Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 1/1 pp. 8-10
  • Darussa Daga Littafin Ezra

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Darussa Daga Littafin Ezra
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • AN SAKE GINA HAIKALI
  • (Ezra 1:1–6:22)
  • EZRA YA KOMA URUSHALIMA
  • (Ezra 7:1–10:44)
  • Jehobah ya Cika Alkawuransa
  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Zai Taimaka Maka In Kana Cikin Wahala
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ezra ya koyar da Dokar Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Yana Son Masu Bauta da Zuciya Daya
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu (2016)
  • Dogara Ga Taimakon Allah
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 1/1 pp. 8-10

Maganar Jehobah Rayayyiya Ce

Darussa Daga Littafin Ezra

LITTAFIN Ezra na Littafi Mai Tsarki ya soma ne daga inda littafin Tarihi na Biyu ya tsaya. Ezra firist wanda shi ne marubucin littafin, ya soma ba da labarin ne da umurnin da Sarkin Farisa Cyrus ya bayar da ya sa raguwar Yahudawa da suke zaman bauta a Babila suka koma ƙasarsu. Labarin ya ƙare ne da matakin da Ezra ya ɗauka na tsarkake mutanen da suka ƙazantar da kansu da mutanen ƙasar. Littafin ya ba da labarin aukuwa na shekara 70, wato daga shekara ta 537 zuwa 467 K.Z.

Sa’ad da yake rubuta littafin, Ezra yana da wata takamammiyar manufa, wato: ya nuna yadda Jehobah ya cika alkawarinsa na ’yanta mutanensa daga bauta a Babila da kuma mai da bauta ta gaskiya a Urushalima. Saboda haka, Ezra ya mai da hankali ne kawai a kan aukuwar da ta shafi wannan manufar. Littafin Ezra na ɗauke da labarin yadda aka sake gina haikali da kuma yadda aka sake kafa bautar Jehobah duk da hamayya da kuma ajizancin mutanen Allah. Labarin yana da muhimmanci a gare mu domin muna zaune ne a lokacin da ake farfaɗo da bauta ta gaskiya. Mutane da yawa suna ta jerin gwano zuwa “dutsen Ubangiji,” kuma dukan duniya ta kusan “cika da sanin darajar Ubangiji.”—Ishaya 2:2, 3; Habakkuk 2:14.

AN SAKE GINA HAIKALI

(Ezra 1:1–6:22)

Don yin na’am da dokar ’yancin da Cyrus ya bayar, kusan Yahudawa 50,000 da suke zaman bauta ne suka koma Urushalima a ƙarƙashin shugabancin Gwamna Zerubbabel, ko Sheshbazzar. Waɗanda suka koma Urushalima sun kafa bagadi kuma sun soma yi wa Jehobah hadaya.

A shekara ta biye, Isra’ilawa sun kafa harsashin gidan Jehobah. Maƙiya sun ci gaba da kawo tangarɗa wajen aikin ginin kuma daga baya sun yi nasara wajen samun ikon hana aikin. Annabawa Haggai da Zechariah sun motsa mutanen har suka koma bakin aikin gina haikalin duk da hanin. Tsoron yin hamayya da umurnin ƙasar Farisa da ba ya canjawa da Cyrus ya bayar ya kori abokan gāba. Binciken da aka ba da umurnin a yi ne ya sa aka fahimci umurnin da Cyrus ya bayar “a kan zancen gidan Allah wanda ke a Urushalima.” (Ezra 6:3) Aikin ya ci gaba kuma an kammala shi.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

1:3-6—Isra’ilawan da ba su koma ƙasarsu ba suna da rarraunar bangaskiya ne? Wataƙila wasu sun ƙi komawa Urushalima ne domin suna son abin duniya ko kuwa domin ba su daraja bauta ta gaskiya ba, amma ba haka duka al’amarin yake ba. Da farko, tafiyar mil 1,000 zuwa Urushalima zai ɗauki watanni huɗu ko biyar. Bugu da ƙari, zama a ƙasar da ta zama kango na shekara 70 da kuma sake gina ta zai bukaci aiki tuƙuru. Saboda haka, matsaloli kamar, cututtuka, tsufa, da kuma bukatu na iyali, babu shakka sun hana wasu komawa ƙasarsu.

2:43—Su wanene Nethinim? Waɗannan mutane ne da ba Isra’ilawa ba, amma bayi ne ko masu hidima na haikali. A cikinsu akwai Gibeyonawa na zamanin Joshua da kuma wasu “waɗanda Dauda da sarakai suka bayas domin taimakon Leviyawa.”—Ezra 8:20.

2:55—Su wanene ’ya’yan bayin Sulemanu? Waɗannan ba Isra’ilawa ba ne amma an ba su gata mai muhimmanci a hidimar Jehobah. Wataƙila sun yi hidima a matsayin marubuta a cikin haikali ko kuwa sun yi sarauta.

2:61-63—Waɗanda suka dawo daga bauta suna da Urim da Thummim da ake amfani da su sa’ad da ake bukatar samun amsa daga Jehobah? Waɗanda suka ce su zuriyar firistoci ne amma sun kasa bayyana asalinsu, da sai su tabbatar da haka ta wajen yin amfani da Urim da Thummim. Ezra ya ambata yiwuwar hakan ne kawai. Nassosi ba su ambata cewa an yi amfani da Urim da kuma Thummim a wannan lokacin ba ko kuma daga baya. Hadisin Yahudawa ya nuna cewa Urim da Thummim sun ɓace sa’ad da aka halaka haikalin a shekara ta 607 K.Z.

3:12—Me ya sa “tsofofi da suka ga gida na farko” na Jehobah suka yi kuka? Waɗannan mutanen sun tuna yadda haikalin da Sulemanu ya gina yake da kyau. Aikin sabon haikalin da ke gabansu a idanunsu “kamar babu” ne idan aka gwada da na dā. (Haggai 2:2, 3) Aikin da suke yi zai sa haikalin ta sami ɗaukakarta na dā? Wataƙila sun fid da zuciya, saboda haka sai suka soma kuka.

3:8-10; 4:23, 24; 6:15, 16—An ɗauki shekara nawa kafin a gama gina haikalin? An kafa harsashin haikalin a shekara ta 536 K.Z., wato ‘a cikin shekara ta biyu ta zuwansu.’ An daina aikin a zamanin Sarkin Artaxerxes, a shekara ta 522 K.Z. Hanin ya ci gaba har shekara ta 520 K.Z., wato a shekara ta biyu ta sarautar Sarki Darius. An kammala haikalin a shekara ta shida ta sarautarsa, ko kuwa shekara ta 515 K.Z. (Ka duba akwatin nan mai jigo “Sarakunan Farisa Daga Shekara Ta 537 Zuwa 467 K.Z.”) Da haka, ginin haikalin ya ɗauki kusan shekara 20.

4:8-6:18—Me ya sa aka rubuta wannan sashe na Ezra da yaren Aramaic?—Wannan sashen na ɗauke ne da wasiƙun da manya cikin gwamnati suka rubuta wa sarakuna da kuma amsoshinsu. Ezra ya kofe su ne daga takardar da ake rubuta sunayen mutane a ciki wadda aka rubuta da yaren Aramaic, kuma wannan shi ne yaren da ake yi a wajen sana’a da kuma al’amuran mulki a zamanin. Wasu sashe na Littafi Mai Tsarki da aka rubuta a wannan yaren na Aramaic sune Ezra 7:12-26, Irmiya 10:11, da kuma Daniel 2:4b–7:28.

Darussa Dominmu:

1:2. Abin da annabi Ishaya ya annabta shekara 200 da ta shige ya cika. (Ishaya 44:28) Annabce-annabce na cikin Kalmar Jehobah suna cika.

1:3-6. Kamar wasu Isra’ilawa da suka yi zamansu a Babila, Shaidun Jehobah da yawa ba su iya shiga hidima ta cikakken lokaci ko kuwa su yi hidima a inda ake da bukata mai girma. Duk da haka suna tallafawa da kuma karfafa waɗanda suka shiga hidima na cikakken lokaci kuma suna ba da kyauta na son rai don ci gaban aikin wa’azin Mulki da kuma almajirantarwa.

3:1-6. A watan bakwai na shekara ta 537 K.Z., (watan Tishri, wanda ya yi daidai da Satumba/Oktoba), masu aminci da suka koma Urushalima sun yi hadayarsu ta farko. Sarki Nebuchadnezzar ya shiga Urushalima a watan biyar (watan Ab, wanda ya yi daidai da Yuli/Agusta) na shekara ta 607 K.Z., kuma bayan watanni biyu, an rugurguje birnin. (2 Sarakuna 25:8-17) Kamar yadda aka annabta, kangon da Urushalima ta zama na shekara 70 ya zo ƙarshe a daidai lokacin da aka annabta. (Irmiya 25:11; 29:10) Duk abin da Kalmar Jehobah ta faɗa, babu shakka zai cika.

4:1-3. Raguwar mutane masu aminci sun ƙi tayin da aka yi musu wanda zai sa su suka hannu a addini da bauta ta karya. (Fitowa 20:5; 34:12) Hakazalika, masu bauta wa Jehobah a yau ba sa saka hannu a kowane irin tsari na arna.

5:1-7; 6:1-12. Jehobah yana iya juya al’amura don nasarar mutanensa.

6:14, 22. Saka hannu a aikin Jehobah da himma na kawo amincewarsa da albarka.

6:21. Samariyawa waɗanda suke zaune a ƙasar Yahudawa da suka ƙyale ayyukan arna, sun gyara rayuwarsu domin sun ga ci gaban aikin Jehobah. Ya kamata mu saka hannu sosai a aikin da Allah ya ba mu, har da aikin sanar da Mulki.

EZRA YA KOMA URUSHALIMA

(Ezra 7:1–10:44)

Shekara hamsin ta wuce tun da aka keɓe gidan Jehobah da aka sake gina. A shekara ta 468 K.Z. Ezra ya tafi Urushalima daga Babila, tare da raguwar mutanen Allah da kuma gudummawar kuɗin da aka bayar. Menene ya gani a wurin?

Hakiman sun gaya wa Ezra cewa: “Jama’ar Isra’ila, da [firistoci] da Lawiyawa ba su keɓe kansu, su rabu da al’umman ƙasa ba, amma suna aika bisa ga irin ƙazamtassu.” Ƙari ga haka, “laifin hakimai da na mukaddasai ya fi yawa a wannan matsala.” (Ezra 9:1, 2) Al’amarin ya ba Ezra mamaki. Amma an ƙarfafa shi ya “yi ƙarfin zuciya, [ya] yi shi.” (Ezra 10:4) Ezra ya daidaita al’amarin kuma mutanen sun saurare shi.

Tambayoyin Nassi da aka Amsa:

7:1, 7, 11—Waɗannan surorin duka suna nuni ne ga Artaxerxes da ya hana aikin ginin? A’a. Artaxerxes suna ne ko laƙabi da ke nuni ga sarakunan Farisa biyu. Wataƙila na farko shi ne Bardiya ko kuwa Gaumata, wanda ya hana aikin haikali a shekara ta 522 K.Z. Artaxerxes da ke sarauta sa’ad da Ezra ya zo Urushalima shi ne Artaxerxes Longimanus.

7:28–8:20—Me ya sa yawancin Yahudawan da ke Babila suka ƙi bin Ezra zuwa Urushalima? Ko da yake shekara 60 ta wuce da rukunin farko na Yahudawa suka koma ƙasarsu, mutanen da ke zaune a Urushalima ba su da yawa. Komawa Urushalima na nufin soma sabuwar rayuwa a cikin yanayi mai wuya kuma mai haɗari. Yanayin Urushalima a wannan lokacin bai jawo hankalin Yahudawan da ke zaune cikin ni’ima a Babila ba. Wani abin da za a yi la’akari da shi, shi ne haɗarin da ke tattare da tafiyar. Masu dawowar suna bukatar su kasance da cikakken imani ga Jehobah, himma ga bauta ta gaskiya, da kuma ƙarfin zuciya na aikatawa. Ezra ya sami ƙarfafa daga wurin Jehobah. Domin ƙarfafan da suka samu daga Ezra, iyalai 1,500, waɗanda wataƙila sun kai mutane 6,000 sun bi shi. Bayan Ezra ya ƙara ɗaukan mataki, Lawiyawa 38 da kuma Nethinim 220, sun bi shi.

9:1, 2—Me ya sa yin auratayya da mutanen ƙasar ba ƙaramin barazana ba ne? Al’ummar da aka mai da sune ya kamata su kasance masu yin ja-gora ga bautar Jehobah har sai Almasihu ya bayyana. Yin auratayya da wasu mazauna ƙasar ba ƙaramin barazana ba ne ga bauta ta gaskiya. Domin wasu sun auri mata masu bauta wa gunki, hakan na iya mai da dukan mazauna ƙasar su zama masu bauta wa gunki. Hakan kuma na iya kawar da bauta ta gaskiya gabaki ɗaya. Idan haka ya faru, waye ne Almasihu zai zo ya sama? Babu shakka, shi ya sa Ezra ya yi mamakin ganin abin da ke faruwa!

10:3, 44—Me ya sa aka kawar da duka mata tare da ’ya’yansu? Idan aka ƙyale yaran, zai yiwu matan da aka kora su dawo domin ’ya’yansu. Bugu da ƙari, yara ƙanana suna bukatar kula daga uwarsu.

Darussa Dominmu:

7:10. A matsayinsa na cikakken ɗalibi da kuma ƙwararren malamin Kalmar Allah, Ezra ya kafa mana misali mai kyau. Cikin addu’a, ya shirya zuciyarsa domin ya bincika Dokar Jehobah. Sa’ad da ya bincika ta, Ezra ya mai da hankali sosai a kan abin da Jehobah ke cewa. Ezra ya yi amfani da abin da ya koya, kuma ya nuna himma sosai wajen koyar da wasu.

7:13. Jehobah yana son bayi masu son ba da kansu da son rai.

7:27, 28; 8:21-23. Ezra ya yaba wa Jehobah, ya roƙe shi sosai kafin ya yi tafiya mai nisa kuma mai haɗari zuwa Urushalima, kuma a shirye yake ya saɗaukar da rayuwarsa domin ɗaukakar Allah. Da haka, ya kafa mana misali mai kyau.

9:2. Ya kamata mu ɗauki umurnin nan na yin aure “cikin Ubangiji” kawai da muhimmanci.—1 Korinthiyawa 7:39.

9:14, 15. Yin tarayya marar kyau na iya jawo rashin amincewar Jehobah.

10:2-12, 44. Mutanen da suka auri mata baƙi, sun tuba cikin tawali’u kuma sun gyara kurakuran da suka yi. Halayensu da kuma aikatawar da suka yi abin koyi ne.

Jehobah ya Cika Alkawuransa

Littafin Ezra na da tamani sosai a gare mu! A cikin lokaci, Jehobah ya cika alkawarinsa na ’yanta mutanensa daga bauta a Babila kuma ya mai da bauta ta gaskiya a Urushalima. Hakan ya ƙarfafa bangaskiyarmu a Jehobah da kuma alkawuransa.

Ka yi tunani game da misalan da littafin Ezra ya bayar. Ezra da raguwar mutanen da suka koma don saka hannu a wajen mai da bauta ta gaskiya a Urushalima sun nuna misali mai kyau na ba da kai ga Allah. Wannan littafin ya taƙaita bangaskiyar baƙi masu tsoron Allah da kuma hali na tawali’u da masu zunubi da suka tuba suka nuna. Hakika, hurarriyar kalmar Ezra ta tabbatar cewa “maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.”—Ibraniyawa 4:12.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba