A Ina Za Ka Samu Kwanciyar Hankali?
Da akwai bambanci da yawa tsakanin lokacinmu da na Thoreau,
da aka ambata a talifi na farko. Bambanci mafi girma shi ne, da akwai isashen shawarwari a kan yadda za a samu kwanciyar hankali. Masana halin mutane da marubuta littattafai na taimako—har da waɗanda suke da sashen rubuta labarai cikin jaridu—suna ba da nasu ra’ayoyi. Shawarwarinsu suna iya yin amfani na ɗan lokaci; amma don a magance yanayin gaba ɗaya, ana bukatar matabbacin abu. Abin da mutane da aka ambata cikin talifi na farko suka gano ke nan.
ANTÔNIO, Marcos, Gerson, Vania, da Marcelo sun fito ne daga wurare dabam dabam, matsalolinsu kuma sun bambanta. Amma sun fuskanci abubuwa uku iri ɗaya. Na ɗaya, akwai lokacin da suke “marasa bege marasa-Allah cikin duniya.” (Afisawa 2:12) Na biyu, suna son kwanciyar hankali. Na uku kuma, dukansu sun sami kwanciyar hankali da suke so bayan sun yarda su yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah. Yayin da suke cin gaba, sun zo ga fahimtar cewa Allah yana sonsu. Hakika, kamar yadda Bulus ya gaya wa mutanen Atina na zamaninsa, Allah “ba shi da nisa da kowane ɗayanmu ba.” (Ayukan Manzanni 17:27) Kasance da wannan tabbaci babban dalili ne a samun kwanciyar hankali.
Me Ya Sa Babu Salama?
Littafi Mai-Tsarki ya ba da muhimman dalilai biyu na rashin salama a duniya—kwanciyar hankali ko salama tsakanin mutane. An ba da bayani na farko a Irmiya 10:23: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.” Mutum ba shi da hikima ko fahimi na yin sarautar kansa babu taimako kuma taimako mai amfanin gaske daga wurin Allah ne. Mutane da ba sa neman ja-gorancin Allah ba za su taɓa samu salama mai daɗewa ba. Dalili na biyu na rashin salama an samo a cikin kalmomin manzo Yohanna: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Idan ba tare da ja-gorancin Allah ba, ƙoƙarce-ƙoƙarce na mutane don samun salama ba za su yi nasara ba domin ayyukan wanda ba a ganinsa wanda ke wanzuwa—mai iko ƙwarai—“Shaiɗan,” mugun.
Domin waɗannan dalilai biyu—yawancin mutane ba sa biɗan ja-gorar Allah kuma Shaiɗan yana aiki sosai a duniya—zuriyar ’yan Adam suna cikin yanayi na baƙin ciki. Manzo Bulus ya kwatanta shi daidai da ya ce: “Dukan talikai suna nishi suna naƙuda tare da mu har yanzu.” (Romawa 8:22) Waye ba zai yarda da wannan furcin ba? A ƙasashe masu arziki da matalauta, matsalolin iyali, yin laifi, rashin gaskiya, jayayya, rashin cin gaban tattalin arziki, ƙiyayya na ƙabila da dangi, zalunci, ciwo, da wasu abubuwa da yawa, suna hana mutane samun kwanciyar hankali.
Inda Za a Sami Kwanciyar Hankali
Lokacin da Antônio, Marcos, Gerson, Vania, da Marcelo suka yi nazarin Kalmar Allah, Littafi Mai-Tsarki, sun koyi abubuwa da ya sake rayuwarsu. Wannan abu shi ne, sun koyi cewa wata rana yanayin duniya zai sake. Wannan ba wata fata ce kawai cewa abubuwa za su gyaru a ƙarshe ba. Matabbacin aminci ne na ƙwarai, cewa Allah yana da nufi ga ’yan Adam da a yanzu ma za mu iya amfana daga ƙudurin idan muka yi nufinsa. Sun yi amfani da abin da suka koya daga Littafi Mai-Tsarki, kuma sun yi gyara. Sun sami farin ciki da salama fiye da yadda suka yi tsammanin zai yiwu.
Antônio ya bar yin zanga-zanga. Ya sani cewa gyara da ake samu ta wannan hanyar ta ɗan lokaci ne kawai. Wannan babban ma’aikaci a dā ya koyi game da Mulkin Allah. Mulkin da miliyoyi suke addu’arsa ke nan yayin da suke maimaita Addu’ar Ubangiji (ko kuwa, na Ya Ubanmu) suna ce wa Allah: “Mulkin ka ya zo.” (Matta 6:10a, New International Version) Antônio ya koyi cewa Mulkin Allah gwamnati ce ta sama ta gaske da za ta kawo salama ta gaskiya ga ’yan Adam.
Marcos ya koyi ya yi amfani da gargaɗi na hikima na Littafi Mai-Tsarki wajen aure. Sakamakon haka shi ne, wannan ɗan siyasa na dā ya sake haɗa kai da matarsa. Shi ma yana sauraron lokacin da, jim kaɗan, da Mulkin Allah zai sake wannan tsarin duniya na haɗama da son kai zuwa mai kyau. Ya fi fahimtar furcin nan cikin Addu’ar Ubangiji da ya ce: “A yi nufinka a duniya yadda ake yi a sama.” (Matta 6:10b, NIV ) Idan aka yi nufin Allah a duniya, mutane za su more rayuwa da ba a taɓa yin irinta ba.
Gerson kuma fa? Ya bar yawace-yawace da sata. Wannan ɗan layi na dā yanzu ya sami ma’ana domin yana amfani da ƙarfinsa a taimaka wa wasu su sami kwanciyar hankali. Kamar yadda waɗannan labaran suka nuna, yin nazarin Littafi Mai-Tsarki da yin amfani da abin da ya ce yakan sake rayuwar mutum zuwa kyau.
Kwanciyar Hankali Cikin Duniya ta Wahala
Wanda yake da matsayi na musamman a cika nufin Allah Yesu Kristi ne, kuma yayin da mutane suka yi nazarin Littafi Mai-Tsarki da Shaidun Jehovah, suna koyan abu da yawa game da shi. A daren da aka haife shi, mala’iku sun yabi Allah: “Alhamdu ga Allah a cikin mafi ɗaukaka, a duniya kuma salama wurin mutanen da ya ke murna da su sarai.” (Luka 2:14) Yayin da Yesu ya yi girma, ya damu ne game da gyara rayuwan mutane. Ya fahimci yadda suke ji, ya nuna juyayi sosai ga waɗanda suke wahala da rashin lafiya. Kuma daidai da kalmomin mala’ikun, ya kawo kwanciyar hankali ga masu tawali’u. A ƙarshen hidimarsa, ya gaya wa almajiransa: “Salama ina bar maku; salamata ni ke ba ku: ba kamar yadda duniya ke bayarwa ni ni ke ba ku ba. Kada zuciyarku ta ɓace, kada ta ji tsoro kuma.”—Yohanna 14:27.
Ba kawai Yesu yana taimaka wa mutane ba. Ya gwada kansa da makiyayi kuma ya kwatanta mabiyansa masu tawali’u da tumaki yayin da ya ce: “Ni na zo domin su sami rai, su same shi a yalwace kuma. Ni ne makiyayi mai-kyau: makiyayi mai-kyau ya kan bada ransa domin tumaki.” (Yohanna 10:10, 11) Hakika, ba kamar shugabanne da yawa a yau da suke kula da kansu ne farko ba, Yesu ya ba da ransa domin tumakinsa.
Ta yaya za mu amfana daga abin da Yesu ya yi? Mutane da yawa sun san kalmomin nan: “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya bada Ɗansa, haifaffe shi kaɗai, domin dukan wanda yana bada gaskiya gareshi kada ya lalace, amma ya sami rai na har abada.” (Yohanna 3:16) Ba da gaskiya ga Yesu, na ɗaya yana bukatar saninsa da Ubansa, Jehovah. Sanin Allah da kuma Yesu Kristi zai iya kai mu ga dangantaka na kurkusa da Jehovah Allah da zai taimake mu samun kwanciyar hankali.
Yesu ya ce: “Tumakina suna jin muryata, na kuwa san su, suna biyona kuma: ina ba su rai na har abada; ba kuwa za su lalace ba daɗai, ba wanda za ya ƙwace su daga cikin hannuna kuma.” (Yohanna 10:27, 28) Lallai kalmomi ne na ta’azantarwa! Gaskiya, Yesu ya faɗe su kusan shekara dubu biyu da ya shige, amma ikonsu daidai yake da can baya. Kar ka manta cewa Yesu Kristi yana nan da rai yana aiki, yana sarauta yanzu Sarki ne wanda aka naɗa na Mulkin Allah na samaniya. Daidai da lokacin da yake duniya shekaru da yawa da suka shige, yana nan yana damuwa game da masu tawali’u da suke neman kwanciyar hankali. Ban da haka ma, shi ne har ila Makiyayin tumakinsa. Idan muka bi shi, zai taimake mu mu sami kwanciyar hankali, wanda ya haɗa da tabbacin fata na samun cikakken salama a nan gaba—wanda zai nufi ƙarshen nuna ƙarfi, yaƙi, da kuma aika laifi.
Taimako na gaske yana zuwa daga sani da kuma gaskata cewa Jehovah, ta wurin Yesu zai taimake mu. Ka tuna da Vania, wadda ƙarama ce da aka bar ta da nawaya mai yawa da take jin Allah ya manta da ita. Yanzu Vania ta sani cewa Allah bai yashe ta ba. Ta ce: “Na koyi cewa Allah yana nan da gaske da halaye masu kyau ƙwarai. Ƙaunarsa ta motsa shi ya aiko da Ɗansa zuwa duniya ya ba mu rai. Muhimmin abu ne sanin wannan.”
Marcelo ya yarda cewa dangantakarsa da Allah ta gaske ce. Wannan mai yawan son annashuwa dā ya ce: “Sau da yawa matasa ba sa sanin abin da za su yi, sai su ɓata kansu kawai. Wasu sukan shiga shan miyagun ƙwayoyi, yadda na yi. Ina fatar za a taimake wasu da yawa, kamar yadda aka taimake ni ta wajen koyar da ni gaskiya game da Allah da Ɗansa.”
Ta wurin nazarin Littafi Mai-Tsarki a hankali, Vania da Marcelo suka gina bangaskiya ta gaske ga Allah da aminci ga yadda yake a shirye ya taimake su su warware matsalolinsu. Idan muka yi abin da suka yi—nazarin Littafi Mai-Tsarki kuma muka yi abin da ya ce—za mu samu kwanciyar hankali, yadda suka samu. Lallai ƙarfafa na manzo Bulus ya aika a wajenmu: “Kada ku yi alhini cikin kowane abu; amma cikin kowane abu, ta wurin addu’a da roƙo tare da godiya, ku bar roƙe roƙenku su sanu ga Allah. Salama kuwa ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka, za ta tsare zukatanku da tunaninku cikin Kristi Yesu.”—Filibbiyawa 4:6, 7.
Neman Salama ta Gaske a Yau
Yesu Kristi yana ja-gorar mutane da suke bukatar gaskiya a kan hanyar da ke kai wa ga rai na har abada cikin duniya ta aljanna. Yayin da yana kai su zuwa bauta mai tsarki na Allah, suna samun salama da ke kama da wadda aka kwatanta cikin Littafi Mai-Tsarki: “Mutanena za su zauna a cikin mazauni na salama, a cikin tabbatattun mazaunai, da cikin mahutaye masu-lafiya.” (Ishaya 32:18) Wannan salama kuwa kaɗan ce kawai idan aka gwada da wadda za su more a nan gaba. Mu karanta: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama. Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.”—Zabura 37:11, 29.
To, za mu iya samun kwanciyar hankali a yau? I. Ban da haka ma, za mu tabbata cewa a nan gaba kaɗan, Allah zai albarkaci mutane masu biyayya da salama da ba a taɓa samu ba. To, me ya sa ba za ka biɗi cikin addu’a ya ba ka salamarsa ba? Idan kana da matsaloli da suke hana ka samun salama, ka yi addu’a yadda Dauda Sarki ya yi: “Wahalar zuciyata ta ƙaru: Ka fishe ni daga masifuna. Ka lura da ƙuncina da wahalata; Ka gafarta dukan zunubaina.” (Zabura 25:17, 18) Ka tabbata cewa Allah ya saurara ga irin addu’o’in nan. Yana miƙa hannunsa ya ba salama ga dukan waɗanda suke biɗanta da gaske. An tabbata mana cewa: “Ubangiji yana kusa da dukan waɗanda su ke kira bisa gareshi, ga dukan waɗanda su ke kira gareshi da gaskiya. Za ya biya muradin waɗanda ke tsoronsa; Za ya kuma ji kukansu, ya cece su.”—Zabura 145:18, 19.
[Bayanin da ke shafi na 5]
Mutum ba shi da hikima ko fahimi na yin sarautar kansa babu taimako kuma taimako mai amfanin gaske daga wurin Allah ne
[Bayanin da ke shafi na 6]
Sanin Allah da kuma Yesu Kristi zai iya kai mu ga dangantaka na kurkusa da Jehovah Allah da zai taimake mu samun kwanciyar hankali
[Hoto a shafi na 7]
Bin gargaɗin Littafi Mai-Tsarki yana kawo rayuwan iyali mai salama