul ya yi wa Dauda laifi!
10. Wane misali mai kyau ne Bulus ya nuna na daraja iko da Allah ya ba wa hukumar mulki, kuma ga menene wannan ya kai?
10 A zamanin Kirista, muna da misalai na musamman na waɗanda suka daraja iko da Allah ya bayar. Alal misali, Bulus. Ya yi biyayya ga shawarwari na hukumar mulki ta ikklisiyar Kirista ta ƙarni na farko. A lokacin ziyarar Bulus ta ƙarshe zuwa Urushalima, hukumar mulki ta yi masa gargaɗi ya tsabtacce kansa don ya nuna wa sauran ba shi da ƙiyayya game da Dokar Musa. Da Bulus ya yi tunani cewa: ‘Waɗannan ’yan’uwa a dā sun gaya mini in bar Urushalima lokacin da ake nema a kashe ni. Yanzu suna so in nuna a fili cewa ina daraja Dokar Musa. Na riga na rubuta wasiƙa ga Galatiyawa na gaya masu su daina bin Dokar. Idan na je haikalin, wasu ba za su gane abin da na ke yi ba, za su yi tunani cewa na koma ina bin aji da suka yi kaciya ne.’ Amma, babu shakka Bulus bai yi tunani haka ba. Tun da yake babu zancen karya ƙa’idar Kirista a ciki, ya yi biyayya kuma ya yi amfani da gargaɗin hukumar mulki na ƙarni na farko. Domin wannan, taron ’yan banza na Yahudawa suka faɗa wa Bulus kuma aka cece shi, bayan haka ya yi shekara biyu cikin fursuna. A ƙarshe dai, abin da Allah yake so ne ya faru. Bulus ya yi shaida a gaban manyan ma’aikata a Kaisariya sai kuma gwamnati ta kai shi Roma ya yi shaida a gaban Kaisar kansa.—Ayukan Manzanni 9:26-30; 21:20-26; 23:11; 24:27; Galatiyawa 2:12; 4:9, 10.
Kana Ba da Girma?
11. Ta yaya za mu ba masu mulki girma?
11 Kana ba waɗanda suke da iko girma da ta dace? An ba Kiristoci umurni su “ba kowa hakinsa, . . . bangirma ga wanda ya isa bangirma.” Hakika, zaman biyayyanmu ga “masu mulki” ba kawai mu biya haraji ba amma ya haɗa da ba masu mulki girma ta wurin halayenmu da maganarmu. (Romawa 13:1-7) Idan ma’aikatan gwamnati da ba su da tausayi sun fuskance mu, yaya za mu yi? A Jihar Chiapas ta Mexico, masu mulki a wani yanki sun kwace gonakin iyalai 57 na Shaidun Jehovah domin waɗannan Kiristoci ba su yi wasu idodi na addinai ba. A taron da aka yi don a warware matsalar, Shaidun da suka sa tufafi masu tsabta, ko da yaushe suna magana da mutunci da kuma daraja. Shekara guda bayan haka, suka ci nasara. Halayensu ya sa masu lura su ba suka ba daraja ba kawai, har su ma sun so su zama Shaidun Jehovah su kansu!
12. Me ya sa yake da muhimmanci mace ta yi zaman ladabi da maigida mara bi?
12 Ta yaya za ka girmama iko da Allah ya bayar cikin iyali? Bayan ya tattauna misalin wahalar da Yesu ya sha, manzo Bitrus ya ce: ‘Hakanan, ku mata kuma, ku yi zaman biyayya ga maza naku; domin ko da akwai waɗansu da ba su yin biyayya da magana, su rinjayu banda magana saboda halayen matansu; suna lura da halayenku masu-tsabta tare da tsoro.’ (1 Bitrus 3:1, 2; Afisawa 5:22-24) Bitrus a nan ya nanata muhimmancin mata ta yi zaman biyayya da mijinta tare da ‘ladabi sosai,’ ko da yake wasu magidanta ba sa kome da zai sa a ba su irin darajar nan. Halin ladabi na mace zai iya canja zuciyar maigidanta mara bi.
13. Ta yaya mata za su girmama mazansu?
13 A cikin matanin waɗannan nassosi, Bitrus ya jawo hankalinmu ga misalin Saratu, wadda mijinta, Ibrahim misali ne na musamman na bangaskiya. (Romawa 4:16, 17; Galatiyawa 3:6-9; 1 Bitrus 3:6) Ya kamata mata su ba mazansu marasa bi daraja fiye da waɗanda mazansu masu bi ne? To, idan ba ki yarda da maigidanki ba game da wasu al’amura kuma fa? Yesu ya ba da wasu shawara da za a yi amfani da su a nan: “Dukan wanda ya tilasta maka tafiya mil ɗaya, tafi tare da shi har biyu.” (Matta 5:41) Ki na girmama maigidanki ta wurin tafiya tare da shi da abubuwa da yake so? Idan wannan yana da wuya sosai, ki faɗa yadda ki ke ji game da batun. Kada ki yi tsammanin ya san yadda ki ke ji. Amma idan za ki faɗa masa yadda ki ke ji, ki yi hakan da ladabi. Littafi Mai-Tsarki ya yi mana gargaɗi: “Bari zancenku kullum ya kasance tare da alheri, gyartace da gishiri, domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”—Kolossiyawa 4:6.
14. Menene girmama iyaye ta ƙunsa?
14 Yara, ku kuma fa? Kalmar Allah ta ba da umurni: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji: gama wannan daidai ne. Ka girmama ubanka da uwarka (ita ce doka ta fari tare da wa’adi).” (Afisawa 6:1-3) Ka lura cewa yin biyayya ga iyayenka tana da ma’ana ɗaya da “girmama ubanka da uwarka.” Kalmar Hellenanci da aka juya “girmama” na nufin “abin da ka daraja ƙwarai” ko kuma “abin da aka ba shi muhimmanci.” Don haka, yin biyayya ya bukaci fiye da bin dokokin iyaye da dole don wataƙila kana ganin ba su da amfani a gareka. Allah ya gaya maka ka ɗaukaka iyayenka sosai kuma ka ɗauki ja-gorarsu da muhimmanci.—Misalai 15:5.
15. Ta yaya yara za su ci gaba da girmama iyayensu ko ma suna jin cewa sun yi kuskure?
15 Idan iyayenka sun yi abin da zai sa ka rage yi masu biyayya, me za ka yi? Ka yi ƙoƙari ka gane abin da suke nufi. Ba su ba ne suka “haife ka” kuma su ka yi maka tanadi? (Misalai 23:22) Ba ƙaunarka ba ce ta motsa su? (Ibraniyawa 12:7-11) Ka yi magana da ladabi ga iyayenka, ka bayana cikin ruhun tawali’u yadda ka ke ji. Ko ma sun mayar yadda ba ka so, ka guje yi masu magana da raini. (Misalai 24:29) Ka tuna yadda Dauda ya ci gaba da ba Saul girma har lokacin da sarkin ya bijire daga bin gargaɗin Allah. Ka gaya wa Jehovah ya taimake ka ka kame kanka. Dauda ya ce: “Ku zazzage zuciyarku a gabansa: Allah mafaka ne a garemu.”—Zabura 62:8; Makoki 3:25-27.
Ka Girmama Waɗanda Suke Jagabanci
16. Menene za mu iya koya daga misalan malaman ƙarya da kuma mala’iku?
16 Ruhu mai tsarki ne ya naɗa dattiɓan ikklisiya, duk da haka ajizai ne kuma suna yin kuskure. (Zabura 130:3; Mai-Wa’azi 7:20; Ayukan Manzanni 20:28; Yaƙub 3:2) Saboda haka, wasu cikin ikklisiya ba za su gamsu da dattiɓan ba. Yaya ya kamata mu yi idan muna jin cewa ba a yi wani abu daidai ba a cikin ikklisiya, ko kuma dai kamar haka yake? Ka lura da bambanci tsakanin malaman ƙarya na ƙarni na farko da mala’iku: “Masu-ƙarfin hali ne, masu-taurin kai, [malaman ƙarya] ba su yi rawan jiki ba sa’anda suna yi ma maɗaukaka ƙire: ga fa mala’iku, ko da shi ke sun fi ƙarfi da iko, ba su kai sara ta ƙanƙanci gun Ubangiji a kansu ba.” (2 Bitrus 2:10-13) Yayin da malaman ƙarya suna bakar magana game da “maɗaukaka”—dattiɓai waɗanda suke da iko cikin ikklisiyar Kirista a ƙarni na farko—mala’ikun ba su yi bakar magana ba game da malaman ƙarya waɗanda suke haddasa rashin haɗin kai tsakanin ’yan’uwa. Mala’ikun da shi ke suna da matsayi mai fifiko da kuma azanci mai kyau na shari’a fiye da bil Adam, sun san abin da yake faruwa cikin ikklisiya. Duk da haka, ‘domin girmama Jehovah,’ sun bar masa shari’ar.—Ibraniyawa 2:6, 7; Yahuda 9.
17. Yaya bangaskiyarka ta shigo lokacin da ka ke bi da matsaloli inda kana ji dattiɓai ba su yi daidai ba?
17 Ko idan ma ba a yi wani abu yadda ya kamata ba, ba za mu kasance da bangaskiya cikin Yesu Kristi Shugaban ikklisiyar Kirista ba? Bai san abin da yake faruwa ba ne a tasa ikklisiya ta duniya duka? Bai kamata mu girmama hanyarsa ta bi da yanayi kuma mu fahimci cewa yana iya gudanar da al’amura? Hakika, ‘wanene mu da muke yi wa maƙwabcinmu shari’a?’ (Yaƙub 4:12; 1 Korinthiyawa 11:3; Kolossiyawa 1:18) Me ya sa ba za ka gaya wa Jehovah damuwarka cikin addu’a ba?
18, 19. Menene za ka yi idan kana jin wani dattijo ya yi kuskure?
18 Saboda ajizancin ’yan Adam, wahaloli da matsaloli sukan taso. Akwai lokutta da ƙila wani dattijo zai yi kuskure, ya sa wasu su damu. Yin abu da garaje a irin wannan lokaci ba zai canja yanayin ba. Sai dai ya ƙara matsalar kawai. Waɗanda suke da fahimi na ruhaniya za su jira Jehovah ya daidaita abubuwa kuma ya bayar da kowane horo da ake bukata a nasa lokaci da kuma nasa hanyar.—2 Timothawus 3:16; Ibraniyawa 12:7-11.
19 Yaya idan kana baƙin ciki game da wasu matsaloli? Maimakon ka gaya wa wasu cikin ikklisiya, me ya sa ba za ka je wurin dattiɓai cikin ladabi don taimako ba? Da biyayya, ka bayana yadda abin ya taɓa ka. Ko da yaushe ka kasance ‘mai-juyayi’ game da su, kuma ka ci gaba da yi musu biyayya yayin da ka ke gaya musu damuwarka. (1 Bitrus 3:8) Kada ka soma raini, amma ka dogara ga manyantaka nasu ta Kirista. Ka nuna godiya ga kowace ƙarfafa ta Nassi da suka ba ka. Kuma idan kamar ana bukatar a gyara wasu abubuwa, ka kasance da gaba gaɗi cewa Jehovah zai ja-gorance dattiɓai su yi abin da yake da kyau da kuma daidai.—Galatiyawa 6:10; 2 Tassalunikawa 3:13.
20. Menene za mu bincika a talifi na gaba?
20 Duk da haka, akwai wani fanni tukuna da za a bincika game da girmama da kuma yin biyayya ga waɗanda suke da iko. Bai kamata waɗanda suke da matsayin iko su daraja waɗanda suke ƙarƙashinsu ba? Bari mu bincika wannan a cikin talifi na gaba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wane kyakkyawan dalili muke da shi na girmama waɗanda suke da iko?
• Yaya Jehovah da Yesu suke ɗaukan waɗanda ba sa daraja iko da Allah ya bayar
• Wane misalai masu kyau muke da su na waɗanda suka girmama masu iko?
• Menene za mu iya yi idan wanda yake da iko bisa kanmu kamar ya yi kuskure?
[Hoto a shafi na 8]
Saratu ta girmama matsayin Ibrahim sosai kuma ta yi farin ciki
[Hoto a shafi na 9]
Michal ta ƙi ta girmama matsayin Dauda na shugaban iyali da kuma sarki
[Hoto a shafi na 11]
“Shafaffe na Ubangiji ne kuwa, har da zan miƙa hannu a kansa, da shi ke shafaffe na Ubangiji ne shi.”
[Hoto a shafi na 12]
Me ya sa ba za ka gaya wa Jehovah damuwarka ba cikin addu’a?