Yadda Hukumar Mulki ta Bambanta Daga Rukunin Doka
ANA yin taron shekara shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania tun Janairu na shekara ta 1885. Lokacin da ake tattara shafaffun Kiristoci a kusan ƙarshen ƙarni 19, darektoci da hafsoshin wannan rukunin suna da begen zuwa sama. Hakika, haka yake tun dā.
Akwai abin da ba a haɗa ba. A shekara ta 1940, Hayden C. Covington—mai lura da aikin dokokin Society a lokacin, da yake cikin “waɗansu tumaki,” da ke da begen zama a duniya—an zaɓe shi darekta na Society. (Yahaya 10:16) Ya yi hidima na mataimakin shugaban Society daga shekara ta 1942 zuwa 1945. A wannan lokacin, Ɗan’uwa Covington ya koma gefe daga hidimar darekta, a bin aba da kamar nufin Jehovah ne a lokacin—duka darektoci da hafsoshin rukunin Pennsylvania su kasance shafaffun Kiristoci. Lyman A. Swingle ya ɗauki matsayin Hayden C. Covington a rukunin darektoci, kuma aka zaɓi Frederick W. Franz mataimakin shugaba.
Me ya sa bayin Jehovah suka gaskata cewa duka darektoci da hafsoshin Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania ya kamata su zama shafaffu Kiristoci? Domin a lokacin can, rukunin darektoci da hafsoshi na rukunin Pennsylvania an san su sosai da Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah, waɗanda dukansu maza ne da ruhu mai tsarki ya naɗa.
Taro na Musamman a Tarihi
A taron da aka yi a 2 ga Oktoba, 1944 a Pittsburgh, waɗanda suke cikin rukunin Pennsylvania sun yarda da zartarwa guda shida da ta gyara takardar sharaɗinsu. Takardar sharaɗin ya ce za a ba waɗanda suka tara kuɗaɗe ga aikin Society rabon zaɓen, amma gyara ta uku ta kawar da wannan tanadi. Wani rahoto a kan wannan taron ya lura: “Waɗanda za su kasance cikin Society ba za su fi 500 ba . . . Kowanne da aka zaɓa dole ya zama bawa na cikakken lokaci na Society ko bawa na ƙaramin lokaci na wani kamfani [ikilisiya] na shaidun Jehovah kuma nuna halin Ubangiji.”
Saboda haka, waɗanda suka ba da kansu ga Jehovah ne za su zaɓi darektoci na Society zuwa matsayi, ko da nawa suka ba da don ci gaba da aikin Mulki. Wannan ya zama daidai da gyara mai ci gaba da aka annabta a Ishaya 60:17, inda muka karanta: “Zan kawo miki zinariya maimakon tagulla, Azurfa maimakon baƙin ƙarfe, Tagulla kuma maimakon itace. Za ki sami baƙin ƙarfe maimakon dutse. Masu mulkinki ba za su ƙara zaluntarki ba, Zan sa su yi mulki da gaskiya da salama.” A yin nuni ga ‘masu kula’ da ‘mahukunci,’ wannan annabci yana nuni ga ci gaba a tsarin ƙungiya tsakanin mutanen Jehovah.
Wannan muhimmin matakin kawo ƙungiyar daidai da tsari na Allah ya faru a ƙarshen “kwana dubu biyu da ɗari uku,” da aka ambata a Daniyel 8:14. A lokacin nan, “wuri mai tsarki” an ‘maido da shi daidai da yadda yake a dā.’
Amma, bayan taro na musamman a shekara ta 1914, muhimmiyar tambaya ta kasance. Tun da yake a lokacin an san Hukumar Mulki mutane bakwai ne da suke cikin rukunin darektoci na Pennsylvania, wannan yana nufin ke nan Hukumar Mulki ba za ta taɓa wuce shafaffu Kiristoci bakwai ba? Ƙari ga haka, tun da yake waɗanda suke rukunin ne ke zaɓan darektoci, waɗanda suke cikin rukunin suna zaɓan waɗanda ke Hukumar Mulki a taron da ake yi kowacce shekara ne? Darektoci da hafsoshi na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da Hukumar Mulki ɗaya ne, ko kuwa dabam suke?
Wani Taro na Shekara Shekara da ba Za a Manta Ba
An amsa waɗannan tambayoyi a taron da aka yi a ranar 1 ga Oktoba, 1971. A lokacin, ɗaya cikin masu jawabin ya nuna cewa hukumar mulki ta “amintaccen bawan nan mai hikima” ta riga Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da shekaru ɗarurruwa. (Matiyu 24:45-47) An kafa hukumar mulki a Fentakos a shekara ta 33 A.Z., fiye da ƙarnuka 18 kafin rukunin Pennsylvania ya wanzu. A farko, hukumar mulki ta ƙunshi manzanni 12 ba maza 7 ba. Hakika, an ƙara adadinta daga baya, gama “manzanni da dattawan” a Urushalima suna shugabanci.—Ayyukan Manzanni 15:2.
A shekara ta 1971 mai jawabin nan ya yi bayani cewa waɗanda suke Watch Tower Society ba za su iya zaɓan waɗanda za su kasance cikin Hukumar Mulki da su shafaffu ne ba. Me ya sa? “Domin,” ya ce, “hukumar mulki na ajin ‘bawa’ ba mutane ba ne suka naɗa su. Yesu Kristi Shugaban ikilisiyar Kirista ta gaske da Ubangiji kuma Ubangida na ajin ‘amincaccen bawa mai hikima’ ne . . . ya naɗa ta.” A bayyane yake, waɗanda suke rukunin aikin doka ba za su iya zaɓan waɗanda suke Hukumar Mulki zuwa wani matsayi ba.
Da yake ci gaba, mai jawabin ya yi wannan furci mai muhimmanci: “Hukumar mulkin ba ta da hafsoshi irin waɗanda Rukunin Darektoci na Society suke da shi, wato, shugaba, mataimakin shugaba, ma’ajin sakatare da mataimakin ma’ajin sakatare. Tana da mai kujera ne kawai.” Shekaru da yawa, shugaban rukunin Pennsylvania shi ne a kan gaba cikin Hukumar Mulki. Wannan ba zai ƙara zama haka ba. Ko da yake ba za su kasance daidai da basira ko kuma iyawa, waɗanda suke cikin Hukumar Mulki za su daidaita wajen hakkinsu. Mai jawabin ya daɗa: “Kowane cikin hukumar mulki zai iya zama mai kujera ba tare da zama shugaba na . . . Society ba . . . Duka ya dangana bisa zagayawa na aikin mai kujera cikin hukumar mulkin ne.”
A wannan taro na musamman a shekara ta 1971, an nuna bambanci dalla-dalla da ke tsakanin waɗanda suke Hukumar Mulki da ruhu ya shafe su da darektocin rukunin Pennsylvania. Duk da haka, waɗanda suke cikin Hukumar Mulki sun ci gaba da hidima na darektoci da hafsoshi na Society. Amma, a yau tambaya ta taso: Akwai wani dalili na Nassi da ya nuna cewa darektoci na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania dole su zama waɗanda suke Hukumar Mulki?
Amsar, babu ne. Rukunin Pennsylvania ba shi ne kaɗai rukunin doka da Shaidun Jehovah suke amfani da shi ba. Akwai wasu. Ɗaya shi ne Watchtower Bible and Tract Society of New York, Incorporated. Yana sauƙaƙa aikinmu a United States. Albarkar Jehovah tana kan wannan rukunin, ko da yake darektocinsa da hafsoshinsa daga “waɗansu tumaki” ne. Ana amfani da International Bible Students Association (Rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki na Dukan Ƙasashe) a Britaniya. Wasu rukunin doka ana amfani da su wajen tallafa wa abubuwan Mulki a wasu ƙasashe. Dukansu suna haɗa kai suna taimaka kuma suna da aikin yi a ganin cewa an yi wa’azin bishara a duniya duka. Duk inda suke ko kuma su wanene suke hidima na darektoci ko hafsoshi, Allah ne ke ja-gorar waɗannan rukunin kuma Hukumar Mulki tana amfani da su. Saboda haka, irin wannan rukuni sun ba da aiki da za a yi don abubuwan Mulki ta ci gaba.
Yana da amfani mu samu rukunin doka. Da haka muna bin dokoki na yanki da na ƙasa, yadda Kalmar Allah ta bukace mu. (Irmiya 32:11; Romawa 13:1) Rukunin doka yana sauƙaƙa aikinmu na yaɗa saƙon Mulki ta buga Littafi Mai Tsarki, littattafai, jaridu, mujallu, da wasu abubuwa. Irin wannan rukuni na aikin sarrafa al’amura game da dukiya, kayan agaji, dawajewa a yin amfani da wurin babban taro, da sauransu. Muna godiya don hidimomi na irin waɗannan rukunonin.
Sunan Jehovah na Kan Gaba
A shekara ta 1944, an gyara Talifi na II na takardar sharaɗi na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania don ya nuna manufar wannan rukunin. In ji takardar sharaɗin, manufar Society ta ƙunshi wannan nufi na musamman: “A yi wa’azin bishara na mulkin Allah ƙarƙashin Kristi Yesu ga dukan al’ummai domin shaida ga sunan, kalmarsa da kuma mafificin Maɗaukakin Allah JEHOVAH.”
Tun shekara ta 1926 ‘amintaccen bawan’ ya kawo sunan Jehovah a kan gaba. Abin lura na musamman, shekara ta 1931 ce lokacin da Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka ɗauki sunan nan Shaidun Jehovah. (Ishaya 43:10-12) Littattafai na Society da suka nanata sunan Allah sun ƙunshi littattafan nan Jehovah (a 1934), “Let Your Name Be Sanctified” (a 1961), da kuma “The Nations Shall Know That I Am Jehovah”—How? (a 1971).
Dole a ambata New World Translation of the Holy Scriptures musamman, da aka buga gaba ɗayanta a Turanci a shekara ta 1960. Yana ɗauke da sunan Jehovah a kowane wuri da Tetragrammaton (baƙaƙe huɗu) ya bayyana a Nassosin Ibrananci. Wannan juyin kuma yana ɗauke da sunan Allah a wurare 237 a Nassosin Kirista na Helenanci inda bincike sosai ya nuna cewa wannan daidai yake. Muna godiya cewa, a hanyoyi dabam dabam Jehovah ya ba wa “bawan nan” da Hukumar Mulki izini su yi amfani da hanyar bugu da kuma rukunin doka a sanar da sunansa a duniya duka!
An Ɗaukaka Rarraba Kalmar Allah
Mutanen Jehovah koyaushe suna shaida ga sunansa kuma suna ɗaukaka Kalmarsa ta wajen bugawa da kuma rarraba miliyoyin littattafai masu tushe cikin Littafi Mai Tsarki da kuma Littafi Mai Tsarki kansa. A farkon shekarun 1900, Watch Tower Society ya zama mai hakkin wallafawa na The Emphatic Diaglott, bugun Helenanci na Turanci na Benjamin Wilson na Nassosin Kirista na Helenanci. Society ya fitar da bugun King James Version na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki, wanda ya ƙunshi ƙarin rubutu a matani na ƙarshe mai shafi 500. A shekara ta 1942 ya buga King James Version da hasiya a tsakiya. Sai kuma a shekara ta 1944 Society ya soma buga American Standard Version na 1901, wanda ya yi amfani da sunan Allah. Sunan Jehovah kuma na cikin The Bible in Living English, na Stephen T. Byington, da Society ya buga a shekara ta 1972.
Rukuni da Shaidun Jehovah suke amfani da shi sun taimaka a buga da kuma rarraba dukan waɗannan juyin Littafi Mai Tsarki. Amma, abin da aka fi lura shi ne haɗin kai na kurkusa da ke tsakanin Watch Tower Society da rukunin shafaffu na Shaidun Jehovah da ya haɗa da Kwamitin New World Bible Translation. Muna farin ciki cewa a duka duka ko kuma wasu, yanzu an buga fiye da kofi 106,400,000 na wannan juyin a harsuna 38. Da gaske Watch Tower Bible and Tract Society na Pennsylvania, rukuni ne na Littafi Mai Tsarki!
‘Amintaccen bawan’ an danƙa masa ‘dukan mallakar ubangijinsa.’ Waɗannan sun ƙunshi kayayyakin aiki a hedkwata a New York State, U.S.A., da rassa 110 da suke aiki yanzu a duniya duka. Waɗanda suke ajin bawan sun san za a kira su su ba da lissafin yadda suka yi amfani da abin da aka danƙa musu. (Matiyu 25:14-30) Duk da haka, wannan bai hana ‘bawan’ ya yi amfani da masu kula da suka ƙware daga cikin “waɗansu tumaki” su kula da ayyuka ta doka da kuma ta mulki ba. Hakika, wannan ya ba waɗanda suke cikin Hukumar Mulki zarafi su ƙara ba da lokaci ga “yin addu’a da kuma koyar da Maganar.”—Ayyukan Manzanni 6:4.
Muddin yanayi na wannan duniya ya yarda, Hukumar Mulki, da ke wakiltan “amintaccen bawan nan mai hikima,” za ta yi amfani da rukunin doka. Wannan daidai ne, amma ba wajibi ba ne. Idan gwamnati ta hana wani rukuni ta hanyar doka, har ila aikin wa’azi zai ci gaba. Yanzu ma, a ƙasashe inda aka hana aikin kuma ba a yin amfani da wani rukuni, ana shelar saƙon Mulki, ana almajirantarwa, kuma sarautar Allah tana ci gaba. Wannan yana faruwa domin Shaidun Jehovah suna shuki da ban ruwa, amma ‘Allah ke sa ya yi girma.’—1 Korantiyawa 3:6, 7.
Yayin da muke duba gaba, muna da gaba gaɗi cewa Jehovah zai kula da bukatu na ruhaniya da na jiki na mutanensa. Shi da Ɗansa, Yesu Kristi, za su ci gaba da yin ja-gora daga sama da taimako da ake bukata don a ƙarasa aikin wa’azin Mulki. Babu shakka, ko menene muka cim ma mu bayin Allah mun yi ne ‘ba da ƙarfi, ko iko ba, amma da ruhun Jehovah.’ (Zakariya 4:6) Saboda haka muna addu’a don taimakon Allah, mun sani cewa da ƙarfin da Jehovah yake bayarwa, za mu iya gama aikin da ya ba mu mu yi a wannan ƙarshen zamani!