Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w00 4/1 pp. 24-29
  • Masu Yaƙi Da Allah Ba Za Su Yi Nasara Ba!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Masu Yaƙi Da Allah Ba Za Su Yi Nasara Ba!
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • An Kai Wa Bayin Jehovah Farmaki
  • Ci Gaba da Aikin Wa’azi!
  • Suna Neman Illa
  • An Tsananta Masu Amma Ba Su Yi Shirka Ba
  • Babu Makami da Za a Kirkiro Domin Mu da Zai Yi Nasara
  • Ka Yi Gaba Gaɗi Irin Na Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2004
  • Wa Kake Wa Biyayya, Allah Ko Kuma ’Yan Adam?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ci Gaba Zuwa Nasara Ta Ƙarshe!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2001
  • Darussa Daga Littafin Irmiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
w00 4/1 pp. 24-29

Masu Yaƙi Da Allah Ba Za Su Yi Nasara Ba!

“Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.”—IRMIYA 1:19.

1. Wane umurni aka ba Irmiya, kuma aikinsa ya ci gaba zuwa wane lokaci?

JEHOVAH ya umurci saurayi Irmiya ya zama annabi ga al’ummai. (Irmiya 1:5) Wannan ya faru ne a lokacin sarautar Josiah Sarkin kirki na Yahudiya. Hidimar annabci na Irmiya ya ci gaba har lokacin hargitsi kafin Babila ta ci Urushalima a yaƙi kuma ta kwashe mutanen Allah zuwa hijira.—Irmiya 1:1-3.

2. Ta yaya Jehovah ya ƙarfafa Irmiya, kuma menene yaƙi da annabin yake nufi?

2 Saƙon hukunci da Irmiya zai gabatar babu shakka zai tada hamayya. Saboda haka, Allah ya ƙarfafa shi ga abin da yake zuwa a gaba. (Irmiya 1:8-10) Alal misali, wannan kalmomi sun ƙarfafa ruhun annabin: “Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.” (Irmiya 1:19) Yaƙi da Irmiya yana nufin yaƙi da Allah. A yau, Jehovah yana da bayinsa waɗanda aikinsu yana kama da na Irmiya. Kamar shi, suna gabatar da kalmar annabci na Allah da gabagaɗi. Kuma wannan saƙon ya shafe kowanne mutum da kuma al’ummai, ko da kyau ko da muni, ya dangana ne ga yadda suka ɗauke shi. Kamar dai, a lokacin Irmiya, da akwai waɗanda suke yaƙi da Allah ta wurin yin hamayya da bayinsa kuma da ayyukan da Allah ya sa su.

An Kai Wa Bayin Jehovah Farmaki

3. Me ya sa ake kai wa bayin Jehovah farmaki?

3 Tun daga farkon ƙarnin nan na 20 ake kai wa mutanen Jehovah farmaki. A ƙasashe da yawa, mutane masu mugun nufi sun yi ƙoƙari su hana—i, su sa a daina—shelar bisharar Mulkin Allah. Babban Magabcinmu, Iblis, wanda “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye” shi ne yake zuga su. (1 Bitrus 5:8) Da “zamanan Al’ummai” suka cika a shekara ta 1914, Allah ya naɗa Ɗansa ya zama sabon Sarki na duniya kuma ya umurce shi: “Ka ci sarauta a tsakiyar maƙiyanka.” (Luka 21:24; Zabura 110:2) Ta nuna ikonsa, Kristi ya jefo Shaiɗan daga sammai kuma ya saka shi ya kusanci duniya. Sanin cewa lokacinsa kaɗan ya rage, Iblis ya fusata, da shafaffun Kiristoci da abokan aikinsu. (Ru’ya ta Yohanna 12:9, 17) Menene sakamakon farmaki da masu yaƙi da Allah suka yi ta kawowa a kai a kai?

4. Wane gwaji ne mutanen Jehovah suka fuskanta lokacin Yaƙin Duniya na I, amma menene ya faru a shekara ta 1919 da kuma 1922?

4 Lokacin Yaƙin Duniya na I, shafaffun bayin Jehovah sun fuskanci gwajin bangaskiyarsu da yawa. An yi masu ba’a da ɓatanci, taron ’yan banza sun sa su gaba. Kamar yadda Yesu ya ce, sun zama “abin ƙi ga dukan al’ummai.” (Matta 24:9) A tsakanin hargitsin yaƙi, abokan gāba na Mulkin Allah suka yi amfani da wata dabara da aka yi amfani da ita a kan Yesu Kristi. Suka laka wa mutanen Jehovah wai masu tada zaune tsaye ne, sun taɓa cibiyar ƙungiyar Allah da ake gani. A Mayu 1918, an ba da izini daga gwamnatin tarayya a kama shugaban Watch Tower Society J. F. Rutherford, da kuma abokan tarayyarsa na kurkusa guda bakwai. Waɗannan maza takwas aka yi masu ɗaurin talala kuma aka tura su kurkuku a Atlanta, ta Georgia, U.S.A. Bayan watanni tara aka sake su. A Mayu 1919 kotun afil na ɗa’ira suka ce suna da laifi, sai aka dawo da shari’a baya. Aka soma shari’ar kuma, amma daga baya gwamnati suka janye daga tuhumar, kuma aka sake Ɗan’uwa Rutherford tare da abokan tarayyarsa daga zargin ƙarya da aka yi masu. Suka fara ayyukansu, aka yi babban taro a Cedar Point, Ohio, a 1919 da kuma a 1922 aka sake ba aikin wa’azin Mulkin ƙarfi.

5. Yaya aka yi da Shaidun Jehovah a Nazi na Jamus?

5 A 1930, mulkin kama karya ya soma, Jamus, Italiya, da kuma Japan suka haɗa kai su zama Daula. Ba da daɗewa ba cikin waɗannan shekaru, aka fara tsananta wa mutanen Allah, babu ma kamar Nazi a Jamus. Aka hana ayyukansu. Aka yi ta bincikan gidaje, aka kakkama masu gidajen. Aka kai dubbai kuma a sansanin fursuna domin sun ƙi su tuɓe bangaskiyarsu. Manufar yaƙin nan da Allah da kuma mutanensa shi ne a kawar da Shaidun Jehovah daga inda mulkin kama karya ta mallaka. Lokacin da Shaidun suka je kotu a Jamus da farko don su nemi ’yancinsu, Hukumar Shari’a ta Reich ta shirya dogon ra’ayi don ta tabbatar da cewa ba su yi nasara ba. Ta ce: “Kotu ba ya yin shari’a ta wurin abin da ake gani kawai; amma za su biɗa kuma nemi hanyoyi komin wuyan shari’ar, don su cika nawayoyinsu masu-girma.” Wannan yana nufin cewa ba za su yi gaskiya ba. ’Yan Nazi sun riƙe cewa Shaidun Jehovah abokan gaba ne, kuma ‘suna hana gina Zaman Jama’a.’

6. Waɗanne ƙoƙari ne aka yi a hana aikinmu lokacin Yaƙin Duniya na II da kuma bayan haka?

6 Lokacin Yaƙin Duniya na II, an hana kuma an haramta ayyukan mutanen Allah a Australiya, Canada, da kuma waɗansu ƙasashe da aka san su da renon Britaniya—a Afirka, Asiya, da kuma tsibirai na Caribbiya da na Pacific. A United States, mashahurran abokan gāba da mutane da ba su da cikakken bayani suka fara kawo ‘damuwa ta dokoki.’ (Zabura 94:20) An yi jayayyar matsalar gai da tuta da kuma dokar da ta hana wa’azi gida zuwa gida a kotu, kotu ta fito da shawara mai kyau a United States da ya ba da goyon baya ma ’yancin yin bauta. Godiya ta tabbata ga Jehovah, ƙoƙarin abokan gāba bai yi nasara ba. Da yaƙi ya ƙare a Turai, aka ɗaga duk hanin da aka yi. Aka sake dubban Shaidun da aka tsare a sansanin fursuna, amma yaƙin bai ƙare ba. Ba da jimawa ba bayan Yaƙin Duniya na II, Yaƙin Kare-Dangi ya ɓarke. Al’umman Gabashin Turai suka ƙara matsa ma mutanen Jehovah. Hukuma ta ɗauki mataki, ta sa hannu kuma ta hana ayyukan wa’azinmu, aka dakatar da shigan littattafan Littafi Mai-Tsarki, hana manyan taronmu. Aka ɗaure da yawa a kurkuku ko tura su sansanin aikin dole.

Ci Gaba da Aikin Wa’azi!

7. Menene Shaidun Jehovah suka fuskanta a Poland, Rasha, da kuma wasu ƙasashe a shekarun baya bayan nan?

7 Da shekaru suka shige, aikin wa’azin Mulki ya buɗe. Ko da shi ke Poland tana ƙarƙashin mulkin Kwaminis, ta yarda aka yi babban taro na kwana ɗaya a 1982. Sai kuma taron dukan ƙasashen duniya a wurin a 1985. Taron ƙasashen duniya mafi girma ya biyo baya a 1989, da dubbai suka hallara daga Rasha da kuma Ukraine. A cikin wannan shekara, hukumar Hungary da Poland suka ba Shaidun Jehovah izini. A kaka ta 1989, Garun Berlin ya faɗi. Watanni kaɗan bayan haka, aka ba mu izini a Jamus ta Gabas, ba da jimawa ba aka yi taron ƙasashen dukan duniya a Berlin. A farkon shekarun ƙarshe na wannan ƙarni na 20, an yi ƙoƙari a sadu da ’yan’uwa da suke a Rasha. An je wajen wasu ma’aikatan gwamnati a Moscow, kuma a 1991, Shaidun Jehovah aka yi masu rajista. Tun daga lokacin nan aikin ya bunƙasa sosai a Rasha, da kuma a jamhuriyoyin da suka taɓa zama bangaren Soviet Union.

8. Menene ya faru da mutanen Jehovah a cikin shekara 45 da suka biyo bayan Yaƙin Duniya na II?

8 Da tsananta masu take lafawa a wasu wurare, a wasu kuma sai ƙaruwa take. A shekara 45 bayan ƙare yaƙin duniya na biyu, ƙasashe da yawa sun ƙi su ba Shaidun Jehovah izini. Ƙari ga haka, an hana mu ko kuma ayyukanmu a ƙasashe 23 a Afirka, 9 a Asiya, 8 a Turai, 3 a Latin Amirka, da kuma 4 a waɗansu al’ummai na tsibirai.

9. Menene bayin Jehovah suka fuskanta a Malawi?

9 Shaidun Jehovah a Malawi sun fuskanci zalunci mai tsanani, kamawa daga 1967. Domin tsaka-tsakinsu na Kiristocin gaskiya ’yan’uwanmu da ke ƙasar ba su sayi katin jam’iyyar siyasa ba. (Yohanna 17:16) Bayan taron Malawi Congress Party a 1972, suka sabonta muguntarsu. Aka kore ’yan’uwan daga gidajensu kuma aka hana su aiki. Dubbai suka gudu daga ƙasar don kada a kashe su. Masu yaƙin da Allah da kuma mutanensa sun yi nasara ne? Ko kaɗan! Bayan yanayi ya juya, ƙolin masu shela na Mulki 43,767 ne suka ba da rahoto a Malawi a 1999, kuma sama da 120,000 suka halarci taron gunduma a can. An gina sabon ofishin reshe a babban birninsu.

Suna Neman Illa

10. Kamar yadda yake a al’amari na Daniel, menene ’yan hamayya da mutanen Allah na zamani suka yi?

10 ’Yan ridda, limaman addini, da wasu ba za su iya jimre jin saƙon gaskiya na Kalmar Allah ba. Domin matsi daga waɗansu ɓangaren Kiristendom, ’yan hamayya sun nemi hanya, wai hanyar doka, su nuna suna da gaskiya wajen yaƙi da mu. Wace dabara ce wani lokaci suke amfani da ita? To, Menene waɗanda suka haɗa baki suka yi wajen kai wa annabi Daniel farmaki? A Daniel 6:4, 5, mun karanta: “Sa’annan su shugabannai da hakimai suka nemi illa a wurin Daniel kan zancen mulkin ƙasan; amma ba su iya su sami illa ko laifi ba; domin shi amintacce ne, ba a kuwa iske illa ko laifi a cikinsa ba. Sa’annan waɗannan mutane suka ce, ba za mu sami illa a wurin wannan Daniel ba ko kaɗan, sai dai mun iske ta a kansa na wajen shari’ar Allahnsa.” Hakazalika a yau, ’yan hamayya suna neman illa. Sun tada hayaniya game da “rukuni mai haɗari” suka yi ƙoƙarin su laƙaba ma Shaidun Jehovah irin waɗannan. Ta wurin faɗin abin da ba daidai ba game da mu, ta wajen habaici da kuma ƙarya kai tsaye, sun kai farmaki a hanyar da muke sujada da kuma nacewarmu wa ƙa’idodin Allah.

11. Wace da’awa ce ta ƙarya wasu ’yan hamayya suka yi game da Shaidun Jehovah?

11 A wasu ƙasashe, ’yan addinai da ’yan siyasa ba sa son su yarda cewa muna yin “addini mai-tsarki mara-ɓaci a gaban Allah Ubanmu.” (Yaƙub 1:27) Ko da muna yin ayyukanmu na Kirista a cikin ƙasashe dabam dabam 234 ’yan hamayya suna da’awar cewa mu “ba sanannen addini ba ne.” Ba da daɗewa ba, kafin taron dukan ƙasashen duniya a 1998, wata jarida a Athens ta faɗa abin da wani limamin Greek Orthodox da yake da’awar cewa “[Shaidun Jehovah] ba sanannen addini ba ne,” duk da dokar da Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam ta bayar a ƙasan. Bayan ’yan kwanaki kaɗan, wata jarida a wannan birnin ta ba da rahoton wani mai magana da yawun coci yana cewa: “[Shaidun Jehovah] ba za su taɓa zama ‘ikklisiyar Kirista’ ba tun da ba su da wani abu da ya kamanci bangaskiyar Kirista ga Yesu Kristi.” Wannan abin mamaki ne ƙwarai, don babu wani addinin da ke nanata bin misalin Yesu kamar Shaidun Jehovah!

12. A yaƙinmu na ruhaniya, menene dole mu yi?

12 Muna neman mu kāre kuma mu ƙafa bisharar ta hanyar doka. (Filibbiyawa 1:7) Ƙari ga haka, ba za mu yi shirka ba ko mu yi sako-sako a riƙe mizanan Allah na adalci. (Titus 2:10, 12) Kamar Irmiya, mun yi ‘ɗamara mu faɗi dukan abin da Jehovah ya umurce mu,’ ba za mu yarda masu yaƙi da Allah su tsoratar da mu ba. (Irmiya 1:17, 18) Kalma Mai-Tsarki na Jehovah, ta bayyana mana sarai tafarki da yake daidai da za mu bi. Ba za mu so mu dangana ga “iko na jiki” ko kuma “dogara ga inuwar Masar” ba, watau, wannan duniyar. (2 Labarbaru 32:8; Ishaya 30:3; 31:1-3) A yaƙinmu na ruhaniya, dole ne mu ci gaba da dogara ga Jehovah da dukan zuciyarmu, bari ya yi ma sawayenmu ja-gora, kuma kada mu dogara ga namu fahimi. (Misalai 3:5-7) Idan ba Jehovah ya taimake mu ba kuma shi da kansa ya tsare mu ba, dukan aikinmu zai zama “banza.”—Zabura 127:1.

An Tsananta Masu Amma Ba Su Yi Shirka Ba

13. Me ya sa za a iya cewa farmakin shaiɗanci ga Yesu bai yi nasara ba?

13 Babban misalinmu wanda bai yi shirka ba a ibadarsa ga Jehovah shi ne Yesu, wanda aka yi masa tuhumar ƙarya ta tada zaune tsaye da kuma taka doka da aka kafa. Bayan ya bincika batun Yesu, Bilatus ya yi niyyar ya sake shi. Amma taron mutanen da shugabannan addini suka hanzuga su, suka yi ihu a kashe Yesu, ko da shi ke ba shi da laifi. Maimakon Yesu, suka zaɓi a sake masu Barabbas—mutumin da aka sa shi a fursuna saboda tada zaune tsaye da kuma kisa! Bilatus ya sake ƙoƙarin ya hana ’yan hamayya marasa tunani, amma a ƙarshe ya bi ra’ayin jama’ar. (Luka 23:2, 5, 14, 18-25) Ko da yake Yesu ya mutu bisa gungume, wannan farmaki na mugun ƙiyayya na shaiɗanci ga Ɗan Allah mara-laifi bai yi nasara ba ko kaɗan, domin Jehovah ya tashe Yesu daga matattu kuma ya ɗaukaka shi zuwa hannunsa na dama. Ta wurin Yesu da aka ɗaukaka, aka zubo da ruhu mai-tsarki a ranar Fentikos na 33 A.Z., aka kafa ikklisiyar Kirista—“sabuwar halitta.”—2 Korinthiyawa 5:17; Ayukan Manzanni 2:1-4.

14. Menene ya faru da ’yan addinin Yahudawa suka hana mabiyan Yesu?

14 Ba da jimawa ba bayan haka, ’yan addinin suka yi ma manzannin burga, amma Kiristoci na farko ba su daina faɗin abin da suka ji da dukan abin da suka gani ba. Mabiyan Yesu suka yi addu’a: “Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfin zuciya duka.” (Ayukan Manzanni 4:29) Jehovah ya amsa roƙonsu ta wurin cika su da ruhu mai-tsarki kuma ya ƙarfafa su su ci gaba da shelarsu babu fargaba. Ba da jimawa ba, aka ba manzannin doka su daina wa’azi, amma Bitrus da wasu manzannin suka amsa: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.” (Ayukan Manzanni 5:29) Burga, tsarewa, da yi masu bulala bai hana su faɗaɗa ayyukansu na Mulki ba.

15. Wanene Gamaliel, kuma wace shawara ya ba ’yan addini masu hamayya da mabiyan Yesu?

15 Yaya shugabannin addinin suka ji? “Suka soku har ga zuciyarsu, suna so su kashe su [manzannin].” Amma dai, wani malamin Attaura mai suna Gamaliel, Ba-farisi, yana wajen, kuma dukan mutanen suna ba shi daraja. Da aka fid da manzannin daga cikin majami’ar Majalisar na ɗan lokaci, ya ba ’yan addini masu hamayyan shawara: “Ku mazajen Isra’ila, ku yi hankali da kanku ga zancen mutanen nan, abin da ku ke shirin yi. . . . Yanzu fa ina ce maku, ku hawayi waɗannan mutane, ku ƙyale su: (gama idan wannan shawara ko wannan aiki na mutane ne, za ya rushe: amma idan na Allah ne, ba za ku iya rushe su ba), kada a iske ku kuna yaƙi har da Allah.”—Ayukan Manzanni 5:33-39.

Babu Makami da Za a Kirkiro Domin Mu da Zai Yi Nasara

16. A naka kalmomi, yaya za ka furta tabbaci da Jehovah ya ba mutanensa?

16 Shawarar Gamaliel tana da kyau, muna murna idan wasu suka yi magana mai kyau game da mu. Mun san cewa domin hukunci na alƙalai da yawa masu gaskiya, kotu ya ba da ’yancin yin sujada. Hakika, mannewarmu ga Kalmar Allah yana baƙanta wa limaman Kiristendom rai da waɗansu shugabanne na Babila Babba, daular addinan ƙarya ta duniya. (Ru’ya ta Yohanna 18:1-3) Ko da yake su da waɗansu da suka rinjaya, suna yaƙi da mu, muna da wannan tabbacin: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gāba da ke, a shari’a za ki kayas da shi. Gādon bayin Ubangiji ke nan, adilcinsu wanda shi ke daga wurina, in ji Ubangiji.”—Ishaya 54:17.

17. Ko da yake ’yan hamayya suna yaƙi da mu, me ya sa muke da gabagaɗi?

17 Abokan gābanmu suna yaƙi da mu babu dalili, amma ba mu yi sanyin jiki ba. (Zabura 109:1-3) Ba za mu taɓa yarda maƙiya saƙon Littafi Mai-Tsarki su razanar da mu, su sa mu yi shirka cikin bangaskiyarmu ba. Ko da yake muna tsammanin yaƙinmu na ruhaniya zai yi tsanani, mun san abin da zai faru. Kamar Irmiya, za mu ga cikan kalmomin nan na annabci: “Za su yi yaƙi da kai; amma ba za su yi nasara da kai ba: gama ina tare da kai, in ji Ubangiji, domin in cece ka.” (Irmiya 1:19) Hakika, mun san cewa masu yaƙi da Allah ba za su yi nasara ba!

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa ake kai wa bayin Jehovah farmaki?

• A wane hanyoyi ne ’yan hamayya suka yi yaƙi da mutanen Jehovah?

• Me ya sa za mu tabbata cewa masu yaƙi da Allah ba za su yi nasara ba?

[Hoto a shafi na 24]

An tabbatar wa Irmiya cewa Jehovah yana tare da shi

[Hoto a shafi na 25]

Waɗanda suka tsira daga sansanin fursuna

[Hoto a shafi na 25]

Taron ’yan banza akan Shaidun Jehovah

[Hoto a shafi na 25]

J. F. Rutherford da abokan tarayyarsa

[Hoto a shafi na 28]

A batun Yesu, masu yaƙi da Allah ba su yi nasara ba

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba