Ka Ji Tsoron Jehovah Ka Kiyaye Dokokinsa
“Ji tsoron Allah, ka kiyaye dokokinsa; gama wannan kaɗai ne wajibin mutum.”—MAI-WA’AZI 12:13.
1, 2. (a) Ta yaya tsoro yake kāre mu a zahiri? (b) Me ya sa iyaye masu hikima suna ƙoƙarin su saka tsoro mai kyau a cikin yaransu?
“KAMAR yadda gaba gaɗi yake sa rai a haɗari, tsoro yana kāre shi,” in ji Leonardo da Vinci. Gaba tsaye, yana rufe idanun mutum ga haɗari, amma kuma tsoro yana tunasar masa ya mai da hankali. Alal misali, idan muka je bakin kwari, kuma ga yadda za mu faɗi ƙasa da zurfi, yawancinmu ba magana muna ja baya. Hakanan, tsoro mai kyau ba kawai yana ɗaukaka dangantaka mai kyau da Allah ba, kamar yadda muka koya daga talifi da ya gabata, amma kuma yana taimakawa wajen kāre mu daga rauni.
2 Amma, dole ne a koyi tsoron haɗarurruka na zamani. Tun da yara ba su san haɗarin wutar lantarki ba ko kuma hanyoyin mota a cikin gari, ba zai yi wuya ba za su yi haɗari mai tsanani.a Iyaye masu hikima za su yi ƙoƙari su saka wannan tsoron a cikin yaransu, suna yi musu gargaɗi a kai a kai game da waɗannan haɗarurruka. Iyaye sun sani cewa wannan tsoron zai kāre rayukan yaransu.
3. Me ya sa kuma ta yaya Jehovah ya yi mana gargaɗi game da haɗari na ruhaniya?
3 Haka ma Jehovah yake damu da lafiyarmu. Tun da Uba ne mai ƙauna, yana koyar da mu ta Kalmarsa da ƙungiyarsa mu amfani kanmu. (Ishaya 48:17) Ɓangaren wannan koyarwa na Allah ya ƙunshi gargaɗi ‘a kai a kai’ game da haɗari na ruhaniya saboda mu koyi tsoron irin wannan haɗarin. (2 Labarbaru 36:15; 2 Bitrus 3:1) A cikin dukan tarihi da an guje wa bala’i da yawa na ruhaniya kuma da an kauce wa yawancin wahaloli, ‘da a ce mutane sun koyar da zukatansu su tsoraci Allah kuma su kiyaye dokokinsa.’ (Kubawar Shari’a 5:29) A waɗannan “miyagun zamanu,” ta yaya za mu koyar da zuciyarmu ta ji tsoron Allah domin ta guje wa haɗari na ruhaniya?—2 Timothawus 3:1.
Ka Guje wa Mugunta
4. (a) Wace ƙiyayya Kirista ya kamata ya koya? (b) Yaya Jehovah yake ji game da halin zunubi? (Duba hasiya.)
4 Littafi Mai Tsarki ya yi bayani cewa “tsoron Ubangiji ƙin mugunta ne.” (Misalai 8:13) Ƙamus na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta wannan ƙiyayya da cewa, “hali ne ga mutane ko abubuwa da yake adawa da su, da ake ƙyama, ake raina, wanda mutum ba ya so ya zo kusa da shi ko kuma a ce nasa ne.” Saboda haka, tsoro na ibada ya haɗa da ƙyamar dukan abin da yake mugu a idanun Jehovah.b (Zabura 97:10) Yana motsa mu mu guje wa mugunta, kamar yadda za mu ja baya daga bakin kwari sa’ad da tsoro ya yi mana gargaɗi. “Ta wurin tsoron Ubangiji kuma mutane su kan rabu da mugunta,” in ji Littafi Mai Tsarki.—Misalai 16:6.
5. (a) Ta yaya za mu ƙarfafa tsoronmu na ibada da kuma ƙiyayyarmu ga abin da ke mugu? (b) Menene tarihin al’ummar Isra’ila ya koya mana game da wannan?
5 Za mu iya ƙarfafa tsoronmu da kuma ƙiyayya ga abin da ke mugu ta wajen bincika mummunan sakamako da babu makawa da zunubi yake kawowa. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa za mu girbe abin da muka shuka—ko mun yi shuki bisa ga jiki ko kuma bisa ga ruhu. (Galatiyawa 6:7, 8) Domin wannan Allah ya ba da wannan kwatanci sarai na sakamako mara makawa na ƙin dokokinsa da kuma yasar da bauta ta gaskiya. Idan ba da kāriyar Allah ba, ƙaramar al’umma mara ƙarfi na Isra’ila za ta kasance a cikin hannun miyagun maƙwabta kuma masu ƙarfi. (Kubawar Shari’a 28:15, 45-48) Sakamako na bala’i na rashin biyayya na Isra’ila yana rubuce dalla-dalla a cikin Littafi Mai Tsarki “domin gargaɗi” saboda mu koyi darasi kuma mu koyi tsoro irin na ibada.—1 Korinthiyawa 10:11.
6. Waɗanne ne wasu misalai na Nassi da za mu bincika domin mu koya tsoro irin na ibada? (Duba hasiya.)
6 Banda abin da ya sami al’ummar Isra’ila gabaki ɗayanta, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da tarihi na rayuwa na wasu waɗanda kishi, lalata, kwaɗayi, da kuma fahariya suka sha musu kai.c Wasu cikin waɗannan mutane sun bauta wa Jehovah na shekaru da yawa, amma a wani lokaci ɗaya mai muhimmanci a rayuwarsu, tsoron Allahnsu ba shi da ƙarfi sosai, kuma sun girbe bala’i. Yin bimbini bisa irin wannan misalai zai iya ƙarfafa aniyarmu kada mu yi irin wannan kuskure. Zai zama abin baƙin ciki idan muka jira har sai mun fuskanci bala’i kafin mu bi shawarar Allah! Akasin abin da mutane da yawa suka yarda da shi, abin da muka fuskanta a rayuwa—musamman daga ƙwaɗayi—ba ƙwararren malami ba ne.—Zabura 19:7.
7. Waye Jehovah yake gayyata cikin tantinsa na alama?
7 Wani dalili mai kyau na koya tsoro irin na ibada shi ne muradinmu mu kāre dangantakarmu da Allah. Muna tsoron mu ɓata wa Jehovah rai domin muna daraja abokantaka da shi. Waye Jehovah yake ɗauka aboki, wanda zai gayyata cikin tantinsa na alama? Sai dai ‘wanda yake tafiya babu aibi kuma yana aikin adalci.’ (Zabura 15:1, 2) Idan mun daraja wannan dangantaka ta gata da Mahaliccinmu, za mu mai da hankali mu yi tafiya babu aibi a gabansa.
8. Ta yaya wasu Isra’ilawa a zamanin Malachi suka yi banza da abokantaka na Allah?
8 Abin baƙin ciki, wasu Isra’ilawa a zamanin Malachi sun yi banza da abokanta da Allah. Maimakon su ji tsoronsa kuma su daraja shi, suna miƙa dabbobi da marasa lafiya ne guragu bisa bagadinsa. Rashin tsoro irin na ibadarsu ya bayyana kuma a halinsu game da aure. Domin su auri ’yammata ƙanana, suna sake matansu na ƙuruciya bisa ƙananan dalilai. Malachi ya gaya musu cewa Jehovah yana ‘ƙyamar kisan aure’ kuma cewa halinsu na wulakanci ya ware su daga Allahnsu. Ta yaya Allah zai ɗauki hadayarsu da albarka sa’ad da bagadinsa a alamce yana cike da hawaye—hawayen baƙin ciki na matan da aka yasar da su? Irin wannan taka mizanansa a fili ya motsa Jehovah ya yi tambaya: ‘Ina tsorona da kuke ji?’—Malachi 1:6-8; 2:13-16.
9, 10. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja abokantaka da Jehovah?
9 A yau ma, haka Jehovah yake ganin baƙin cikin mata da yara da yawa marasa laifi waɗanda malalatan maza kuma ubanni masu son kai suka yasar da su har ma mata ko iyaye. Hakika yana ɓata masa rai. Abokin Allah zai ɗauki al’amura yadda Allah yake ɗaukansu kuma zai yi aiki tuƙuru domin ya ƙarfafa aurensa, kuma ya guji tunani irin na duniya da bai ɗauki aure kome ba, da kuma “guje ma fasikanci.”—1 Korinthiyawa 6:18.
10 A aure da kuma wasu ɓangarorin rayuwa, ƙyamar abin da yake mugu a gaban Jehovah, tare da soyayya sosai na abokantakarsa, zai kawo tagomashi da kuma yardar Jehovah. Manzo Bitrus ya ce: “Hakika na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (Ayukan Manzanni 10:34, 35) Muna da misalai da yawa na Nassi yadda tsoro irin na ibada ya motsa mutane suka yi abin da yake nagari a yanayi masu wuya.
Mutane Uku da Suka Ji Tsoron Allah
11. A cikin wane yanayi ne aka ce Ibrahim “mai-tsoron Allah” ne?
11 Akwai mutumin da a cikin Littafi Mai Tsarki Jehovah da kansa ya ce da shi abokinsa—Ibrahim uban iyali. (Ishaya 41:8) An gwada tsoro na ibada na Ibrahim sa’ad da aka ce ya miƙa ɗan tilonsa Ishaƙu, domin hadaya, wanda ta wajensa Allah zai cika alkawarinsa ga Ibrahim cewa zuriyar Ibrahim za ta zama babbar al’umma. (Farawa 12:2, 3; 17:19) Shin “abokin Allah” zai yi nasara a wannan gwaji kuwa? (Yaƙub 2:23) A lokacin da Ibrahim ya ɗaga wuƙarsa zai kashe Ishaƙu, mala’ikan Jehovah ya ce: “Kada ka sa hannunka bisa saurayin, kada kuwa ka yi masa wani abu: gama yanzu na sani mai-tsoron Allah ne kai, da shi ke ba ka hana mini ɗanka ba, tilonka.”—Farawa 22:10-12.
12. Menene ya motsa tsoro na ibada na Ibrahim, kuma yaya za mu nuna irin wannan halin?
12 Ko da yake Ibrahim da farko shi mai tsoron Jehovah ne, a wannan yanayi ya nuna tsoronsa na ibada a hanya ta musamman. Yardar ransa ya yi hadaya da Ishaƙu ya wuce nuna daraja kawai da biyayya. Dogara ce ƙwarai ga Ubansa na samaniya ta motsa Ibrahim cewa zai cika alkawarinsa ta wajen ta da Ishaƙu daga matattu idan ya wajaba. Kamar yadda Bulus ya rubuta, Ibrahim ya ‘sakankance sarai, Allah yana da iko ya cika abin da ya alkawarta.’ (Romawa 4:16-21) Muna shirye mu yi nufin Allah ko ma idan yin hakan zai bukaci hadaya mai girma? Muna da cikakken tabbaci cewa irin wannan biyayyar za ta kawo amfani na dogon lokaci, da sanin cewa Jehovah “mai-sakawa ne ga waɗanda ke biɗarsa”? (Ibraniyawa 11:6) Wannan shi ne ainihin tsoron Allah.—Zabura 115:11.
13. Me ya sa Yusufu zai iya kwatanta kansa daidai cewa shi mutum ne mai ‘tsoron Allah na gaskiya’?
13 Bari mu sake bincika wani misalin tsoro na ibada—na Yusufu. Bawa ne a gidan Potiphar, kowacce rana Yusufu yana samun kansa cikin matsi na ya yi zina. Hakika babu hanyar da zai guje wa matar mai gidansa, da ta nace tana rinjayar. A ƙarshe, da ta “kama shi,” shi kuma “ya gudu, ya fita waje.” Me ya motsa shi ya gudu daga mugunta nan da nan? Babu shakka, babban dalilin shi ne tsoron Allah, muradinsa na ya guje wa yin ‘mugunta mai-girma, ya yi zunubi ga Allah.’ (Farawa 39:7-12) Yusufu zai iya kwatanta kansa daidai cewa shi mutum ne mai ‘tsoron Allah na gaskiya.’—Farawa 42:18.
14. Ta yaya jinƙai na Yusufu ya nuna tsoron Allah da gaske?
14 Wasu shekaru daga baya Yusufu ya sadu fuska da fuska da ’yan’uwansa, waɗanda suka sayar da shi babu tausayi ga bauta. Da zai yi amfani da bukatarsu ƙwarai na abinci a kan zarafi ne ya rama mugunta da suka yi masa. Amma yi wa mutane mugunta ba ya nuna tsoron Allah. (Leviticus 25:43) Saboda haka, sa’ad da ya samu isashen tabbaci cewa ’yan’uwansa sun canja zuciyarsu, ya yi musu jinƙai ya gafarta musu. Kamar Yusufu, tsoro na ibada da muke da shi zai motsa mu mu rinjayi mugunta da nagarta.—Farawa 45:1-11; Zabura 130:3, 4; Romawa 12:17-21.
15. Me ya sa halin Ayuba ya faranta wa Jehovah zuciya?
15 Ayuba wani shahararren misali ne na wanda ya ji tsoron Allah. Jehovah ya ce wa Iblis: “Ko ka lura da bawana Ayuba? Babu mai-kama da shi cikin duniya, kamili ne, mutum mai-adalci, mai tsoron Allah, yana ƙin mugunta.” (Ayuba 1:8) Halin Ayuba marar aibi ya faranta wa Ubansa na samaniya rai na shekaru da yawa. Ayuba ya ji tsoron Allah domin ya san cewa ya yi abin da ya dace ne kuma hanyar rayuwa ce mafi kyau. “Ga shi, tsoron Ubangiji, shi ne hikima,” in ji Ayuba, “rabuwa da mugunta kuma shi ne fahimi.” (Ayuba 28:28) Da yake ma’auraci ne, Ayuba ba ya sha’awar ’yammata ƙanana, ko kuma ya yi sha’awar zina a zuciyarsa. Ko da yake attajiri ne, ya ƙi ya dogara ga dukiyarsa, kuma ya guje dukan ire-iren bautar gumaka.—Ayuba 31:1, 9-11, 24-28.
16. (a) A waɗanne hanyoyi ne Ayuba ya nuna ƙauna? (b) Ta yaya Ayuba ya nuna cewa bai ƙi ya gafarta ba?
16 Tsoron Allah, yana nuna yin abin da yake nagari da kuma guje wa abin da yake mugu. Saboda haka, Ayuba ya ji tausayin makafi, guragu, da kuma matalauta. (Leviticus 19:14; Ayuba 29:15, 16) Ayuba ya fahimci cewa “wanda ya ke bakin suma, sai abokinsa shi nuna masa alheri, domin kada shi rabu da tsoron Mai-iko duka.” (Ayuba 6:14) Hana alheri zai iya haɗa da ƙin gafartawa ko kuma riƙe mutum a zuciya. A bin umurnin Allah, Ayuba ya yi addu’a domin abokanansa uku, da suka azabtar da shi. (Ayuba 42:7-10) Ta yaya mu ma za mu nuna irin wannan hali na gafartawa ga ɗan’uwa mai bi wanda ya ɓata mana rai a wata hanya? Addu’a ta gaskiya domin waɗanda suka ɓata mana rai za ta taimake mu guje wa fushi. Albarkar da Ayuba ya more domin tsoronsa na ibada ya ba mu taɓin ‘alheri mai yawa na Jehovah da ya tare domin waɗanda suke tsoronsa.’—Zabura 31:19; Yaƙub 5:11.
Tsoron Allah da Tsoron Mutum
17. Menene tsoron mutane zai yi mana, amma me ya sa wannan tsoron babu fahimi ciki?
17 Yayin da tsoron Allah zai motsa mu mu yi abin da yake nagari, tsoron mutum zai iya yi wa bangaskiyarmu zagon ƙasa. Domin wannan dalilin, sa’ad da yake ƙarfafa manzannin su kasance masu wa’azin bishara da ƙwazo, Yesu ya gaya musu: “Kada ku ji tsoron waɗannan da su ke kisan jiki, ba su kuwa da iko su kashe rai: gwamma dai ku ji tsoron wannan wanda yana da iko ya halaka rai duk da jiki cikin Jahannama.” (Matta 10:28) Tsoron mutane ba shi da nisa, Yesu ya yi bayani, domin mutane ba za su iya halaka rayuwarmu ta nan gaba ba. Bugu kan ƙari, muna tsoron Allah domin mun fahimci ikonsa mai ban fargaba, in aka gwada da na mutane, na mutane ba kome ba ne. (Ishaya 40:15) Kamar Ibrahim muna da cikakken tabbaci ga ikon Jehovah ya ta da bayinsa amintattu da suka mutu. (Ru’ya ta Yohanna 2:10) Saboda haka, muna faɗa da tabbaci: “Idan Allah ke wajenmu, wa ke gaba da mu?”—Romawa 8:31.
18. A wace hanya ce Jehovah yake sāka ma waɗanda suka ji tsoron shi?
18 Ko mai hamayya da mu wani a iyalinmu ne ko kuma wani mugu ne a makaranta, za mu ga cewa “a cikin tsoron Ubangiji akwai sakankancewa mai-ƙarfi.” (Misalai 14:26) Za mu iya yi wa Allah addu’a domin ƙarfi, tun da mun san zai ji mu. (Zabura 145:19) Jehovah ba ya taɓa manta da waɗanda suke jin tsoronsa. Ta wajen annabinsa Malachi, ya tabbatar mana da cewa: “Sa’annan su waɗanda suka ji tsoron Ubangiji suka yi zance da junansu; Ubangiji kuma ya kasa kunne, ya ji, aka rubuta littafin tunawa a gabansa, domin waɗanda su ke jin tsoron Ubangiji, masu-tunawa da sunansa.”—Malachi 3:16.
19. Wane irin tsoro ne zai ƙare, amma wane iri ne zai kasance har abada?
19 Lokaci ya yi kusa da kowa a duniya zai bauta wa Jehovah kuma tsoron mutum zai shuɗe. (Ishaya 11:9) Tsoron yunwa, cuta, yin laifi, da kuma yaƙi zai wuce. Amma tsoron Allah ne zai rage har abada yayin da bayinsa masu aminci a sama da kuma a duniya za su ci gaba da daraja shi, su yi masa biyayya, kuma girmama shi. (Ru’ya ta Yohanna 15:4) Amma yanzu, bari mu karɓi wannan gargaɗin Sulemanu da aka hure da zuciyarmu: “Kada zuciyarka ta ji kishin masu-zunubi: amma ka kasance cikin tsoron Ubangiji dukan yini. Gama hakika da akwai lada: ba kuwa za a yanke maka begenka ba.”—Misalai 23:17, 18.
[Hasiya]
a Wasu mutane suna ƙangara ga tsoro idan aikinsu yana sa su a yanayi mai haɗari a kai a kai. Da aka yi tambaya me ya sa masassaƙa da yawa suna rashin yatsa, wani gwani sassaƙa ya ce: “Sun daina tsoron zarto mai inji mai gudu.”
b Jehovah kansa yana wannan ƙyamar. Alal misali, Afisawa 4:29 ya kwatanta batsa da “ruɓaɓen zance.” Kalmar Helenanci da aka yi amfani da ita na “ruɓaɓen” a zahiri tana nufin ruɓaɓɓen ’ya’yan itace, kifi, ko nama. Irin wannan kalmar ta nuna ƙwarai yadda ya kamata mu ji game da zagi da kuma batsa. Hakanan, gumaka sau da yawa ana kwatanta su cikin Nassi da ‘najasa.’ (Kubawar Shari’a 29:17; Ezekiel 6:9) Yadda muke ƙyamar najasa, ko kashi, ya taimake mu mu fahimci yadda Allah yake ƙyamar kowacce irin bautar gunki.
c Alal misali, ka bincika tarihin Kayinu (Farawa 4:3-12; Dauda (2 Samu’ila 11:2–12:14); Gehazi (2 Sarakuna 5:20-27); da Uzziah (2 Labarbaru 26:16-21).
Ka Tuna?
• Ta yaya muke koya mu ƙi abin da ke mugu?
• Ta yaya wasu Isra’ilawa a zamanin Malachi suka yi banza da abokantakar Jehovah?
• Menene za mu koya daga Ibrahim, Yusufu, da kuma Ayuba game da tsoron Allah?
• Wane irin tsoro ne zai kasance, kuma me ya sa?
[Hoto a shafi na 25]
Iyaye masu hikima suna saka tsoro mai kyau a zuciyar yaransu
[Hoto a shafi na 26]
Kamar yadda tsoro yake sa mu guje wa haɗari, haka tsoro na ibada yake sa mu guji mugunta
[Hoto a shafi na 29]
Ayuba ya kasance da tsoronsa na Allah har a lokacin da ya fuskanci abokan ƙarya uku
[Inda aka Dauko]
Daga fassarar Littafi Mai Tsarki Vulgata Latina, 1795