Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 2/1 p. 27
  • Sanarwa Ta Musamman

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Sanarwa Ta Musamman
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Hukumar Mulki ta Bambanta Daga Rukunin Doka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Mene ne Aikin “Bawan nan Mai Aminci, Mai Hikima”?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Ka Yi Biyayya Ga Kristi Da Kuma Amintaccen Bawansa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Su Wa Suke Yi wa Mutanen Allah Ja-gora a Yau?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 2/1 p. 27

Sanarwa Ta Musamman

A ƘARSHEN taron shekara shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania da aka yi a ranar 7 ga Oktoba, 2000, mai kujeran John E. Barr na Hukumar Mulki ya yi wata sanarwa ta musamman. Wannan sanarwa ta dangana bisa jawabin da Theodore Jaracz da Daniel Sydlik suka bayar da farko a ranar.—Dubi shafuffuka 3-7 da 24-27 na wannan jarida.

Da yake ba da darasi na musamman, Ɗan’uwa Barr ya ce: “ ‘Amintaccen bawan nan, mai hikima’ da Hukumar Mulkinsa sun danƙa musu abubuwa masu girma fiye da waɗanda aka ba rukunin doka. Takardar sharaɗi da aka kafa na irin wannan rukuni al’amura ce da za su iya. Amma, Ubangijinmu Yesu Kristi ya naɗa ajin amintaccen bawan bisa dukan ‘mallaka’ tasa, ko kuma abubuwan Mulki a nan duniya.”—Matiyu 24:45-47.

Game da ƙungiya na Pennsylvania, Ɗan’uwa Barr ya daɗa: “Tun daga somawarta a shekara ta 1884, Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania ya kasance da muhimmiyar matsayi a tarihinmu na zamani. Har ila, kayan aiki ne kawai da ‘amintaccen bawan nan mai hikima’ yake amfani da shi inda bukata ta kama.”

A jawabansu, ’Yan’uwa Sydlik da Jaracz sun ba da bayani cewa abubuwan Ubangiji da ke duniya da aka danƙa wa “amintaccen bawan nan mai hikima” bai hana ajin bawan nan daga ƙyale mutane da suka cancanta a tsakanin “waɗansu tumaki” su kula da wasu hakki na aikin mulki ba. (Yahaya 10:16) Babu dalili na Nassi da ya nace cewa duka ko kuma wani na darektocin rukunin da Shaidun Jehovah za su yi amfani da su, su zama shafaffun Kiristoci.

Ɗan’uwa Barr ya gaya wa masu sauraro cewa a baya bayan nan wasu cikin Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah da suke hidima na darektoci da hafsoshi sun daina da son ransu daga zama darektoci na duka rukunin da “amintaccen bawan nan mai hikima” ke amfani da su a United States. An zaɓe ’yan’uwa masu riƙon amana na ajin waɗansu tumaki su ɗauki matsayinsu.

Wannan shawarar tana da amfani sosai. Ya ba waɗanda suke Hukumar Mulki zarafi su ba da lokaci a shirya abinci na ruhaniya da kuma kula da bukatu na ruhaniya na ’yan’uwancin duniya duka.

A kammalawa, mai kujeran ya gaya wa masu sauraronsa da suke murna: “Yayin da an ba masu kula da sun ƙware ayyuka dabam dabam na doka da kuma na tsara ayyuka, . . . dukansu suna hidima a ƙarƙashin ja-gora ta ruhaniya ta Hukumar Mulkin ne. . . . Dukanmu muna addu’a muna zuba wa Jehovah ido don albarkarsa bisa haɗaɗɗen ƙoƙarce-ƙoƙarcenmu a yin nufinsa, ga ɗaukaka da yabo na sunansa mai girma.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba