Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 10/1 pp. 26-31
  • Ku Yi Matuƙar Amfani Da Lokaci Don Karatu Da Nazari

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Yi Matuƙar Amfani Da Lokaci Don Karatu Da Nazari
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Samun Lokaci Domin Karatu da Kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Dole Mu Tsara Abubuwa da Suka Fi Muhimmanci
  • Yadda Wasu Suka Ba da Lokaci Domin Nazari
  • ‘Abinci a Kan Kari’
  • Ka Gina Tsarin Cin Abinci Mai Kyau
  • Amfani na Ruhaniya Daga Karatu da Yin Nazari
  • Karatun Littafi Mai Tsarki—Mai Amfani Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Yadda Za Ka Amfana Daga Karanta Littafi Mai Tsarki
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Koya wa Yaranka Su So Yin Karatu da Kuma Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ka Riƙe Kalmar Allah Gam
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 10/1 pp. 26-31

Ku Yi Matuƙar Amfani Da Lokaci Don Karatu Da Nazari

“Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne.”—AFISAWA 5:16.

1. Me ya sa hikima ce mu tsara lokacinmu, kuma menene yadda muke amfani da lokacinmu zai nuna game da mu?

AN CE “zaɓan lokaci, adana lokaci ne.” Mutumin da ya ba da takamaiman lokaci domin wani abu da ya kamata ya yi, sau da yawa yana cin ribar lokacinsa. Sarki mai hikima Sulemanu ya rubuta: “Kowane abu yana da nasa sa’a, da akwai lokacin kome a ƙarƙashin sama.” (Mai Hadishi 3:1, Moffatt) Dukan mu lokaci ɗaya muke da shi; ya dangana ne a kan yadda muka yi amfani da shi. Yadda muka shirya abubuwan da suka fi mana muhimmanci da kuma yadda muke ba su lokaci yana nuna abin da ya fi muhimmanci a zukantanmu.—Matiyu 6:21.

2. (a) A Huɗubarsa a Kan Dutse, menene Yesu ya ce game da bukatunmu na ruhaniya? (b) Waɗanne bincike ya kamata mu yi wa kanmu?

2 An wajabce mu mu yi amfani da lokaci wajen cin abinci da kuma barci domin waɗannan abubuwa ne da jikinmu ke bukata. Amma bukatunmu na ruhaniya fa? Mun sani cewa dole ne mu biya masa bukata. A Huɗubarsa a Kan Dutse, Yesu ya ce: “Albarka tā tabbata ga waɗanda suka san talaucinsu na ruhu.” (Matiyu 5:3) Dalili ke nan da “amintaccen bawan nan mai hikima” yake tunasar da mu a kai a kai ga muhimmancin ba da lokaci domin karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazarinsa. (Matiyu 24:45) Za ka fahimci yadda wannan yake da muhimmanci, amma za ka ga cewa kai dai ba ka da lokacin da za ka yi nazari ko kuma ka yi karatun Littafi Mai Tsarki. Idan haka ne, to, bari mu bincika hanyoyi da kuma yadda za mu iya samun lokaci a rayuwarmu domin karatun Kalmar Allah, nazari na kanmu, da kuma bimbini.

Samun Lokaci Domin Karatu da Kuma Nazarin Littafi Mai Tsarki

3, 4. (a) Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya bayar game da amfani da lokaci, kuma menene wannan ya ƙunsa? (b) Menene Bulus yake nufi da ya gargaɗe mu mu “yi matuƙar amfani da lokaci”?

3 Domin lokatai da muke ciki, dukanmu ya kamata mu kasa kunne ga kalmomin manzo Bulus: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne. Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da ke nufin Ubangiji.” (Afisawa 5:15-17) Hakika, wannan gargaɗi ya shafi dukan rayuwarmu na keɓaɓɓun Kiristoci, haɗe da samun lokaci don addu’a, nazari, taro, da kuma yin wa’azin “bisharan nan ta Mulkin” gwargwadon iyawarmu.—Matiyu 24:14; 28:19, 20.

4 Da yawa a cikin bayin Jehovah a yau yana musu wuya su saka karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazari mai zurfi ya zama sashen rayuwarsu. Hakika, ba za mu iya ƙara ko sa’a guda wa rayuwarmu ba, saboda haka gargaɗin manzo Bulus yana nufin wani abu ne dabam. A Helenanci, furcin nan “yi matuƙar amfani da lokaci” yana nufin yin amfani da lokacin wani abu domin wani. A cikin Expository Dictionary, shi W. E. Vine ya ba sa ma’anar cewa “yin amfani da kowane zarafi, juya kowane yanayi don abu mai kyau, tun da babu wanda za a iya samu idan ya ɓata.” Daga menene ko kuma daga ina za mu yi amfani da matuƙar lokaci don karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki?

Dole Mu Tsara Abubuwa da Suka Fi Muhimmanci

5. Me ya sa kuma ta yaya za mu “zaɓi abubuwa mafifita”?

5 Ƙari ga abubuwa da ke wajibi, muna da abubuwa na ruhaniya da yawa da suke bukatar hankalinmu. Mu keɓaɓɓun bayin Jehovah, muna bukatar “himantuwa ga aikin Ubangiji.” (1 Korantiyawa 15:58) Saboda wannan dalilin, Bulus ya umarci Kiristoci a Filibi su “zaɓi abubuwa mafifita.” (Filibiyawa 1:10) Wannan yana nufin cewa dole a tsara abubuwa da suka fi muhimmanci. Abubuwan ruhaniya ko da yaushe ya kamata su zo bisa abin duniya. (Matiyu 6:31-33) Duk da haka, ana bukatar daidaita abubuwa domin mu cika wajibanmu na ruhaniya. Yaya muke raba lokacinmu tsakanin sashen rayuwarmu ta Kirista dabam dabam? Masu kula masu ziyara sun ba da rahoto cewa tsakanin “abubuwa mafifita” da Kirista ya kamata ya yi, ana ƙyaliya a zancen nazari da kuma karatun Littafi Mai Tsarki.

6. Menene amfani da matuƙar lokaci ya ƙunsa idan ya zo ga ayyuka na waje da kuma na cikin gida?

6 Kamar yadda muka gani, “yi matuƙar amfani da lokaci” ya ƙunshi “yin amfani da kowane zarafi” kuma “juya kowane yanayi don abu mai kyau.” Saboda haka idan halin karatu da nazarinmu na Littafi Mai Tsarki ba shi da kyau, zai dace idan muka bincika yadda muke amfani da lokacinmu. Idan aikinmu yana ɗaukan yawancin lokacinmu da ƙarfinmu, mu yi addu’a a kan batun ga Jehovah. (Zabura 55:22) Za mu iya yin gyara da zai ba mu lokacin yin abubuwa masu muhimmanci da suke da alaƙa da bautar Jehovah, wanda ya haɗa da nazari da kuma karatun Littafi Mai Tsarki. Gaskiya ce da ake cewa aikin mace ba ya ƙarewa. Saboda haka dole ne ’yan’uwa mata su tsara abubuwa da suka fi muhimmanci kuma su ba da lokaci takamaimai don karatun Littafi Mai Tsarki da kuma nazari da natsuwa.

7, 8. (a) Daga waɗanne ayyuka ne sau da yawa za a iya samun lokaci don karatu da nazari? (b) Menene manufar nishaɗi, kuma ta yaya tunawa da wannan zai taimake mu mu tsara abubuwa da suka fi muhimmanci?

7 Galibi dai, yawancinmu za mu iya matuƙar amfani da lokaci don nazari a maimakon yin wasu ayyuka. Za mu iya tambayar kanmu, ‘Sa’o’i nawa nake yi wajen karatun mujallu da jaridu na duniya, wajen kallon telibijin, wajen sauraron waƙe-waƙe, ko kuma wajen wasan bidiyo? Ina ɓad da sa’o’i da yawa ne a gaban na’ura mai ƙwaƙwalwa fiye da yadda nake yi a karatun Littafi Mai Tsarki?’ Bulus ya ce: “Kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da ke nufin Ubangiji.” (Afisawa 5:17) Rashin azanci wajen kallon telibijin shi ne dalili mafi girma da ya sa da yawa cikin Shaidu ba sa ba da isashen lokaci domin nazari na kansu da kuma karatun Littafi Mai Tsarki.—Zabura 101:3; 119:37, 47, 48.

8 Wasu za su ce ba za su iya nazari ko da yaushe ba, za su bukaci su yi nishaɗi. Ko da yake wannan gaskiya ne, zai yi kyau idan aka gwada sa’o’in da ake ɓatarwa wajen shaƙatawa da sa’o’in da ake yi wajen nazari da kuma karatun Littafi Mai Tsarki. Sai abin ya ba ka mamaki. Nishaɗi da shaƙatawa, ko da yake wajibi ne, dole ne kuma a ajiye su a inda ya dace. Manufarsu don su wartsake mana jiki ne domin ayyuka na ruhaniya. Yawancin wasanni na telibijin da kuma wasannin bidiyo sukan gajiyar da mutum, yayin nan kuma karatu da nazarin Kalmar Allah yana wartsakewa da kuma ba da ƙarfi.—Zabura 19:7, 8.

Yadda Wasu Suka Ba da Lokaci Domin Nazari

9. Menene amfanin bin shawara da aka bayar a cikin littafin nan Examining the Scriptures Daily—1999?

9 Gabatarwa na littafin nan Examining the Scriptures Daily na 1999 ya ce: “Zai kasance da amfani mai girma mu karanta aya kowace rana da kuma kalami a kanta daga wannan littafin da safe. Za ka ji kamar Jehovah, Babban Mai Koyarwa, yana tashinka a barci da umarnansa. An yi maganar Yesu Kristi cikin annabci cewa yana amfana daga umarnin Jehovah kowace rana: ‘A kowace safiya [Jehovah] yakan sa in yi marmarin jin abin da zai koya wa koyayyunsa.’ Irin wannan koyarwar ya ba wa Yesu ‘abin da zai faɗa’ saboda ya ‘ƙarfafa marar ƙarfi da magana.’ (Ishaya 30:20; 50:4; Matiyu 11:28-30) Ka tashi ga gargaɗi na kan lokaci daga Kalmar Allah kowace safiya ba kawai zai taimake ka ka jure wa matsalolinka ba amma zai taimake ka da ‘abin da za ka faɗa’ ka taimake wasu.”a

10. Ta yaya wasu suka ba da lokaci ga yin karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, da wace albarka?

10 Kiristoci da yawa suna bin shawarar nan ta wajen karanta ayar kowace rana da kalami da kuma ta wajen karatun Littafi Mai Tsarki ko kuma yin nazari da sassafe kowace rana. A Faransa wata amincecciyar majagaba takan tashi da sassafe kowace rana ta yi karatun Littafi Mai Tsarki na minti 30. Menene ya taimake ta yin haka cikin shekaru? Ta ce: “Abin ya motsa ni ƙwarai, kuma na manne wa tsari na na karatu ko da menene ya faru!” Kowane lokaci muka zaɓa, abu mafi muhimmanci shi ne mu manne wa tsarinmu. René Mica, wanda yake aikin majagaba na fiye da shekara 40 a Turai da kuma Afirka ta Arewa, ya ce: “Tun daga shekarar 1950 buri na ne in karanta Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa sau ɗaya a shekara, abin da na yi sau 49 yanzu. Na ga wannan yana da muhimmanci a riƙe dangantakata kusa da Mahaliccina. Bimbini a kan Kalmar Allah ya taimake ni na fahimci shari’ar gaskiya ta Jehovah da wasu halayensa da kyau kuma wannan ya kasance tushen ƙarfi a gare ni.”b

‘Abinci a Kan Kari’

11, 12. (a) Wane ‘ba da abinci’ ne “amintaccen wakilin” ya yi tanadinsa? (b) Ta yaya ake tanadin ‘abincin’ a kan kari?

11 Kamar yadda tsari mai kyau na cin abinci yake gyara lafiyar jiki, tsarin nazari da kuma karatun Littafi Mai Tsarki a kai a kai yana da kyau ga lafiya ta ruhaniya. A Linjilar Luka, mun karanta kalmomin Yesu: “Wanene amintaccen wakilin nan mai hikima, da ubangijinsa zai ba shi riƙon gidansa, ya riƙa ba su abincinsu a kan kari?” (Luka 12:42) Fiye da shekara 120 yanzu, ana tanadin ‘abinci a kan kari’ a cikin Hasumiyar Tsaro, da wasu littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki.

12 Ka lura da furcin nan “a kan kari.” A lokaci da ya dace, ‘Mai Koyarwa Mai Girma,’ Jehovah, ta wurin Ɗansa da kuma ajin bawa, ya ja-goranci mutanensa a batutuwan koyarwa da kuma ɗabi’a. Ya kasance kamar dai dukanmu mun ji murya tana ce mana: “Idan kuka kauce daga hanya zuwa dama ko hagu, za ku ji muryarsa a bayanku tana cewa, ‘Ga hanyar nan, ku bi ta.’ ” (Ishaya 30:20, 21) Bugu da ƙari, lokacin da mutane suka mai da hankali suka karanta Littafi Mai Tsarki da dukan littattafan masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki, sau da yawa suna jin cewa abubuwa da ke rubuce ciki an rubuta ne saboda su. Hakika, gargaɗi daga Allah da kuma ja-gora za su zo a kan kari domin mu, su taimake mu mu tsayayya wa jaraba ko kuma mu tsai da shawara mai kyau.

Ka Gina Tsarin Cin Abinci Mai Kyau

13. Waɗanne ne tsarin cin abinci da ba su da kyau?

13 Domin a amfana sosai daga irin wannan ‘abinci’ da ake tanadinsa a kan kari, muna bukatar tsarin cin abinci mai kyau. Dole ne mu kasance muna da tsarin karatun Littafi Mai Tsarki da kuma na nazari na kanmu kuma mu manne masa. Kana da tsarin cin abinci na ruhaniya mai kyau da kuma lokaci na yin nazari mai zurfi na kanka? Ko kuma dai kana nazari sama sama ne na abin da aka shirya shi sosai dominmu, kamar a ce kana cin abinci ne a guje, kana ƙyale wasu lokacin abinci ma gabaki ɗaya? Tsarin cin abinci na ruhaniya da babu kyau ya kai wasu raunana a bangaskiya—har ma sun fanɗare.—1 Timoti 1:19; 4:15, 16.

14. Me ya sa yake da amfani mu maimaita abin da kamar mun riga mun fahimta?

14 Wasu za su ji cewa sun riga sun san muhimman koyarwa saboda haka ba dukan talifi ba ne yake magana a kan sabon abu. Saboda haka nazari a kai a kai ba dole ba ne da kuma halartar taro. Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa muna bukatar a riƙa tunasar da mu abubuwan da muka koya. (Zabura 119:95, 99; 2 Bitrus 3:1; Yahuza 5) Kamar yadda wadda ta iya girki take amfani da kayayyakin girki iri ɗaya ta girka abinci masu daɗi iri dabam dabam, ajin bawa na tanadin abinci na ruhaniya mai gamsarwa a hanyoyi dabam dabam. Har a cikin talifofi da suka yi magana a kan abubuwa da aka yi magana a kansu sau da yawa, da akwai darussa masu kyau da ba za mu so mu kasa fahimtarsu ba. Gaskiyar ita ce, abin da muka samu daga abin da muka karanta ya dangana ne sosai bisa ƙoƙari da lokaci da muka bayar wajen yin nazarinsa.

Amfani na Ruhaniya Daga Karatu da Yin Nazari

15. Ta yaya karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki yake taimaka mana mu zama ministocin Kalmar Allah na ƙwarai?

15 Amfani da muke samu daga karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki suna da yawa. Suna taimakonmu mu cika ɗaya cikin muhimman hakkinmu na Kirista, wato, saboda kowannenmu ya zama “ma’aikaci wanda ba hanya ya kunyata, mai kuma fassarar Maganar gaskiya daidai.” (2 Timoti 2:15) Da zarar mun yi karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki, haka zuciyarmu za ta cika da tunanin Allah. Da haka, kamar manzo Bulus, za mu iya yin ‘muhawwara da mutane daga cikin Nassosi muna yi musu bayani, muna kuma tabbatar’ da gaskiya mai ban mamaki na nufe-nufen Jehovah. (Ayyukan Manzanni 17:2, 3) Hikimarmu ta malamtaka ta ƙaru, kuma taɗinmu, da jawabinmu, da kuma gargaɗin zai gyara wasu sosai a ruhaniya.—Karin Magana 1:5.

16. A wace hanya ce muke amfana daga karatun da kuma nazarin Kalmar Allah?

16 Ƙari ga haka, lokacin da muke amfani da shi wajen bincika Kalmar Allah zai taimake mu daidaita rayuwarmu sosai da hanyoyin Jehovah. (Zabura 25:4; 119:9, 10; Karin Magana 6:20-23) Zai ƙarfafa halinmu na ruhaniya, kamar su tawali’u, aminci, da kuma farin ciki. (Maimaitawar Shari’a 17:19, 20; Wahayin Yahaya 1:3) Idan muka yi amfani da ilimi da muka samu daga karatu da nazarin Littafi Mai Tsarki, muna samun ruhun Allah a rayuwarmu, wanda yake kaiwa ga samun ’ya’yan ruhu da yawa a dukan abin da muke yi.—Galatiyawa 5:22, 23.

17. Ta yaya yawan karatunmu da kuma kyansa ya shafi dagantakarmu da Jehovah?

17 Mafi muhimmanci, lokacin yin wasu abubuwa da muka yi amfani da su wajen karatu da kuma nazarin Kalmar Allah zai kawo riba sosai a dangantakarmu da Allah. Bulus ya yi addu’a cewa ’yan’uwansa Kiristoci a ‘cika su da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu, domin su yi zaman da ya cancanci bautar Jehovah, suna faranta masa ta kowane fanni.’ (Kolosiyawa 1:9, 10) Haka ma a gare mu, domin mu “yi zaman da ya cancanci bautar Ubangiji,” dole a ‘cika mu da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu.’ Hakika, samun albarkar Jehovah da kuma yardarsa ta dangana ne ƙwarai a kan yawa da kuma kyan karatunmu da nazarin Littafi Mai Tsarki.

18. Waɗanne albarka ne za su kasance namu idan muka bi kalmomin Yesu da suke rubuce cikin Yahaya 17:3?

18 “Rai madawwami kuwa, shi ne su san ka, Allah Makaɗaici na gaskiya, da kuma Yesu Almasihu da ka aiko.” (Yahaya 17:3) Wannan ɗaya ne daga cikin nassosi da Shaidun Jehovah suke amfani da shi sosai domin su taimake wasu su ga muhimmancin yin nazarin Kalmar Allah. Babu shakka, yana da muhimmanci mu yi hakan da kanmu. Begenmu na rayuwa har abada ya dangana ne a kan ƙarin sanin Jehovah da kuma Ɗansa, Yesu Kristi. Ka yi tunanin abin da wannan yake nufi. Ƙara koya game da Jehovah da za mu yi ba zai taɓa ƙarewa ba—kuma za mu koya game da shi har dawwama!—Mai Hadishi 3:11; Romawa 11:33.

[Hasiya]

a Watchtower Bible and Tract Society of New York, Inc., ne suka buga.

b Ka duba talifin nan “Lokacin da Suke Karanta Shi da Kuma Yadda Suka Amfana,” wanda aka buga a cikin Hasumiyar Tsaro (Turanci) 1 ga Mayu, 1995, shafuffuka 20-21.

Tambayoyin Maimaitawa

• Me zai bayyana ta yadda muke amfani da lokacinmu?

• Daga waɗanne ayyuka ne za mu iya samun lokaci domin karatu da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

• Me ya sa za mu lura da tsarin cin abincinmu na ruhaniya?

• Waɗanne riba ake samu daga karatu da yin nazarin Nassosi?

[Hotuna a shafuffuka na 28, 29]

Karatu da kuma nazari a kai a kai za su sa mu ‘fassara Maganar gaskiya daidai’

[Hotuna a shafi na 31]

Daidaita wasu ayyuka a rayuwarmu da ta shagala da biɗan abubuwan ruhaniya za ta kawo riba mai yawa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba