Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 5/15 p. 29
  • Yadda Aka Tsara Hukumar Mulki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Yadda Aka Tsara Hukumar Mulki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Makamantan Littattafai
  • Su Waye ne Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah?
    Tambayoyin da Ake Yawan Yi
  • Haɗin Kai Cikin Ƙauna—Rahoton Taron Shekara-Shekara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ku Rika “Girmama Irin Waɗannan Mutane”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Mene Ne Ake Yi a Ofishin Reshe?
    Su Wane Ne Suke yin Nufin Jehobah A Yau?
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 5/15 p. 29

Yadda Aka Tsara Hukumar Mulki

HUKUMAR Mulki na Shaidun Jehobah ta ƙunshi maza shafaffu bayin Allah da suka keɓe kansu. Sune wakilan ajin bawan nan mai aminci mai hikima da ke da hakkin yin tanadin abinci na ruhaniya da kuma ba da ja-gora da tabbatar da cewa aikin wa’azin Mulki a dukan duniya shi ne kan gaba.—Mat. 24:14, 45-47.

Hukumar Mulki tana yin taro a ranar Laraba a kowane mako. Wannan na taimaka wa waɗannan ’yan’uwan su yi aikinsu da haɗin kai. (Zab. 133:1) Waɗanda suke cikin Hukumar Mulki suna hidima a kwamitoci dabam dabam. Don su kula da ayyukan Mulki, kowane kwamiti na da wurin da yake kula da shi kamar yadda aka tsara a gaba.

◼ KWAMITI MAI KULA: Wannan kwamitin ya ƙunshi mai kula da kowanne cikin kwamitoci na Hukumar Mulki da kuma sakatare wanda yake cikin Hukumar Mulki. Wannan kwamitin na tabbatar da cewa dukan kwamitocin na aiki da kyau ba tare da wata matsala ba. Yana kuma kula da bukatun gaggawa, tsanantawa, tsarar bala’i, da wasu batutuwa na gaggawa da suke shafan Shaidun Jehobah a dukan duniya.

◼ KWAMITIN MA’AIKATA: An ɗanka wa ’yan’uwan da suke wannan kwamitin aikin kula da bukatu na zahiri da na ruhaniya da kuma taimaka wa waɗanda suke cikin iyalin Bethel a dukan duniya. Wannan kwamitin yana kula da zaɓa da kuma gayyatar sababbi zuwa Bethel da kuma amsa tambayoyi game da hidimarsu a Bethel.

◼ KWAMITIN BUGA LITTATTAFAI: Wannan kwamitin na kula da buga, wallafa, da aika littattafai na Littafi Mai Tsarki zuwa dukan duniya. Yana kula da na’urar buga littattafai da kayayyaki na ma’aikata dabam dabam da Shaidun Jehobah suke amfani da shi. Wannan kwamitin na tsara yadda za a yi amfani da kyau da gudummawar da aka bayar don aikin Mulki na dukan duniya.

◼ KWAMITIN HIDIMA: Waɗanda suke wannan kwamitin suna kula da aikin wa’azi da abubuwan da suka shafi ikilisiyoyi, majagaba, dattawa, da masu kula masu ziyara. Yana kula da shirya Our Kingdom Ministry da kuma gayyatar ɗaliban Makarantar Gilead da kuma Makarantar Koyar da Masu Hidima, bayan ɗaliban sun sauke karatu, kwamitin zai aika su zuwa inda za su yi hidima.

◼ KWAMITIN KOYARWA: Wannan kwamitin na kula da jawabai da ake ba da wa a manyan taro, taron gunduma, da na ikilisiya. Yana shirya tsarin ayyuka na ruhaniya don waɗanda suke Bethel da kuma makarantu dabam dabam kamar su Gilead da Makarantar Hidima na Majagaba da kuma shirya faifai na kaset da bidiyo.

◼ KWAMITIN RUBUCE-RUBUCE: Hakkin wannan kwamitin ne ya kula da rubuta abinci na ruhaniya kuma rarraba su ga ’yan’uwa da mutanen waje. Wannan kwamitin yana amsa tambayoyi na Littafi Mai Tsarki kuma ya amince da wasan kwaikwayo da awutlayi. Kuma yana kula da aikin fassara da ake yi a dukan duniya.

Manzo Bulus ya kamanta ikilisiya na shafaffu da jikin ’yan adam kuma ya nanata matsayi masu muhimmanci da duka suke da shi da yadda suke dogara da juna, ƙaunarsu da kuma haɗin kansu wajen yin aikin da Allah ya ba su. (Rom. 12:4, 5; 1 Kor. 12:12-31) Shugaba Yesu Kristi yana ba jiki abin da ake bukata don haɗin kai mai kyau, shiri, da abinci na ruhaniya. (Afis. 4:15, 16; Kol. 2:19) Hakan ne aka tsara Hukumar Mulki su yi shugabanci yayin da Jehobah yake yi musu ja-gora da ruhu mai tsarki.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba