Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w01 2/1 pp. 30-31
  • Shaidun Jehovah—Suna Cin Gaba da Haƙƙaƙewa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Shaidun Jehovah—Suna Cin Gaba da Haƙƙaƙewa!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Cin Nasara Bisa Sihiri da Gaskiyar Littafi Mai Tsarki a Haiti
  • Ƙwazo a Yanki Mai Faɗi na Koriya
  • Biyar Bukatar Girma a Mexico
  • Riƙe Aminci Cikin Hargitsi a Saliyo
  • Tsarin Gini Mai Girma a Afirka ta Kudu
  • Sabuwar Tsarar Shaidu a Ukraine
  • Wasu Abubuwa Masu Ban Sha’awa na Tsarin Ayyukan
  • Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
  • Haɗin Kai Cikin Ƙauna—Rahoton Taron Shekara-Shekara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
w01 2/1 pp. 30-31

Shaidun Jehovah—Suna Cin Gaba da Haƙƙaƙewa!

Rahoton Taron Shekara Shekara

A WAƊANNAN zamani na shakka, Shaidun Jehovah ne suka kasance Kiristoci masu haƙƙaƙewa. An bayyana wannan a taron shekara shekara na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania, da aka yi a Jersey City, Babban Majami’ar Taro na Shaidun Jehovah a New Jersey ranar Asabar 7 ga Oktoba, 2000.a

A maganarsa ta buɗewa, mai kujerar, John E. Barr, wanda yake Hukumar Mulki na Shaidun Jehovah, ya ce: “A cikin mutane biliyoyi na duniya, mu ne muka san cewa kuma muka gaskata cewa ƙaunatacce Ɗan Jehovah, Kristi Yesu, yanzu an naɗa shi sarki a sama, yana sarauta tsakanin magabtansa.” An nuna tabbaci na haƙƙaƙewa nan a rahotanni shida masu ban sha’awa da aka samo daga dukan duniya.

Cin Nasara Bisa Sihiri da Gaskiyar Littafi Mai Tsarki a Haiti

Sihiri ya cika ko’ina a Haiti. “Yadda yake,” in ji mai kula da Kwamitin Reshe John Norman, “mutane suna yin sihiri domin su tsare kansu.” Wani boka ya soma shakka lokacin da ya yi hasarar ƙafarsa ɗaya a haɗari. Ya yi mamaki: ‘Yaya wannan zai faru da ni idan ruhohi suna kāre ni?’ Kamar wasu da yawa, Shaidun Jehovah sun koya wa wannan mutumin gaskiya kuma aka taimake shi ya ’yantu daga sihiri. An ga alamar girma a Haiti, a 19 ga Afrilu, 2000, waɗanda suka halarci Abin Tunawa na mutuwar Kristi sun yi ninki huɗu na adadin masu shelar Mulki a ƙasar.

Ƙwazo a Yanki Mai Faɗi na Koriya

A Koriya, kashi 40 bisa ɗari na Shaidun Jehovah suna hidima ta cikakken lokaci. “Da wannan runduna mai girma,” in ji mai kula da Kwamitin Reshe Milton Hamilton, “ana gama yankinmu mai mutane fiye da miliyan 47 wajen sau ɗaya a wata.” Abin lura ta musamman ita ce girma a ikilisiyoyin yaren alama. A wata da’ira ta yaren alama, ana tafiyar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida guda 800. Wannan matsakaici ne na nazari guda ga kowane mai shela. Abin baƙin ciki, har ila ana ɗaure ’yan’uwa maza matasa a kurkuku domin tsakatsakancinsu. Amma, waɗannan Kiristoci masu aminci ana bi da su da kyau, sau da yawa ana ba su aikin da yake bukatar mai gaskiya.

Biyar Bukatar Girma a Mexico

Ƙolin masu shelar Mulki 533,665 ne suka ba da rahoto na hidimar fage a Mexico a watan Agusta 2000. Mutane da suka halarci Tunawa sun kai fiye da sau uku na wannan adadin. “Burinmu bana shi ne mu gina ƙarin Majami’un Mulki 240,” in ji mai kula da Kwamitin Reshe Robert Tracy. “Har ila,” ya daɗa cewa, “muna bukatar ƙarin wasu da yawa.”

Matasa tsakanin Shaidun Jehovah a Mexico abin koyi ne. Game da wani matashi, wani firist na Katolika ya ce: “Zan so na samu ɗaya kamarsa kawai a cikin mabiyana. Ina son waɗannan mutane don gaba gaɗinsu da amfani da kyau da suke yi da Littafi Mai tsarki. Sun riƙe amincinsu ga Allah, ko ma za su yi hasarar rayukansu.”

Riƙe Aminci Cikin Hargitsi a Saliyo

Tun Afrilun shekara ta 1991, lokacin da yaƙin basasa ya ɓarke a Saliyo, an kashe dubban mutane, an ji wa wasu rauni, ko kuma an naƙasa su. “Yaƙi da wahala sun shafi mutane sosai,” mai kula da Kwamitin Reshe Bill Cowan ya ba da rahoto. “Mutane da yawa da ba sa son saƙonmu yanzu suna saurara sosai. Ba abin mamaki ba ne mutane su shigo cikin Majami’un Mulkinmu babu gayyata, su halarci taronsu na farko. Sau da yawa ana tsayar da ’yan’uwanmu a kan titi don neman nazarin Littafi Mai Tsarki.” Duk da wahala da ta ci gaba a ƙasar, aikin wa’azin Mulki yana ba da ’ya’ya a Saliyo.

Tsarin Gini Mai Girma a Afirka ta Kudu

A yanzu, akwai bukata ta dubban Majami’un Mulki a yankunan da ofishin reshe da ke Afirka ta Kudu ke kula da su. An riga an gina ɗarurruwan majami’u. “Maimakon yin taro a ɗaki ko ƙarƙashin bishiya, yadda ake dā, ’yan’uwanmu suna taruwa a inda ya dace da wurin zama mai kyau,” John Kikot da ke cikin Kwamitin Reshe ya lura da haka. “Ko da yawancin waɗannan Majami’un Mulki ba gini masu tsada ba ne, sun kasance gine-gine da sun fi burgewa a yankunansu. A wasu wurare an lura cewa bayan an gina Majami’ar Mulki, ikilisiyar za ta ƙaru fiye da ninki biyu a shekara ta biye.”

Sabuwar Tsarar Shaidu a Ukraine

Cikin shekarar hidima ta 2000, wannan ƙasar ta samu ƙolin masu shela 112,720. Fiye da 50,000 na waɗannan sun koyi gaskiyar Littafi Mai Tsarki cikin shekara biyar da ta shige. “Da gaske, Jehovah ya ta da sabuwar tsarar matasa na Shaidu su sanar da sunansa!” in ji mai kula da Kwamitin Reshe John Didur. Ya daɗa: “Cikin shekaru biyu da suka shige mun ba da fiye da jaridu miliyan 50, wanda ya yi daidai da yawan jama’ar ƙasar. Kowane wata, muna samun matsakaicin wasiƙu dubu daga mutane da suke da marmari suna neman ƙarin bayani.”

Wasu Abubuwa Masu Ban Sha’awa na Tsarin Ayyukan

Daniel Sydlik, wanda yake cikin Hukumar Mulki, ya ba da jawabi mai kwashe hankali. Talifin nan, “Yadda Hukumar Mulki ta Bambanta Daga Rukunin Doka,” da ke cikin wannan jarida, yana bisa wannan koyarwa mai kyau.

Theodore Jaracz na Hukumar Mulki ya ba da jawabi mai sa tunani mai jigo “Masu Kula da Kuma Bayi Masu Hidima Allah ne Ya Naɗa Su.” Ɗaya cikin talifi da yake cikin wannan jarida yana bisa wannan batu.

Taron ya haɗa da jawabi mai motsawa da David Splane wanda ke cikin Hukumar Mulki ya bayar bisa jigon shekara don shekara ta 2001. Bisa kalmomin manzo Bulus, “Ku dage, kuna cikakku, masu haƙƙaƙewa cikin dukkan nufin Allah.” (Kolosiyawa 4:12) Shaidun Jehovah a dukan duniya sun ƙuduri aniyyar su yi wannan yayin da suke wa’azin bishara na Mulkin Allah a duka duniya cikin aminci.—Matiyu 24:14.

[Hasiya]

a An yaɗa wannan ta waya zuwa wurare dabam dabam, dukan adadin waɗanda suka hallara ya kai 13,082.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba