Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w06 5/1 pp. 12-16
  • Bari Hannuwanku Su Yi Ƙarfi

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bari Hannuwanku Su Yi Ƙarfi
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Abubuwa da Suka fi Muhimmanci
  • Tabbataccen Goyon Baya
  • Albarka na Dindindin
  • “Ina Tare Da Ku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Darussa Daga Littattafan Haggai da Zakariya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2007
  • Karusa da Kambi Suna Kāre Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2017
  • Ka Ga Abin da Zakariya Ya Gani Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
w06 5/1 pp. 12-16

Bari Hannuwanku Su Yi Ƙarfi

“Bari hannuwanku su yi ƙarfi, ku da ku ke ji cikin waɗannan kwanaki zantattukan nan daga bakin annabawa.”—ZECHARIAH 8:9.

1, 2. Me ya sa ya kamata mu mai da hankali ga littattafan Haggai da Zechariah?

AN RUBUTA annabce-annabcen Haggai da Zechariah a shekaru 2,500 da suka shige, duk da haka, suna da muhimmanci a rayuwarka. Labaran Littafi Mai Tsarki kamar waɗanda suke cikin Haggai da Zechariah ba tarihi ba ne kawai. Suna cikin “iyakar abin da aka rubuta a dā aka rubuta su domin koyarwarmu.” (Romawa 15:4) Yawancin abubuwa da muke karantawa a cikin waɗannan littattafan, suna sa mu yi tunani game da ainihin abubuwa da suke faruwa tun lokacin da aka kafa Mulki a sama a shekara ta 1914.

2 Sa’ad da yake yin nuni ga aukuwa da kuma yanayin da mutanen Allah suka fuskanta a dā, manzo Bulus ya ce: “Waɗannan al’amura dai suka same su watau misali ne; kuma aka rubuta su domin gargaɗi garemu, mu waɗanda matuƙan zamanu sun zo a kanmu.” (1 Korinthiyawa 10:11) Kana iya mamaki, ‘Wane amfani ne littattafan Haggai da Zechariah suke da shi a zamaninmu?’

3. Haggai da Zechariah sun mai da hankali ga menene?

3 Kamar yadda talifin da ya gabata ya nuna, annabce-annabcen Haggai da Zechariah sun ƙunshi lokacin da Yahudawa suka koma ƙasar da Allah ya ba su bayan da aka sako su daga bauta a Babila. Annabawan sun mai da hankali ga sake gina haikali. Yahudawa sun kafa harsashi na haikalin a shekara ta 536 K.Z. Ko da yake wasu tsofaffin Yahudawa sun mai da hankali ga abin da ya faru a dā, sun “yi ihu da ƙarfi domin farinciki.” Hakika, abin da ya fi wannan muhimmanci ma ya faru a zamaninmu. Ta yaya?—Ezra 3:3-13.

4. Menene ya faru bayan Yaƙin Duniya ta ɗaya?

4 Bayan Yaƙin Duniya ta ɗaya, an saki shafaffun Jehobah daga bauta ta Babila Babba. Wannan ya nuna goyon bayan Jehobah. Da farko, kamar dai shugabannan addinai da mabiyansu na siyasa sun kawo ƙarshen aikin wa’azi da koyarwa na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. (Ezra 4:8, 13, 21-24) Amma Jehobah Allah ya kawar da duk wata tangarɗar da za ta hana aikin wa’azin Mulki da almajirantarwa. Shekaru da yawa bayan shekara ta 1919, aikin Mulkin ya ci gaba kuma babu abin da ya iya tsayar da shi.

5, 6. Ga wane abu da za a cim ma ne Zechariah 4:7 ta yi maganarsa?

5 Muna da tabbaci cewa Jehobah zai ci gaba da tallafa wa aikin wa’azi da koyarwa da bayinsa masu biyayya a zamaninmu suke yi. Zechariah 4:7 ta ce: “Za ya kuwa fito da dutse na kukewa, ana ta sowa dominsa, ta bar kalla, ta bar kalla!” Amma wace cika mai girma wannan take nunawa a zamaninmu?

6 Zechariah 4:7 tana nuna lokacin da bauta ta gaskiya ta Ubangiji Mai Ikon Mallaka za ta kawo kamiltaccen yanayi a farfajiya ta duniya na haikalinsa na ruhaniya. Wannan haikalin tsarin Jehobah ne na bauta masa bisa hadayar Yesu Kristi. Hakika, haikali mai girma na ruhaniya ya kasance tun ƙarni na farko A.Z. Amma, bauta ta gaskiya a farfajiya ta duniya za ta kamilta nan ba da daɗewa ba. Miliyoyin Kiristoci suna yin bauta a farfajiya ta duniya na ruhaniya. Waɗannan da miliyoyi da aka tashe su daga matattu za su zama kamiltattu a lokacin sarautar Yesu Kristi na Shekara Dubu Ɗaya. Masu bauta wa Allah da gaske ne kawai za a ƙyale a duniya da aka tsabtacce a ƙarshen sarauta ta shekara dubu ɗaya.

7. Wane hakki ne Yesu yake da shi wajen sa bauta ta gaskiya ta kasance cikin kamiltaccen yanayi a zamaninmu, kuma me ya sa ya kamata wannan ya ƙarfafa mu?

7 Gwamna Zarubabel da Babban Firist Joshuwa suna wajen don su ga cewa an kammala ginin haikalin a shekara ta 515 K.Z. Zechariah 6:12, 13 sun annabta hakkin Yesu wajen sa bauta ta gaskiya ta kasance cikin kamiltaccen yanayi: “Hakanan Ubangiji mai-runduna ya faɗi, ga mutum wanda sunansa Zuriya ne; za ya tsiro kuma daga wajensa; shi kuma za ya gina haikalin Ubangiji; shi . . . za ya ɗauki daraja, ya zauna kuma ya yi mulki a bisa kursiyinsa; za ya zama firist a bisa kursiyinsa.” Domin Yesu yana sama kuma yana sa zuriyar Dauda ta sarakuna ta yi girma yana kuma tallafa wa aikin Mulki a haikali na ruhaniya, akwai wanda zai iya hana ta ci gaba? Babu! Ya kamata wannan ya ƙarfafa mu mu ci gaba da hidimarmu, kuma kada mu ƙyale damuwa ta yau da kullum ta janye hankalinmu.

Abubuwa da Suka fi Muhimmanci

8. Me ya sa za mu saka aikin haikali na ruhaniya ta zama na farko a rayuwarmu?

8 Don mu sami taimakon Jehobah da albarkarsa, dole ne mu sa aikin haikali na ruhaniya farko a rayuwarmu. Ba kamar Yahudawan da suka ce, “Lokacin zuwanmu ba ya yi ba,” dole mu tuna cewa lokacin da muke ciki “kwanaki na ƙarshe” ne. (Haggai 1:2; 2 Timothawus 3:1) Yesu ya annabta cewa almajiransa masu aminci za su yi wa’azin bishara na Mulkin da kuma almajirantarwa. Dole ne mu mai da hankali kada mu yi watsi da gatarmu ta hidima. Ba a gama aikin wa’azi da koyarwa da aka soma a shekara ta 1919 ba bayan da hamayya ta duniya ta tsayar da aikin na ɗan lokaci. Amma, ya kamata ka kasance da tabbaci cewa babu shakka za a kammala wannan aikin!

9, 10. Me ya kamata mu yi don mu sami albarkar Jehobah, kuma menene wannan ke nufi a garemu?

9 Za a albarkace mu idan muka ci gaba da yin aikin sosai, mu duka ko ɗaɗɗaya. Yi la’akari da alkawarin da Jehobah ya yi wanda hakan zai iya ba mu tabbaci. Idan har Yahudawa suka soma bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya kuma suka soma kafa harsashin haikalin, Jehobah ya ce: “Daga yau zan albarkace ku.” (Haggai 2:19) Za su ji daɗin maido da tagomashinsa. Ka yi la’akari da albarkar da yake tare da alkawarin Allah: “Iri na salama za ya kasance a wurin; kuringar anab za ta bada ’ya’yanta; ƙasa kuma za ta bada amfaninta, sama za ta bada raɓatta kuma; zan sa ringin mutanen nan su gāji waɗannan abu duka.”—Zechariah 8:9-13.

10 Kamar yadda Jehobah ya yi wa Yahudawa alkawarin samun albarka ta ruhaniya da ta zahiri, hakazalika, zai albarkace mu yayin da muke yin aiki da ya ba mu da ƙwazo da kuma zuciya ɗaya. Waɗannan albarkatu sun haɗa da samun salama a tsakaninmu, kāriya, ni’ima, da kuma ci gaba ta ruhaniya. Amma ka kasance da tabbaci cewa za mu ci gaba da samun albarkar Allah idan muna aikinmu a haikali na ruhaniya yadda Jehobah yake so.

11. Ta yaya za mu iya bincika makasudinmu?

11 Yanzu ne lokaci da ‘za mu lura da al’amuranmu.’ (Haggai 1:5, 7) Ya kamata dukanmu mu ɗauki lokaci mu bincika abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwarmu. Samun albarkar Jehobah a yau ya dangana ne da yadda muke ɗaukaka sunansa kuma muke ci gaba a aikinmu a haikalinsa na ruhaniya. Za ka iya tambayar kanka: ‘Makasudai na sun canja? Ina nuna ƙwazo ga aikin Jehobah, da gaskiyarsa, kamar sa’ad da na yi baftisma? Son jin daɗin rayuwa yana ɗauke lokacin da nake ba Jehobah da Mulkinsa ne? Ina barin tsoron mutane ya hana ni yabon sunan Jehobah da yin aikin haikalinsa na ruhaniya?’—Ru’ya ta Yohanna 2:2-4.

12. Wane yanayi ne game da Yahudawa aka nanata a Haggai 1:6, 9?

12 Babu shakka, ba za mu so Allah ya hana mu albarkarsa domin mun yi watsi da aikin ɗaukaka sunansa ba. Haggai 1:9 ta ce bayan da suka fara gina haikali, Yahudawa da suka koma ƙasarsu ‘suna gudu, kowa zuwa nasa gida.’ Sun shagala da nasu bukatu. Duk da haka, suna “girbi kaɗan,” suna karancin abinci da abin sha mai kyau, kuma suna rashin tufafi. (Haggai 1:6) Jehobah ya daina yi musu albarka. Da darassi da za mu koya a nan kuwa?

13, 14. Ta yaya za mu iya yin amfani da darasin da ke Haggai 1:6, 9, kuma me ya sa yake da muhimmanci?

13 Ka yarda cewa idan muna so mu ci gaba da samun albarkar Jehobah, dole ne mu daina biɗan abubuwa na kanmu da za su hana mu mu bauta wa Jehobah? Dole ne mu guji abubuwan da za su rinjayi hankalinmu zuwa neman dukiya, tsarin samun arziki na dare ɗaya, shirin ƙarin ilimi mai ɗaukan lokaci, da kuma tsarin cim ma burinmu.

14 Irin waɗannan abubuwa ba laifi ba ne. Duk da haka, waɗannan “matattun ayyuka” ne idan aka gwada su da rai madawwami. (Ibraniyawa 9:14) Menene hakan ke nufi? Matattu ne a ruhaniya, wofi, kuma marasa amfani. Idan mutum ya nace da yin su, irin waɗannan ayyuka za su kawo mutuwa ta ruhaniya. Hakan ya taɓa faruwa ga wasu shafaffun Kiristoci a zamanin manzanni (Filibbiyawa 3:17-19) Ya faru ga wasu a namu zamanin. Wataƙila kun san wasu da suka ja baya daga hidiman Kirista da kuma ikilisiya; kuma ba sa son su dawo cikin hidimar Jehobah. Kuma muna da tabbacin cewa waɗannan za su koma ga Jehobah, amma gaskiyar ita ce biɗan “matattun ayyuka” za su iya jawo rashin tagomashin Jehobah da kuma albarkarsa. Irin waɗannan ayyuka suna iya jawo baƙin ciki. Hakan zai jawo rashin farin ciki da kuma salamar da ruhun Allah ke bayarwa. Kuma ka yi tunanin irin rashin da za ka yi idan ka rabu da ’yan’uwa Kirista!—Galatiyawa 1:6; 5:7, 13, 22-24.

15. Ta yaya ne Haggai 2:14 ta nuna muhimmancin bautar mu?

15 Wannan batu yana da muhimmanci sosai. Ka lura da yadda Jehobah ya ɗauki Yahudawan da suka ƙyale gidansa na bauta a zahiri ko kuma a alamance a Haggai 2:14 don su gina nasu gidajen. “Hakanan wannan jama’a ta ke, hakanan kuma wannan al’ummai ta ke a gabana, in ji Ubangiji; hakanan ne kuma kowane aikin hannuwansu; abin da su ke yin hadaya da shi a wurin kuma marar-tsarki ne.” Ba a amince da kowace hadaya da Yahudawa suke miƙawa a kan bagadi a Urushalima ba muddin sun ƙyale bauta ta gaskiya.—Ezra 3:3.

Tabbataccen Goyon Baya

16. Bisa ga wahayin da Zechariah ya gani, wane tabbaci ne Yahudawa suke da shi?

16 Ta wurin wahayi takwas da Zechariah ya gani, an tabbatar wa Yahudawa masu biyayya da suka yi aiki wajen sake gina haikalin cewa Allah zai taimake su. Wahayi na farko ya tabbatar da cewa za a gama haikalin kuma Urushalima da Yahuda za su sami ni’ima muddin Yahudawa sun yi aikin da ya kamata su yi. (Zechariah 1:8-17) Wahayi na biyu ya yi alkawarin cewa za a kawo ƙarshen dukan gwamnatoci da ke hamayya da bauta ta gaskiya. (Zechariah 1:18-21) Sauran wahayin sun ba da tabbaci cewa Allah zai kāre aikin ginin, kuma mutane daga al’ummai masu yawa za su yi jerin gwano zuwa gidan bauta wa Jehobah da aka gama, za su sami salama da kwanciyar rai, za a kawar da tangarɗa masu girma da za su iya hana aikin Allah, za a cire mugunta, kuma mala’iku za su zama masu kula kuma su yi kāriya. (Zechariah 2:5, 11; 3:10; 4:7; 5: 6-11; 6: 1-8) Yanzu kun fahimci abin da ya sa irin wannan tabbaci na taimako daga Allah ya sa masu biyayya suka gyara salon rayuwarsu kuma suka mai da hankali su kammala aikin da ya sa Allah ya ’yantar da su.

17. Bisa ga alkawarin da Allah ya yi mana, me ya kamata mu tambayi kanmu?

17 Hakanan ma, sanin cewa bauta ta gaskiya za ta yi nasara ya kamata ya motsa mu mu yi aiki kuma mu yi tunani sosai game da gidan bauta na Jehobah. Ka tambayi kanka: ‘Idan na gaskata cewa yanzu ne lokacin da za a yi aikin wa’azin bisharar Mulki da almajirantarwa, shin muradina da salon rayuwana sun yi daidai da tabbacina kuwa? Ina ba da isashen lokaci kuwa wajen nazarin Kalmar annabci na Allah, ina sa ya zama damuwa na, ina magana game da ita da ’yan’uwa Kiristoci da kuma waɗanda na sadu da su?’

18. Me zai faru a nan gaba, kamar yadda Zechariah sura 14 ta ambata?

18 Zechariah ya yi maganar halaka Babila Babba, bayan haka kuma za a yi yaƙin Armageddon. Ya ce: “Za ya zama yini ɗaya, sananne ne ga Ubangiji; ba dare ba rana; amma da yamma za a yi haske.” Ranar Jehobah za ta yi duhu ga magabtansa a duniya! Amma za ta zama lokacin haske da tagomashi ga masu bauta wa Jehobah da aminci. Zechariah ya sake kwatanta yadda kowace halitta za ta yi shelar tsarkakar Jehobah a sabuwar duniya. Bauta ta gaskiya a haikali na ruhaniya na Allah za ta zama bauta kaɗai da ake yi a duniya. (Zechariah 14:7, 16-19) Wannan tabbaci ne na gaske! Za mu ga cikar abin da aka annabta kuma mu ga yadda aka ƙunita ikon mallakar Jehobah. Za ta zama rana ta musamman ga Jehobah!

Albarka na Dindindin

19, 20. Me ya sa kuke ganin cewa Zechariah 14:8, 9 tana da ban ƙarfafa?

19 Bayan wannan cikar ta ban mamaki, za a saka Shaiɗan da aljannunsa a yanayin rashin aiki. (Ru’ya ta Yohanna 20:1-3, 7) Sa’an nan za a sami albarka a lokacin Sarautar Kristi ta Shekara Dubu. Zechariah 14:8, 9 ta ce: “Za ya zama kuwa a ranan nan, ruwa mai-rai za ya fito Urushalima; rabi zuwa teku na gabas, rabi kuma zuwa wajen teku na yamma; ko da damana, ko da rani haka za ya yi. Ubangiji za ya zama sarki bisa dukan duniya; a cikin wannan rana Ubangiji ɗaya ne, sunansa kuma ɗaya ne.”

20 “Ruwan rai,” ko kuma “kogin ruwa na rai,” na wakiltar tanadin da Jehobah ya yi don rai, da zai gudano daga mazaunin Mulkin Almasihu. (Ru’ya ta Yohanna 22:1, 2) Taro mai girma cikin masu bauta wa Jehobah da suka tsira daga Armageddon za su amfana, za a sake su daga hukuncin mutuwa da Adamu ya jawo. Har ma waɗanda suka mutu za su amfana ta wajen tashin matattu. Wannan zai buɗe sabon sashe na sarautar Jehobah bisa dukan duniya. A dukan faɗin duniya mutane za su fahimci cewa Jehobah ne Mamallakin Sararin Samaniya kuma shi kaɗai ne za a bauta wa.

21. Menene ya kamata ya zama ƙudurinmu?

21 Domin dukan abubuwa da Haggai da Zechariah suka annabta da kuma waɗanda suka cika, muna da ƙarfafan dalili na ci gaba da yin aikin da Jehobah ya ce mu yi a farfajiya ta duniya a haikalinsa na ruhaniya. Kafin lokacin da bauta ta gaskiya za ta kasance cikin kamiltaccen yanayi, bari dukanmu mu yi ƙoƙari mu sa al’amuran Mulki ta zama na farko. Zechariah 8:9 ta aririce mu: “Bari hannuwanku su yi ƙarfi, ku da ku ke jin cikin waɗannan kwanaki zantattukan nan daga bakin annabawa.”

Ka Tuna?

• Wane kwatanci ne a dā ya sa littattafan Haggai da Zechariah suka dace da zamaninmu?

• Waɗanne darussa ne littafin Haggai da Zechariah suka koya mana game da abubuwan da suka fi muhimmanci?

• Me ya sa yin la’akari da Haggai da Zechariah ya ba mu tabbaci na nan gaba?

[Hoto a shafi na 13]

Haggai da Zechariah sun ƙarfafa Yahudawa su yi aiki da zuciya ɗaya domin su sami albarka

[Hotuna a shafi na 14]

Kana ‘gudu saboda gidanka’?

[Hoto a shafi na 15]

Jehobah ya yi alkawari kuma ya cika

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba