Ku Rika “Girmama Irin Waɗannan Mutane”
A SHEKARA ta 1992, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta naɗa kwararrun dattawa don sun taimaka wa kwamitoci dabam-dabam na hukumar don su cim ma ayyukansu.a An zaɓi waɗannan masu taimako ne daga “waɗansu tumaki” kuma suna taimaka wa Hukumar sosai. (Yoh. 10:16) Suna halartar taron mako-mako na kwamiti da suke yi wa hidima. Aikin su shi ne ba da shawarwari da kuma wasu labaran da ake bukata. Hukumar ce take yanke shawara sa’an nan masu taimako su aiwatar da waɗannan shawarwarin da kuma duk wani aikin da aka ba su. Masu taimakon suna bin membobin hukumar zuwa manyan taro na musamman da na kasashe. Kari ga haka, ana iya aika su ofisoshin Shaidun Jehobah a kasashe dabam-dabam don su yi hidima a matsayinsu na wakilan hedkwatar Shaidun Jehobah.
Ɗaya daga cikin masu taimakon da ya yi hidima a wannan matsayin tun da aka kafa wannan tsarin ya ce: “Idan na kula da aikin da aka danka mini, hakan yana ba wa hukumar dama ta mai da hankali sosai ga ayyukanta.” Wani ɗan’uwa da ya yi sama da shekara 20 yana hidima a matsayinsa na mataimaki ya ce: “Wannan gatan ya fi duk wani abin da na zata.”
Hukumar da ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah ta danka wa waɗannan masu taimako ayyuka da yawa kuma suna godiya saboda hidima mai kyau da waɗannan ’yan’uwa masu kwazo suke yi. Bari mu rika “girmama irin waɗannan mutane.”—Filib. 2:29.
a Za ka sami takaitaccen bayani game da ayyukan da kwamitoci shida na Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suke yi a shafi na 131 na littafin Mulkin Allah Yana Sarauta!