Wa Kake Wa Biyayya, Allah Ko Kuma ’Yan Adam?
“Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—AYUKAN MANZANNI 5:29.
1. (a) Menene ayar jigon wannan talifin? (b) Me ya sa aka kama manzanni?
ALƘALAN kotun ƙoli na Yahudawa mai yiwuwa sun fusata ƙwarai. Fursunonin sun ɓace. Manzannin Yesu Kristi ne, mutumin da alƙalan babban kotu suka yanke wa hukuncin kisa ’yan makonni da suka shige. Yanzu kotun yana shirye ya ji ma mabiyansa na kud da kud. Amma sa’ad da dogarai suka tafi su kawo su gaban kotun, sai suka ga babu kowa cikin kurkuku ko da yake an kulle ƙofofin. Ba da daɗewa ba dogaran suka sami labari cewa manzannin suna cikin haikali a Urushalima, suna koya wa mutane game da Yesu Kristi da gabagaɗi, aikin da ya sa aka kama su! Dogaran suka tafi haikalin kai tsaye suka kama manzannin kurkuku suka tsai da su a gaban majalisa.—Ayukan Manzanni 5:17-27.
2. Menene mala’ika ya umurci manzannin su yi?
2 Mala’ika ne ya saki manzannin daga kurkuku. Domin kada a tsananta musu ne? A’a. Domin mazauna Urushalima su ji bishara game da Yesu Kristi. Mala’ikan ya umurci manzannin su “faɗa ma jama’a dukan maganar wannan Rai.” (Ayukan Manzanni 5:19, 20) Dalilin da ya sa ke nan, sa’ad da dogaran suka isa haikalin suka iske manzannin suna biyayya da wannan umurni.
3, 4. (a) Sa’ad da aka umurce su su daina wa’azi, yaya Bitrus da Yohanna suka amsa? (b) Ta yaya wasu manzanni suka aikata?
3 Manzanni Bitrus da Yohanna masu wa’azi da himma, an saka su a kurkuku da farko, yadda babban alƙali Yusufu Kayafa ya kwaɓe su kuma ya tuna musu. Ya ce: “Muka dokace ku da ƙarfi, kada ku koyar cikin wannan suna [Yesu]: ga shi kuwa, kun gama Urushalima da koyarwarku.” (Ayukan Manzanni 5:28) Bai kamata Kayafa ya yi mamakin ganin an sake dawo da Bitrus da Yohanna kotu ba. Sa’ad da aka umurce su su daina wa’azi da farko, manzannin biyu sun amsa: ‘Ko daidai ne gaban Allah mu fi jinku da Allah, sai ku hukunta: gama ba shi yiwuwa a garemu mu rasa faɗin abin da muka ji muka gani.’ Kamar annabi Irmiya na dā, Bitrus da Yohanna ba za su iya daina aikinsu na wa’azi ba.—Ayukan Manzanni 4:18-20; Irmiya 20:9.
4 Yanzu ba Bitrus da Yohanna kaɗai ba ne suke da zarafin faɗin matsayinsu a kotu ba amma dukan manzannin, har da Matiyas da aka zaɓa ba da daɗewa ba. (Ayukan Manzanni 1:21-26) Sa’ad da aka umurce su su daina wa’azi, sun faɗa da gaba gaɗi: ‘Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.’—Ayukan Manzanni 5:29.
Biyayya ga Allah ko Kuwa Biyayya ga Ɗan Adam?
5, 6. Me ya sa manzannin ba su yi biyayya ga dokar kotun ba?
5 Manzannin mutane ne masu bin doka da ba za su ƙi biyayya ga umurnin kotun ba. Amma ba ɗan adam, ko menene matsayinsa da yake da ikon gaya wa wani kada ya bi umurnin Allah. Jehobah ne “Maɗaukaki bisa dukan duniya.” (Zabura 83:18) “Mai-shari’an dukan duniya” ne mai ba da Doka mafi girma, kuma Sarkin zamanai. Kowane umurnin kotu da ya saɓa wa dokokin Allah ba daidai ba ne a gabansa.—Farawa 18:25; Ishaya 33:22.
6 Ƙwararrun Lauyoyi sun san haka gaskiya ne. Alal misali, lauya Bature na ƙarni na 18, William Blackstone ya rubuta cewa bai kamata a ƙyale dokar ’yan adam ta saɓa wa “dokar da aka bayyana” da yake cikin Littafi Mai Tsarki ba. Saboda haka, Majalisar ta wuce gona da iri sa’ad da ta umurci manzannin su daina wa’azi. Manzannin ba za su iya yin biyayya ga wannan dokar ba.
7. Me ya sa aikin wa’azi ya sa manyan firistoci suka yi fushi?
7 Da yake manzannin suna da aniyar su ci gaba da wa’azi, hakan ya sa babban firistoci sun yi fushi. Wasu cikin firistocin, har da Kayafa da kansa wanda Saduki ne, ba su gaskata da tashin matattu ba. (Ayukan Manzanni 4:1, 2; 5:17) Duk da haka, manzannin sun ci gaba da faɗan cewa an tashi Yesu daga matattu. Ƙari ga haka, wasu cikin babban firistoci sun yi ƙoƙari sosai su sami tagomashin masu mulki na Romawa. Sa’ad da aka ba su zarafi su amince cewa Yesu sarkinsu ne a lokacin gwajinsa, babban firistoci suka ta da murya suka ce: “Ba mu da wani sarki sai Kaisar.” (Yohanna 19:15)a Manzannin sun ba da tabbacin cewa an tashi Yesu daga matattu kuma sun koyar da cewa ban da sunan Yesu “babu wani suna ƙarƙashin sama, da aka bayar wurin mutane, inda ya isa mu tsira.” (Ayukan Manzanni 2:36; 4:12) Firistocin suna tsoro cewa Romawa suna iya mallakarsu kuma shugabannin Yahudawa su rasa ‘wurinsu duk da al’ummarsu,’ idan mutanen suka fahimci cewa Yesu da aka ta da daga matattu ne ainihin Shugabansu.—Yohanna 11:48.
8. Wane gargaɗi ne mai kyau Gamaliel ya yi wa ’yan Majalisa?
8 Kamar dai manzannin Yesu Kristi za su fuskanci wahala a nan gaba. Alƙalan Majalisa sun ƙudiri aniya su kashe su. (Ayukan Manzanni 5:33) Amma, abubuwa sun canja yadda ba a yi tsammaninsa ba. Gamaliel wanda ƙwararren Lauya ne, ya tashi tsaye, ya yi wa abokansa gargaɗi kada su yi garaje. Ya ce cikin hikima: “Idan wannan shawara ko wannan aiki na mutane ne, za ya rushe: amma idan na Allah ne, ba za ku iya rushe su ba.” Sai Gamaliel ya daɗa abu mai muhimmanci: “Kada a iske ku kuna yaƙi har da Allah.”—Ayukan Manzanni 5:34, 38, 39.
9. Menene ya nuna cewa aikin manzannin daga wurin Allah ne?
9 Abin mamaki, kotun ya saurari shawarar Gamaliel. ’Yan Majalisa “suka duke su, suka dokace su kada su yi zance cikin sunan Yesu, kāna suka sake su.” Manzannin ba su tsorata ba amma sun ƙuduri aniya su yi biyayya da umurnin mala’ika su je su yi wa’azi. Shi ya sa bayan da aka sake su “kowace rana fa, cikin haikali da cikin gida, [manzannin] ba su fāsa koyarwa da yin wa’azi kuma Yesu Kristi ne.” (Ayukan Manzanni 5:40, 42) Jehobah ya albarkace su. Ta yaya? “Maganar Allah kuwa ta yawaita; yawan masu-bi kuma cikin Urushalima ya riɓanɓanya ƙwarai.” Hakika “babban taro kuma na malamai suka yi biyayya ga imanin.” (Ayukan Manzanni 6:7) Wannan abin damuwa ne ga manyan firistoci! Da akwai tabbaci sosai cewa aikin manzannin daga wurin Allah ne!
Masu Yaƙi da Allah ba Za Su Yi Nasara Ba
10. A ganin mutum, me ya sa Kayafa ya ji ba za a cire shi daga matsayinsa ba, amma me ya sa gaba gaɗinsa ba daidai ba ne?
10 A ƙarni na farko, masu mulki na Romawa ne suke naɗa manyan firistoci na Yahudawa. Valerius Gratus ne ya ɗora Yusufu Kayafa mai arziki a matsayin da yake, kuma ya riƙe wannan matsayin na dogon lokaci fiye da manyan firistoci da suka riga shi. Wataƙila Kayafa yana ganin ya cim ma wannan ne domin iya hulɗar jakadanci da kuma abokantakarsa da Bilatus maimakon ikon Allah. Amma, dogararsa ga mutane ba daidai ba ne. Shekara uku bayan da aka kai manzannin gaban Majalisa, Kayafa ya yi rashin tagomashi a gaban masu mulki na Romawa kuma aka cire shi daga babban firist.
11. Ta yaya Bilatus Babunti da zamanin Yahudawa suka kai ƙarshensu, menene wannan ya koya maka?
11 Umurni cewa a tuɓe Kayafa daga matsayinsa ya zo ne daga wurin Lucius Vitellius shugaban Bilatus, wato gwamnan Suriya, Bilatus abokin Kayafa na kud da kud bai iya hana hakan ba. Hakika, bayan shekara guda da tuɓe Kayafa, aka cire Bilatus da kansa daga matsayinsa kuma aka tuhume shi sosai a Roma. Shugabannin Yahudawa kuma da suka dogara da Kaisar, Romawa suka kwace ‘wurinsu duk da al’ummarsu.’ Wannan ya faru ne a shekara ta 70 A.Z., sa’ad da sojojin Romawa suka halaka birnin Urushalima, da haikali da kuma majami’ar Majalisa. Kalmomin mai zabura gaskiya ne: “Kada ku dogara ga sarakuna, ko kuwa ɗan adam, wanda babu taimako gareshi.”—Yohanna 11:48; Zabura 146:3.
12. Ta yaya batun Yesu ya nuna cewa yi wa Allah biyayya tafarki ne na hikima?
12 Akasin haka, Allah ya naɗa Yesu Kristi da aka ta da daga matattu Babban Firist na haikalin ruhaniya mai girma. Babu mutumin da zai iya cire shi daga matsayinsa. Hakika, Yesu “yana da [matsayinsa na firist] wanda ba ya koma ma wani ba.” (Ibraniyawa 2:9; 7:17, 24; 9:11) Allah ya naɗa Yesu ya yi wa masu rai da matattu shari’a. (1 Bitrus 4:5) A wannan matsayin, Yesu ne zai tsai da ko Yusufu Kayafa da Bilatus Babunti za su rayu a nan gaba.—Matta 23:33; Ayukan Manzanni 24:15.
Masu Wa’azin Mulki na Zamani da Gaba Gaɗi
13. A wannan zamanin, wane aiki ne na ’yan adam, kuma wannene na Allah? Ta yaya ka sani?
13 Yadda yake a ƙarni na farko, akwai masu ‘yaƙi da Allah’ da yawa a yau. (Ayukan Manzanni 5:39) Alal misali, sa’ad da Shaidun Jehobah a Jamus suka ƙi yarda cewa Adolf Hitler shugabansu ne, Hitler ya ƙudura ya halaka su. (Matta 23:10) Yana da rukuni masu kisa da suke aikin da kyau. ’Yan Nazi sun yi nasara wajen kama dubban Shaidu kuma suka saka su a sansani. Suka kashe wasu Shaidun. Amma ’yan Nazi ba su sa Shaidun sun ja da baya a ƙudurinsu na bauta wa Allah shi kaɗai ba, kuma sun kasa kawar da rukunin bayin Allah. Aikin waɗannan Kiristocin daga wurin Allah ne, ba daga ɗan adam ba, kuma ba za a iya rushe aikin Allah ba. Bayan shekara sattin, masu aminci da suka tsira wa sansanin fursuna na Hitler suna bauta wa Jehobah ‘da dukan zuciyarsu, da dukan ransu, da dukan azancinsu’ amma ana tuna Hitler da ’yan Nazi don muguntarsu.—Matta 22:37.
14. (a) Waɗanne ƙoƙarce-ƙoƙarce ’yan hamayya suka yi don su tsegunta bayin Allah, kuma menene sakamakon haka? (b) Irin waɗannan abubuwa za su yi wa mutanen Allah lahani na dindindin ne? (Ibraniyawa 13:5, 6)
14 Shekaru da yawa bayan abubuwan da ’yan Nazi suka yi, wasu sun sa hannu a yaƙi da Jehobah da mutanensa amma ba su yi nasara ba. A ƙasashe da yawa a Turai, mutanen addini da na siyasa masu wayo sun ce Shaidun Jehobah ‘ɗarika mai haɗari’ ce, zargi da aka yi wa Kiristoci na ƙarni na farko. (Ayukan Manzanni 28:22) Hakika, Kotun Turai na ’Yancin ’Yan Adam sun fahimci cewa Shaidun Jehobah addini ne ba ɗarika ba. Babu shakka, waɗannan masu hamayya suna sane da abin da kotun ya faɗa. Duk da haka, sun ci gaba da tsegunta Shaidun. Domin wannan yaudarar, an sallami wasu cikin waɗannan Kiristoci daga aikinsu. An matsa wa yara shaidu a makaranta. Masu ba da gidan haya da suka tsorata sun hana Shaidu su yi amfani da gidajensu inda suke taro da daɗewa. A wani yanayi, ma’aikatan gwamnati sun ƙi ba mutane izinin zaman ƙasa domin su Shaidun Jehobah ne! Duk da haka Shaidun ba su karaya ba.
15, 16. Yaya Shaidun Jehobah a Faransa suka aikata ga hamayya da aikinsu na Kirista, me ya sa suka ci gaba da yin wa’azi?
15 Alal misali, a Faransa mutane suna da sanin ya kamata kuma suna saurarar ra’ayin wasu. Amma wasu ’yan hamayya sun kafa dokoki don a hana aikin Mulki. Ta yaya Shaidun Jehobah da suke wajen suka aikata? Sun daɗa ƙwazo a aikinsu na wa’azi kuma sun sami sakamako masu kyau. (Yaƙub 4:7) A cikin wata shida, adadin nazarin Littafi Mai Tsarki na gida ya ƙaru da kashi 33 bisa ɗari a wannan ƙasar! Babu shakka, ganin masu zuciyar kirki sun saurari bishara a Faransa ya sa Iblis fushi. (Ru’ya ta Yohanna 12:17) ’Yan’uwanmu a Faransa suna da tabbaci cewa kalmomin annabi Ishaya zai zama gaskiya a yanayinsu: “Babu alatun da aka halitta domin ciwutanki da za ya yi albarka; iyakar harshe kuma da za shi tashi gaba da ke, a shari’a za ki kayar da shi.”—Ishaya 54:17.
16 Shaidun Jehobah ba sa jin daɗin tsanantawa. Amma, da yake suna biyayya da umurnin Allah ga dukan Kiristoci, ba za su iya daina faɗan abin da suka ji ba. Suna ƙoƙari su zama mazauna ƙasa na kirki. Amma inda dokar ’yan adam ta saɓa wa ta Allah, dole su yi biyayya da ta Allah.
Kada Ku Ji Tsoronsu
17. (a) Me ya sa ba za mu ji tsoron magabtanmu ba? (b) Wane irin hali ne ya kamata mu nuna wa masu tsananta mana?
17 Magabtanmu suna cikin yanayi na haɗari. Suna yaƙi da Allah. Da haka, daidai da umurnin Yesu, maimakon mu ji tsoronsu, muna yi wa waɗanda suke tsananta mana addu’a. (Matta 5:44) Muna addu’a cewa Jehobah ya buɗe idanun wani da yake hamayya da Allah cikin jahilci ya san gaskiya, yadda aka yi wa Shawulu na Tarsus. (2 Korinthiyawa 4:4) Shawulu ya zama manzo Bulus kuma ya sha wahala sosai a hannun masu iko na zamaninsa. Duk da haka, ya ci gaba da tuna wa ’yan’uwa masu bi su “yi biyayya ga mahukunta, ga masu-iko; su ji magana, su zama shiryayyu ga kowane kyakkyawan aiki, kada su ambaci kowa da mugunta, [har ma waɗanda suka fi tsananta musu] su kasance marasa-faɗa, masu-laushin hali, suna nuna iyakacin tawali’u ga dukan mutane.” (Titus 3:1, 2) Shaidun Jehobah da suke Faransa da wasu wurare suna ƙoƙari su yi biyayya da wannan umurnin.
18. (a) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah zai ceci mutanensa? (b) Menene zai zama sakamako na ƙarshe?
18 Allah ya gaya wa annabi Irmiya: “Ina tare da kai domin in cece ka.” (Irmiya 1:8) Ta yaya Jehobah zai cece mu daga tsanantawa a yau? Yana iya ta da alƙali mai sanin ya kamata kamar Gamaliel. Ko kuma ya sa a cire ma’aikaci mai ɓatanci ko mai hamayya a saka mai sauƙin kai. Wani lokaci, Jehobah yana iya ƙyale a ci gaba da tsananta wa mutanensa. (2 Timothawus 3:12) Idan Allah ya ƙyale a tsananta mana, zai ci gaba da ba mu ƙarfi da za mu jimre wa tsanantawar. (1 Korinthiyawa 10:13) Ko menene Allah ya ƙyale, sakamako na ƙarshe shi ne cewa, waɗanda suke yaƙi da mutanen Allah suna yaƙi da Allah ne, kuma masu yaƙi da Allah ba za su yi nasara ba.
19. Menene jigon shekara ta 2006, kuma me ya sa ya dace?
19 Yesu ya gaya wa almajiransa cewa za a tsananta musu. (Yohanna 16:33) Saboda haka, kalmomin da ke rubuce a Ayukan Manzanni 5:29 ya fi dacewa yanzu: ‘Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.’ Saboda haka, an zaɓi waɗannan kalmomi masu ban sha’awa su zama jigon shekara na Shaidun Jehobah a shekara ta 2006. Bari mu ƙudiri aniya mu fi biyayya ga Allah ko da menene zai faru a shekara mai zuwa da kuma har abada!
[Hasiya]
a “Kaisar” da manyan firistoci suka nuna sun amince masa a fili Tibariyas ne Daular Roma, wanda munafuki ne kuma mai kisa. An kuma san Tibariyas da ayyukan lalata.—Daniel 11:15, 21.
Za Ka Iya Amsawa?
• A yadda suka fuskanci hamayya wane misali mai ban ƙarfafa ne manzannin suka kafa mana?
• Me ya sa dole ne mu fi biyayya ga Allah da mutane?
• Masu hamayya da mu ainihi suna hamayya da waye?
• Wane sakamako waɗanda suka jimre wa tsanantawa za su samu?
[Bayanin da ke shafi na 15]
Jigon shekara ta 2006 zai zama: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29
[Hoto a shafi na 11]
“Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane”
[Hoto a shafi na 13]
Kayafa ya dogara ga mutane maimakon ga Allah