Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w23 Nuwamba pp. 14-19
  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Zai Taimaka Maka In Kana Cikin Wahala

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Zai Taimaka Maka In Kana Cikin Wahala
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA MATSALOLIN SUKA SHAFI YAHUDAWA DA SUKA DAWO URUSHALIMA
  • KA MAI DA HANKALI GA YIN NUFIN ALLAH
  • YADDA ZA MU IYA ƘARA DOGARA GA JEHOBAH
  • KA CI-GABA DA DOGARA GA JEHOBAH HAR ZUWA ƘARSHE
  • Darussa Daga Littafin Ezra
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ezra ya koyar da Dokar Allah
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • “Ina Tare Da Ku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Bari Hannuwanku Su Yi Ƙarfi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
w23 Nuwamba pp. 14-19

TALIFIN NAZARI NA 48

Ka Kasance da Tabbaci Cewa Jehobah Zai Taimaka Maka In Kana Cikin Wahala

“Ku yi ƙarfin zuciya, . . . gama Ni Yahweh Mai Runduna ina tare da ku.”—HAG. 2:4.

WAƘA TA 118 Ka “Ƙara Mana Bangaskiya”

ABIN DA ZA A TATTAUNAa

1-2. (a) Ta yaya yanayinmu ya yi ɗaya da na Yahudawa da suka dawo daga Urushalima? (b) Ka taƙaita matsalolin da Yahudawan suka fuskanta. (Ka duba akwatin nan “Zamanin Haggai da Zakariya da kuma Ezra.”)

SHIN a wasu lokuta, kakan damu game da yadda rayuwarka za ta kasance a nan gaba? Mai yiwuwa an kore ka daga aiki, kuma kana damuwa a kan yadda za ka kula da iyalinka. Wataƙila kuma kana tunani a kan yadda za ka kāre iyalinka saboda rigingimun siyasa da ake yi, ko tsanantawa, ko kuma ana hamayya da waꞌazin da muke yi. Shin kana fuskantar ɗaya daga cikin abubuwan nan? Idan haka ne, za ka amfana sosai idan ka yi laꞌakari da yadda Jehobah ya taimaka wa Israꞌilawa a dā saꞌad da suka fuskanci matsaloli kamar haka.

2 Akwai Yahudawan da a Babila ne aka haife su. Saboda haka, suna bukatar bangaskiya sosai don su iya barin abubuwan da suke mora a Babila kuma su koma Urushalima. Jim kaɗan bayan sun isa Urushalima, sai suka fara fuskantar matsalar tattalin arziki, da rigingimun siyasa da kuma hamayya. Hakan ya sa ya yi ma wasunsu wuya su mai da hankali ga gina haikalin Jehobah. Don haka, a wajen shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu, Jehobah ya naɗa annabawa guda biyu, wato annabi Haggai da kuma Zakariya don su ƙarfafa mutanen su ci-gaba da yin ginin. (Hag. 1:1; Zak. 1:1) Za mu ga yadda ƙarfafa da annabawa biyun nan suka yi wa mutanen ya taimaka musu. Amma kusan shekaru 50 bayan haka, Yahudawan nan da suka dawo daga Babila sun sake yin sanyin gwiwa. Don haka, Ezra, wanda ya iya kwafan Dokar Allah sosai, ya dawo Urushalima daga Babila don ya ƙarfafa bayin Allah su sake mai da hankali ga bauta ta gaskiya.—Ezra 7:​1, 6.

Zamanin Haggai da Zakariya da kuma Ezra

Shekarun da muhimman abubuwa suka faru a zamanin Haggai, da Zakariya, da kuma Ezra (dakun shekaru kafin haihuwar Yesu ne). 537: Yahudawa na barin Babila. 520: Annabi Haggai da Zakariya suna magana da Israꞌilawa a Urushalima. 515: Haikalin da ke Urushalima. 484: Gimbiya Esther ta je gun Sarki Ahasuerus. 468: Ezra yana tafiya tare da wasu Yahudawa. 455: Katangar Urushalima.

DUKAN KWANAKIN WATAN K.H.Y.

  1. 537: Rukunin Yahudawa na farko da suka koma Urushalima

  2. 520: Haggai da Zakariya suna annabci a Urushalima

  3. 515: An gama gina haikalin

  4. 484: Esther ta ɗauki mataki bayan Xerxes na Ɗaya (Ahasuerus) ya ba da umurni a kakkashe dukan Yahudawa

  5. 468: Ezra da kuma rukunin Yahudawa na biyu suna komawa Urushalima

  6. 455: An gama gina katangar Urushalima

3. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna? (Karin Magana 22:19)

3 Annabcin da Haggai da kuma Zakariya suka yi ya taimaka wa mutanen Allah a dā su ci-gaba da dogara gare shi duk da cewa suna fuskantar hamayya. Mu ma annabce-annabcen nan za su taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli. (Karanta Karin Magana 22:19.) Yayin da muke tattauna saƙon da Jehobah ya aika ma Israꞌilawan ta bakin Haggai da Zakariya, da kuma tattauna misalin Ezra, za mu amsa tambayoyin nan: Ta yaya matsalolin suka shafi Yahudawa da suka dawo? Me ya sa zai dace mu ci-gaba da sa yin nufin Allah farko a rayuwarmu saꞌad da muke fuskantar matsaloli? Kuma ta yaya za mu ƙara dogara ga Jehobah saꞌad da muke fuskantar matsaloli?

YADDA MATSALOLIN SUKA SHAFI YAHUDAWA DA SUKA DAWO URUSHALIMA

4-5. Waɗanne abubuwa ne wataƙila suka sa Israꞌilawan su yi sanyin gwiwa saꞌad da suke gina haikalin?

4 Da Israꞌilawan suka isa Urushalima, sun tarar da ayyuka da yawa da suke bukatar su yi. Nan-da-nan, suka sake gina bagade na Jehobah, kuma suka yi tushen haikalin. (Ezra 3:​1-3, 10) Amma sun fuskanci matsaloli da dama kuma hakan ya sa sun yi sanyin gwiwa. Me ya sa? Ban da ginin haikalin da suke yi, suna bukatar su gina nasu gidajen, su yi shuki kuma su ciyar da iyalinsu. (Ezra 2:​68, 70) Ban da haka, maƙiyansu ba su so su gina haikalin ba, kuma sun yi ƙulle-ƙulle don su hana su.—Ezra 4:​1-5.

5 Israꞌilawan da suka dawo Urushalima sun kuma fuskanci matsalar tattalin arziki, da kuma rigingimun siyasa. A lokacin, ƙasarsu na ƙarƙashin Daular Fashiya. Bayan sarkin Fashiya mai suna Cyrus ya rasu a shekara ta 530 kafin haihuwar Yesu, magājinsa mai suna Cambyses yana so ya ci ƙasar Masar da yaƙi. Saꞌad da shi da sojojinsa suke zuwa Masar, mai yiwuwa sun bi ta yankin Israꞌila kuma sun tilasta wa Israꞌilawan su ba su abinci, da ruwan sha, da kuma wurin kwana, kuma hakan ya ƙara sa Israꞌilawan cikin wahala. A farko-farkon sarautar magājin Cambyses, wato Darius na 1, an yi fama da matsaloli da dama a daular, kamar tawaye, da kuma tashe-tashen hankula. Ba mamaki, matsalolin nan sun sa Israꞌilawan damuwa a kan yadda za su iya tanada wa iyalinsu abubuwan da suke bukata. Saboda matsalolin da suke fuskanta a lokacin, wasu Yahudawan sun ce bai dace su sake gina haikalin a lokacin ba.—Hag. 1:2.

6. Waɗanne ƙarin matsaloli ne Israꞌilawan suka fuskanta, kuma bisa ga Zakariya 4:​6, 7, wane tabbaci ne Zakariya ya ba su?

6 Karanta Zakariya 4:​6, 7. Ban da matsalar tattalin arziki, da rigingimun siyasa, Yahudawan sun kuma fuskanci tsanantawa. A shekara ta 522 kafin haihuwar Yesu, maƙiyansu sun ruɗi sarkin Fashiya, sai ya umurci Yahudawan su daina gina haikalin. Amma ta bakin annabi Zakariya, Jehobah ya gaya wa Yahudawan cewa zai yi amfani da ruhunsa don ya cire duk matsalolin da suke fuskanta. A shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu, Sarki Darius ya amince Israꞌilawan su ci-gaba da gina haikalin. Ƙari ga haka, ya ba su kuɗi kuma ya umurci gwamnonin yankinsu su taimaka musu.—Ezra 6:​1, 6-10.

7. Da Yahudawan suka mai da hankali ga yin nufin Jehobah, wace albarka ce suka samu?

7 Ta bakin annabi Haggai da kuma Zakariya, Jehobah ya gaya wa mutanensa cewa idan sun fi mai da hankali ga gina haikalin, zai taimaka musu. (Hag. 1:​8, 13, 14; Zak. 1:​3, 16) Yahudawan sun sami ƙarfafa daga annabawan, kuma hakan ya sa sun sake soma gina haikalin a shekara ta 520 kafin haihuwar Yesu. Kafin shekara biyar, sun gama gina haikalin. Da yake Yahudawan sun mai da hankali ga gina haikalin Jehobah duk da matsalolin da suke fuskanta, Jehobah ya tanada musu abubuwan da suke bukata kuma ya taimaka musu su yi kusa da shi. Hakan ya sa sun bauta wa Jehobah da farin ciki.—Ezra 6:​14-16, 22.

KA MAI DA HANKALI GA YIN NUFIN ALLAH

8. Ta yaya abin da ke Haggai 2:4 zai taimaka mana mu ci-gaba da mai da hankali ga yin nufin Allah? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

8 Yayin da ƙunci mai girma yake gabatowa, yana da muhimmanci mu tuna cewa muna bukatar mu yi waꞌazin Mulkin Allah da gaggawa kamar yadda aka umurce mu mu yi. (Mar. 13:10) Amma zai iya yi mana wuya mu mai da hankali ga yin waꞌazi idan muna fama da rashin kuɗi, ko kuma ana hamayya da waꞌazin da muke yi. Me zai iya taimaka mana mu sa Mulkin Allah farko a rayuwarmu? Abin da zai taimaka mana shi ne, mu kasance da tabbaci cewa “Yahweh Mai Runduna”b yana tare da mu. Zai taimaka mana idan muka ci-gaba da sa mulkinsa farko a rayuwarmu. Don haka, ba ma bukatar mu ji tsoro.—Karanta Haggai 2:4.

9-10. Ta yaya wasu maꞌaurata suka ga yadda alkawarin da Yesu ya yi a Matiyu 6:33 ya cika a rayuwarsu?

9 Ka yi laꞌakari da misalin Ɗanꞌuwa Oleg da matarsa Irina.c Su maꞌaurata ne da ke hidimar majagaba. Bayan sun ƙaura zuwa wani yanki don su taimaka ma wata ikilisiya, sun rasa aikin da suke yi domin ƙasarsu tana fama da matsalar tattalin arziki. Ko da yake sun yi shekara ɗaya ba su sami aiki na dindindin ba, sun ga yadda Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwansu Kiristoci suka taimaka musu. Me ya taimaka musu su iya jimre matsalar? Da farko, Oleg ya damu sosai, amma daga baya ya ce: “Mun yi amfani da yawancin lokacinmu muna waꞌazi, kuma hakan ya taimaka mana mu mai da hankali ga abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwa.” Yayin da shi da matarsa suke neman aiki, sun ci-gaba da yin waꞌazi da ƙwazo.

10 Da suka dawo daga waꞌazi wata rana, sai suka ji cewa wani abokinsu ya zo daga wurin da ke da nisan wajen kilomita 160, kuma ya kawo musu kayan abincin da ya cika jakunkuna biyu. Oleg ya ce: “Hakan ya sake nuna mana yadda Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu a ikilisiya suke ƙaunar mu sosai. Yanzu muna da tabbaci cewa Jehobah ba zai taɓa yashe bayinsa ba, ko da suna ganin kamar yanayinsu ba zai taɓa yin kyau ba.”—Mat. 6:33.

11. Wane abu ne za mu samu idan muka mai da hankali ga yin nufin Allah?

11 Jehobah yana so mu mai da hankali ga taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Kamar yadda aka ambata a sakin layi na 7, Haggai ya umurci Yahudawan su ƙara ƙwazo wajen sake gina haikalin. Idan sun yi hakan, Jehobah ya yi alkawari cewa zai ‘sa musu albarka.’ (Hag. 2:​18, 19) Mu ma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai yi mana albarka idan mun mai da hankali ga yin aikin da ya ce mu yi.

YADDA ZA MU IYA ƘARA DOGARA GA JEHOBAH

12. Me ya sa Ezra da Yahudawan da suka dawo daga Babila suke bukatar bangaskiya sosai?

12 A shekara ta 468 kafin haihuwar Yesu, Ezra ya zo Urushalima tare da rukunin Yahudawa na biyu da suka bar Babila. Ezra da Yahudawan suna da bangaskiya sosai shi ya sa suka iya yin tafiyar domin hanyar da suka bi tana da haɗari sosai, kuma suna ɗauke da zinariya da azurfa mai yawan gaske da aka bayar a matsayin gudummawa don gina haikalin. Hakan zai iya sa ɓarayi su tare su a hanya. (Ezra 7:​12-16; 8:31) Ban da haka, sun gano cewa ko Urushalima da kanta ma babu tsaro. Babu mutane da yawa a birnin kuma katangar da ƙofofin birnin sun lalace. Ta yaya misalin Ezra zai taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah?

13. Ta yaya Ezra ya ƙara dogara ga Jehobah? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

13 Ezra ya ga yadda Jehobah ya taimaka wa mutanensa saꞌad da suke fuskantar matsaloli. Da alama Ezra yana Babila a shekara ta 484 kafin haihuwar Yesu saꞌad da Sarki Ahasuerus ya ba da umurni cewa a kashe dukan Yahudawa da ke Daular Fashiya. (Esta 3:​7, 13-15) Hakan ya sa ran Ezra da sauran Yahudawan cikin haɗari. Da suka ji game da umurnin, sun damu sosai har suka kasa cin abinci. Sun yi kuka kuma sun roƙi Jehobah ya taimaka musu. (Esta 4:3) Ka yi tunanin yadda Ezra da ꞌyanꞌuwansa Yahudawa suka ji saꞌad da aka kashe waɗanda suke so su kakkashe Yahudawan. (Esta 9:​1, 2) Abin da ya faru da Ezra a wannan mawuyacin yanayin, ya ba shi ƙarfin fuskantar matsalolin da za su taso daga baya, kuma ba mamaki hakan ya ƙara tabbatar masa cewa Jehobah zai iya kāre bayinsa.d

14. Wane darasi ne wata ꞌyarꞌuwa ta koya daga yadda Jehobah ya taimaka mata saꞌad da take fuskantar matsaloli?

14 Idan muka ga yadda Jehobah ya taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli, za mu ƙara kasance da tabbaci cewa zai taimaka mana idan muka fuskanci matsaloli a nan gaba. Ka yi laꞌakari da misalin wata ꞌyarꞌuwa mai suna Anastasia da ke zama a Gabashin Turai. Ta daina aikin da take yi domin abokan aikinta suna ƙoƙarin sa ta ta goyi bayan wani ɓangare na siyasa. Ta ce: “Wannan shi ne karo na farko da na rasa kuɗi a rayuwata.” Sai ta ƙara da cewa: “Na danƙa kome a hannun Jehobah, kuma na ga yadda ya taimaka mini. Idan na sake rasa aikina, ba zan ji tsoro ba. Tun da yake Ubana na sama yana taimaka mini a yau, ina da tabbaci cewa zai taimaka mini a nan gaba.”

15. Mene ne ya taimaka wa Ezra ya ci-gaba da dogara ga Jehobah? (Ezra 7:​27, 28)

15 Ezra ya ga hannun Yahweh a rayuwarsa. Ba mamaki Ezra ya ƙara dogara ga Jehobah saꞌad da ya yi tunani a kan hanyoyi da dama da Jehobah ya taimaka masa. Ka lura cewa Ezra ya ce “hannun Yahweh Allahna yana tare da ni.” (Karanta Ezra 7:​27, 28.) Ezra ya yi amfani da irin furucin nan har sau 6 a littafin da ke ɗauke da sunansa.—Ezra 7:​6, 9; 8:​18, 22, 31.

A waɗanne yanayoyi ne za mu iya ganin hannun Jehobah a rayuwarmu? (Ka duba sakin layi na 16)e

16. A wane yanayoyi ne za mu iya ganin hannun Jehobah a rayuwarmu? (Ka kuma duba hoton.)

16 Jehobah zai iya taimaka mana saꞌad da muke fuskantar matsaloli. Alal misali, Saꞌad da muka roƙi shugabanmu a wurin aiki ya ba mu izini don mu je taron yanki, ko kuma muka roƙe shi ya canja lokacin da muke aiki don mu iya halartan kowane taro, hakan zai sa mu ga hannun Jehobah a rayuwarmu. Za mu iya yin mamakin jin abin da shugabanmu zai gaya mana. Kuma hakan zai sa mu ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana.

Ezra tare da wasu Israꞌilawa a haikali suna makoki. Shekaniya yana daga Ezra.

Ezra yana yin adduꞌa yana kuka a haikali don zunuban mutanen. Jamaꞌar ma suna kuka. Sai Shekaniya ya zo yana taꞌazantar da Ezra, yana cewa: “Akwai sauran sa zuciya domin Israꞌila. . . . Mu kuwa muna goyan bayanka.”​—⁠Ezra 10:​2, 4 (Ka duba sakin layi na 17)

17. Ta yaya Ezra ya nuna sauƙin kai saꞌad da yake fuskantar matsaloli? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)

17 Ezra ya roƙi Jehobah ya taimaka masa. A duk lokacin da yake damuwa don aikin da aka ba shi, Ezra yakan roƙi Jehobah ya taimaka masa. (Ezra 8:​21-23; 9:​3-5) Domin Ezra ya dogara ga Jehobah, hakan ya ƙarfafa abokansa su ma su dogara ga Jehobah. (Ezra 10:​1-4) Idan muna yawan damuwa game da abubuwan da muke bukata ko kuma lafiyar iyalinmu, zai dace mu roƙi Jehobah da tabbacin cewa zai taimaka mana.

18. Mene ne zai iya taimaka mana mu ƙara dogara ga Jehobah?

18 Idan muka ƙaskantar da kanmu, muka nemi taimakon Jehobah, kuma muka yarda ꞌyanꞌuwanmu su taimaka mana, za mu iya ƙara kasance da tabbacin cewa Jehobah zai taimaka mana a nan gaba. Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Erika, ta ci-gaba da kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mata duk da cewa wani mummunan balaꞌi ya abka mata. Jim kaɗan bayan ta yi ɓarin ciki, ta rasa maigidanta. Ga abin da ta faɗa game da abubuwan da suka faru da ita: “Da farko, ba za ka san yadda Jehobah zai taimaka maka ba. Zai iya taimaka maka a hanyar da ba ka zata ba. Na lura cewa Jehobah ya amsa yawancin adduꞌoꞌina ta wurin furuci da kuma ayyukan abokaina. Idan na gaya wa abokaina abin da ke faruwa da ni, zai yi musu sauƙi su taimaka mini.”

KA CI-GABA DA DOGARA GA JEHOBAH HAR ZUWA ƘARSHE

19-20. Mene ne muka koya daga Yahudawan da suka ƙasa koma Urushalima?

19 Za mu kuma iya koyan darasi mai kyau daga Yahudawa da suka ƙasa koma Urushalima. Wasu sun ƙasa koma Urushalima domin tsufa ko rashin lafiya ko kuma matsalolin iyali. Duk da haka, sun yi farin cikin ba ma waɗanda za su koma abubuwan da suke bukata don su iya gina haikalin. (Ezra 1:​5, 6) Da alama cewa har shekaru 19 bayan rukunin Yahudawa na farko suka isa Urushalima, waɗanda suka ƙasa komawa sun ci-gaba da aika gudummawa zuwa Urushalima.—Zak. 6:10.

20 Ko da ba ma iya yin abubuwan da muke so mu yi a bautar mu ga Jehobah, za mu iya kasance da tabbacin cewa Jehobah yana farin ciki domin muna yin iya ƙoƙarinmu mu bauta masa. Ta yaya muka san da hakan? A zamanin annabi Zakariya, Jehobah ya umurci annabi Zakariya ya ƙera hular mulki daga zinariya da kuma azurfa wanda Yahudawan da ke Babila suka aika. (Zak. 6:11) “Hular mulkin” zai riƙa tuna wa Yahudawan da gudummawar da suka yi da dukan zuciyarsu. (Zak. 6:14) Don haka, za mu iya kasance da tabbacin cewa Jehobah ba zai taɓa manta da yadda muka yi iya ƙoƙarinmu don mu bauta masa saꞌad da muke fuskantar matsaloli ba.—Ibran. 6:10.

21. Mene ne zai ba mu tabbaci cewa Jehobah zai kasance tare da mu idan mun fuskanci matsaloli a nan gaba?

21 Ba shakka, za mu ci-gaba da fuskantar matsaloli a wannan kwanakin ƙarshe kuma yanayin duniya zai ci-gaba da yin muni. (2 Tim. 3:​1, 13) Amma bai kamata mu riƙa damuwa game da abubuwan da za su iya faruwa da mu ba. Ka tuna da abin da Jehobah ya gaya wa mutanensa a zamanin annabi Haggai, ya ce: “Ina tare da ku . . . saboda haka kada ku ji tsoro.” (Hag. 2:​4, 5) Mu ma za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai kasance tare da mu, muddin muna yin nufinsa. Idan muka bi abin da muka koya daga annabi Haggai da Zakariya kuma muka yi koyi da Ezra, za mu ci-gaba da kasancewa da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana ko da mun shiga matsala ba zato.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya matsaloli za su iya sa mu yi sanyin gwiwa a hidimarmu ga Jehobah?

  • Me ya sa ya dace mu mai da hankali ga yin nufin Jehobah ko da muna fuskantar matsaloli?

  • Ta yaya za mu ƙara dogara ga Jehobah saꞌad da muke fuskantar matsaloli?

WAƘA TA 122 Mu Tsaya Daram, Babu Tsoro!

a Wannan talifin zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka mana idan muna fama da matsalar tattalin arziki, ko rigingimun siyasa ko kuma ana hamayya da aikin da muke yi.

b Furucin nan “Yahweh Mai Runduna” ya bayyana har sau 14 a littafin Haggai, hakan ya tuna wa Yahudawan da mu ma a yau cewa Jehobah yana da iko marar iyaka, kuma yana da miliyoyin malaꞌiku da suke aiki a ƙarƙashinsa.—Zab. 103:​20, 21.

c An canja wasu sunayen.

d Ezra mutum ne da ya iya kwafan dokar Jehobah sosai. Don haka, ya gaskata alkawura da Jehobah ya yi da dukan zuciyarsa tun kafin ya koma Urushalima.—2 Tar. 36:​22, 23; Ezra 7:​6, 9, 10; Irm. 29:14.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Wani ɗanꞌuwa ya roƙi shugabansa a wurin aiki ya ba shi dama ya je taron yanki, amma shugaban bai yarda ba. Ya yi adduꞌa ga Jehobah ya taimake shi yayin da yake shirin sake tattaunawa da shugabansa. Ya nuna wa shugabansa takardar gayyata na taron, kuma ya bayyana masa yadda taron yake sa mu zama mutanen kirki. Hakan ya burge shugabansa, kuma ya amince masa ya halarci taron.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba