“Ina Tare Da Ku”
“Manzon Ubangiji . . . ya ce, Ina tare da ku, in ji Ubangiji.”—HAGGAI 1:13.
1. Waɗanne annabce-annabce ne Yesu ya kwatanta da zamaninmu?
MUNA zaune ne a lokaci mai muhimmanci a tarihi. Kamar yadda cikar annabci na Littafi Mai Tsarki ya nuna, muna zaune a “ranar Ubangiji” tun shekara ta 1914. (Ru’ya ta Yohanna 1:10) Wataƙila ka san wannan annabcin, ka ga yadda Yesu ya kwatanta “kwanakin Ɗan mutum” a cikin iko na Mulki da “kwanakin Nuhu” da kuma “kwanakin Lutu.” (Luka 17:26, 28) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa waɗannan annabce-annabce ne game da zamaninmu. Duk da haka, akwai wani kwatanci da ya kamata mu yi la’akari da shi.
2. Wane aiki ne Jehobah ya ba Haggai da Zechariah?
2 Bari mu yi la’akari da yanayin zamanin annabawa Ibraniyawa, Haggai da Zechariah. Wane saƙo ne da yake da amfani ga mutanen Jehobah a zamaninmu waɗannan amintattun annabawa biyu suka ba da? Haggai da Zechariah ‘manzannin Jehobah ne’ ga Yahudawa bayan da suka dawo daga zaman bauta a ƙasar Babila. An aike su ne su tabbatar wa Isra’ilawa cewa Allah na tare da su wajen sake gina haikalin. (Haggai 1:13; Zechariah 4:8, 9) Ko da yake littattafan da Haggai da Zechariah suka rubuta ba su da yawa, amma suna cikin “kowane Nassi [wanda] hurarre ne daga wurin Allah mai-amfani ne ga koyarwa, tsautawa, ga kwaɓewa, ga horo kuma da ke cikin adalci.”—2 Timothawus 3:16.
Ya Kamata su Shafe Mu
3, 4. Me ya sa ya kamata mu saurari saƙon Haggai da Zechariah?
3 Babu shakka, saƙonnin Haggai da Zechariah sun yi wa Isra’ilawa na zamaninsu amfani, kuma annabce-annabcensu sun cika a zamaninsu. Me ya sa ya kamata mu kasance da tabbacin cewa waɗannan littattafan biyu sun shafe mu a yau? Mun sami amsa a littafin Ibraniyawa 12:26-29. A cikin waɗannan ayoyi, manzo Bulus ya yi ƙaulin Haggai 2:6 wadda ta ce Allah yana “raurawadda sammai, da duniya.” Raurawar za ta “kaɓantadda kursiyin Mulkoki [kuma za ta] hallaka ƙarfin Mulkoki na al’ummai.”—Haggai 2:22.
4 Sa’ad da ya yi ƙaulin Haggai, Bulus ya faɗi abin da zai sami “mulkoki na al’ummai” ya kuma yi magana a kan Mulki mai girma da shafaffun Kiristoci za su karɓa. (Ibraniyawa 12:28) Yanzu kun fahimci cewa annabce-annabcen Haggai da Zechariah suna nuni ne ga nan gaba a lokacin da aka rubuta littafin Ibraniyawa a ƙarni na farko na zamaninmu. Har yanzu akwai raguwar shafaffun Kiristoci a duniya, waɗanda suka gaji Mulkin Almasihu tare da Yesu. Saboda haka, annabce-annabcen Haggai da Zechariah suna da muhimmanci a zamaninmu.
5, 6. Menene ya faru kafin annabcin Haggai da Zechariah?
5 Littafin Ezra ya ba da tarihin wasu abubuwan da suka faru kafin annabcin. Bayan da Yahudawa suka dawo daga zaman bauta a ƙasar Babila a shekara ta 537 K.Z., Gwamna Zarubabel da Babban Firist Joshuwa (ko kuma Jeshuwa) ne suka kula da harsashin sabon haikali da ake kafawa a shekara ta 536 K.Z. (Ezra 3:8-13; 5:1) Ko da yake wannan abin farin ciki ne, amma ba a daɗe ba, sai Yahudawan suka soma jin tsoro. Ezra 4:4 ta ce, maƙiya, wato “mutanen ƙasan suka kashe ƙarfin hannuwan mutanen Yahuda, suka tsoratadda su cikin gini.” Waɗannan maƙiyan, musamman Samariyawa, sun yi wa Yahudawa zargin ƙarya. Waɗannan ’yan hamayyar sun rinjayi sarkin Farisa ya tsayar da aikin gina haikalin.—Ezra 4:10-21.
6 Ƙwazon da Yahudawa suka nuna da farko a aikin gina haikalin ya ragu. Sai suka koma neman abin kansu. Bayan shekaru 16 da suka ƙafa harsashin haikalin, a shekara ta 520 K.Z., Jehobah ya aiki Haggai da Zechariah su motsa mutanen don su soma gina haikalin. (Haggai 1:1; Zechariah 1:1) Bayan da annabawan Allah suka motsa su kuma suka fahimci cewa Jehobah yana tare da su, Yahudawan sun soma aikin gina haikalin kuma sun kammala shi a shekara ta 515 K.Z.—Ezra 6:14, 15.
7. Wane yanayi ne a zamanin annabawa Haggai da Zechariah ya yi daidai da na zamaninmu?
7 Ka san muhimmancin waɗannan a gare mu? Muna da aikin wa’azin “bisharan Mulki.” (Matta 24:14) An nuna ƙwazo a wannan aikin bayan Yaƙin Duniya ta I. Kamar yadda aka saki Yahudawa na dā daga bauta a ƙasar Babila ta zahiri, haka ma aka sako mutanen Jehobah na zamani daga bauta a Babila Babba, wato, daular duniya ta addinin ƙarya. Shafaffu na Allah sun sa ƙwazo a yin wa’azi, koyarwa, da kuma yi wa mutane ja-gora zuwa bauta ta gaskiya. An sami ci gaba a wannan aikin a yau, wataƙila kai ma kana cikin masu yin wannan wa’azin. Yanzu ne ya kamata a yi wa’azi, saboda ƙarshen wannan mugun zamanin ya kusa! Dole ne mu ci gaba da wannan aikin da Allah ya ba mu har sai Jehobah ya sa hannu a harkokin ’yan Adam a ranar “ƙunci mai-girma.” (Matta 24:21) Wannan zai kawar da mugunta kuma ya sa bauta ta gaskiya ta cika dukan duniya.
8. Me ya sa ya kamata mu tabbata cewa Allah yana tare da mu a aikinmu na wa’azi?
8 Kamar yadda annabce-annabcen Haggai da Zechariah suka nuna, ya kamata mu kasance da tabbacin cewa Jehobah yana tare da mu kuma zai albarkace mu sa’ad da muke yin wannan aiki da zuciya ɗaya. Duk da ƙoƙarin da wasu suka yi don su hana bayin Allah yin wa’azi, babu gwamnatin da ta iya tsayar da aikin wa’azi. Ka yi la’akari da yadda Jehobah ya albarkaci aikin Mulki da ƙaruwa a shekarun da suka biyo bayan Yaƙin Duniya ta 1 har zuwa yau. Har yanzu, akwai ayyuka masu yawa da za a yi.
9. Wane yanayi ne na dā ya kamata mu lura da shi, kuma me ya sa?
9 Ta yaya abubuwan da muka koya daga Haggai da Zechariah suka ƙarfafa mu mu yi biyayya ga dokar Allah na yin wa’azi da koyarwa? Bari mu duba wasu darussa da za mu koya daga littattafan nan biyu na Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ka yi la’akari da wasu abubuwa game da aikin gina haikali da Yahudawan da suka komo ƙasarsu za su yi. Kamar yadda aka ambata, Yahudawa da suka koma Urushalima daga Babila ba su nace ga aikinsu na gina haikali ba. Bayan sun kafa harsashin, sai suka yi sanyi. Wani ra’ayi ne da bai dace ba ya taso a tsakanin su? Kuma me za mu koya daga wannan?
Kasancewa da Ra’ayin da ya Dace
10. Wane ra’ayi ne da bai dace ba Yahudawa suka nuna, kuma menene sakamakon haka?
10 Yahudawan da suka koma Urushalima suna cewa: “Lokacin zuwanmu bai ya yi ba.” (Haggai 1:2) Sa’ad da suka soma gina haikalin, kuma suka soma kafa harsashin a shekara ta 536 K.Z., Yahudawan ba sa cewa “lokacin zuwanmu ba ya yi ba.” Amma sai suka ƙyale hamayya daga gwamnati da kuma ƙasashen da suka kewaye su ya shafe su. Yahudawan suka soma kula da gidajensu da kuma rayuwarsu. Yin la’akari da bambanci da ke tsakanin gidajensu da aka yi wa ado da katakai masu kyau da kuma haikalin da ke neman gyara, Jehobah ya tambaye su: “Ko lokaci ya yi da ku da kanku za ku zauna cikin sorayenku, wannan gida fa kango ne?”—Haggai 1:4.
11. Me ya sa Jehobah ya gargaɗi Yahudawa na zamanin Haggai?
11 Yahudawan sun canza ra’ayinsu na yin aikin da ya fi muhimmanci. Maimakon su sa nufin Jehobah na sake gina haikali ya zama na farko, mutanen Allah sun mai da hankali a kan rayuwarsu da wurin gidajensu. Kuma sun yi watsi da aikin haikalin da ake yi wa Allah bauta. Kalmar Jehobah a Haggai 1:5 ta ƙarfafa Yahudawan su ‘kula da al’amuransu.’ Jehobah yana gaya musu ne cewa su yi bimbini bisa abin da suke yi, kuma su yi la’akari da yadda ƙin mai da aikin gina haikali abu na farko a rayuwansu yake shafansu.
12, 13. Ta yaya Haggai 1:6 ta kwatanta yanayin da Yahudawa suke ciki, kuma menene ayar take nufi?
12 Kamar yadda kuka sani, canza makasudin da Yahudawa suka yi ya shafe su. Ku yi la’akari da abin da Allah ya ce a cikin littafin Haggai 1:6: “Kun yi shuka dayawa, kun yi girbi kaɗan; kun ci, ba ku ƙoshi ba; kun sha, ba ku ƙoshi da sha ba; kun sa tufafi, amma ba wanda ya ji ɗumi; wanda yana samun albashi yana samu domin ya sa cikin jaka mai-kofaye.”
13 Ko da yake Yahudawa suna cikin ƙasar da Allah ya yi masu alkawarinta, duk da haka, ƙasar ba ta ba da amfani yadda suke so. Jehobah ya hana su albarkarsa, kamar yadda ya gargaɗe su. (Kubawar Shari’a 28:38-48) Ba tare da taimakonsa ba, Yahudawa suka yi shuka amma sun girbe kaɗan wanda ba zai ishe su ci ba. Saboda sun yi rashin albarkarsa, Yahudawa sun kasa samun tufafi masu sa ɗumi. Kuma kuɗin da suke samu kuwa, kamar suna zubawa ne a cikin hujajjen aljihu, domin kuɗin bai yi musu amfanin komi ba. Menene ma’anar wannan furcin: “Kun sha ba ku ƙoshi da sha ba”? Ba zai yi daidai a ce yin maye ne ke kawo albarkar Allah ba; saboda Allah ya haramta yin maye. (1 Samuila 25:36; Misalai 23:29-35) Akasin haka, bayanin ya nuna cewa Yahudawa sun yi rashin albarkar Allah. Duka ruwan inabin da za su yi ba zai ishe su yin maye ba. Haggai 1:6 ta ce: “Kun sha, ba ku ƙoshi da sha ba.”
14, 15. Wane darasi ne muka koya a Haggai 1:6?
14 Darasin da ya kamata mu koya daga waɗannan abubuwa ba wai na yadda za mu gina ko yi wa gidajenmu kwalliya ba ne. Kafin su tafi zaman bauta a Babila, annabi Amos ya tsauta wa masu arziki a Isra’ila game da “gidaje na hauri” da kuma yadda suke “kwantawa a bisa gadajen hauren giwa.” (Amos 3:15; 6:4) Gidajensu da kuma kayan ɗaki masu kyau ba su daɗe ba. Maƙiyansu da suka ci su a yaƙi sun kwashe waɗannan abubuwa. Duk da haka, bayan shekaru 70 na zaman bauta a Babila, mutanen Allah da yawa ba su koyi darasi daga abin da ya faru a dā ba. Za mu iya koya daga abin da ya faru? Zai yi kyau idan muka tambayi kanmu: ‘Wane irin ƙwazo ne nake nunawa domin gyara gidana? Ko kuma wane irin shiri ne nake yi domin ƙaro ilimi, wanda zai ɗauki shekaru masu yawa, kuma ya sa in kasa cika wasu fasaloli na ruhaniya masu muhimmanci?’—Luka 12:20, 21; 1 Timothawus 6:17-19.
15 Abin da muka karanta a Haggai 1:6 ya kamata ya sa mu yi tunanin albarkar Allah a rayuwarmu. Yahudawa na dā sun yi rashin albarkar Allah, kuma hakan ya shafe su sosai. Idan muna da abin duniya da yawa ko kaɗan, amma ba mu da albarkar Allah, hakan zai shafi dangantakarmu da Allah. (Matta 25:34-40; 2 Korinthiyawa 9:8-12) Ta yaya za mu iya samun wannan albarkar?
Jehobah Yana Taimako ta Wurin Ruhunsa
16-18. A ma’anarta na dā, mecece Zechariah 4:6 take nufi?
16 An hure Zechariah abokin annabi Haggai ya nanata yadda Jehobah ya ƙarfafa kuma ya albarkaci waɗanda suka keɓe kansu a dā. Wannan ya nuna yadda zai albarkace ka. Mun karanta: “Ba ta wurin ƙarfi ba, ba kuwa ta wurin iko ba, amma ta wurin ruhuna, in ji Ubangiji mai-runduna.” (Zechariah 4:6) Ka sha jin ana karanta wannan ayar, amma me yake nufi ga Yahudawa na kwanakin Haggai da Zechariah, kuma me yake nufi a gare ka?
17 Ka tuna cewa hurarriyar kalmomin Haggai da Zechariah suna da muhimmanci a dā. Abin da annabawa biyun nan suka ambata ya ƙarfafa amintattun Yahudawa. Haggai ya fara annabci a wata ta shida a shekara ta 520 K.Z. Zechariah ya soma annabcinsa a wata na takwas a wannan shekarar. (Zechariah 1:1) Kamar yadda ka gani a Haggai 2:18, an soma gina harsashi na haikali da ƙwazo a wata na tara. Shi ya sa Yahudawa suka sami ƙarfi, suka yi biyayya ga Allah da tabbacin cewa zai taimake su. Kalmar da take Zechariah 4:6 ta nuna mana yadda Allah ya taimake su.
18 Sa’ad da Yahudawa suka koma ƙasarsu a shekara ta 537 K.Z., ba su da mayaƙa. Duk da haka, Jehobah ya kāre su sa’ad da suka bar Babila. Bugu da ƙari, ruhunsa yana tare da su sa’ad da suka fara aiki a haikali bayan da suka dawo ƙasarsu. Idan suka soma aikin kuma da zuciya ɗaya, Jehobah zai taimake su ta wurin ruhunsa.
19. Wane irin tasiri ne ruhun Allah ya kawar?
19 Ta wurin wahayi takwas, Jehobah ya tabbatar wa Zechariah cewa zai kula da mutanensa, har su gama gina haikalin. Wahayi na huɗu da aka ambata a sura 3, ya nuna cewa Shaiɗan ne yake ƙoƙarin ya hana Yahudawa su kammala ginin haikali. (Zechariah 3:1) Babu shakka, Shaiɗan ba zai yi murnan ganin Babban Firist Joshuwa yana yin hadaya a madadin mutanen Allah a sabon haikalin ba. Ko da yake Iblis ya hana Yahudawa gina haikali, ruhun Jehobah zai kawar da matsalolin da suke fuskanta ya kuma ƙarfafa su su ci gaba da gina haikali har sai sun kammala ginin.
20. Ta yaya ne ruhu mai tsarki ya taimaki Yahudawa su cika nufin Allah?
20 Yadda ma’aikatan gwamnatin suka sa aka hana aikin gina haikalin ya sa hamayyar ta zama kamar babban dutsen da ba za a iya kawar wa ba. Duk da haka, Jehobah ya yi alkawari cewa za a cire ‘dutsen’ kuma zai zama “bai ɗaya.” (Zechariah 4:7) Kuma hakan ya faru! Sarki Darius na I ya yi bincike kuma ya samu wasiƙa inda Cyrus ya ba Yahudawa izinin komawa ƙasarsu domin su sake gina haikali. Darius ya ɗaga hanin ya kuma ba da izini cewa a cire kuɗi daga ma’aji na sarauta a ba wa Yahudawa domin biyan bukatar aikin gina haikalin. Wannan juyi ne mai ban mamaki! Ruhun Allah ya taimaka kuwa? Hakika, muna da wannan tabbacin. An kammala gina haikalin a shekara ta 515 K.Z., a shekara ta shida ta sarautar Darius na ɗaya.—Ezra 6:1, 15.
21. (a) A zamanin dā, ta yaya ne Allah ya “raurawadda da dukan dangogi,” kuma ta yaya “muradin dukan dangogi” suka fito? (b) Menene cikarsa ta zamaninmu?
21 A Haggai 2:5, annabin ya tuna wa Yahudawa alkawarin da Allah ya yi da su a Dutsen Sinai sa’ad da “dukan dutse kuma ya yi rawa ƙwarai.” (Fitowa 19:18) A zamanin Haggai da Zechariah, Jehobah zai sake yin wata raurawa kamar yadda aka kwatanta a furci na alama a ayoyi ta 6 da 7. Ko da yake harkoki a Daular Farisa sun canja, za a ci gaba da aikin haikali har zuwa ƙarshe. Waɗanda ba Yahudawa ba ne, watau “muradin dukan dangogi,” za su soma ɗaukaka Allah tare da Yahudawa a haikali. A wata hanya ta musamman a zamaninmu, Allah ya “raurawadda dukan dangogi” ta hanyar wa’azi, kuma “muradin dukan dangogi” sun fito su bauta wa Allah tare da shafaffun Kiristoci da suka rage. Hakika, shafaffu tare da waɗansu tumaki a yanzu suna cika gidan Jehobah da ɗaukaka. Waɗannan masu bauta ta gaskiya suna jiran ranar da Jehobah zai “raurawadda sammai da duniya” a wata hanya. Hakan zai faru ne domin a hamɓarar kuma hallakar da ƙarfin mulkoki na al’ummai.—Haggai 2:22.
22. Ta yaya ne aka ‘raurawar da’ al’ummai, da wane sakamako, kuma menene zai faru a nan gaba?
22 An tuna mana matsalolin da suka faru a wurare dabam dabam da suke nufin “sammai da duniya da teku da ƙasa.” Dalili ɗaya shi ne an jefo Shaiɗan Iblis da aljanunsa zuwa duniya. (Ru’ya ta Yohanna 12:7-12) Bugu da ƙari, wa’azin da shafaffun Kiristoci suke ja-gorarsa na raurawar da duniya a wannan zamanin. (Ru’ya ta Yohanna 11:18) Duk da haka, “taro mai-girma” na muradin dukan dangogi sun haɗu da Isra’ila ta ruhaniya ta wurin bauta wa Jehobah. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10) Taro mai girma suna aiki tare da shafaffun Kiristoci a wa’azin bishara cewa ba da daɗewa ba Jehobah zai raurawar da al’ummai a Armageddon. Wannan zai sa bauta ta gaskiya ta zama kamiltacciya a dukan duniya.
Ka Tuna?
• Yaushe ne kuma a cikin wane irin yanayi ne Haggai da Zechariah suka yi hidima?
• Ta yaya za ka iya yin amfani da saƙon da Haggai da kuma Zechariah suka sanar?
• Me ya sa Zechariah 4:6 take da ban ƙarfafa?
[Hotuna a shafi na 7]
Abin da Haggai da Zechariah suka rubuta ya tabbatar mana cewa Allah zai taimaka mana
[Hoto a shafi na 10]
“Ko lokaci ya yi da ku da kanku za ku zauna cikin sorayenku, wannan gida fa kango ne?”
[Hoto a shafi na 11]
Mutanen Jehobah suna cikin masu neman “muradin dukan dangogi”