Maganar Jehobah Rayayya Ce
Darussa Daga Littattafan Haggai da Zakariya
A SHEKARA ta 520 K.Z. An gina harsashin haikalin Jehobah a Urushalima bayan shekara goma sha shida da dawowar Yahudawa daga zaman bauta a Babila. Duk da haka ba a gama gina haikalin ba kuma an hana aikin ginin. Jehobah ya aiki annabi Haggai kuma bayan watanni biyu ya aika annabi Zakariya ya faɗi kalmarsa.
Haggai da Zakariya suna da manufa ɗaya: Su sa mutanen su soma aiki na sake gina haikalin. Ƙoƙarin waɗannan annabawan ya yi nasara, kuma aka kammala haikalin a shekara biyar. An rubuta abin da Haggai da Zakariya suka annabta a littattafan Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da sunansu. An kammala littafin Haggai a shekara ta 520 K.Z., kuma Zakariya a shekara ta 518 K.Z. Kamar waɗannan annabawa, mu ma muna da aikin da Allah ya ba mu wanda dole ne mu gama shi kafin ƙarshen wannan zamanin. Aikin wa’azin Mulki ne da almajirantarwa. Bari mu ga yadda littattafan Haggai da Zakariya suka ƙarfafa mu.
KU “LURA DA AL’AMURANKU”
(Haggai 1:1–2:23)
Haggai ya isar da saƙonni huɗu masu motsawa cikin kwanaki 112. Na farkon shi ne: “Lura da al’amuranku. Hau wurin duwatsu, ku ɗauko ice, ku gina gidana; ni ma in ji daɗi da shi, in ɗaukaka, in ji Ubangiji.” (Haggai 1:7, 8) Mutanen sun saurari saƙon. Saƙo na biyu yana ɗauke ne da wannan alkawarin: “[Ni Jehobah] zan cika wannan gida da ɗaukaka.”—Haggai 2:7.
Bisa ga saƙo na uku, yadda suka yi banza da sake gina haikalin ya sa ‘mutanen da aikin hannuwansu’ su zama abubuwa marar tsabta a gaban Jehobah. Amma daga ranan da aikin sake ginin ya soma Jehobah zai “albarkace” su. In ji saƙo na huɗu, Jehobah zai “hallaka ƙarfin mulkoki na al’ummai” kuma ya mai da Gwamna Zerubbabel “kamar hatimi.”—Haggai 2:14, 19, 22, 23.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:6, 7, 21, 22—Wanene ko kuma menene ya sa ake raurawa, da wane sakamako? Jehobah yana ‘raurawarda dukan dangogi’ ta wajen wa’azin saƙon Mulki a dukan duniya. Aikin wa’azi yana sa a kawo “muradin dukan dangogi” zuwa gidan Jehobah, da haka ana cika ta da ɗaukaka. Da shigewar lokaci “Ubangiji mai-runduna” zai raurawar da “sammai, da duniya, da teku, da sandararriyar ƙasa,” wanda hakan zai halakar da wannan mugun zamani.—Ibraniyawa 12:26, 27.
2:9—Ta waɗanne hanyoyi ne “ɗaukaka ta baya ta wannan gida za ta fi ta farin”? Hakan zai kasance ta hanyoyi uku: shekarun da haikalin ya yi, da wanda ya koyar a wurin, da kuma waɗanda suka je wajen don su bauta wa Jehobah. Ko da yake haikali mai ɗaukaka na Sulemanu ya yi shekaru 420, wato daga shekara ta 1027 K.Z. zuwa shekara ta 607 K.Z., an yi amfani da ‘gida na baya’ fiye da shekaru 580, wato, daga lokacin da aka kammala ginin a shekara ta 515 K.Z., zuwa lokacin da aka rushe shi a shekara ta 70 A.Z. Ƙari ga haka, Almasihu, Yesu Kristi ya koyar a ‘gida na baya’ kuma mutane da yawa sun shiga ciki fiye da gida “ta farin” domin su bauta wa Allah.—Ayukan Manzanni 2:1-11.
Darussa Dominmu:
1:2-4. Bai kamata hamayya ga aikinmu na wa’azi ya sa mu canja zaɓin da muka yi na “fara biɗan mulkin” zuwa biɗar abubuwan da muke so.—Matta 6:33.
1:5, 7. Yana da kyau mu ‘lura da al’amuranmu’ kuma mu yi tunanin yadda abin da muke yi da rayuwarmu ya shafi dangantakarmu da Allah.
1:6, 9-11; 2:14-17. Yahudawa na zamanin Haggai suna aiki tuƙuru wajen biɗar nasu abubuwa amma ba sa more amfanin aikinsu. Sun yi watsi da haikalin saboda haka ba su sami albarkar Allah ba. Ya kamata mu sa biɗar abubuwa na ruhaniya farko a rayuwarmu kuma mu bauta wa Allah da dukan zuciyarmu, mu riƙa tuna cewa “albarkar Ubangiji ta kan kawo wadata” ko muna da abin duniya kaɗan ko mai yawa.—Misalai 10:22.
2:15, 18. Jehobah ya gaya wa Yahudawa su lura da al’amuransu tun daga wannan ranar, ba a kan watsi da suka yi da aikin ba a dā amma a kan sake ginin. Ya kamata mu ma mu yi ƙoƙari mu mai da hankali ga bautar da muke yi ga Allah.
“BA TA WURIN IKO BA, AMMA TA WURIN RUHUNA”
(Zechariah 1:1–14:21)
Zakariya ya soma aikinsa na annabci ta wajen yin kira ga Yahudawa su ‘koma wurin Jehobah.’ (Zechariah 1:3) Wahayi takwas na gaba sun tabbatar da cewa Allah yana goyon bayan aikin sake gina haikalin. (Ka duba akwatin nan “Wahayi Takwas da Zakariya ya Gani Cikin Alama.”) Za a kammala aikin gini “ba ta wurin ƙarfi ba, ba kuwa ta wurin iko ba, amma ta wurin ruhun [Jehobah].” (Zechariah 4:6) Mutumin da ake kira Zuriya “shi kuwa za ya gina haikalin Ubangiji” kuma “ya zama priest a bisa kursiyinsa.”—Zechariah 6:12, 13.
Mutanen Bethel sun aika wakilai su tambayi firistoci game da yin azumi don tuna da halakar Urushalima. Jehobah ya gaya wa Zakariya cewa za a canja makokin da aka yi a lokacin azumi guda huɗu don tuna bala’in da ya faɗa wa Urushalima zuwa “farinciki da murna . . . da bukukuwa masu-daɗi.” (Zechariah 7:2; 8:19) Shela biyu da aka yi bayan hakan ya haɗa da hukunci a kan al’ummai da annabawan ƙarya, annabce-annabce game da Almasihu da kuma saƙon dawowar mutanen Allah.—Zechariah 9:1; 12:1.
Tambayoyin Nassi da Aka Amsa:
2:1—Me ya sa wani mutum yake gwada Urushalima da igiya? Wataƙila wannan yana nuna cewa za a gina bangon da zai kāre birnin. Mala’ikan ya gaya wa mutumin cewa za a faɗaɗa Urushalima kuma Jehobah zai kāre ta.—Zechariah 2:3-5.
6:11-13—Ƙambin da aka ɗaura a kan Joshua Babban Firist yana nufin cewa shi sarki da firist ne? A’a, Joshua bai fito daga zuriyar Dauda ba. Amma ƙambin da aka ɗaura masa yana nuni ne ga Almasihu a annabce. (Ibraniyawa 6:20) Annabci game da “Zuriya” ya cika a kan Yesu Kristi wanda Sarki ne da kuma Firist a sama. (Irmiya 23:5) Kamar yadda Joshua ne babban firist ga Yahudawan da suka dawo a lokacin sake gina haikali, haka ma Yesu ne Babban Firist a bauta ta gaskiya a haikali na ruhaniya na Jehobah.
8:1-23—A waɗanne lokaci ne shela goma da aka ambata a waɗannan ayoyin suka cika? Furcin nan “hakanan Ubangiji mai-runduna ya ce” ya gabaci dukan shelar da aka yi kuma alkawari ne da Allah ya yi wa mutanensa na zaman lafiya. Wasu cikin waɗannan shelar sun cika a ƙarni na shida K.Z., amma wataƙila dukansu sun riga sun cika tun shekara ta 1919 A.Z., ko kuma suna cika yanzu.a
8:3—Me ya sa aka kira Urushalima “birni na gaskiya”? Urushalima “birni mawulakanciya ce” kafin a halaka ta a shekara ta 607 K.Z., kuma lalatattun annabawa da firistoci da kuma mutane marasa bangaskiya ne suke zaune a cikinta. (Zephaniah 3:1; Irmiya 6:13; 7:29-34) Da aka sake gina haikalin kuma mutanen suka koma bauta wa Jehobah, an yi bauta ta gaskiya a wajen kuma hakan ya sa aka kira Urushalima “birni na gaskiya.”
11:7-14—Mecece sandar da ake kira “Alheri” da kuma wanda ake kira “Maɗaura” da Zakariya ya raba take nufi? An kwatanta Zakariya kamar wanda aka aika ya “yi kiwon garken yanka,” wato, mutane masu kama da tumaki da shugabanninsu suke cutan su. A matsayinsa na makiyayi, Zakariya yana wakiltar Yesu Kristi, wanda aka aika zuwa wajen mutanen da Allah ya yi alkawari da su amma suka ƙi shi. ‘Alherin’ da aka raba ya nuna cewa Allah zai karya Dokar alkawari da ya yi da Yahudawa kuma zai daina yi musu alheri. ‘Maɗaurin’ da aka raba yana nufin ɓata gamin ’yan’uwantaka na bauta wa Allah da ke tsakanin Yahuda da Isra’ila.
12:11—Menene “makoki na Hadadrimmon cikin kwarin Megiddon”? An kashe Sarki Josiah na Yahuda a yaƙin da ya yi da Fir’auna na Neko na Masar a “cikin kwarin Megiddon,” kuma an yi shekaru da yawa ana ‘makokinsa.’ (2 Labarbaru 35:25) Saboda haka “makoki na Hadadrimmon” wataƙila yana nufin makokin mutuwar Josiah.
Darussa Dominmu:
1:2-6; 7:11-14. Jehobah yana farin ciki kuma yana soma dangantaka da waɗanda suka tuba da aka yi musu horo kuma suka koma wurinsa ta wajen bauta masa da dukan zuciyarsu. A wani ɓangare kuma, ba ya taimakon waɗanda suka ci gaba da ‘taurare zuciyarsu, suka toshe kunnuwansu domin kada su ji’ saƙonsa.
4:6, 7. Ruhun Jehobah ya sha kan kowane tangarɗa da take so ta hana kammala aikin sake gina haikalin. Za mu iya sha kan dukan matsalolin da muka fuskanta a hidimarmu ga Allah ta wajen ba da gaskiya ga Jehobah.—Matta 17:20.
4:10. Da taimakon Jehobah, Zerubbabel da mutanensa sun kammala haikalin bisa ga mizanai mai girma na Allah. Yin rayuwar da ta jitu da nufin Jehobah ba shi da wuya ga ’yan adam ajizai.
7:8-10; 8:16, 17. Don mu sami alherin Jehobah dole ne mu kasance masu adalci, mu nuna ƙauna ta alheri, mu nuna jin ƙai kuma mu riƙa faɗa wa juna gaskiya.
8:9-13. Jehobah zai albarkace mu idan ‘hannuwanmu suka yi ƙarfi’ wajen yin aikin da ya ba mu. Waɗannan albarkatai sun ƙunshi salama, kwanciyar hankali da kuma samun ci gaba a ruhaniya.
12:6. Ya kamata waɗanda suke shugabanci tsakanin mutanen Jehobah su zama “kamar cukwimar wuta,” wato, su zama masu himma sosai.
13:3. Ya kamata mu kasance da aminci ga Allah da ƙungiyarsa fiye da kowane mutum ko idan mu abokai ne na kud da kud.
13:8, 9. Waɗannan ’yan ridda da Jehobah ya ƙi suna da yawa, wato kashi biyu cikin uku na mutanen ƙasar. Kashi na ukun ne kawai aka yi wa gyara kamar da wuta. A zamaninmu Jehobah ya riga ya ƙi Kiristendam wadda ita ce ta fi yawa tsakanin waɗanda suke da’awar su Kiristoci ne. Mutane kaɗan ne kawai, wato, shafaffun Kiristoci suke ‘kira bisa sunan Jehobah’ kuma suka ba da kansu ga gyara da aka yi musu. Su da ’yan’uwansu masu bi Shaidun Jehobah ne na gaskiya.
Mu Nuna Ƙwazo Sosai
Ta yaya ne abin da Haggai da Zakariya suka yi shelarsa ya shafe mu a yau? Sa’ad da muka yi tunani a kan yadda saƙonsu ya motsa Yahudawa su mai da hankali ga aikin sake gina haikali, wannan zai motsa mu mu kasance da ƙwazo wajen yin wa’azin Mulki da kuma aikin almajirantarwa.
Zakariya ya annabta cewa Almasihu zai zo yana “haye a kan jaki,” za a ci amanarsa don “azurfa talatin,” za a buge shi kuma “tumaki kuwa za su watse.” (Zechariah 9:9; 11:12; 13:7) Yin bimbini a kan cikar waɗannan annabce-annabcen Zakariya game da Almasihu zai shafi bangaskiyarmu sosai! (Matta 21:1-9; 26:31, 56; 27:3-10) Zai ƙarfafa tabbacinmu ga Kalmar Jehobah da kuma abubuwa da ya yi tanadinsu don mu sami ceto.—Ibraniyawa 4:12.
[Hasiya]
a Ka duba Hasumiyar Tsaro na 1 ga Janairu, 1996, shafofi na 17-30.
[Akwati a shafi na 19]
WAHAYI TAKWAS DA ZAKARIYA YA GANI CIKIN ALAMA
1:8-17: Sun ba da tabbaci cewa za a kammala haikalin kuma sun nuna cewa za a yi wa Urushalima da sauran biranen da ke Yahuda albarka.
1:18-21: Wannan ya yi alkawari cewa za a halaka ‘ƙahoni huɗu da suka watsa Yahuda,’ wato, dukan gwamnatocin da suke hamayya da bautar Jehobah.
2:1-13: Wannan ya nuna cewa za a faɗaɗa Urushalima kuma cewa Jehobah zai zama “bangon wuta gareta kewaye da ita,” wato, zai kāre ta.
3:1-10: Wannan ya nuna cewa Shaiɗan yana cikin waɗanda suka yi hamayya da aikin ginin da kuma cewa an ceci Joshua Babban Firist kuma an tsarkake shi.
4:1-14: Wannan ya ba da tabbaci cewa za a kawar da manyan tangarɗa kuma Gwamna Zerubbabel zai kammala gina haikalin.
5:1-4: A nan an hukunta masu aika laifi da ba a yi musu horo ba.
5:5-11: Wannan ya annabta ƙarshen mugunta.
6:1-8: A nan an yi alkawarin samun kula da kāriya na mala’ika.
[Hoto a shafi na 16]
Menene manufar saƙon Haggai da Zakariya?
[Hoto a shafi na 18]
Ta yaya ne waɗanda suke shugabanci suke “kamar cukwimar wuta”?