Ci Gaba Zuwa Nasara Ta Ƙarshe!
“Ga farin doki; wanda ya ke zaune a kansa kuma yana da baka; kuma aka ba shi rawani: a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.” —RU’YA TA YOHANNA 6:2.
1. Menene zai faru a nan gaba da Yohanna ya gani a cikin wahayi?
TA WAJEN hurewa daga Allah manzo Yohanna ya ga abin da zai faru shekara 1,800 a nan gaba kuma ya kwatanta naɗa Kristi ya zama Sarki. Yohanna yana bukatar bangaskiya ya gaskata da abin da ya gani a cikin wahayi. A yau mu muna da tabbaci sarai cewa wannan naɗin ya faru a shekara ta 1914. Da idanun bangaskiya mun ga Yesu Kristi “a kan nasara ya fita, garin yin nasara kuma.”
2. Me Iblis ya yi a kafuwar Mulki, kuma wannan tabbacin menene ne?
2 Bayan an kafa Mulkin, aka fitar da Shaiɗan daga sama, shi ya sa yake ƙoƙari ƙwarai kuma da hasala amma ina, bai kyautata zarafinsa na yin nasara ba. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) Hasalarsa ta sa yanayin duniya ya ƙara muni ƙwarai. Kamar dai jama’a sai rarrabuwa suke yi. Ga Shaidun Jehovah wannan tabbaci ne cewa Sarkinsu yana ci gaba “garin yin nasara.”
Ana Kafa Sabuwar Jama’a ta Duniya
3, 4. (a) Waɗanne canje-canje aka yi a tsarin ikilisiyar Kirista tun daga kafuwar Mulkin, kuma me ya sa waɗannan tabbas ne? (b) Kamar yadda Ishaya ya annabta, menene amfanin waɗannan canje-canje?
3 Da zarar an kafa Mulkin, lokaci ne da za a kawo ikilisiyar Kirista da aka maido—yanzu da ƙarin hakki na Mulki—da take daidai da abubuwa da ikilisiyar Kiristoci na ƙarni na farko suke da shi. Saboda haka, Hasumiyar Tsaro fitar 1 da kuma 15 ga Yuni, 1938 (Turanci), ta yi bayanin yadda ya kamata a gudanar da ikilisiyar Kiristoci. Daga baya, fitar 15 ga Disamba, 1971 (Turanci), ta ba da ƙarin bayani game da Hukumar Mulki ta zamani a talifin nan “Hukumar Mulki Dabam Daga Hukumar Doka.” A shekara ta 1972, aka naɗa rukunin dattawa don su ba da taimako ga ikilisiya.
4 Maido da kulawa mai kyau ya ƙarfafa ikilisiyar Kirista sosai. Har ila ƙari ga wannan shi ne tanadi da Hukumar Mulki ta yi don koyar da dattawa bisa ga aikinsu, haɗe da koyar da su game da batun shari’a. Bunƙasa a hankali da ta shafi tsarin ƙungiyar Allah da ake gani da kuma sakamakonsu mai kyau, an annabta su cikin Ishaya 60:17: “Maimakon jangaci zan kawo zinariya, maimakon baƙin ƙarfe kuma in kawo azurfa, maimakon itace kuma jangaci, maimakon duwatsu kuma baƙin ƙarfe: zan sa salama ta zama mulkinki, adalci kuma ya zama mahukuncinki.” Waɗannan gyara masu kyau sun nuna albarkar Allah ce da kuma yardarsa ga waɗanda suka fito da ƙwazo wajen tallafa wa Mulkinsa.
5. (a) Menene Shaiɗan ya yi domin albarkar Jehovah bisa Mutanensa? (b) Cikin jituwa da Filibbiyawa 1:7, me mutanen Jehovah suka yi domin hasalar Shaiɗan?
5 Ƙauna da kuma ja-gora da Allah ya yi wa mutanensa bayan kafuwar Mulkin, Shaiɗan ya lura da wannan. Alal misali, a shekara ta 1931 wannan ƙaramin rukunin Kiristoci sun sanar a fili cewa su ba Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba ne kawai. Cikin jituwa da Ishaya 43:10, su Shaidun Jehovah ne! Ko idan ya faru ne kawai ko babu, Shaiɗan ya zubo tsanantawar da babu irinta a dukan duniya. Har a ƙasashe da aka san su da ’yancin addini, kamar su Amurka, Canada, da kuma Jamus, aka tilasta wa Shaidun su yi yaƙi ta shari’a domin su riƙe ’yancin bautarsu. A shekara ta 1988, Babban Kotun Amurka ya maimaita abubuwa 71 da suka shafi Shaidun Jehovah, waɗanda kashi biyu cikin uku an yanke hukunci da ya goyi bayansu. A yau, a cikin dukan duniya, yaƙi ta shari’a ya ci gaba, kamar na ƙarni na farko, saboda ‘kāriyar bishara da ƙarfafawarta ta shari’a.’—Filibbiyawa 1:7.
6. Shin hani da kuma takunkumi suna hana mutanen Jehovah ci gaba ne? Ka ba da misali.
6 A lokacin shekaru na 1930, a kwanakin da suka kai Yaƙin Duniya na II, gwamnatin mulkin kama karya ta hana ko kuma ta kafa takunkumi bisa ayyukan Shaidun Jehovah a Jamus, Spain, da kuma Japan, a lissafa uku kawai. Amma a shekara ta 2000, waɗannan ƙasashe uku kawai suna da masu shelar Mulkin Allah da ƙwazo kusan 500,000. Wannan adadi ya kai wajen sau goma na dukan Shaidu a dukan duniya a shekara ta 1936! Babu shakka, hani da kuma takunkumi ba za su iya hana mutanen Jehovah ci gaba ba a ƙarƙashin Shugabansu mai nasara, Yesu Kristi.
7. Wane abu na musamman ne ya auku a shekara ta 1958, kuma wane canji ne na ban mamaki ya faru tun da daɗewa?
7 Bayyana ce kuwa ta ci gabansa, da a shekara ta 1958, a New York City aka yi taron gunduma mafi girma da Shaidun Jehovah suka yi, “Divine Will International Assembly,” da ƙolin waɗanda suka hallara ya kai 253,922. A shekara ta 1970 an riga an ƙyale aikinsu a ƙasashe uku da aka ambata a baya, ban da wurin da a lokacin aka san da shi Jamus na Gabas. Amma har ila an hana ayyukan Shaidun a babbar ƙasar Rasha da kuma al’ummai da suke kawanci da ita a ƙarƙashin yarjejeniya ta Warsaw Pact. A yau, a waɗannan al’umman Mulkin Kama Karya, akwai Shaidu masu himma fiye da rabin miliyan.
8. Menene sakamakon albarkar Jehovah bisa mutanensa, kuma mecece Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1950 ta ce game da wannan?
8 An albarkaci Shaidun Jehovah da ƙarin mutane domin su ci gaba da “biɗan mulkin [Allah], da adalcinsa.” (Matta 6:33) A zahiri, annabcin Ishaya ya cika: “Ƙaramin za ya zama dubu, ƙanƙanin kuma za ya zama al’umma mai ƙarfi: ni, Ubangiji, zan hanzarta wannan a lotonsa.” (Ishaya 60:22) Ƙaruwar za ta ci gaba. A shekara goma da ta shige, adadin masu shelar Mulki da ƙwazo ya ƙaru da mutane fiye da 1,750,000. Waɗannan sun zama sashen rukunin da Hasumiyar Tsaro ta shekara ta 1950 ta yi wannan maganar: “Allah yana shirya sabuwar jama’a ta duniya. . . . Wannan cibiyar za ta bi cikin Armageddon, . . . na farko cikin fagen aiki a ‘sabuwar duniya’ . . . an shirya su daidai yadda Allah yake mulki, sun kuma san ƙa’idar shirye-shirye.” Talifin ya kammala da cewa: “Mu ci gaba babu sauyewa, dukanmu tare, tun da mu sabuwar jama’a ta duniya ce!”
9. Ta yaya abubuwa da Shaidun Jehovah suka koya da shigewar shekaru ya kasance da amfani?
9 Domin haka, wannan sabuwar jama’a ta duniya da take ƙaruwa kullayaumi ta koyi iya yin abubuwa waɗanda suka kasance da muhimmanci a yau kuma wataƙila za su yi hakan a lokacin ayyukan fara maidowa bayan Armageddon. Alal misali, Shaidun sun koyi su shirya manyan taro, su ba da taimakon kayan agaji, kuma su yi gini da sauri. Waɗannan ayyuka sun sa mutane da yawa suna sha’awa da kuma daraja Shaidun Jehovah.
Gyara Ɓata Suna
10, 11. Ka kwatanta yadda aka gyara ɓata sunan Shaidun Jehovah.
10 Har ila yau, akwai mutane da suke tuhumar Shaidun Jehovah da cewa ba su jitu ba da tarayyar jama’a. Wannan saboda ra’ayinsu ne na Littafi Mai Tsarki a cikin al’amura kamar su ƙarin jini, tsakatsaki, shan taba, da kuma ɗabi’a. Amma jama’a suna ƙara yarda cewa ra’ayin Shaidun ya cancanci a bincika. Alal misali, wata likita a Poland ta yi wa ofishin gudanar da ayyukan Shaidun Jehovah waya, ta ce ita da abokanan aikinta a asibiti sun yi awoyi suna musu a kan batun ƙarin jini. Abin da ya bayyana a ranar a jaridar Dziennik Zachodni na Poland ta ta da musun. “Ni kaina na yi nadama da yawan amfani da jini da ake yi a asibiti,” in ji likitar. “Dole ne a sake wannan, kuma ina murna da yake wani ya ta da batun. Zan bukaci ƙarin bayani.”
11 A lokacin wani taro bara, masu iko wajen ba da magani daga Amurka, Canada, Isra’ila, da kuma Turai, sun tattauna sanarwa da aka shirya domin taimaka wa likitoci su yi wa majiyyata jinya ba tare da amfani da jini ba. An nuna a wannan taron da aka yi a Switzerland, cewa adadin majiyyata da suke mutuwa waɗanda suka karɓi ƙarin jini sun fi waɗanda ba su karɓa ba yawa, wannan ya sha bambam da ra’ayin yawancin mutane. Shaidu majiyyata an fi sallamarsu da wuri fiye da waɗanda aka yi musu jinya da ƙarin jini, kuma wannan yakan rage kuɗin jinyar.
12. Ka ba da misalin yadda manyan mutane suka yabi dagewar da Shaidun Jehovah suka yi game da tsakatsakinsu cikin siyasa.
12 An yi kalami masu kyau game da tsakatsakin Shaidun Jehovah kafin da kuma lokacin Yaƙin Duniya na II da suka jimre da ’yan Nazi. Bidiyon nan Jehovah’s Witnesses Stand Firm Against Nazi Assault, da Shaidun Jehovah suka yi da aka nuna a sansanin fursuna na Ravensbrück a Jamus a ranar 6 ga Nuwamba, 1996, ya jawo kalami masu kyau. A farkon irin wannan nunin a sanannan sansanin fursuna na Bergen-Belsen a ranar 18 ga Afrilu, 1998, shugaban Center for Political Education a Lower Saxony, Dokta Wolfgang Scheel, ya ce: “Gaskiya ɗaya mai kunyartawa a tarihi ita ce cewa Shaidun Jehovah sun ƙi ɗaukaka mulkin kama karya na ƙasa da niyya ƙwarai fiye da cocin Kirista. . . . Ko yaya muke ji game da koyarwa da kuma ƙwazon Shaidun Jehovah, dagewarsu lokacin mulkin Nazi ya cancanci daraja.”
13, 14. (a) Wane abu ne aka lura da shi na hikima domin Kiristoci na farko da ya fito daga tushen da ba a yi tsammani ba? (b) Ka ba da misalin kalami masu kyau da aka yi domin mutanen Allah a yau.
13 Lokacin da manyan mutane ko kuma kotu suka tsai da shawara da ta ɗaukaka Shaidun Jehovah game da al’amura na gardama, yana rage ƙin wane kuma ya sa a ɗan kasance da ra’ayi mai kyau game da Shaidun. Wannan sau da yawa ya buɗe musu hanyar yi wa mutane da dā ba sa so su saurare su magana. Shaidun Jehovah suna son irin wannan, kuma suna godiya saboda waɗannan. Wannan ya tunasar da mu abin da ya faru a ƙarni na farko a Urushalima. Lokacin da Majalisa, babban kotun Yahudawa, suke so su gama da Kiristoci domin himmarsu wajen wa’azi, Gamaliel, “mai-koyarda Attaurat, wanda yana da girma wurin dukan jama’a,” ya yi gargaɗi, ya ce: “Ku mazajen Isra’ila, ku yi hankali da kanku ga zancen mutanen nan, abin da ku ke shirin yi. . . . Ku hawayi waɗannan mutane, ku ƙyale su: gama idan wannan shawara ko wannan aiki na mutane ne, za ya rushe: amma idan na Allah ne, ba za ku iya rushe su ba, kada a iske ku kuna yaƙi har da Allah.”—Ayukan Manzanni 5:33-39.
14 Kamar Gamaliel, manyan mutane ba da daɗewa ba sun yi magana wajen ɗaukaka ’yancin addini na Shaidun Jehovah. Alal misali, mai kujera na dā na International Academy for Freedom of Religion and Belief ya aririta: “Bai kamata a hana hakkin addini ba domin kawai jama’a ba su yarda da koyarwarsa ba ko kuma ba daidai ba ne.” Shehun malami na kimiyyar addini a jami’ar Leipzig ya yi muhimmiyar tambaya game da hukuma da gwamnatin Jamus ta naɗa ta bincika addinai da wai su ɗariku ne, ya yi tambaya: “Me ya sa ƙananan addinai ne kawai za a bincika, ban da manyan coci biyu [Roman Katolika da kuma Cocin Luther]?” Don samun amsar bai kamata mu wuce maganar wani ma’aikacin Jamus na dā ba, wanda ya rubuta: “Babu shakka cewa a ɓoye, ’yan zafin hali kan addini ne suke faɗan abin da hukuma ta gwamnati take yi.”
Wa Muke Zuba wa Ido Ya Kawo Sauƙi?
15, 16. (a) Me ya sa abin da Gamaliel ya yi yana da iyaka? (b) Ta yaya wasu uku masu rinjaya suke da iyaka a abin da za su yi domin Yesu?
15 Abin da Gamaliel ya faɗa ya nanata gaskiyar cewa aikin da yake da goyon bayan Allah ba zai rushe ba. Babu shakka Kiristoci na farko sun amfana daga wannan maganar ga Majalisa, amma ba su manta ba cewa maganar game da tsananta wa mabiyansa gaskiya ce. Abin da Gamaliel ya yi ya hana shirin shugabannan addini su gama da su, amma wannan bai kawar da tsanantawa ba gabaƙi ɗaya, domin mun karanta: “Suka yarda da shawararsa: sa’anda suka kirawo manzannin, suka duke su, suka dokace su kada su yi zance cikin sunan Yesu, kāna suka sake su.”—Ayukan Manzanni 5:40.
16 Lokacin da ake tuhumar Yesu, Bilatus Babunti, da bai sami laifi ba a gare shi, ya yi ƙoƙarin ya saki Yesu. Amma bai yi nasara ba. (Yohanna 18:38, 39; 19:4, 6, 12-16) Har biyu cikin ’yan Majalisar, Nikodimu da Yusufu na Arimathiya, waɗanda suke abokantaka da Yesu, ba su da wani abin da za su yi su hana kotun yanke hukunci bisa Yesu. (Luka 23:50-52; Yohanna 7:45-52; 19:38-40) Sauƙin da mutane suke samu idan suka tsaya a kāre mutanen Allah—ko menene dalilin dai—yana da iyaka. Duniya za ta ci gaba da ƙin mabiyan Kristi na gaskiya, kamar yadda ta ƙi shi. Cikakken sauƙi zai zo ne daga Jehovah kaɗai.—Ayukan Manzanni 2:24.
17. Wane ra’ayi ne Shaidun Jehovah suke da shi, amma me ya sa ba su yi sanyin jiki ba a niyyarsu ta ci gaba da wa’azin bishara?
17 Hakika, Shaidun Jehovah suna tsammanin ci gaba na tsanantawa. Hamayya za ta ƙare idan aka ci nasara bisa tsarin abubuwa na Shaiɗan ne kawai a ƙarshen nan. Duk da haka, wannan tsanantawa, ko da yake babu daɗi, ba ya hana Shaidun cika aikinsu na yin wa’azin Mulki. Me zai sa, tun da suna da goyon bayan Allah? Suna zuba wa Shugabansu mai gaba gaɗi, Yesu Kristi, ido tun da shi ne abin koyi da ya dace.—Ayukan Manzanni 5:17-21, 27-32.
18. Wace wahala ce take gaban mutanen Jehovah, amma menene suka tabbata zai zama ƙarshensa?
18 Tun daga farkonsa, addini na gaskiya ya fuskanci hamayya mai tsanani. Ba da daɗewa ba zai zama abin farmaki ƙwarai ga Gog, Shaiɗan a cikin yanayinsa na ƙanƙanci tun da aka jefo shi daga sama. Amma addini na gaskiya zai tsira. (Ezekiel 38:14-16) ‘Sarakunan dukan duniya’ a ƙarƙashin ja-gorar Shaiɗan, “za su yi gāba da Ɗan rago, Ɗan rago kuma za ya ci su, gama shi ne Ubangijin iyayengiji, da Sarkin sarakuna.” (Ru’ya ta Yohanna 16:14; 17:14) Hakika, Sarkinmu yana ci gaba zuwa nasara ta ƙarshe kuma ba da daɗewa ba zai ‘yi nasara.’ Gata ce mu ci gaba tare da shi, da sanin cewa ba da daɗewa ba babu wanda zai sake ƙaryata masu bauta wa Jehovah idan suka ce: “Allah ke wajenmu”!—Romawa 8:31; Filibbiyawa 1:27, 28.
Za Ka Iya Bayyanawa?
• Menene Jehovah ya yi don ya ƙarfafa ikilisiyar Kirista tun lokacin da aka kafa Mulkin?
• Menene Shaiɗan ya yi a ƙoƙarin ya hana Kristi yin nasararsa, kuma menene sakamakon haka?
• Wane daidaicaccen ra’ayi ya kamata mu kasance da shi game da ayyukan kirki na waɗanda ba Shaidu ba?
• Menene Shaiɗan zai yi ba da daɗewa ba?
[Hoto a shafi na 26]
Manyan taro bayyana ce ta ci gaba na mutanen Jehovah
[Hoto a shafi na 28]
Tsakatsakin Shaidun lokacin Yaƙin Duniya na II har yanzu yana kawo yabo ga Jehovah