Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • wp17 Na 1 p. 16
  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Allah yana jawo wahala kuwa?
  • Wahala za ta taɓa ƙarewa kuwa?
  • Me Ya Sa Allah Ya Kyale Wahala?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Yaya Allah yake ji game da wahalar da kake sha?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2018
  • Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
    Wahala Za Ta Ƙare Kuwa?
  • Me Ya Sa Muke Shan Wahala Sosai?
    Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Wa’azi)—2017
wp17 Na 1 p. 16
Wata mata ta rungumi yaronta a lokacin yaki

Shin Allah ne yake jawo wahala a duniya?

Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Allah yana jawo wahala kuwa?

Me za ka ce?

  • E

  • A’a

  • Wataƙila

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

“Sam, Allah ba mai aikata mugunta ba ne, a wurin Mai Iko Duka ba kuskure.” (Ayuba 34:​10, Littafi Mai Tsarki) Ba Allah ba ne yake jawo mugunta da wahalar da ke duniyar nan ba.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • “Sarkin duniya,” wato Shaiɗan Iblis ne yake jawo wahala.​—Yohanna 14:30.

  • Ƙari ga haka, wahala da mugunta suna faruwa sanadiyyar zaɓi marar kyau da mutane suke yi.​—Yaƙub 1:​14, 15.

Wahala za ta taɓa ƙarewa kuwa?

Wasu sun yi imani cewa ’yan Adam za su iya cire wahala idan sun haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yin hakan. Wasu kuma sun ce da kyar duniyar nan ta gyaru. Mene ne ra’ayinka?

Abin da Littafi Mai Tsarki ya ce

Allah zai cire shan wahala. “Mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​—Ru’ya ta Yohanna 21:​3, 4.

Me kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

  • Allah zai yi amfani da Yesu wajen cire wahalar da Shaiɗan ya jawo.​—1 Yohanna 3:8.

  • Masu adalci za su rayu a duniya cikin salama har abada.​—⁠Zabura 37:​9-11, 29.

Don sanin dalilin da ya sa Allah bai cire wahala ba tukun, ka duba babi na 11 na littafin nan Me Za Mu Koya Daga Littafi Mai Tsarki?, Shaidun Jehobah ne suka wallafa shi

Za ka kuma iya samunsa a dandalin www.pr418.com/⁠ha

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba