Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 7/1 pp. 3-4
  • Za Ka Iya Samun Kwanciyar Hankali?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Za Ka Iya Samun Kwanciyar Hankali?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Sun Nemi Kwanciyar Hankali
  • A Ina Za Ka Samu Kwanciyar Hankali?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ta Yaya Za Mu Zama Masu Salama?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Ka Yi Koyi da Yesu Don Ka Kasance da Kwanciyar Rai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 7/1 pp. 3-4

Za Ka Iya Samun Kwanciyar Hankali?

A dā can a shekara ta 1854, mawallafi na Amirka Henry Thoreau ya rubuta: “Yawancin mutane suna fid da rai wajen rayuwa.”

Lallai a kwanakinsa, yawancin mutane ba su more kwanciyar hankali ba. Amma, wannan kusan shekara 150 ne da ya shige. Abubuwa sun bambanta ne a yau? Ko dai har yanzu kalmomin Thoreau suna cika? Kai kuma fa? Ka samu isashen kwanciyar hankali? Ko kuma dai ba ka da kwanciyar rai, ba ka da tabbaci game da nan gaba, kamar yadda Thoreau ya ce, ‘a hankali kana fid da rai’?

ABIN baƙin ciki kuwa, da akwai abubuwa da yawa a duniya da ke hana mutane kwanciyar hankali. Bari mu ambata kalilan kawai cikinsu. A ƙasashe da yawa rashin aiki da rashin kuɗi yana jawo talauci da fid da rai wajen tattalin arziki. A wasu ƙasashe yawanci suna ɓata rayuwarsu a neman arziki da abin duniya. Amma, sau da yawa rayuwar gasa tana jawo ɗawainiya, ba salama ba. Ciwo, yaƙi, yin laifi, rashin gaskiya, da kuma zalunci suna hana mutane salama.

Sun Nemi Kwanciyar Hankali

Mutane da yawa ba sa son bin duniya cikin halin da take a yanzu. Antônioa babban ma’aikaci ne a São Paulo, Brazil. Da fatar zai gyara yanayin rayuwa, ya shiga yin zanga-zanga, amma bai ba shi kwanciyar hankali ba.

Wasu suna jin cewa aure zai iya ba su kwanciyar rai a rayuwansu, amma sun yi kuskure. Marcos, wani ɗan kasuwa ne mai samu. Ya dulmiya cikin siyasa ya zama galadiman wani birni mai ma’aikata. Amma, iyalinsa ta sha ƙyaliya. Lokacin da yaransa suka fice daga gida, shi da matarsa suka rabu don ba sa jituwa da juna.

Gerson, wani ɗan layi a Salvador, Brazil, yana son ya shiga wani haɗari. Yana tafiya daga birni zuwa birni tare da direbobin manyan motoci. Ba da daɗewa ba, sai ya fara shan miyagun ƙwayoyi, ya fara fashi don ya biya wa kansa bukata. Sau da yawa ’yan sanda suna kama shi. Amma, duk da zafin halinsa, da nuna ƙarfin, Gerson yana so ya sami kwanciyar hankali. Shin zai iya samu kuwa?

Vania tana ƙarama lokacin da mamarta ta mutu, Vania ta soma kula da gida, da kuma ’yar’uwarta da take rashin lafiya. Vania tana tafiya coci amma ta ga kamar Allah ya yashe ta. Lallai ba ta da kwanciyar hankali.

Ga Marcelo kuma. Abin da Marcelo yake so kawai shi ne annashuwa. Yana son ya yi ta biki da sauran matasa—su yi rawa, su sha giya, su sha miyagun ƙwayoyi. Wata rana suka yi faɗā ya ji wa ɗayan saurayin rauni. Bayan haka, ya yi baƙin cikin abin da ya yi, sai ya yi addu’a don taimako wajen Allah. Shi ma yana son kwanciyar hankali.

Waɗannan labarai sun nuna wasu yanayi da suke tada hankali. Akwai wata hanya ce da babban ma’aikacin nan, ɗan siyasan, ɗan layi, yarinya mai yawan nawaya, da kuma mai son biki za su sami kwanciyar hankali da suke nema? Abin da ya faru da su ya koya mana wani abu kuwa? Amsar tambayoyi nan biyu, i ne, yadda za mu gani a talifi na gaba.

[Hasiya]

a An sake wasu sunayen.

[Hoto a shafi na 3]

Kana son kwanciyar hankali?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba