Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 9/1 pp. 21-26
  • Ka Kasance Da Halin Jira!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance Da Halin Jira!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance da Halin Jira
  • Kasance da Ra’ayi na Gaske
  • Jira—Dalilin ne na Baƙin Ciki ko Kuma na Farin Ciki?
  • Ka Kasance Da Irin Halin Almasihu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Zama Masu Hakuri Zai Taimaka Mana Mu Jimre
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Ka Yi Farin Ciki Yayin da Kake Jiran Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Kana Shirye Ka Jira Jehobah da Hakuri?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 9/1 pp. 21-26

Ka Kasance Da Halin Jira!

“Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni.”—MIKA 7:7.

1, 2. (a) Ta yaya hali mara kyau ya yi wa Isra’ilawa lahani a cikin daji? (b) Me zai iya faruwa da Kirista wanda bai koyi hali mai kyau ba?

ABUBUWA da yawa a rayuwa yadda aka ɗauke su ko da kyau ko da muni, ya dangana ne bisa halinmu. Lokacin da Isra’ilawa suke cikin daji, an yi musu tanadin manna ta wajen mu’ujiza. Da sun duba busassun wuraren da suka kewaye su da sun yi wa Jehovah godiya sosai don tanadin abinci da ya yi musu. Da wannan zai nuna hali mai kyau. Maimakon haka, suka tuna da abinci iri iri masu yawa na Masar kuma suka yi gunaguni cewa manna ba ta da daɗi. Lalle mummunan hali ne, mara kyau!—Littafin Ƙidaya 11:4-6.

2 Haka halin Kirista a yau zai iya sa abubuwa su bayyana da kyau ko kuma da muni. Idan ba tare da hali mai kyau ba, zai yi sauƙi Kirista ya yi hasarar farin cikinsa, kuma wannan zai zama abu ne mai tsanani, domin kamar yadda Nehemiya ya ce: “Farin cikin da Ubangiji ya ba [mu] shi ne ƙarfin[mu].” (Nehemiya 8:10) Hali mai kyau, na farin ciki yana taimaka mana mu zama da ƙarfi kuma mu gabatar da salama da haɗin kai a cikin iklisiya.—Romawa 15:13; Filibiyawa 1:25.

3. Yaya halin kirki ya taimaki Irmiya cikin lokatai masu wuya?

3 Duk da lokatai masu wuya da ya kasance ciki, Irmiya ya nuna hali mai kyau. Har lokacin da ya shaida bala’i na faɗiwar Urushalima a shekara ta 607 K.Z., ya iya ganin abubuwa masu kyau. Jehovah ba zai manta da Isra’ila ba, kuma al’ummar za ta tsira. Irmiya ya rubuta cikin littafin Makoki: “Ƙaunar Ubangiji ba ta ƙarewa, haka kuma jiyejiyanƙansa ba su ƙarewa. Su sababbi ne kowace safiya, amincinka kuma mai girma ne.” (Makoki 3:22, 23) Duk cikin tarihi, bayin Allah a cikin yanayi mafi muni sun biɗi su kasance da hali mai kyau, har na farin ciki.—2 Korantiyawa 7:4; 1 Tasalonikawa 1:6; Yakubu 1:2.

4. Wane hali ne Yesu ya kasance da shi, kuma ta yaya ya taimake shi?

4 Shekara 600 bayan Irmiya, Yesu ya jure domin halinsa mai kyau. Mun karanta: “Domin farin cikin da aka sa gaban [Yesu] ya daure wa [azaba a kan gungume], bai mai da shi wani abin kunya ba, yanzu kuma a zaune yake dama ga kursiyin Allah.” (Ibraniyawa 12:2) Ko da wace irin hamayya da tsanani da Yesu zai fuskanta—har azaba a kan gungume—ya sa zuciyarsa a kan “farin cikin da aka sa gabansa.” Farin cikin nan gatar kunita ikon mallaka na Jehovah da kuma tsarkake sunansa ne da begen kawo albarka mai yawa ga mutane masu biyayya a nan gaba.

Ka Kasance da Halin Jira

5. Wane yanayi ne halin jira zai taimake mu mu ɗauki abubuwa daidai wa daida?

5 Idan mun koyi hali irin na Yesu, ba za mu yi rashin farin ciki na Jehovah ko idan abubuwa ba sa tafiya daidai yadda muke so kuma a lokacin da muka zata. Annabi Mika ya ce: “Amma ni zan kafa ido ga Ubangiji, zan jira ceton Allahna, Allahna zai ji ni.” (Mika 7:7; Makoki 3:21) Mu ma za mu nuna halin jira. Ta yaya? A hanyoyi da yawa. Abu ɗaya shi ne, ƙila za mu ga cewa wani ɗan’uwa da yake da iko ya yi kuskure kuma mu ga ana bukatar gyara na nan da nan. Halin jira zai taimake mu mu lura, ‘Shin da gaske ne ya yi kuskure, ko dai ni nake ganin haka? Idan kuskure ya yi, ba zai yiwu cewa wataƙila Jehovah yana ƙyale abubuwa su bayyana ba ne domin ya san ko mutumin zai yi gyara don haka ba za a bukaci wani tsautawa ba?’

6. Yaya halin jira zai taimake wani wanda yake fama da tasa matsala?

6 Ana bukatar halin jira yayin da mun damu da wata matsala ta kanmu ko muna fama da wani kumammanci. A ce mun roƙi taimakon Jehovah kuma matsalar ta ci gaba. To, me za mu yi? Za mu ci gaba da yin duk abin da za mu iya don mu warware matsalar kuma mu kasance da bangaskiya cikin kalmomin Yesu: “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.” (Luka 11:9) Ka ci gaba da yin addu’a kuma ka zuba ido ga Jehovah. A lokacin da ya dace kuma a tasa hanyar, Jehovah zai amsa addu’o’inka.—1 Tasalonikawa 5:17.

7. A wace hanya ce halin jira zai taimaka mana a gyara ra’ayinmu na ci gaba da ƙara fahimtar Littafi Mai Tsarki?

7 Yayin da annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ke cika, muna ƙara fahimtar Nassosi. Amma, a wasu lokatai za mu iya tunanin cewa ya kamata a yi wani abu da muke ganin ana jinkiri da shi. Idan bai zo lokacin da muka fi so ba, za mu iya jira? Ka tuna cewa Jehovah ya ga ya dace ya bayyana “asirin Almasihu” da kaɗan kaɗan a cikin shekara 4,000. (Afisawa 3:3-6) Muna da wani dalilin da zai sa mu yi rashin haƙuri ne? Muna shakkar cewa an naɗa ‘amintaccen bawan nan mai hikima’ ya ba wa mutanen Jehovah “abincinsu a kan kari?” (Matiyu 24:45, tafiyar tsutsa tamu ce.) Me ya sa za mu hana wa kanmu farin ciki na ibada don kawai ba dukan abu aka fahimta sosai ba? Ka tuna, Jehovah ne yake da shawara ko yaushe kuma ta yaya zai bayyana ‘asirin al’amuransa.’—Amos 3:7.

8. Ta yaya haƙurin Jehovah ya zama da amfani ga mutane da yawa?

8 Wasu suna iya karaya domin suna jin cewa bayan shekaru da yawa na amintaccen hidima, ƙila ba za su ga “babbar ranar nan mai bantsoro ta Ubangiji” a lokacin da suke da rai ba. (Yowel 2:30, 31) Har ila, za su iya samun ƙarfafa idan suka lura da wasu fannoni masu kyau. Bitrus ya yi gargaɗi: “Ka ɗauki haƙurin Ubangijinmu ceto ne.” (2 Bitrus 3:15) Haƙurin Jehovah ya sa miliyoyi masu zuciyar kirki su koyi gaskiya. Wannan ba da girma yake ba? Ƙari ga haka, idan Jehovah ya ci gaba da haƙuri, za mu sami ƙarin lokaci don “[mu] yi ta yin aikin ceton nan na[mu] da halin bangirma tare da matsananciyar kula.”—Filibiyawa 2:12; 2 Bitrus 3:11, 12.

9. Idan muna da iyaka game da abin da za mu iya yi a hidimar Jehovah, yaya halin jira zai iya taimakonmu mu jimre wa yanayin?

9 Halin jira yana taimakonmu kada mu karaya lokacin da hamayya, ciwo, da tsufa, ko kuma wasu matsaloli suka hana hidimarmu ta Mulki. Jehovah yana so mu bauta masa da zuciya ɗaya. (Romawa 12:1) Amma, Ɗan Allah, wanda “yakan ji tausayin gajiyayyu da matalauta,” ba ya biɗan abin da ba za mu iya bayarwa ba; haka ma Jehovah kansa. (Zabura 72:13) Domin wannan, ana ƙarfafa mu mu yi iyakacin abin da za mu iya, muna jira cikin haƙuri har sai yanayin ya canja—a cikin wannan tsarin abubuwa ko a cikin na mai zuwa. Ka tuna: “Allah ba marar adalci ba ne, har da zai ƙi kula da aikinku, da kuma ƙaunar sunansa da kuka yi wajen yi wa tsarkaka hidima, har yanzu ma kuna yi.”—Ibraniyawa 6:10.

10. Wane irin hali ne mutum zai iya guje wa ta wurin kasancewa da halin jira? Ka yi bayani.

10 Halin jira har ila yana taimakonmu mu guje wa girman kai. Wasu sun zama ’yan ridda saboda rashin haƙuri. Wataƙila sun ji cewa da akwai bukatar gyara, ƙila cikin fahimtar Littafi Mai Tsarki ko kuma cikin al’amuran ƙungiyar. Duk da haka ba su fahimci cewa ruhun Jehovah ne yake motsa amintaccen bawa mai hikima ya yi gyare-gyare a Nasa lokaci, ba lokacin da muke jin yake daidai ba. Kuma kowace gyara tilas ce ta yi daidai da nufin Jehovah, ba namu ra’ayoyi ba. ’Yan ridda sun ƙyale girman kai ya toshe musu tunani ya kuma sa suka yi tuntuɓe. Amma da sun bi halin Kristi, da sun riƙe farin cikinsu kuma sun kasance har ila tsakanin mutanen Jehovah.—Filibiyawa 2:5-8.

11. Ta yaya za mu yi amfani mai kyau da lokaci da muke jira, a bin misalan su wa?

11 Hakika, riƙe halin jira ba ya nufin mutum ya zama rago ko kuma maƙyuyaci. Muna da abubuwan yi. Alal misali, ya kamata mu shagala cikin nazarin Littafi Mai Tsarki na kanmu kuma mu nuna irin himmar nan ga abubuwa na ruhaniya yadda annabawa masu aminci har da mala’iku suka nuna. Da yake magana game da himmar nan, Bitrus ya ce: “Annabawan da suka yi annabci a kan alherin da zai zama naku, sun tsananta bin diddigi a kan wannan ceto . . . Su ne kuwa abubuwan da mala’iku ke ɗokin gani.” (1 Bitrus 1:10-12) Ba nazari na kanmu kawai yake da muhimmanci ba amma har da halartan taro kullum da kuma addu’a ma. (Yakubu 4:8) Waɗanda suke nuna sun damu game da bukatarsu na ruhaniya ta wurin cin abinci na ruhaniya a kai a kai da yin tarayya da ’yan’uwa Kirista suna nuna cewa sun koyi hali irin na Kristi.—Matiyu 5:3.

Kasance da Ra’ayi na Gaske

12. (a) Wane ’yanci ne Adamu da Hauwa’u suka biɗa? (b) Me ya zama sakamakon bin Adamu da Hauwa’u da mutane suka yi?

12 Lokacin da Allah ya halicci mata da miji na farko, ya bar wa kansa ikon kafa mizanai na abin da ke daidai da wanda ba daidai ba. (Farawa 2:16, 17) Adamu da Hauwa’u sun so ’yancin kai daga wajen Allah, sakamakon wannan shi ne abin da muke gani a duniya da ta kewaye mu a yau. Manzo Bulus ya ce: “Zunubi ya shigo duniya ta dalilin mutum ɗaya, zunubi kuwa shi ya jawo mutuwa, ta haka mutuwa ta zama gadō ga kowa, don kowa ya yi zunubi.” (Romawa 5:12) Tarihin ’yan Adam na shekara dubu shida tun lokacin Adamu ya tabbatar da gaskiyar kalmomin Irmiya: “Ya Ubangiji, na sani al’amuran mutum ba a hannunsa suke ba, ba mutum ne ke kiyaye takawarsa ba.” (Irmiya 10:23) Fahimtar cewa kalmomin Irmiya gaskiya ne ba ragonci ba ne. Hakika, ya bayyana a duk ƙarnuka masu tsawo da “waɗansu sukan sami mulki, waɗansu kuwa su sha wuya a ƙarƙashinsu” domin mutane sun yi mulki da ’yanci daga Allah.—Mai Hadishi 8:9.

13. Wane ra’ayi mai kyau ne Shaidun Jehovah suke da shi na abin da ’yan Adam za su iya cim ma?

13 Game da yanayin mutane, Shaidun Jehovah sun san cewa da akwai iyaka ga abin da za a iya cim ma cikin tsarin abubuwa na yanzu. Hali mai kyau zai taimake mu riƙe farin cikinmu, amma ba shi ne maganin kome ba. A farkon shekarun 1950, wani limamin Amirka ya buga wani littafi da aka fi saya da aka kira The Power of Positive Thinking. Littafin ya nuna cewa za a iya warware matsaloli da yawa ta wurin hali mai kyau. Lallai tunani mai kyau abin sha’awa ne. Amma abin da ya faru ya nuna cewa ilimi, fasaha, dukiya, da wasu abubuwa da yawa sukan hana mu cim ma abin da za mu so mu yi. A duniya duka, matsaloli sun yi wa ’yan Adam yawa ainun da ba za su iya magance su ba—ko yaya kyan tunaninsu!

14. Shaidun Jehovah ba su da hali mai kyau ne? Ka yi bayani.

14 Domin yadda suka fahimci abubuwan nan sosai, wasu lokatai ana tuhumar Shaidun Jehovah cewa ba su da hali mai kyau. Maimako haka, suna ɗokinta a gaya wa mutane game da Wanda shi kaɗai ne zai iya gyara ta dindindin a rayuwar mutane. A wannan ma suna yin koyi da halin Kristi. (Romawa 15:2) Kuma sun shagala a taimakon mutane su sami dangantaka mai kyau da Allah. Sun sani cewa a ƙarshe, wannan zai cim ma abu mafi kyau.—Matiyu 28:19, 20; 1 Timoti 4:16.

15. Ta yaya ne aikin Shaidun Jehovah yake gyara mutane?

15 Shaidun Jehovah ba sa banza da matsalolin jama’a—musamman ayyukan waɗanda suka saɓa wa Nassosi—da suke gani ya kewaye su. Kafin mutum da yake da marmari ya zama Shaidan Jehovah, zai yi canje-canje, sau da yawa dole ya kawar da munanan halaye da suke baƙanta wa Allah rai. (1 Korantiyawa 6:9-11) Da haka, Shaidun Jehovah sun taimake waɗanda suke da zuciyar kirki su daina maye, su bar shan mugun ƙwayoyi, su daina lalata, da kuma yin caca. Waɗanda aka sabonta su sun koyi su yi wa iyalinsu tanadi a hanya mai kyau kuma na gaskiya. (1 Timoti 5:8) Yayin da aka taimaki mutane da kuma iyalai haka, matsaloli za su ragu tsakanin jama’a—ba za a ga masu shan mugun ƙwayoyi da yawa ba, da nuna ƙarfi cikin iyali, da sauransu. Da yake su kansu ma masu bin doka ne ta wurin taimakon wasu su canja rayuwarsu don ya yi kyau, Shaidun Jehovah suna rage wahalar gwamnati waɗanda aikinsu ne su warware matsalolin jama’a.

16. Me ya sa Shaidun Jehovah ba sa sa hannu cikin hanyoyin gyara na duniya?

16 Saboda haka, za a ce Shaidun Jehovah sun canja yanayin lalata na duniyar nan ne? To, a shekaru goma da sun shige, adadin Shaidu masu aiki ya ƙaru daga 3,800,000 kaɗan babu zuwa kusan 6,000,000. Ƙaruwa ke nan na kusan 2,200,000, yawancinsu sun bar ayyukansu marasa adalci yayin da suka zama Kirista. Rayuka da yawa sun gyaru! Duk da haka, wannan adadin kaɗan ne kawai idan aka gwada da ƙaruwar yawan jama’a a duniya a lokaci ɗaya—sun kai 875,000,000! Shaidun Jehovah suna ɗaukansa tushin samun farin ciki su taimake mutane masu zuciyar kirki, ko da sun sani cewa kalilan ne daga cikin ’yan Adam za su bi hanyar samun rai. (Matiyu 7:13, 14) Yayin da Shaidun suke jira canje-canje mai kyau a dukan duniya wanda Allah ne kaɗai zai iya yi, ba sa sa hannu cikin hanyoyin gyara na duniya, waɗanda sau da yawa sukan fara da nufi mai kyau amma su ƙare cikin ruɗani ko kuma faɗā.—2 Bitrus 3:13.

17. Menene Yesu ya yi don ya taimake waɗanda suke tare da shi, amma menene bai yi ba?

17 A bin tafarkin nan, Shaidun Jehovah suna nuna tabbacin da suke da shi cikin Jehovah wanda Yesu ya kasance da shi yayin da yake duniya. Can baya cikin ƙarni na farko, Yesu ya yi mu’ujizar warkarwa. (Luka 6:17-19) Har ya ta da matattu. (Luka 7:11-15; 8:49-56) Amma bai kawar da matsalar ciwo ko kuma magabciya mutuwa ba. Ya sani cewa lokacin Allah domin wannan bai kai ba tukuna. Da iyawarsa mai girma na kamili lalle da Yesu ya yi aiki sosai don ya warware matsalolin siyasa da na jama’a. Kamar dai waɗanda suke a lokacin sun so ya yi amfani da iko ya yi wannan, amma Yesu ya ƙi. Mun karanta: “Da jama’a suka ga mu’ujizar da ya yi, suka ce, ‘Lalle, wannan shi ne annabin nan mai zuwa duniya!’ Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su ɗauke shi ƙarfi da yaji su naɗa shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen, shi kaɗai.”—Yahaya 6:14, 15.

18. (a) Ta yaya Yesu ya nuna halin jira kullayaumi? (b) Ta yaya aikin Yesu ya canja tun a shekara ta 1914?

18 Yesu ya ƙi ya sa hannu cikin siyasa ko kuma aiki na taimakon jama’ar ƙasa kawai domin ya sani cewa lokacin da zai yi amfani da ikon sarauta don ya tafiyar da ayyukan warkarwa ga kowa a ko’ina bai kai ba tukuna. Har bayan ya hau zuwa rayuwa mara mutuwa na ruhu a cikin sama, ya nuna yarda ya jira lokaci na Allah kafin ya fara aiki. (Zabura 110:1; Ayyukan Manzanni 2:34, 35) Amma, tun da aka naɗa shi Sarki na Mulkin Allah a 1914, yana aiki don “yana mai nasara domin ya ƙara cin nasara.” (Wahayin Yahaya 6:2; 12:10) Muna godiya sosai da muka miƙa kai ga sarautarsa, ko da wasu da wai su Kiristoci ne sun zaɓi su kasance cikin jahilci game da koyarwar Littafi Mai Tsarki na Mulkin!

Jira—Dalilin ne na Baƙin Ciki ko Kuma na Farin Ciki?

19. Yaushe ne jira yake sa “zuciya ta karai,” kuma yaushe yake abin farin ciki?

19 Sulemanu ya sani cewa jira yakan sa mutum baƙin ciki. Ya rubuta: “Idan ba bege, sai zuciya ta karai.” (Karin Magana 13:12) Hakika, idan mutum yana da bege da ba tabbas ba ne, zuciya ta karai don rashin cika. Amma jiran wasu abubuwa na farin ciki—wataƙila aure, haihuwa, ko kuma sake saduwa da mutane da muke ƙauna—zai sa mu cika da farin ciki da daɗewa kafin ranar. Farin cikin zai ƙaru idan muka yi amfani da lokacin da muke jiran da kyau, muka yi shiri don bikin.

20. (a) Waɗanne aukuwa na mamaki muke jira mu gani? (b) Ta yaya za mu iya samun farin ciki yayin da muke jira nufe-nufen Jehovah su cika?

20 Idan muna da cikakken tabbaci cewa abin da muke zato zai zo—ko idan ba mu san ko yaushe zai cika ba—lokacin jiran ba zai sa “zuciya ta karai” ba. Amintattun masu bauta wa Allah sun sani cewa Sarautar Kristi na Shekara Duba ta kusa. Suna da tabbaci cewa za su ga ƙarshen mutuwa da cuta. Da zato na ƙwarai suna jiran lokaci da za su yi maraba wa biliyoyi daga matattu, har da ƙaunatattunsu da suka mutu. (Wahayin Yahaya 20:1-3, 6; 21:3, 4) A cikin wannan lokaci na lalacin ƙasa, za su yi tsammanin ganin Aljanna da aka kafa a duniya. (Ishaya 35:1, 2, 7) Hakika hikima ce a yi amfani da lokacin jira da kyau, “kullum kuna himantuwa ga aikin Ubangiji”! (1 Korantiyawa 15:58) Ka ci gaba da cin abinci na ruhaniya. Ka gina dangantaka na kurkusa sosai da Jehovah. Ka biɗi wasu da zukatansu ya motsu su bauta wa Jehovah. Ka ƙarfafa ’yan’uwa masu bi. Ka yi amfani sosai da duk lokaci da Jehovah har ila ya bari. Da haka, jiran Jehovah ba zai taɓa sa ‘zuciyarka ta karai’ ba. Maimako, zai sa ka yi farin ciki!

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Ta yaya Yesu ya nuna halin jira?

• A waɗanne yanayi ne Kiristoci suke bukatar halin jira?

• Me ya sa Shaidun Jehovah suke da niyyar su jira Jehovah?

• Ta yaya za a iya mai da jiran Jehovah ya zama dalilin farin ciki?

[Hotuna a shafi na 22]

Yesu ya jimre don farin ciki da ke gabansa

[Hoto a shafi na 23]

Har bayan shekaru da yawa na hidima, za mu iya riƙe farin cikinmu

[Hotuna a shafi na 25]

Miliyoyi sun gyara rayukansu ta wurin zama Shaidun Jehovah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba