Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w13 4/15 pp. 27-31
  • Kada Ka Yi ‘Suwu’

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Yi ‘Suwu’
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • TARO DON ƘARFAFA DA IBADA
  • NEMAN MASU ZUKATAN KIRKI
  • KA AMFANA DAGA LITTATTAFANMU
  • KA GOYI BAYAN ƘUNGIYAR JEHOBAH
  • KA YI AYYUKAN DA ZA SU FARANTA WA ALLAH RAI
  • ‘Ka gwada Mafifitan Al’amura’
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
  • Jehobah Yana Yi wa Kungiyarsa Ja-goranci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Kana Bin Ƙungiyar Jehobah Sau da Kafa Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
  • Me Ya Sa Ya Kamata Mu Rika Halartan Taro don Ibada?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2016
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
w13 4/15 pp. 27-31

Kada Ka Yi ‘Suwu’

“Kada mu yi kasala kuma cikin aikin nagarta.”—GAL. 6:9.

MECE CE AMSARKA?

  • Waɗanne tanadi ne suke taimaka mana mu kasance da ƙwazo?

  • Mene ne za mu yi idan muka tuna cewa bauta wa Jehobah ne ainihin dalilinmu na halartar taro?

  • Ta yaya shawarar da muka tsai da za ta sa mu jimre a hidimarmu ko kuma mu yi suwu?

1, 2. Mene ne wahayi game da ƙungiyar Jehobah yake motsa mu mu yi?

ABIN mamaki ne sanin cewa muna cikin sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama da kuma duniya. Wahayin da ke littafin Ezekiyel sura ta 1 da Daniyel sura ta 7 sun bayyana yadda Jehobah yake aiki don cika nufinsa. Yesu yana ja-gora a sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya. Yana ja-gora a aikin wa’azi kuma yana koyar da ƙarfafa waɗanda suke yin wannan aikin. Ƙari ga hakan, yana taimaka wa mutane su zama bayin Jehobah. Hakan yana motsa mu mu dogara ga ƙungiyar Jehobah.—Mat. 24:45.

2 Shin muna bin misalin wannan ƙungiyar ta wajen yin ƙwazo a hidimar Jehobah? Ko kuma mun soma yin sanyi-sanyi? Hakan ya faru wa wasu Kiristoci a ƙarni na farko. Sai manzo Bulus ya tuna musu yadda Yesu yake yin ƙwazo. Ya kuma ce hakan zai taimaka musu kada su gaji ko ‘su yi suwu cikin rayukansu.’ (Ibran. 12:3) A talifin da ya gabata, mun tattauna ayyuka masu ban al’ajabi da ƙungiyar Jehobah take cim ma a yau. Kamar yadda misalin Kristi ya ƙarfafa Kiristoci a ƙarni na farko, hakan ma misalin ƙungiyar Jehobah zai iya taimaka mana a yau mu jimre a hidimar Jehobah kuma mu kasance da ƙwazo.

3. Mene ne muke bukatar mu yi don kada mu yi suwu, kuma me za mu tattauna a wannan talifin?

3 Ko da yake muna bukatar mu yi tunani game da ƙungiyar Jehobah idan ba ma son mun yi suwu, amma ba shi ke nan ba. Bulus ya ce muna bukatar mu ci gaba da yin “aikin nagarta.” (Gal. 6:9) Bari mu tattauna abubuwa biyar da za su taimaka mana mu ci gaba da yin ƙwazo, kuma mu bi ja-gorar ƙungiyar Jehobah. Hakan zai sa mu ga ko akwai inda mu ko iyalinmu ke bukatar ɗan gyara.

TARO DON ƘARFAFA DA IBADA

4. Me ya sa za mu ce taro sashe ne mai muhimmanci na bautarmu?

4 Taro yana da muhimmanci sosai ga bayin Jehobah. Jehobah yana yin taro da mala’ikunsa a sama. (1 Sar. 22:19; Ayu. 1:6; 2:1; Dan. 7:10) Allah ya gaya wa Isra’ilawa a zamanin dā su taru “domin su ji, su koya” kuma. (K. Sha 31:10-12) A ƙarni na farko, Yahudawa sukan taru a kai a kai a majami’u don su karanta Nassosi. (Luk 4:16; A. M. 15:21) A lokacin da aka kafa ikilisiyar Kirista ma, ba a daina taro ba, kuma har ila sashe ne mai muhimmanci a bautarmu. Kiristoci na gaskiya suna ‘lura da juna domin su tsokani juna zuwa ga ƙauna da nagargarun ayyuka.’ Muna bukatar mu ci gaba da ƙarfafa juna “balle fa yanzu, da [muke] ganin ranan [Jehobah] tana gusowa.”—Ibran. 10:24, 25.

5. Ta yaya za mu iya ƙarfafa juna a taronmu?

5 Wata hanya mai muhimmanci da za mu iya ƙarfafa ’yan’uwanmu a taro ita ce ta wajen ba da kalamai. Alal misali, za mu iya amsa tambayar da ke sakin layi ko mu faɗi yadda za a yi amfani da wata ƙa’idar Nassi ko kuma mu ba da wani labari da ya nuna yadda bin ƙa’idodin Nassosi za su amfane mu. (Zab. 22:22; 40:9) Hakika, ko da mun daɗe muna halartar taro, kalaman ’yan’uwanmu matasa da tsofaffi suna ƙarfafa mu sosai.

SASHEN ƘUNGIYAR JEHOBAH DA KE DUNIYA YA ƘUNSHI:

  1. Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah

  2. Kwamitin da ke Kula da Reshe

  3. Masu kula masu ziyara

  4. Rukunin dattawa

  5. Ikilisiyoyi

  6. Kowane mai shela

6. A waɗanne hanyoyi ne taronmu yake taimaka mana?

6 Mene ne kuma ya sa halartar taro a kai a kai yake da muhimmanci? Taron ikilisiya da kuma manyan taro suna sa mu kasance da gaba gaɗin yin wa’azi da kuma jimre da tsanani da muke fuskanta a yankinmu. (A. M. 4:23, 31) Jawabai da kuma abubuwa da ake tattaunawa daga Nassosi suna ƙarfafa mu. (A. M. 15:32; Rom. 1:11, 12) Yin tarayya da ’yan’uwa yana sa mu farin ciki da gaske kuma yana ta’azantar da mu. (Zab. 94:12, 13) Kwamitin Koyarwa da ke cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne yake tsara koyarwar da ake yi a duk taron bayin Jehobah a faɗin duniya. Muna godiya sosai domin gargaɗin da muke samu a taronmu kowace mako.

7, 8. (a) Mene ne dalili mafi muhimmanci na zuwa taro? (b) Ta yaya taro yake taimaka maka?

7 Amma, akwai dalili mafi muhimmanci da ya sa muke halartar taro. Wannan dalilin shi ne don bauta wa Jehobah. (Karanta Zabura 95:6.) Babban gata ne mu rera waƙar yabo ga Allahnmu mai ban al’ajabi. (Kol. 3:16) Muna kuma yabon Jehobah ta wajen kalaman da muke yi a taro. Jehobah ya isa mu yaba masa ta waɗannan hanyoyin. (R. Yoh. 4:11) Hakan ya nuna cewa bai kamata mu riƙa “fasa tattaruwanmu, kamar yadda waɗansu sun saba yi” ba.—Ibran. 10:25.

8 Shin muna ɗaukan taron Kirista a matsayin tanadin da Jehobah ya yi mana don mu jimre har sai ya halaka wannan muguwar duniyar? Idan ra’ayinmu ke nan, taro zai zama mana ɗaya cikin “mafifitan al’amura” da bai kamata mu yi watsi da shi ba, duk da cewa muna shagala cikin ayyuka da yawa a rayuwa. (Filib. 1:10) Hakan zai sa ba za mu taɓa fasa taro ba gaira ba dalili ba.

NEMAN MASU ZUKATAN KIRKI

9. Ta yaya muka san cewa aikin wa’azi yana da muhimmanci?

9 Idan ba ma son ƙungiyar Jehobah ta bar mu a baya, wajibi ne mu shagala a aikin wa’azi. Yesu ne ya soma wa’azi sa’ad da yake duniya. (Mat. 28:19, 20) Tun daga lokacin, aikin wa’azi da kuma almajirantarwa ya zama ɗaya cikin ayyuka masu muhimmanci da ƙungiyar Jehobah take yi. Labarai na kwanan nan sun nuna cewa mala’iku suna taimaka mana kuma suna ja-gorar mu zuwa wurin masu son saƙonmu. (A. M. 13:48; R. Yoh. 14:6, 7) Ainihin manufar sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya ita ce ta tsara da kuma tallafa wa aikin wa’azi. Kai kuma fa, shin aikin wa’azi ɗaya ne cikin abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarka?

10. (a) Mene ne ya taimaki wani ɗan’uwa ya ci gaba da son gaskiya? (b) Ta yaya hidima ta taimake ka ka ci gaba da son gaskiya?

10 Yin wa’azi da ƙwazo yana taimaka mana mu daɗa son gaskiya. Wani dattijo da kuma majagaba mai suna Mitchel ya yarda da hakan. Ya ce: “Ina jin daɗin gaya wa mutane gaskiya game da Allah. Ina tunani a kan hikima da fahimi da ke cikin kowane talifi na Hasumiyar Tsaro ko kuma Awake! da kuma yadda talifofin suke bayyana abubuwa daidai wa daida. Hakan yana motsa ni in fita wa’azi, don in ji ra’ayin mutane a kan waɗannan bayanan kuma in ga yadda zan sa su so saƙonmu. Hidimata tana taimaka mini in mai da hankali ga mafifitan al’amura, kuma ba na ƙyale kome ya hana ni yin wa’azi.” Hakan nan ma, za mu iya jimre a waɗannan kwanaki na ƙarshe, idan muka shagala a hidimar Allah.—Karanta 1 Korintiyawa 15:58.

KA AMFANA DAGA LITTATTAFANMU

11. Me ya sa ya kamata mu karanta da kuma yi bimbini a kan littattafanmu?

11 Jehobah ya tanadar da littattafai da yawa da za su ƙarfafa mu. Wataƙila za ka tuna da lokacin da ka karanta wani littafi, sai ka ce, ‘Ainihin abin da nake bukata ke nan! Kamar dai don ni ne Jehobah ya sa aka rubuta shi!’ Akwai abin da ya sa kake jin hakan. Jehobah yana koya mana da kuma yi mana ja-gora ta wajen waɗannan littattafan. Jehobah ya ce: “Zan koya maka hanyar da za ka bi.” (Zab. 32:8 Littafi Mai Tsarki) Muna ƙoƙartawa wajen karanta dukan littattafan da muke karɓa, kuma mu yi bimbini a kansu? Hakan zai taimaka mana mu jimre, kuma mu ci gaba da yin hidima ga Allah da ƙwazo a waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Karanta Zabura 1:1-3; 35:28; 119:97.

12. Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki littattafanmu da tamani sosai?

12 Za mu ɗauki littattafanmu da tamani sosai, idan muka yi la’akari da yadda ake shirya su. Ana bukatar a bincika da rubuta da zaɓan hotunan da za a saka da kuma fassara kowane littafin da ake bugawa da kuma sakawa a Yanar gizonmu. Kuma, Kwamitin Rubuce-Rubuce da ke cikin Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ne yake ja-gorar wannan aikin. Ofisoshin reshe da ke buga waɗannan littattafan suna aika su zuwa ikilisiyoyi masu yawa. Me ya sa ake waɗannan ayyukan? Domin mutanen Jehobah su samu gargaɗi da kuma ja-gorar da suke bukata don su kasance da aminci. (Isha. 65:13) Ya kamata mu ci gaba da amfana daga dukan littattafan da ƙungiyar Jehobah ke tanadarwa.—Zab. 119:27.

KA GOYI BAYAN ƘUNGIYAR JEHOBAH

13, 14. Su wane ne suke goyon bayan ƙungiyar Jehobah a sama, kuma ta yaya za mu yi hakan a duniya?

13 A wahayin da aka saukar wa manzo Yohanna, ya ga Yesu yana sukuwa a kan farin doki don ya halaka waɗanda suke tawaye da Jehobah. (R. Yoh. 19:11-15) Ya kuma ga amintattun mala’iku da kuma shafaffu da aka ta da daga matattu zuwa sama biye da Yesu a kan nasu dawakan. Hakan ya nuna cewa suna goyon bayan Yesu a matsayin shugabansu. (R. Yoh. 2:26, 27) Sun kafa mana misali mai kyau na goyon bayan waɗanda suke ja-gora a ƙungiyar Jehobah.

14 Hakazalika, babban garke suna goyon bayan Kiristoci shafaffu da suka ragu a duniya, kuma suke ja-gorar ƙungiyar Jehobah a yau. (Karanta Zakariya 8:23.) Ta yaya za ka nuna cewa kana goyon bayan wannan ƙungiyar? Za ka iya yin hakan ta wajen yin biyayya ga waɗanda suke ja-goranci. (Ibran. 13:7, 17) Ya kamata mu soma yin hakan a cikin ikilisiyarmu. Shin hirar da muke yi game da dattawa tana daraja su da kuma aikin da suke yi? Muna koya wa yaranmu su riƙa daraja waɗannan maza amintattu kuma su bi shawararsu? Ƙari ga haka, muna tattauna yadda za mu tallafa wa aikin wa’azi ta wajen ba da gudummawa a matsayin iyali? (Mis. 3:9; 1 Kor. 16:2; 2 Kor. 8:12) Shin muna saka hannu don tsabtace da kuma kula da wajen da muke taro? Jehobah zai ba mu ruhunsa, idan ya lura da yadda muke goyon bayan ƙungiyarsa a waɗannan hanyoyin. Ruhunsa kuma zai taimaka mana mu ci gaba da jimrewa a waɗannan kwanaki na ƙarshe.—Isha. 40:29-31.

KA YI AYYUKAN DA ZA SU FARANTA WA ALLAH RAI

15. Me ya sa muke bukatar mu riƙa fama kullum don mu yi nufin Jehobah?

15 A ƙarshe, wajibi ne mu yi abubuwa da za su faranta wa Jehobah rai idan muna son mu jimre, kuma mu ci gaba da bin ja-gorar ƙungiyar Jehobah. (Afis. 5:10, 11) A koyaushe, muna fama don kada kasawarmu da Shaiɗan da kuma duniyarsa su shawo kanmu. ’Yan’uwa, wasu a cikinku suna fama kowace rana don su kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah. Hakan yana sa Jehobah ya ƙaunace ku sosai. Kada ku yi suwu! Muna da tabbaci cewa Jehobah zai amince da mu, kuma za mu more rayuwa mai ma’ana da farin ciki idan muna faranta masa rai.—1 Kor. 9:24-27.

16, 17. (a) Idan mun yi zunubi mai tsanani, mene ne ya dace mu yi? (b) Mene ne za mu koya daga misalin Anne?

16 Amma idan mun yi zunubi mai tsanani fa, mene ya kamata mu yi? Yin ɓoye-ɓoye ba zai taimaka mana ba. Ka nemi taimako nan da nan. Ka tuna da Dauda. Ya ce sa’ad da ya yi ƙoƙarin ɓoye zunubinsa, sai ‘ƙasusuwasa suka tsufa domin kukansa da ya yini yana yi.’ (Zab. 32:3) Hakika, za mu daina yin farin ciki kuma dangantakarmu da Jehobah za ta yi tsami idan muka yi ƙoƙarin ɓoye zunubanmu. Amma, “wanda ya faɗe su ya kuwa rabu da su za ya sami jinƙai.”—Mis. 28:13.

17 Ka yi la’akari da misalin wata mai suna Anne.a Sa’ad da take matashiya ta yi hidimar majagaba, amma kuma tana yin wasu zunubai a ɓoye. Hakan ya sa zuciyarta ta riƙa damunta. Ta ce: “Ba na farin ciki kuma ina damuwa kowane lokaci.” Wane mataki ne ta ɗauka? Ta ce sa’ad da take taro wata rana, sai aka tattauna littafin Yaƙub 5:14, 15. Hakan ya sa ta fahimci cewa tana bukatar taimako, kuma ta je wajen dattawa don su taimaka mata. Anne ta ce: “Waɗannan nassosin suna kamar magani da zai sa mutum ya gyara dangantakarsa da Jehobah. Wannan maganin yana da ɗaci, amma yana warkarwa. Bin shawarar da ke cikin nassosin ya taimaka mini.” Yanzu Anne ta soma bauta wa Jehobah da ƙwazo kuma zuciyarta ta daina damunta.

18. Mene ne ya kamata mu ci gaba da yi?

18 Gata ne cewa muna cikin ƙungiyar Jehobah a waɗannan kwanaki na ƙarshe. Bari mu ƙudurta cewa ba za mu yi watsi da abubuwan da muke da su ba. Maimakon haka, mu ƙoƙarta a matsayin iyali wajen halartar taro a kai a kai da yin wa’azi a yankinmu da ƙwazo, kuma mu riƙa amfana sosai daga littattafanmu. Mu goyi bayan waɗanda suke ja-gora kuma mu yi ayyukan da za su faranta wa Jehobah rai. Idan muka yi hakan, ƙungiyar Jehobah ba za ta bar mu a baya ba kuma ba za mu yi suwu ba.

a An canja sunan.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba