Kana Bin Ƙungiyar Jehobah Sau da Kafa Kuwa?
“Idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci.”—1 BIT. 3:12.
1. Wace ƙungiya ce Allah ya zaɓa don ta maye gurbin al’ummar Isra’ila da ta yi ridda? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)
MUTANEN Jehobah a yau suna bauta masa yadda yake so. A dā, Allah ya zaɓi al’ummar Isra’ila ta zama mutanensa. Amma sun yi ridda kuma hakan ya sa Jehobah ya kirkiro wata sabuwar al’umma da ta ƙunshi mabiyan Kristi. Ta haka, suka zama ƙungiyar da take ɗaukaka sunan Allah. Wannan ƙungiyar ta tsira a lokacin da aka halaka Urushalima a shekara ta 70 a zamaninmu. (Luk 21:20, 21) Waɗannan abubuwan da suka faru a ƙarni na farko suna nuni ne ga wasu aukuwa da suka shafi Shaidun Jehobah a zamaninmu. Ba da daɗewa ba, za a halaka wannan muguwar duniya amma ƙungiyar Allah za ta tsira. (2 Tim. 3:1) Ta yaya za mu tabbata da hakan?
2. Mene ne Yesu ya faɗa game da “ƙunci mai-girma,” kuma ta yaya za a soma ƙuncin?
2 Yesu ya annabta game da abin da zai faru a kwanaki na ƙarshe kuma ya ce: “Za a yi ƙunci mai-girma, irin da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya har yanzu, ba kuwa za a yi ba dadai.” (Mat. 24:3, 21) Za a soma wannan ƙunci mai girma a lokacin da Jehobah zai yi amfani da gwamnatocin ’yan Adam wajen halaka “Babila Babba,” wato dukan addinan ƙarya. (R. Yoh. 17:3-5, 16) Me zai biyo bayan haka?
FARMAKIN SHAIƊAN ZAI TA DA YAƘIN ARMAGEDDON
3. Wane farmaki ne za a kai wa mutanen Allah bayan an halaka addinin ƙarya?
3 Shaiɗan da bayinsa za su kai wa bayin Allah farmaki bayan an halaka addinin ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya annabta game da “Gog, na ƙasar Magog,” yana cewa: “Za ka hau; kamar hadari za ka zo, kamar girgije za ka rufe ƙasan, kai da dukan rundunan tattarmukanka, da dangi da yawa tare da kai.” Zai zama kamar Shaidun Jehobah ba su da kāriya a lokacin, da yake ba su da masu yaƙi kuma su mutane ne masu son salama. Amma wannan farmakin da za su kawo ɓatan basira ne.—Ezek. 38:1, 2, 9-12.
4, 5. Wane mataki ne Jehobah zai ɗauka sa’ad da aka kai wa mutanensa farmaki?
4 A lokacin da Shaiɗan da mabiyansa suka kai wa mutanen Allah farmaki, zai zama kamar Jehobah ne ake kai wa farmakin. (Karanta Zakariya 2:8.) Wane mataki ne zai ɗauka? Jehobah, Maɗaukakin Sarki zai ɗauki mataki nan da nan don ya ceci bayinsa. Bayan Jehobah ya ceci mutanensa, za a halaka duniyar Shaiɗan a Armageddon, wato “yaƙin babbar rana ta Allah Mai-iko duka.”—R. Yoh. 16:14, 16.
5 Littafi Mai Tsarki ya yi annabci game da Armageddon cewa: “Ubangiji yana shari’a da al’ummai, za ya kai dukan masu-rai garin shari’a; don miyagu kuwa, za ya bashe su ga takobi in ji Ubangiji. Hakanan Ubangiji mai-runduna ya faɗi, Ku duba, masifa za ta fito daga wani dangi zuwa wani, babban hadari kuwa za ya taso daga iyakar duniya. A ran nan fa za a ga kisassun Ubangiji tun daga wannan iyakar duniya zuwa wannan iyaka: ba za a yi makokinsu ba, ba za a tattara, ba kuwa za a binne su ba; za su zama taki a fuskar ƙasa.” (Irm. 25:31-33) Armageddon zai halaka wannan mugun zamanin, amma sashen ƙungiyar Allah da ke duniya zai tsira.
DALILIN DA YA SA ƘUNGIYAR JEHOBAH TAKE SAMUN CI GABA A YAU
6, 7. (a) Daga ina ne mutanen da suke cikin “taro mai girma” suka fito? (b) Wane ƙaruwa ne aka samu a shekarun baya bayan nan?
6 Sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya yana samun ci gaba don ya ƙunshi mutane masu adalci da Jehobah ya amince da su. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idanun Ubangiji suna bisa masu-adalci, kunnuwansa kuma suna buɗe ga jin roƙonsu.” (1 Bit. 3:12) Masu adalcin sun ƙunshi “taro mai-girma” waɗanda “suka fito daga cikin babban tsananin,” wato ƙunci mai girma. (R. Yoh. 7:9, 14) Waɗanda za su tsira ‘taro mai-girma’ ne don suna da yawan gaske. Shin kana ganin kanka cikin waɗanda za su tsira wa ƙunci mai girma?
7 Daga ina ne mutanen da suke cikin wannan taron suka fito? Wa’azin da ake yi ne ya haɗa su wuri ɗaya. Yesu ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Mat. 24:14) Wannan shi ne ainihin aikin da ƙungiyar Allah take yi a duniya a waɗannan kwanaki na ƙarshe. A sakamakon wannan wa’azin da Shaidun Jehobah suke yi, miliyoyin mutane sun koyi yadda za su bauta wa Jehobah “cikin Ruhu da cikin gaskiya.” (Yoh. 4:23, 24) Alal misali, mutane fiye da mutane 2,707,000 ne suka yi baftisma a tsakanin shekara ta 2003 da 2012. A yau, mu Shaidun Jehobah mun fi 7,900,000 a dukan duniya, kuma a kowace shekara miliyoyin mutane da suka fi wannan adadin suna halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu. Ba ma fahariya cewa da ƙarfinmu ne muka cim ma hakan, amma “Allah ne ya ba da amfani.” (1 Kor. 3:5-7) Babu shakka, muna da tabbaci cewa taro mai girma yana ci gaba da ƙaruwa a kowace shekara!
8. Me ya sa adadin mutanen da ke shiga ƙungiyar Jehobah yake ƙaruwa sosai?
8 Bayin Allah suna ƙaruwa sosai domin Jehobah yana tare da Shaidunsa, wato sashen ƙungiyarsa da ke duniya. (Karanta Ishaya 43:10-12.) Ishaya ya yi annabci game da kwanaki na ƙarshe cewa: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama alumma mai-ƙarfi: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Isha. 60:22) A dā, “Isra’ila na Allah” wato shafaffu suna kama da wannan “ƙanƙanin,” amma Allah ya albarkaci wa’azin da suka yi. Kuma adadin su ya ƙaru sosai yayin da Jehobah ya kawo wasu shafaffu zuwa ƙungiyarsa. (Gal. 6:16) Ƙari ga haka, miliyoyin mutanen da suke da begen rayuwa a duniya sun shigo ƙungiyarsa.
ABIN DA JEHOBAH YAKE SO MU YI
9. Me za mu yi idan muna so mu amfana daga alkawari mai kyau da Allah ya yi mana a Littafi Mai Tsarki?
9 Ko da muna cikin shafaffu ne ko kuma taro mai girma, dukanmu za mu more rayuwa a sabuwar duniya da Allah ya yi mana alkawarinta a Littafi Mai Tsarki. Idan muna so mu more wannan rayuwar, ya kamata mu bi umurnan Jehobah. (Isha. 48:17, 18) Alal misali, Jehobah ya bukaci Isra’ilawa su kiyaye Dokarsa. Me ya sa? Domin Dokar za ta kāre su kuma ta taimaka musu su san yadda za su yi zaman lafiya da iyalansu da kuma abokansu. Ƙari ga haka, Dokar za ta kuma sa su yi gaskiya a kasuwanci kuma su riƙa yin alheri. (Fit. 20:14; Lev. 19:18, 35-37; K. Sha 6:6-9) Idan muka bi dokokin Allah za mu amfana sosai. Hakika, yin nufin Allah bai da wuya. (Karanta 1 Yohanna 5:3.) Idan muka kiyaye dokokin Allah, za mu kasance da farin ciki kuma abu mafi muhimmanci shi ne za mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah.—Tit. 1:13.
10. Me ya sa yake da muhimmanci mu keɓe lokaci don yin nazarin Littafi Mai Tsarki da Ibada ta Iyali da yamma?
10 Sashen ƙungiyar Jehobah a duniya tana samun ci gaba sosai a hanyoyi da yawa. Alal misali, muna ƙara fahimtar koyarwar Littafi Mai Tsarki da kyau. Hakan ba abin mamaki ba ne don Littafi Mai Tsarki ya ce, “Tafarkin mai-adalci yana kama da haske na ketowar alfijir, wanda ya ke haskakawa gaba gaba har zuwa cikakkiyar rana.” (Mis. 4:18) Amma ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa: ‘Ina sane da wasu koyarwar Littafi Mai Tsarki da aka ba da ƙarin haske a kansu kuwa? Ina karanta Littafi Mai Tsarki a kowace rana kuwa? Ina jin daɗin karanta littattafanmu kuwa? Ni da iyalina muna Ibada ta Iyali da yamma a kai a kai kuwa? Dukanmu za mu yarda cewa bai da wuya sosai mu yi waɗannan abubuwan, amma wajibi ne mu keɓe lokaci don yin su. Yana da muhimmanci mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah kuma mu bi abin da muka koya don mu ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah da yake ƙarshen ya yi kusa.
11. A waɗanne hanyoyi ne taron da Isra’ilawa suka yi a dā da kuma waɗanda muke a yau suke da amfani?
11 Ƙungiyar Jehobah ta ƙarfafa mu mu bi kashedin Bulus cewa: “Bari kuma mu lura da juna domin mu tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka; kada mu fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi, amma mu gargaɗar da juna; balle fa yanzu, da kuna ganin ranan nan tana gusowa.” (Ibran. 10:24, 25) Isra’ila ta dā ta saba yin taro don bauta wa Jehobah don su ƙarfafa dangantakarsu da shi. Yin Idin Bukkoki ya sa mutane farin ciki sosai a zamanin Nehemiya. (Fit. 23:15, 16; Neh. 8:9-18) Hakazalika, a yau ma muna amfana daga taron ikilisiya da manyan taro da kuma taron gunduma. Bari mu ci gaba da halartan waɗannan taron duka don hakan zai sa mu kusaci Jehobah kuma mu kasance da farin ciki.—Tit. 2:2.
12. Yaya ya kamata mu ɗauki wa’azin bishara ta Mulki?
12 Ya kamata mu yi “hidimar bisharar Allah” a matsayin waɗanda suke cikin ƙungiyar Jehobah. (Rom. 15:16) Idan muka yi hakan mu ‘abokan aikin’ Allah “Mai-tsarki” Jehobah ne. (1 Kor. 3:9; 1 Bit. 1:15) Yin wa’azin bishara yana tsarkake suna mai tsarki na Jehobah. Babu shakka, wannan aikin “bishara ta darajar Allah mai-albarka” gata ne babba a gare mu.—1 Tim. 1:11.
13. Rayuwarmu da dangantakarmu da Jehobah sun dangana ga yin me?
13 Jehobah yana so mu amfana sosai ta wajen yin biyayya da shi da kuma tallafa wa ƙungiyarsa a hanyoyi dabam-dabam. Abin da Musa ya gaya wa Isra’ilawa ya shafe mu a yau, ya ce: “Ina kira sama da ƙasa su shaida a kanku yau, na sa rai da mutuwa a gabanka, albarka da la’ana: ka zaɓi rai fa, domin ka rayu, da kai da zuriyarka: garin ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka, ka ji muryatasa, ka manne masa: gama shi ne ranka, da tsawon kwanakinka: domin ka zauna cikin ƙasa wadda Ubangiji ya rantse wa ubanninka, Ibrahim, da Ishaku, da Yakub, za ya ba su ita.” (K. Sha 30:19, 20) Rayuwarmu ta dangana ne ga ƙaunar Jehobah da yin nufinsa da kuma bin umurninsa da na ƙungiyarsa a koyaushe.
14. Mene ne ra’ayin wani ɗan’uwa game da sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya?
14 Wani ɗan’uwa mai suna Pryce Hughes da ya kasance da aminci ga Allah kuma ya bi ƙungiyarsa sau da kafa, ya ce: “Ina godiya ga Allah cewa na ci gaba da yin nufin Jehobah tun kwanakin da suka gabaci 1914 . . . Wani darasi da na koya shi ne bin umurnin sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya sau da kafa. Bin tunanin ɗan Adam ɓatan basira ne. Sa’ad da na fahimci hakan, sai na ƙuduri niyyar kasancewa da aminci ga ƙungiyar Jehobah. Ta wannan hanyar ne kawai Jehobah zai albarkace mu.”
KA CI GABA DA BIN ƘUNGIYAR JEHOBAH SAU DA KAFA
15. Wane misali na Littafi Mai Tsarki ne yake koya mana yadda ya kamata mu ɗauki ƙarin haske da muke samu game da koyarwar Littafi Mai Tsarki?
15 Jehobah yana so mu ci gaba da tallafa wa ƙungiyarsa kuma mu riƙa amincewa da ƙarin haske da muke samu game da koyarwar Littafi Mai Tsarki da yadda muke wa’azi. A ƙarni na farko, wasu Yahudawa da suka zama Kiristoci suna so su ci gaba da bin dokar da aka ba da ta hannun Musa. (A. M. 21:17-20) Amma, sa’ad da Bulus ya taimaka musu ta wasiƙar da ya rubuta ga Ibraniyawa, sai suka amince cewa ba ta hadayun da ake “miƙawa bisa ga shari’a” aka gafarta zunubansu ba, amma ta wurin hadayar “jikin Yesu Kristi” ne. (Ibran. 10:5-10) Babu shakka, waɗannan Kiristoci Yahudawa sun bukaci su daidaita tunaninsu don su ci gaba da ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Hakazalika, mu ma muna bukata mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da littattafanmu sosai kuma mu kasance da sauƙin kai wajen amincewa da ƙarin haske da ake samu game da koyarwar Littafi Mai Tsarki ko kuma yadda muke wa’azi.
16. (a) Waɗanne abubuwa ne za su sa rayuwa a Aljanna ta yi daɗi? (b) Mene ne kake begensa a sabuwar duniya?
16 Jehobah zai ci gaba da albarkar duk waɗanda suke bin umurninsa da kuma ja-gorar da ƙungiyarsa take bayarwa. Shafaffu masu aminci za su sami gatan yin sarauta tare da Yesu a sama. (Rom. 8:16, 17) Idan muna da begen yin rayuwa a Aljanna a duniya, ka yi tunanin yadda za mu ji daɗin rayuwa a lokacin. A matsayin waɗanda suke cikin ƙungiyar Jehobah, muna da gatan gaya wa mutane game da wannan begen. (2 Bit. 3:13) Zabura 37:11 ta ce: “Masu-tawali’u za su gāji ƙasan; za su faranta zuciyarsu kuma cikin yalwar salama.” Mutane “za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki” kuma za su ji daɗin “aikin hannuwansu.” (Isha. 65:21, 22) Ba za a ƙara yin mugunta ko talauci ko yunwa ba. (Zab. 72:13-16) Addinan ƙarya ba za su ƙara yaudarar mutane ba don za a kawar da su gaba ɗaya. (R. Yoh. 18:8, 21) Za a ta da waɗanda suka mutu kuma a ba su damar yin rayuwa har abada. (Isha. 25:8; A. M. 24:15) Idan muka ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah kuma muka ci gaba da bin ƙungiyarsa sau da kafa, za mu shaida cikar waɗannan alkawuran.
17. Wane irin ra’ayi ne ya kamata mu kasance da shi game da bautar Jehobah da kuma ƙungiyarsa?
17 Da yake wannan mugun zamanin yana gab da ƙarewa, yana da muhimmanci mu ƙarfafa bangaskiyarmu kuma mu riƙa bauta wa Jehobah tare da ƙungiyarsa. Ra’ayin da Dauda ya kasance da shi ke nan sa’ad da ya ce: “Abu guda ɗaya na yi roƙo ga Ubangiji, shi zan nema; in zauna cikin gidan Ubangiji dukan kwanakin raina, domin in dubi jamalin Ubangiji, in yi ta tunani cikin haikalinsa.” (Zab. 27:4) Bari dukanmu mu kusaci Jehobah kuma mu ci gaba da bin ƙungiyarsa sau da kafa.