Za a halaka dukan makaman yaƙi
Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
Za a sake zaman lafiya a duniya kuwa?
Me za ka ce?
E
A’a
Wataƙila
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
A Mulkin Allah, Yesu zai kawo “salama mai-yawa, har sai wata ya faɗi,” wato har abada.—Zabura 72:7.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
Za a halaka masu mugunta, hakan zai sa masu adalci “su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.”—Zabura 37:10, 11.
Allah zai sa a daina yin yaƙi a dukan duniya.—Zabura 46:8, 9.
Zai yiwu a kasance da kwanciyar hankali yanzu kuwa?
Wasu sun yi imani cewa . . .ba zai yiwu a kasance da kwanciyar hankali ba idan har an ci gaba da yin rashin adalci a duniya. Mene ne ra’ayinka?
Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce
Ko a yanzu ma, waɗanda suke yin nufin Allah za su iya kasancewa da ‘salama ta Allah, wadda ta fi gaban ganewa duka.’—Filibiyawa 4:6, 7.
Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?
Allah ya yi alkawari cewa zai cire dukan rashin adalci da wahala, kuma ya “sabonta dukan abu.”—Ru’ya ta Yohanna 21:4, 5.
Za mu kasance da kwanciyar hankali idan muka “ƙulla dangantaka da Allah.”—Matta 5:3, New World Translation.