Haɗin Kai Cikin Ƙauna—Rahoton Taron Shekara-Shekara
WAƊANDA suka taru don taron shekara-shekara a Majami’ar Taro na Shaidun Jehobah a Birnin Jersey, New Jersey, a Amirka sun yi farin ciki sosai. Da safiyar ranar 3 ga Oktoba, 2009, fiye da mutane 5,000 ne suka taru don taron shekara-shekara na 125 na Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania. Dubbai sun saurari tsarin ayyukan ta wurin rediyo kuma wasu sun kalli tsarin ayyukan ta wurin bidiyo da aka haɗa da gidajen Bethel guda uku da ke Amirka da Bethel na Kanada. Gabaki ɗaya, mutane dubu ɗari sha uku da ɗari biyu da talatin da biyar da suka haɗa kai cikin ƙaunarsu ga Jehobah ne suka ji daɗin taron na awa uku.
Geoffrey Jackson na Hukumar Mulki ne mai kujeran taro. Ya buɗe taron ne da gabatar da masu waƙa daga Bethel da suka rera waƙoƙi daga sabon littafinmu na waƙa. David Splane da ke cikin Hukumar Mulki ne ya ja-goranci rukunin mawaƙan, kuma ya ɗan tattauna muhimmancin waƙa a bauta ta gaskiya. An gayyaci masu sauraro su rera sababbin waƙoƙi guda uku a taron; rukunin mawaƙan ne suka soma, bayan hakan sai mawaƙan da masu sauraro suka rera tare. An yi amfani da rukunin mawaƙan don wannan taro na musamman ne; ba tsarin da za a riƙa bi ba ne a taron ikilisiyoyi, da’irori, ko kuma taron gunduma.
Rahotanni Daga Rassa
Kwamitin Reshe da suka kawo ziyara sun ba da rahotanni daga rassa biyar. Kenneth Little ya faɗi cewa ba da daɗewa ba Kanada za ta soma buga yawancin mujallu don Amirka da kuma Kanada, hakan zai kawo ƙarin ninki goma na littattafan da ake bugawa a wannan reshen. Don a cim ma hakan, sabuwar na’urar buga littattafai da aka sayo zai riƙa aiki sa’o’i sha shida a rana.
Reiner Thompson ya ba da rahoton aikin Mulki a Jamhuriyar Dominica, kuma Albert Olih ya bayyana ayyukanmu a Nijeriya. Emile Kritzinger daga Mazambik ya bayyana cewa bayan shekaru da yawa na fuskantar tsanantawa a ƙasar, an yi wa Shaidun Jehobah rajista a shekara ta 1992. Ba da daɗewa ba, dukan waɗannan ƙasashe uku sun samu ƙarin adadin masu shela da yawa. Viv Mouritz daga reshen Australiya ya ambata ci gaban da ake samu a Timor ta Gabas, kuma ’yan’uwa daga Australiya ne suke kula da wajen.
Kwamitocin Hukumar Mulki
A shekara ta 1976 ce kwamitoci shida na Hukumar Mulki suka soma kula da dukan ayyukan Shaidun Jehobah. Daga baya aka naɗa waɗanda suke cikin rukunin waɗansu tumaki su zama masu taimako. A yanzu su ashirin da uku ne suke taimakawa a aikin da ake yi. An gana da guda shida a cikinsu. Sun yi shekaru 341 a hidima na cikakken lokaci, wato, kowannensu ya yi avirejin shekaru 57.
Don Adam, wanda ya shiga Bethel a shekara ta 1943, ya bayyana cewa Kwamiti Mai Kula ya ƙunshi masu tsara ayyukan kwamitoci biyar, waɗanda suke tabbatar da cewa dukan kwamitoci biyar ɗin suna aiki tare yadda ya kamata. Wannan kwamitin yana ɗaukan mataki da ya dace wajen kula da yanayi na gaggawa, tsanantawa, shari’o’i na kotu, bala’o’i, da wasu batutuwa na gaggawa da suke shafan Shaidun Jehobah a dukan duniya.
Dan Molchan ya bayyana aikin Kwamitin Ma’aikata, wanda yake kula da bukatu na zahiri da na ruhaniya na mutane 19,851 waɗanda suke cikin iyalin Bethel a dukan duniya. David Sinclair ya yi magana game da yadda Kwamitin Buga Littattafai yake kula da sayan kayayyaki da na’urori ga rassa. Bayan haka, Robert Wallen, wanda ya yi hidima a Bethel na kusan shekara 60, ya faɗi yadda Kwamitin Hidima yake kula da ayyukan mutanen Jehobah a fage da kuma ikilisiyoyi. William Malenfant ya bayyana aiki tuƙuru da Kwamitin Koyarwa suke yi don su shirya tsarin ayyuka na taron gunduma. A ƙarshe, John Wischuk ya bayyana yadda Kwamitin Rubuce-Rubuce suke kula da shirya da kuma yin rubuce-rubuce na littattafanmu.a
Jigon Shekara na 2010 Ya Mai da Hankali a kan Ƙauna
Waɗanda suke cikin Hukumar Mulki ne suka ba da jawabai uku na gaba. Gerrit Lösch ya soma ne da tambaya, “Kana son mutane su ƙaunace ka?” Ya bayyana cewa ’yan adam suna bukatan ƙauna, kuma dukanmu muna samun ci gaba sa’ad da aka nuna mana ƙauna. Muna rayuwa ne saboda ƙauna domin Jehobah ya halicce mu cikin ƙauna babu son kai. Don muna ƙaunar Jehobah ne ainihin dalilin da ya sa muke wa’azi da kuma koyarwa.
Muna nuna ƙauna da ke bisa ƙa’ida ba kawai ga maƙwabtanmu ba amma har da magabcinmu. (Mat. 5:43-45) An ƙarfafa masu sauraro su yi la’akari da wahalar da Yesu ya sha dominmu, an yi masa bulala, ba’a, an tofa masa miyau, kuma an tsire shi. Duk da haka, ya yi wa sojojin da suka tsire shi addu’a. Hakan bai motsa mu mu ƙara ƙaunarsa ba? Sai Ɗan’uwa Lösch ya sanar da jigon shekara ta 2010: 1 Korintiyawa 13:7, 8, ‘Ƙauna tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.’ Muna da begen yin rayuwa har abada da kuma nuna ƙauna ga mutane su kuma su ƙaunace mu har abada.
Kana da Isashen Māi Kuwa?
Ɗan’uwa Samuel Herd ya soma jawabinsa ne da kwatanci. A ce wani abokinka ya ɗauke ka ku yi tafiya na kilomita 50. Daga kujerar fasinjar da kake zaune sai ka lura cewa gējin māi ya nuna cewa māi ya kusan ƙarewa. Ka gaya wa abokinka cewa mān ya kusan ƙarewa. Sai ya ce kada ka damu, mān da ke cikin tankin ya kai galan. Amma, ba da daɗewa ba, sai mān ya ƙare. Ya dace ne ka yi ‘tafiya babu mai’ da sanin cewa motar za ta iya tsayawa a kan hanya? Ya fi kyau ka cika tankinka! A alamance, muna bukatan mu cika tankinmu, mān shi ne sanin Jehobah.
Saboda haka, muna bukatan mu saye isashen māi kuma mu riƙa yin haka a kowane lokaci. Da akwai hanyoyi huɗu da za mu yi hakan. Na farko, nazari na kanmu, sanin Littafi Mai Tsarki sosai ta wajen karanta shi kullayaumi. Ba karanta kalmomi kawai ba, amma dole ne mu fahimci abin da muka karanta. Na biyu, yin amfani sosai da Bauta ta Iyali da yamma. Muna cika tankinmu a kowane mako ko kuma muna saka kaɗan ne kawai? Na uku, nazari na ikilisiya da kuma halartan taro. Na huɗu, yin bimbini inda babu wanda zai dame mu, mu riƙa tunani game da hanyoyin Jehobah. Zabura 143:5 ta ce: “Ina tuna da kwanakin dā; ina tunani da dukan al’amuranka.”
“Masu-Adalci Za Su Haskaka”
Ɗan’uwa John Barr ne ya ba da jawabi na uku kuma na ƙarshe, wanda ya bayyana kwatancin Yesu na alkama da kuma zawan. (Mat. 13:24-30, 38, 43) Wannan kwatancin ya yi nuni ga “lokacin kaka” da aka tara “’ya’yan mulki” kuma aka ware zawan aka ƙona su.
Ɗan’uwa Barr ya bayyana sarai cewa tattarawar ba za ta ci gaba har abada ba. Ya yi nuni ga Matta 24:34, wadda ta ce: “Wannan tsara ba za ta shuɗe ba, sai an cika waɗannan abubuwa duka.” Ya karanta wannan furcin sau biyu: “Yesu yana nufin cewa wasu cikin shafaffun da suke raye sa’ad da alama ta soma bayyana a shekara ta 1914 za su rayu a matsayin tsara da sauran shafaffun da za su ga somawar ƙunci mai girma.” Ba mu san ainihin tsawon “wannan tsarar” ba, amma ya ƙunshi waɗannan rukuni biyu da za su rayu a matsayin tsara. Ko da yake shekarun shafaffun sun bambanta, waɗanda suke cikin rukuni biyun da suka haɗu suka zama tsarar suna raye ne a lokaci guda a kwanaki na ƙarshe. Abin ban ƙarfafa ne mu san cewa dukan matasan da ke cikin wannan tsara na tsofaffin shafaffu da suka fahimci alamar sa’ad da ya bayyana a shekara ta 1914 ba za su mutu gabaki ɗaya ba kafin ƙunci mai girma ya soma!
“’Ya’yan mulki” cikin ɗoki suna jiran ladarsu ta samaniya, amma dole ne dukanmu mu kasance da aminci, muna haskakawa har zuwa ƙarshe. Muna da gatan ganin tattara “zawan” a zamaninmu.
Bayan waƙar rufewa, ɗan’uwa Theodore Jaracz na Hukumar Mulki ne ya yi addu’ar rufewa. Taron na shekara-shekara ya kasance tsarin ayyuka mai ban ƙarfafa!
[Hasiya]
a Don ganin yadda aka tsara aikin kwamitoci shida na Hukumar Mulki, ka duba Hasumiyar Tsaro na 15 ga Mayu, 2008, shafi na 29.
[Akwati da ke shafi na 5]
MAKARANTA DON DATTAWA
A taron na shekara-shekara, Anthony Morris, wanda yake cikin Hukumar Mulki, ya sanar da cewa za a ci gaba da koyar da dattawan ikilisiya. An soma makaranta da ake koyar da dattawa a Amirka a farkon shekara ta 2008 a cibiyar koyarwa a Patterson, New York. Ba a daɗe da kammala aji na 72 ba, a yanzu an koyar da dattawa 6,720. Har ila, da sauran rina a kaba. A Amirka kaɗai, da akwai fiye da dattawa 86,000. Saboda haka, Hukumar Mulki ta amince a ƙafa ƙarin makaranta a Brooklyn, New York, somawa daga 7 ga Disamba, 2009.
Za a koyar da masu kula masu ziyara guda huɗu har tsawon watanni biyu don su zama malamai a Patterson. Za a kai su Brooklyn don su riƙa koyarwa, kuma za a ƙara koyar da huɗu. Sai su koyar a makarantar da ke Brooklyn, kuma huɗu da aka koyar da farko za su koyar da makarantar da ke Majami’un Babban Taro da Majami’un Mulki. Za a maimaita hakan har a samu malamai sha biyu da za su riƙa koyarwa a kowane mako a makarantu shida na Turanci a Amirka. Bayan hakan za a koyar da malamai guda huɗu da za su koyar a Sfanisanci. Wannan makarantar ba za ta sauya Makarantar Hidima na Mulki na yanzu ba; manufarta ita ce a taimaka wa dattawa su ƙara ruhaniyarsu. Rassa a dukan duniya za su soma yin makarantar a Majami’un Babban Taro da Majami’un Mulki a shekarar hidima ta 2011.
[Hotuna da ke shafi na 4]
An soma taron shekara-shekara da rera waƙoƙi daga sabon littafinmu na waƙa, “Sing to Jehovah”