Ka Ci Gaba Da Yin Tafiya Tare Da Ƙungiyar Jehovah
“Allah mai zartar da salama . . . ya kammala ku da kowane irin kyakkyawan abu domin ku aikata nufinsa.”—IBRANIYAWA 13:20, 21.
1. Nawa ne adadin jama’ar duniya, kuma nawa suke cikin wasu addinai?
A SHEKARA ta 1999, adadin jama’ar duniya ya kai biliyan shida! The World Almanac (Kalandar Duniya) ta nuna cewa cikin wannan adadi 1,165,000,000 Musulmai ne; 1,030,000,000 kuma ’yan Roma Katolika ne; 762,000,000 kuma ’yan Hindu ne; 354,000,000 kuma ’yan Buddha ne; 316,000,000 kuma ’yan Farostatan ne; da kuma 214,000,000 ’yan Orthodox.
2. Me za a ce game da yanayin addinai a yau?
2 Saboda jayayya da ɗimaucewa na addinai da suke a yau, dukan waɗannan miliyoyin suna aikata abubuwa cikin jituwa da nufin Allah ne? A’a, “domin Allah ba Allahn ruɗu ba ne, na salama ne.” (1 Korantiyawa 14:33) A wata sassa, ’yan’uwanci na bayin Jehovah a dukan ƙasashe kuma fa? (1 Bitrus 2:17) Bincike sosai ya nuna cewa ‘Allah mai zartar da salama ya kammala su da kowane irin kyakkyawan abu domin su aikata nufinsa.’—Ibraniyawa 13:20, 21.
3. Menene ya faru a Urushalima a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., kuma me ya sa?
3 Babu shakka, adadi mai yawa na mutane da suke tarayya da Shaidun Jehovah ba shi ne magwaji ba na sanin ko za su more alherin Allah; ba kuwa yawan adadi ne yake burge Allah ba. Bai zaɓi Isra’ilawa domin sun “fi sauran al’ummai yawa ba.” Su ne “mafiya ƙanƙanta.” (Maimaitawar Shari’a 7:7) Amma domin Isra’ila ta yi rashin aminci, a Fentakos na shekara ta 33 A.Z., Jehovah ya mai da alherinsa zuwa kan sabuwar ikilisiya da mabiyan Yesu Kristi suke ciki. An shafa su da ruhu mai tsarki na Jehovah kuma sun ci gaba da himma suna shelar gaskiya game da Allah da Kristi ga wasu.—Ayyukan Manzanni 2:41, 42.
Suna Ci Gaba Kullayaumi
4. Me ya sa za ka ce ikilisiyar Kirista ta farko ta ci gaba a kai a kai?
4 A ƙarni na farko, ikilisiyar Kirista ta ci gaba a kai a kai, a buɗe sababbin yankuna, ta almajirantarwa, kuma ta sami fahimta mai girma na nufe-nufen Allah. Kiristoci na farko sun ci gaba da bin wayewa ta ruhaniya da aka yi tanadinta ta wasiƙu da Allah ya hure. Ziyara na manzanni da kuma ta wasu ta motsa su, suka cika hidimarsu. An rubuta wannan da kyau a cikin Nassosin Kirista na Helenanci.—Ayyukan Manzanni 10:21, 22; 13:46, 47; 2 Timoti 1:13; 4:5; Ibraniyawa 6:1-3; 2 Bitrus 3:17, 18.
5. Me ya sa ƙungiyar Allah take ci gaba a yau, me ya sa ya kamata mu yi tafiya tare da ita?
5 Kamar Kiristoci na farko, Shaidun Jehovah na zamanin yau sun taso ne daga kaɗan kaɗan. (Zakariya 4:8-10) Tun daga kusan ƙarshen ƙarni na 19, akwai tabbaci sarai cewa ruhun Allah yana tare da ƙungiyarsa. Domin mun dogara, ba ga ƙarfin mutum ba, amma a kan ja-gorar ruhu mai tsarki, mun ci gaba da fahimtarmu na Nassosi da kuma wajen yin nufin Allah. (Zakariya 4:6) Yanzu da muke “zamanin ƙarshe,” yana da muhimmanci mu ci gaba da tafiya da ƙungiyar Jehovah mai ci gaba. (2 Timoti 3:1-5) Yin hakan zai taimake mu sa begenmu ya zama na gaske, mu saka hannu cikin yin wa’azi game da Mulkin Allah da aka kafa kafin ƙarshen wannan tsarin abubuwa.—Matiyu 24:3-14.
6, 7. Za mu bincika waɗanne wurare uku ne da ƙungiyar Jehovah ta ci gaba?
6 A cikinmu akwai waɗanda suka soma tarayyarsu da ƙungiyar Jehovah a shekara ta 1920, ta 1930, da kuma ta 1940. A waɗannan shekaru na farko, wanene a tsakaninmu zai yi tunanin girma na musamman da ci gaba na ƙungiyar har zuwa yanzu? Ka yi tunanin ci gaba ta musamman da aka kai a tarihinmu na zamanin yau! Hakika, yana da albarka a ruhaniya a yi tunani a kan abin da Jehovah ya cim ma ta mutanensa da ya tsara bisa tsarinsa.
7 Dauda na dā ya yi tunani sosai a kan ayyukan Jehovah masu ban al’ajabi abin ya burge shi ƙwarai. “Idan na yi ƙoƙari in faɗe su duka,” in ji shi, “sun fi ƙarfin in faɗa.” (Zabura 40:5) Muna da irin wannan kasawar, ba ma iya faɗin manyan ayyuka da suka isa yabo na Jehovah a zamaninmu. Duk da haka, bari mu bincika wurare uku da ƙungiyar Jehovah ta ci gaba: (1) wayewa ta ruhaniya da take cin gaba, (2) hidima da aka gyara kuma aka faɗaɗa, na (3) gyara na kan lokaci a tsarin ƙungiyar.
Godiya don Wayewa ta Ruhaniya
8. Cikin jituwa da Karin Magana 4:18, mecece wayewa ta ruhaniya ta sa muka fahimta game da Mulkin?
8 Game da wayewa ta ruhaniya mai ci gaba, Karin Magana 4:18 ta kasance gaskiya. Ta ce: “Hanyar da adalai ke bi kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske, har ta take tsaka.” Muna godiya don wayewa ta ruhaniya mai ci gaba da muka samu! A shekara ta 1919 a babban taro a Cedar Point, Ohio, an nanata game da Mulkin Allah. Jehovah zai yi amfani da Mulkin ya tsarkake sunansa kuma ya kunita ikon mallakarsa. Hakika, wayewa ta ruhaniya ta taimake mu muka fahimci cewa daga Farawa har zuwa Wahayin Yahaya, Littafi Mai Tsarki ya nuna nufin Jehovah na tsarkake sunansa ta Sarautar Ɗansa. Wannan ne muhimmin bege ga dukan masu ƙaunar adalci.—Matiyu 12:18, 21.
9, 10. A shekarun 1920, me muka koya game da Mulkin da kuma game da ƙungiyoyi biyu da suke hamayya da juna, kuma ta yaya wannan ya yi taimako?
9 A babban taron Cedar Point a shekara ta 1922, mai jawabi na musamman J. F. Rutherford, ya aririce mutanen Allah “su sanar, su sanar, su sanar, da Sarkin da kuma mulkinsa.” A cikin talifin nan “Birth of the Nation,” (Haihuwar Al’umma) da aka buga cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Maris, 1925 (Turanci), an jawo hankali ga fahimi na ruhaniya game da annabce-annabce da sun yi nuni ga kafa Mulkin Allah a shekara ta 1914. An kuma gano cewa a shekara ta 1920 akwai ƙungiya biyu da suke hamayya da juna—ta Jehovah da ta Shaiɗan. Har ila suna kan faɗā, za mu kasance a gefe da za ta ci nasara idan mun ci gaba da tafiya tare da ƙungiyar Jehovah.
10 Ta yaya irin wannan wayewa ta ruhaniya ta taimake mu? Tun da yake Mulkin Allah da Sarki Yesu Kristi ba na duniya ba ne, mu ma ba za mu kasance na ta ba. Ta kasancewa dabam daga duniya, muna nuna cewa muna gefen gaskiya. (Yahaya 17:16; 18:37) Yayin da muka lura da matsaloli masu yawa da suke damun wannan mugun tsari, muna godiya cewa ba ma cikin ƙungiyar Shaiɗan! Lalle an yi mana alheri da shi ke muna da kwanciyar rai ta ruhaniya cikin ƙungiyar Jehovah!
11. Wane suna ne na Nassi mutanen Allah suka ɗauka a shekara ta 1931?
11 A babban taro da aka yi a shekara ta 1931, a Columbus, Ohio, an yi amfani da ya dace da Ishaya 43:10-12. Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ɗauki suna na musamman Shaidun Jehovah. Gata ce mai girma a sanar da sunan Allah don wasu su kira gare shi domin su samu ceto!—Zabura 83:18; Romawa 10:13.
12. Wace wayewa ce ta ruhaniya game da ƙasaitaccen taro aka yi tanadinta a shekara ta 1935?
12 Kafin shekarun 1930, mutanen Allah da yawa ba su da tabbaci game da begensu na rayuwa ta nan gaba. Wasu sun yi tunanin rayuwa a sama amma sun yi marmarin koyarwar Littafi Mai Tsarki game da rayuwa a duniya. A babban taro a shekara ta 1935 a Washington, D.C., abar sha’awa ce da aka koyi cewa taro mai girma, ko ƙasaitaccen taro, na Wahayin Yahaya sura 7 rukuni ne da suke da begen zama a duniya. Tun lokacin, tattara ƙasaitaccen taron ta ci gaba sosai. Ba za mu yi godiya ba cewa mun san ƙasaitaccen taron? Gaskiyar cewa za a tattara mutane da yawa daga dukan al’ummai, ƙabilai, da harsuna na motsa mu mu yi aiki sosai don mu yi tafiya tare da ƙungiyar Jehovah.
13. Wane batu na musamman aka bayyana a babban taro da aka yi a St. Louis a shekara ta 1941?
13 An nanata batu na musamman da ya kamata jam’iyyar ’yan Adam su damu da shi a babban taro na St. Louis, Missouri a shekara ta 1941. Sarauta ta duniya, ko kuma ikon mallaka. Wannan batu ne da ba da daɗewa ba za a warware, kuma babbar ranan nan mai ban tsoro da za a yi wannan tana zuwa da sauri! Abin da aka yi maganarsa kuma a shekara ta 1941 game da riƙe gaskiya ne, wanda yake sa mu nuna tsayawarmu kowannenmu game da ikon mallakar Allah.
14. A babban taro na dukan ƙasashe a shekara ta 1950, me aka koya game da hakimai da aka ambata a Zabura 45:16?
14 A taro na dukan ƙasashe da aka yi a shekara ta 1950 a New York City, an bayyana hakimai na Zabura 45:16 (NW ). Lokaci na ban motsawa ne ƙwarai yayin da Ɗan’uwa Frederick Franz ya yi magana a kan wannan batu kuma ya bayyana cewa hakimai na sabuwar duniya suna tsakaninmu. A wannan babban taro da waɗanda suka biyo bayan, an haskaka ganewa na ruhaniya da yawa. (Zabura 97:11) Muna godiya cewa hanyarmu “kamar fitowar rana ce, sai ta yi ta ƙara haske”!
Ci Gaba a Hidimarmu
15, 16. (a) Yaya muka ci gaba a hidimarmu cikin shekarun 1920 da 1930? (b) Waɗanne littattafai ne suka ba da ƙarfi ga hidima ta Kirista a shekarun bayan nan?
15 Hanya ta biyu da ƙungiyar Jehovah take cin gaba ita ce a aikinmu na musamman—wa’azin Mulki da almajirantarwa. (Matiyu 28:19, 20; Markus 13:10) Don a cika wannan aiki, ƙungiyar ta sa a gabanmu muhimmancin faɗaɗa hidimarmu. A shekara ta 1922 an aririci duka Kiristoci su sa hannu a aikin wa’azi. Ya rage kowanne ya bar haskensa ya haskaka, da haka sa hannu a yin shaida ga gaskiya. (Matiyu 5:14-16) A shekara ta 1927 an ɗauki mataki a keɓe Lahadi don hidimar fage. Somawa daga Fabrairu ta shekara ta 1940, ana ganin Shaidu a kan tituna suna ba da Hasumiyar Tsaro da kuma Consolation (yanzu Awake!).
16 A shekara ta 1937 aka fito da ƙasidar nan Model Study, da ke nanata bukatar koma ziyara don a koya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Shekaru bayan haka, an nanata aikin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai. An ba da ƙarfi ga wannan fanni na hidima ta wajen littafin nan “Let God Be True” a shekara ta 1946 da kuma Gaskiya mai bishe zuwa Rai Madauwami a shekara ta 1971. Yanzu, muna amfani da littafin nan Sanin Da ke Bishe Zuwa Rai na Har Abada. Gama yin nazarin irin wannan littafi yana kafa tushe na Nassi mai kyau don almajirantarwa.
Ci Gaba a Gyarar Tsari na Ƙungiyar
17. Cikin jituwa da Ishaya 60:17, yaya ƙungiyar Jehovah ta ci gaba?
17 Hanya ta uku da ƙungiyar ta ci gaba ita ce ta gyara tsari na ƙungiyar. A Ishaya 60:17, Jehovah ya yi alkawari: “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla, Azurfa maimakon baƙin ƙarfe, Tagulla kuma maimakon itace. Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse. Masu mulkinki ba za su ƙara zaluntarki ba, Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.” Cikin jituwa da wannan annabci, an ɗauki matakai a gyara yadda ake kula da aikin wa’azin Mulki da na kiwon garken.
18, 19. Waɗanne gyara a tsari na ƙungiyar aka yi cikin shekaru?
18 A shekara ta 1919 aka naɗa shugaba na hidima da ke shirya hidimar fage a kowacce ikilisiya. Wannan ya ba hidimarmu a fage ƙarfi. Zaɓan dattawa ta jefa ƙuri’a da dikon an daina a shekara ta 1932, da ke nuna mun bar hanya ta dimokuraɗiyya. An kai wata aukuwa ta musamman a shekara ta 1938 lokacin da aka fara naɗa dukan bayi cikin ikilisiya daidai da tsari na naɗi na tsarin Allah a cikin ikilisiyar Kirista ta farko. (Ayyukan Manzanni 14:23; 1 Timoti 4:14) A shekara ta 1972 an naɗa dattawa da bayi masu hidima su yi hidima, yadda irin waɗannan maza suka yi tsakanin Kiristoci na farko. Maimako a sa mutum guda yana hidima na mai kula da ikilisiya, Filibiyawa 1:1 da wasu nassosi sun nuna cewa waɗanda suke cika farillai na Nassi na masu kula sa zama rukunin dattawa.—Ayyukan Manzanni 20:28; Afisawa 4:11, 12.
19 A shekara ta 1975 aka soma bin tsari na kasancewa da kwamiti na Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah su lura da ayyukan ƙungiyar Allah a duka duniya. An naɗa Kwamitin Reshe su lura da aiki na yankinsu. Tun lokacin, an mai da hankali ga sauƙaƙa aikin da ake yi a hedkwata da kuma a rassa na Watch Tower Society don a yi “abubuwa mafifita.” (Filibiyawa 1:9, 10) Hakki da mataimakan Kristi suke da shi ya ƙunshi shugabanci a aikin wa’azi, koyarwa a cikin ikilisiya, kiwon garken Allah da kyau.—1 Timoti 4:16; Ibraniyawa 13:7, 17; 1 Bitrus 5:2, 3.
Shugabancin Yesu da Ƙwazo
20. Ci gaba da yin tafiya tare da ƙungiyar Jehovah na bukatar mu amince da menene game da matsayin Yesu?
20 Yin tafiya tare da ƙungiyar Jehovah mai ci gaba na bukatar mu amince da matsayi da Allah ya ba Yesu Kristi na “shugaban ikilisiya.” (Afisawa 5:22, 23) Abin da za a lura kuma shi ne Ishaya 55:4, inda aka gaya mana: “[Jehovah] na sa ya zama shugaba, da shugaban yaƙi na al’ummai, ta wurinsa kuwa na nuna musu girmana.” Babu shakka Yesu ya san yadda ake shugabanci. Ya kuma san tumakinsa da ayyukansu. Hakika, lokacin da ya bincika ikilisiyoyi bakwai a Asiya Ƙarama, ya ce sau biyar: “Na san ayyukanka.” (Wahayin Yahaya 2:2, 19; 3:1, 8, 15) Yesu ya san bukatunmu, yadda Ubansa, Jehovah ya sani. Kafin ya koyar da Addu’ar Misali, Yesu ya ce: “Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.”—Matiyu 6:8-13.
21. Yaya shugabancin Yesu yake a cikin ikilisiyar Kirista?
21 Yaya shugabancin Yesu yake? Hanya ɗaya ita ce ta masu kula Kirista, ‘kyauta a mutane.’ (Afisawa 4:8) Wahayin Yahaya 1:16 ya kwatanta masu kula shafaffu suna hannun dama na Kristi, ƙarƙashin ja-gorarsa. A yau, Yesu ne ke ja-gorar tsari na dattawa, ko mutanen nan suna da bege na sama ko na duniya. Yadda aka bayyana a talifi da ya shige, ruhu mai tsarki ne ya naɗa su cikin jituwa da farillai na Nassi. (1 Timoti 3:1-7; Titus 1:5-9) A ƙarni na farko, rukunin dattawa a Urushalima da ke cikin hukumar mulki ne ke lura da ikilisiyoyi da aikin wa’azin Mulki gaba ɗaya. Irin wannan misali ne ake bi cikin ƙungiyar Jehovah a yau.
Ka Ci Gaba da Bi!
22. Wane taimako Hukumar Mulki take tanadinsa?
22 An danƙa wa “amintaccen bawan nan mai hikima,” abubuwan Mulki na duniya, wanda Hukumar Mulki ta Shaidun Jehovah ke wakiltanta. (Matiyu 24:45-47) Muhimmiyar damuwa na Hukumar Mulki ita ce yin tanadin koyarwa ta ruhaniya da ja-gorar ikilisiyar Kirista. (Ayyukan Manzanni 6:1-6) Amma, lokacin da tsarar bala’i ta shafi ’yan’uwa masu bi, Hukumar Mulki tana aika ɗaya ko wasu na hukumar su yi tanadin kayan agaji kuma ta yi gyara da sake gina gidaje da Majami’un Mulki da suka lalace. Idan an bi da wasu Kiristoci da rashin tausayi ko an tsananta musu, ana ɗaukan matakai a gina su a ruhaniya. “Ko da yaushe,” ana ƙoƙari sosai don aikin wa’azi ya ci gaba.—2 Timoti 4:1, 2.
23, 24. Ko da menene ya faɗa wa mutanensa, menene Jehovah yake tanadinsa a kai a kai, me ya kamata ya zama ƙudurinmu?
23 Ko menene ya fāɗa wa mutanensa, Jehovah yana tanadin abinci na ruhaniya da ja-gora da ake bukata a kai a kai. Allah yana kuma ba ’yan’uwa da suke da hakki ja-gora fahimi da basira su yi shiri don ƙarin ci gaba da gyara a tsarin ƙungiya. (Maimaitawar Shari’a 34:9; Afisawa 1:16, 17) Ba tare da kasawa ba, Jehovah yana tanadin abin da muke bukata don mu cika aikinmu na almajirantarwa kuma mu cika hidimarmu a dukan duniya.—2 Timoti 4:5.
24 Muna da gaba gaɗi sosai cewa Jehovah ba zai taɓa yasar da mutanensa masu aminci ba; zai kuɓutar da su a “matsananciyar wahala” mai zuwa. (Wahayin Yahaya 7:9-14; Zabura 94:14; 2 Bitrus 2:9) Muna da dalilin riƙe aminci da muke da shi da farko sosai har zuwa ƙarshe. (Ibraniyawa 3:14) Saboda haka, bari mu ƙuduri aniyyar ci gaba da yin tafiya tare da ƙungiyar Jehovah.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa za mu faɗi cewa ƙungiyar Jehovah tana ci gaba?
• Wane tabbaci ne akwai na nuna cewa mutanen Allah suna more wayewa ta ruhaniya mai ci gaba?
• Yaya aka samu ci gaba a hidimar Kirista?
• Waɗanne gyara na kan lokaci aka yi a tsarin ƙungiyar tsakanin bayin Jehovah?
[Hoto a shafi na 8]
Kamar Dauda, ba za mu iya faɗan dukan ayyuka masu ban al’ajabi na Jehovah ba
[Hoto a shafi na 9]
Garken Allah sun amfana daga gyara na kan lokaci na tsarin ƙungiyar