Ka Koya wa Yaranka Su So Yin Karatu da Kuma Nazari
YIN ƙoƙari sosai domin ka koya wa yaranka yin karatu da kuma yin nazari yana ɗaya daga cikin hanyoyi mafi muhimmanci da za ka iya kyautata rayuwarsu ta nan gaba. Kuma waɗannan ayyukan suna kawo farin ciki! Abin da wasu mutane suka fi tunawa sa’ad da suke yara shi ne yadda iyayensu suke yi masu karatu. Karatu yana da daɗi, kamar yadda sakamakonsa yake. Hakan gaskiya ne musamman ga bayin Allah, tun da yake muna ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Wani mahaifi Kirista ya faɗa, “Abubuwan da muka fi ɗauka da tamani suna da nasaba da karatu da nazari.”
Hali mai kyau game da nazari yana iya taimaka wa yaranka su ƙulla dangantaka na kud da kud da Allah. (Zab. 1:1-3, 6) Ko da yake iya karatu ba bukata ba ce ta samun ceto, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa karatu yana iya kawo mana albarka mai girma. Alal misali, Ru’ya ta Yohanna 1:3 ta ce: “Mai-albarka ne duk wanda ya karanta, da duk waɗanda ke jin zantattukan annabcin.” Bugu da ƙari, an nuna amfanin mai da hankali sosai, wanda sashe ne mai muhimmanci na nazari a hurarriyar shawarar manzo Bulus ga Timotawus: “Ka yi ƙwazo cikin waɗannan al’amura; ka bada kanka gare su sosai.” Me ya sa? “Domin cingabanka ya bayanu ga kowa.”—1 Tim. 4:15.
Hakika, sanin yadda ake karatu da nazari kawai ba tabbaci ba ne cewa waɗannan iyawa za su amfani mutum. Mutane da yawa da suke da wannan iyawa ba sa amfani da shi, maimakon haka, suna yin abubuwan da ba za su amfane su sosai ba. Saboda haka, yaya iyaye za su koya wa yaransu su yi sha’awar ilimin da zai amfane su?
Ƙaunarka da Kuma Misalinka
Yara suna jin daɗin yin nazari sa’ad da aka yi hakan cikin ƙauna. Owen da Claudia, ma’aurata Kirista, sun tuna wani abu game da yaransu biyu: “Suna ɗokin lokacin nazari domin lokaci ne na musamman, ba sa jin tsoro kuma suna sakin jiki. Sun haɗa wannan tsarin da mahalli na ƙauna.” Ko sa’ad da yara suke shiga shekaru na goma sha da suke fuskantar ƙalubale, nuna ƙauna a lokacin nazari na iyali zai ci gaba da shafan ra’ayinsu game da nazari. Yaran Owen da Claudia sun zama majagaba kuma suna ci gaba da amfana daga son karatu da nazari da aka koya musu.
Wani abin taimako sosai cikin ƙauna shi ne misali. Yaran da suke ganin iyayensu a koyaushe suna karatu da nazari za su ɗauki waɗannan ayyukan a matsayin sashen rayuwarsu. Amma yaya kai a matsayinka na mahaifi za ka kafa irin wannan misalin idan yin karatu yana yi maka wuya? Wataƙila kana bukatan ka daidaita abubuwan da ka fi so ko kuma halinka idan ya zo ga yin karatu. (Rom. 2:21) Idan yin karatu sashe ne mai muhimmanci a tsarinka na kullum, hakan zai shafi yaranka sosai. Ƙwazonka, musamman a karatun Littafi Mai Tsarki, shirya taro, da nazari na iyali, zai sa su fahimci muhimmancin waɗannan ayyukan.
Saboda haka, ƙaunarka da misalinka suna da muhimmanci wajen cusa wa yaranka sha’awar yin karatu. Amma waɗanne matakai masu amfani ne za ka ɗauka don ka ƙarfafa su?
Taimaka wa Yara Su So Yin Karatu
Waɗanne matakai masu muhimmanci ne kake bukatan ka ɗauka wajen koya wa yaranka su so yin karatu? Ka riƙa ba su littattafai tun suna ƙanana. Wani dattijo Kirista wanda iyayensa suka koya masa ya so yin karatu ya ba da wannan shawarar: “Ka sa yaranka su saba riƙe littattafai da kuma yin amfani da su. Ta hakan, littattafai za su zama abokansu da kuma sashen rayuwarsu.” Yara da yawa suna son riƙe littattafai da ke bayyana Littafi Mai Tsarki, kamar su Ka Koya Daga Wurin Babban Malami da kuma Littafi Na, Na Labarun Bible, tun kafin su iya karatu. Sa’ad da kake karanta irin waɗannan littattafan da yaranka, kana koya musu yare ne da kuma “al’amura masu ruhaniya” da ‘kalamai na ruhaniya.’—1 Kor. 2:13.
Ka riƙa karatu a kai a kai da babbar murya. Ka kafa tsarin yin karatu tare da yaranka a kowace rana. Yin hakan yana koya musu furta kalmomi daidai kuma yana ƙarfafa su su kasance da halin yin karatu. Yadda kake karatu yana da muhimmanci. Idan kana karatu da ban sha’awa, su ma za su yi hakan. Hakika, kana iya ganin yaranka suna cewa ka ci gaba da karanta musu wannan labarin a kai a kai. Ka yi yadda suka gaya maka! Da shigewar lokaci, za su so su bincika sababbin batutuwa. Amma ka mai da hankali kada ka tilasta musu yin karatu da kai. Yesu ya kafa misali mai kyau ta wurin koya wa masu sauraronsa kaɗai “gwalgwadon jinsu.” (Mar. 4:33) Idan ba ka tilasta wa yaranka, za su riƙa yin ɗokin kowane lokacin karatu, kuma zai sa ka kusaci cim ma makasudinka na koya musu iya yin karatu.
Ka ƙarfafa su su yi kalami, da kuma tattauna abin da ku ka karanta. Abin farin ciki, ba da daɗewa ba yaranka za su iya sanin kalmomi, su furta su, kuma su fahimci ma’anar kalmomi masu yawa. Tattauna abin da ku ka karanta zai sa su samu ci gaba sosai. Tattauna abin da kuka karanta zai taimaka musu su samu ci gaba sosai. Tattaunawa yana taimaka wa yara su “koyi kalmomin da suke bukatan su fahimta nan gaba sa’ad da suke karatu,” in ji wani littafi a kan batun yadda za a taimaka wa yara su iya karatu sosai. Littafin ya ci gaba: “Ga yara ƙanana da suke ƙoƙarin su koyi karatu da rubutu, tattauna batutuwa masu ma’ana da su yana da muhimmanci.”
Ka sa yaranka su yi maka karatu, kuma ka ƙarfafa su su yi tambayoyi. Kana iya yin tambayoyi kuma ka faɗi abin da wataƙila zai zama amsoshinsu. A wannan hanyar, yara za su koyi cewa littattafai tushen samun bayani ne kuma kalmomin da suke karantawa suna da ma’ana. Hakan zai taimaka sosai idan abin da kake karantawa ya fito ne daga Kalmar Allah, littafi mafi ma’ana.—Ibran. 4:12.
Kada ka manta cewa yin karatu abu ne mai wuya. Zai ɗauki lokaci da kuma gwadawa kafin a iya.a Ka tabbata ka ƙarfafa matasa da suke son yin karatu ta wajen yaba musu. Yaba wa yaranka zai ƙarfafa su su so yin karatu.
Karatu Yana da Amfani Kuma Yana da Daɗi
Koya wa yaranka yadda za su yi nazari yana sa karatu ya kasance da ma’ana. Nazari ya ƙunshi koyan gaskiya da kuma fahimtar dangatakarsu da juna. Yana bukatan iya tsarawa, tunawa, da kuma yin amfani da bayanin. Da zarar yaro ya koyi yadda ake nazari kuma ya fahimci yadda nazarin zai taimake shi, hakan zai kasance da amfani da kuma daɗi.—M. Wa. 10:10.
Ka gabatar da abubuwa masu muhimmanci don nazari. Bauta ta iyali da yamma, tattauna nassosin yini, da makamancinsu suna kawo zarafi mafi kyau na koya wa yaranka yadda ake nazari. Zama a waje ɗaya da mai da hankali ga wani darasi na ɗan lokaci zai koya wa yaranka mai da hankali, wanda yake da muhimmanci ga koyon abubuwa. Ƙari ga haka, kana iya ƙarfafa ɗanka ya gaya maka yadda abin da ya koya yake da nasaba da abin da ya riga ya sani. Wannan yana koya masa gwada abubuwa. Kana iya gaya wa ’yarka ta taƙaita abin da ta karanta da nata kalmomi. Wannan zai taimaka mata ta fahimci ma’anar kuma ta tuna abin da ta koya. Maimaitawa, wato, sake ambata muhimman darussa bayan sun karanta wani talifi, wani abu ne da za ka koya musu da zai taimake su su riƙa tuna abin da suka karanta. Ana iya koya wa har ƙananan yara su ɗan yi rubutu a lokacin nazari ko kuma a taron ikilisiya. Wannan zai taimaka musu su riƙa mai da hankali! Waɗannan hanyoyi masu sauƙi suna sa tsarin koyo ya yi daɗi kuma ya kasance da ma’ana a gare ka da kuma yaranka.
Ka kafa yanayin da ya dace da nazari. Samun isashen iska da haske, tare da yanayin da ya dace inda babu surutu, zai sa mai da hankali ya kasance da sauƙi. Hakika, yadda iyaye suke ɗaukan nazari yana da muhimmanci. “Yana da muhimmanci sosai ka riƙa keɓe lokaci don karatu da nazari a kai a kai,” in ji wata uwa. “Wannan zai taimaka wa yaranka su kasance masu tsari. Za su koyi ainihin abubuwan da ake bukatan a cim ma a lokaci kaza.” Iyaye da yawa suna hana yin ayyuka a lokacin nazari. In ji wani mutum, wannan hanya ce mafi kyau na koya wa yara kasancewa da halin nazari mai kyau.
Ka nanata amfanin yin nazari. A ƙarshe, ka taimaka wa yaranka su ga yadda za su yi amfani da abin da suka koya. Yin amfani da abin da suka koya yana nanata ainihin manufar nazarin. Wani ɗan’uwa matashi ya ce: “Idan ban ga amfanin abin da nake nazarinsa ba, yana yi mini wuya na so ci gaba da yin nazarin. Amma idan zan iya amfani da bayanin ga kaina, sai ya zama abin da nake son na fahimta.” Sa’ad da matasa suka ɗauki nazari a matsayin hanyar cim ma abu mai muhimmanci, za su shaƙu da yinsa. Za su soma sha’awar yin nazari, kamar yadda suke son yin karatu.
Albarka Mafi Kyau
Wannan mujallar ba za ta iya ɗaukan dukan fa’idojin da ke tattare da koya wa yaranka su so yin karatu ba. Yin nasara a makaranta, a wajen aiki, yin dangantaka da mutane, fahimtar abubuwan da ke faruwa cikin duniya da ma’anarsu, da kuma ƙulla dangantaka na kud da kud tsakanin iyaye da yaro suna cikin amfani masu yawa da za a iya samu, ban da gamsuwar da za a samu daga yin karatu da nazari.
Fiye da kome, son karatu zai taimaka wa yaranka su zama mutane masu jin tsoron Allah. Son nazari zai taimaka musu su buɗe zuciyarsu su san “fāɗi da ratar da tsawon da zurfin” koyarwar Nassi. (Afis. 3:18) Hakika, iyaye Kiristoci suna da abubuwa da yawa da za su koya wa yaransu. Yayin da iyaye suka keɓe lokaci kuma suka mai da wa yaransu hankali kuma suka yi iya ƙoƙarinsu don yaransu su soma rayuwa mai kyau, suna fatan cewa yaransu daga baya za su zaɓi su zama masu bauta wa Jehobah. Koya wa yaranka halin nazari mai kyau yana taimaka musu su kāre ruhaniyarsu kuma su ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Saboda haka, kana da dalilai da yawa na yin addu’a ga Jehobah ka nemi albarkarsa yayin da kake ƙoƙarin ka motsa yaranka su so yin karatu da nazari.—Mis. 22:6.
[Hasiya]
a Yin karatu da nazari yana kawo ƙalubale na musamman ga yaran da ba sa iya koyon abubuwa don rashin lafiya. Game da abin da iyaye za su yi don su taimaka musu, ka duba Awake! na 22 ga Fabrairu, 1997, shafuffuka 3-10.
[Akwati/Hotuna da ke shafi na 26]
Yin Karatu . . .
• Ka yi tanadin littattafai
• Ka yi karatu da babbar murya
• Ka ƙarfafa yin kalami
• Ku tattauna abin da kuka karanta
• Ka sa yaranka su yi maka karatu
• Ka ƙarfafa yaranka su yi tambayoyi
Yin Nazari . . .
• Ku kafa misali mai kyau a matsayin iyaye
• Ka koya wa yaranka su riƙa . . .
○ mai da hankali
○ gwadawa
○ taƙaitawa
○ maimaitawa
○ yin rubutu
• Ka kafa yanayin da suka dace don nazari
• Ka nanata amfanin yin nazari