Ka More Rayuwa Don Kana Tsoron Jehobah
“Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa: Gama babu rashi ga masu-tsoronsa.”—ZABURA 34:9.
1, 2. (a) Waɗanne ra’ayoyi dabam dabam ne Kiristendom suke da shi game da tsoron Allah? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika yanzu?
MALAMAN addinan Kiristendom da suke koyar da tsoron Allah a kowane lokaci, suna yin haka ne ba bisa koyarwar nassi ba, suna cewa Allah yana yi wa masu zunubi horo a cikin wuta har abada. Wannan koyarwar ba ta jitu ba da abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da Jehobah wanda Allah ne mai ƙauna kuma mai adalci. (Farawa 3:19; Kubawar Shari’a 32:4; Romawa 6:23; 1 Yohanna 4:8) Wasu malaman Kiristendom sun ɗauki wani gurbi dabam. Ba su taɓa ambata cewa mu ji tsoron Allah ba. Maimakon haka, suna koyar da cewa Allah yana nuna halin ba komi kuma yana karɓan kowa ko da rayuwar da yake yi ba shi da kyau. Littafi Mai Tsarki bai koyar da wannan ba.—Galatiyawa 5:19-21.
2 Babu shakka, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu ji tsoron Allah. (Ru’ya ta Yohanna 14:7) Wannan gaskiyar ta jawo wasu tambayoyi. Me ya sa Allah mai ƙauna yake son mu ji tsoronsa? Wane irin tsoro ne Allah yake bukata? Ta yaya ne tsoron Allah zai amfane mu? Za mu tattauna waɗannan tambayoyin sa’ad da muka ci gaba da tattauna Zabura ta 34.
Dalilin da Ya Sa Za Mu Ji Tsoron Allah
3. (a) Menene ra’ayinka game da dokar da ta ce mu ji tsoron Allah? (b) Me ya sa masu jin tsoron Jehobah suke farin ciki?
3 Jehobah ya cancanci mu ji tsoronsa domin shi ne Mahalicci da kuma Mamallakin sararin samaniya. (1 Bitrus 2:17) Amma, wannan tsoron ba mugun tsoro ba ne na azzalumin allah. Wannan tsoro ne na ibada domin Jehobah shi ne Mahalicci. Kuma tsoro ne na ɓata masa rai. Tsoron Allah tsoro ne mai kyau kuma mai kyautata rayuwa, ba mai razanarwa ba. Jehobah “Allah mai-albarka,” yana son mutane su more rayuwa. (1 Timothawus 1:11) Amma, idan muna son mu cim ma haka, muna bukatar mu yi rayuwar da ta jitu da bukatun Allah. Ga yawanci, hakan na bukatar canza salon rayuwarsu. Duka waɗanda suka yi wannan canjin suna shaida gaskiyar kalaman mai zabura Dauda: “Ku ɗanɗana, ku duba, Ubangiji nagari ne: mai-albarka ne mutum wanda ya ke dogara gareshi. Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa: Gama babu rashi ga masu-tsoronsa.” (Zabura 34:8, 9) Duka waɗanda suke tsoron Jehobah ba sa rasa abubuwa masu kyau domin suna da dangantaka mai kyau da Allah.
4. Wane tabbaci ne Dauda da Yesu suka ba da?
4 Kamar yadda ake yi a zamaninsa, Dauda ya daraja mutanensa ta wajen kiransu ‘tsarkakku.’ Su sashe ne na tsarkakar al’ummar Allah. Kuma sun sadaukar da ransu ta wajen bin Dauda. Ko da yake sun yi gudun hijira ne daga Sarki Saul, Dauda yana da tabbacin cewa Jehobah zai ci gaba da biya musu bukatunsu. Dauda ya rubuta: “ ’Ya’yan zaki su kan rasa, su kan ji yunwa: Amma waɗanda su ke biɗan Ubangiji ba za su rasa kowane abu mai-kyau ba.” (Zabura 34:10) Yesu ya ba mabiyansa irin wannan tabbacin.—Matta 6:33.
5. (a) Wane irin mutane ne yawancin mabiyan Yesu? (b) Wace shawara ce Yesu ya bayar game da batun tsoro?
5 Yawancin waɗanda suka saurari Yesu Yahudawa ne marasa galihu. Saboda haka, Yesu “ya yi juyayi a kansu, domin suna wahala, suna watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matta 9:36) Irin waɗannan marar galihu za su kasance da gaba gaɗin bin Yesu? Idan suna son su yi haka, suna bukatar su ji tsoron Jehobah, ba mutane ba. Yesu ya ce: “Kada ku ji tsoron waɗanda ke kisan jiki, daga baya ba su sauran wani abin da za su yi ba. Amma ni, in faɗakadda ku wanda za ku ji tsoronsa: Ku ji tsoron wannan, wanda bayanda ya kashe yana da iko ya jefas cikin Jahannama; i, ina ce maku, Shi za ku ji tsoro. Ba a kan sayar da gwara biyar a bakin anini huɗu ba? ko ɗaya kuwa a cikinsu ba a manta da shi wurin Allah ba. Amma har da gasussuwan kanku duka an ƙididdige su. Kada ku ji tsoro: kun fi gwarare masu-yawa daraja.”—Luka 12:4-7.
6. (a) Waɗanne kalaman Yesu ne suka ƙarfafa Kiristoci? (b) Me ya sa Yesu ne misali mafi kyau na nuna tsoron Allah?
6 Sa’ad da masu jin tsoron Jehobah suka fuskanci matsi daga magabtansu don suna so su hana su bauta wa Allah, suna iya tuna da shawarar Yesu: “Kowanene da za shi shaida ni a gaban mutane, Ɗan mutum kuma za ya shaida shi a gaban malaikun Allah: amma wanda ya yi musun sanina a gaban mutane, za a yi musunsa a gaban malaikun Allah.” (Luka 12:8, 9) Waɗannan kalaman sun ƙarfafa Kiristoci, musamman a ƙasashen da aka hana bauta ta gaskiya. Waɗannan sun ci gaba da yaba wa Jehobah da hikima a taron Kirista da kuma hidimar fage. (Ayukan Manzanni 5:29) Yesu ya kafa misali mafi kyau na ‘tsoron Allah.’ (Ibraniyawa 5:7) Sa’ad da take magana game da shi, Kalmar annabci ta ce: “Ruhun Ubangiji za ya zauna bisansa, ruhun . . . tsoron Ubangiji: jin daɗinsa kuma za ya kasance a cikin tsoron Ubangiji.” (Ishaya 11:2, 3) Saboda haka, Yesu ya cancanci ya koya mana amfanin tsoron Allah.
7. (a) Ta yaya ne Kiristoci, suke na’am ga irin gayyar da Dauda ya yi? (b) Ta yaya ne iyaye za su iya bin misali mai kyau na Dauda?
7 Duka waɗanda suka bi misalin Yesu kuma suka yi biyayya ga koyarwarsa, suna yin na’am ne ga irin gayyar da Dauda ya yi: “Ku zo, ku yara, ku kasa kunne gareni: ni koya muku tsoron Ubangiji.” (Zabura 34:11) Daidai ne Dauda ya kira mabiyansa “yara” domin shi ne shugabansu. A ɓangarensa, Dauda ya ba mabiyansa taimako na ruhaniya domin su kasance da haɗin kai kuma su more tagomashin Allah. Wannan misali ne mai kyau ga iyaye Kiristoci! Jehobah ya ba su iko game da ’ya’yansu domin su “goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Ta wajen tattauna batutuwa na ruhaniya da yaransu da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki a kowane lokaci, iyaye suna taimaka wa yaransu su more rayuwa ta wajen jin tsoron Jehobah.—Kubawar Shari’a 6:6, 7.
Yadda Za a Ji Tsoron Allah
8, 9. (a) Me ya sa rayuwa da tsoron Allah na da kyau? (b) Menene kāre harshenmu ya ƙunsa?
8 Kamar yadda aka ambata a baya, jin tsoron Jehobah ba ya hana mu jin daɗi. Dauda ya yi tambaya: “Wane mutum ne wanda ya ke son rai, Shi na begen yawan kwanaki kuma, da za shi ga alheri?” (Zabura 34:12) Babu shakka, tsoron Jehobah shi ne zai sa mu more doguwar rayuwa kuma mu ga alheri. Amma, yana da sauƙi mu ce “Ina tsoron Allah.” Amma ba shi da sauƙi mu nuna haka ta wajen ɗabi’armu. Saboda haka, Dauda ya ci gaba da bayyana yadda za mu nuna tsoron Allah.
9 “Ka kiyayadda harshenka ga barin mugunta, Leɓunanka kuma ga barin maganar algus.” (Zabura 34:13) An hure manzo Bitrus ya yi ƙaulin wannan sashe na Zabura ta 34 bayan ya shawarci Kiristoci su bi da juna cikin ƙauna. (1 Bitrus 3:8-12) Kāre harshenmu daga abin da ba shi da kyau na nufin guje wa yaɗa gulma. Maimakon haka, za mu yi ƙoƙarin ƙarfafa mutane sa’ad da muke magana da su. Bugu da ƙari, za mu yi ƙoƙarin kasancewa da gaba gaɗi kuma mu faɗi gaskiya.—Afisawa 4:25, 29, 31; Yaƙub 5:16.
10. (a) Ka bayyana abin da guje wa mugunta ke nufi? (b) Menene yin nagarta ya ƙunsa?
10 “Ka rabu da mugunta, ka yi nagarta; Ka biɗi salama, ka bi ta kuma.” (Zabura 34:14) Muna ƙin abubuwan da Allah ya ƙi, kamar su lalata, hoton batsa, sata, sihiri, nuna ƙarfi, maye, da kuma shan ƙwaya. Kuma muna ƙin wasannin da suke nuna irin waɗannan abubuwa marar kyau. (Afisawa 5:10-12) Maimakon haka, muna yin amfani da lokacinmu mu yi abubuwa masu nagarta. Abu mafi kyau da za mu iya yi shi ne yin wa’azin Mulki da kuma aikin almajirantarwa a kowane lokaci, wato taimaka wa wasu su sami ceto. (Matta 24:14; 28:19, 20) Yin nagarta ya ƙunshi yin shirin halartar taron Kirista, ba da kyauta ga aikin dukan duniya, kula da Majami’ar Mulki, da kuma damuwa da bukatun Kiristoci mabukata.
11. (a) Ta yaya ne Dauda ya bi abin da ya ce game da salama? (b) Menene za ka iya yi don ka ‘biɗi salama’ a cikin ikilisiya?
11 Dauda ya kafa misali mai kyau na biɗar salama. Ya sami damar kashe Saul sau biyu. A waɗannan lokuttan, ya guje wa mugunta kuma ya yi wa sarkin magana cikin ladabi, wataƙila hakan zai kawo salama. (1 Samuila 24:8-11; 26:17-20) Menene za a iya yi a yau idan wani yanayi yana son ya jawo rashin salama a cikin ikilisiya? Ya kamata mu ‘biɗi salama, kuma mu bi ta.’ Da haka, idan muka fahimci cewa dangantakarmu da wani mai bi ba shi da kyau sosai, ya kamata mu yi biyayya da shawarar Yesu: “Sulhuntu da ɗan’uwanka tukuna.” Bayan haka sai mu ci gaba da sauran fasaloli na bauta ta gaskiya.—Matta 5:23, 24; Afisawa 4:26.
Jin Tsoron Allah na Kawo Lada Mai Yawa
12, 13. (a) Waɗanne amfani ne masu jin tsoron Allah suke morewa yanzu? (b) Wane sakamako mai girma ne masu bauta wa Allah cikin aminci za su more nan ba da daɗewa ba?
12 “Idanun Ubangiji suna fuskanta wajen masu-adalci; kunnuwansa kuma a buɗe su ke ga jin ƙarassu.” (Zabura 34:15) Yadda Allah ya bi da Dauda ya nuna cewa waɗannan kalaman gaskiya ne. A yau, muna more farin ciki da kwanciyar hankali domin mun san cewa Jehobah yana kāre mu. Muna da tabbaci cewa zai ba mu abin da muke bukata a kowane lokaci, har ma a lokacin matsi. Mun san cewa nan ba da daɗewa ba, duka masu bauta ta gaskiya za su fuskanci harin da aka annabta na Gog na Magog da kuma “ranar Ubangiji . . . mai-ban razana.” (Joel 2:11, 31; Ezekiel 38:14-18, 21-23) Duk yanayin da muka fuskanta, kalaman Dauda za su shafe mu: “Masu-adilci suka yi kuka, Ubangiji ya ji, Ya tsamadda su daga dukan wahalansu.”—Zabura 34:17.
13 Abin al’ajabi ne mu ga yadda Jehobah zai ɗaukaka sunansa mai girma! Zuciyarmu za ta cika da girmamawa sosai fiye da dā, kuma duka masu hamayya za su yi mutuwar kunya. “Fuskar Ubangiji tana gāba da masu-aikin mugunta, Domin ya shafe tunawa da su daga duniya.” (Zabura 34:16) Lada ce mai girma mu shaida irin wannan ceto zuwa cikin sabuwar duniya ta Allah!
Alkawuran da Suke Taimaka Mana Mu Jimre
14. Menene zai taimaka mana mu jimre duk da wahala?
14 A yanzu, yin biyayya ga Jehobah a wannan lalataciyar duniyar na bukatar jimiri. Tsoron Allah zai taimaka mana sosai mu yi biyayya. Domin lokacin wahala da muke ciki, wasu bayin Jehobah suna fuskantar wahalolin da ke sa su baƙin ciki kuma suna sa su sanyin gwiwa. Amma suna da tabbaci cewa idan suka dogara ga Jehobah, zai taimaka musu su jimre. Kalaman Dauda suna da ban ƙarfafa: “Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton irin waɗanda su ke da ruhu mai-tuba.” (Zabura 34:18) Dauda ya ci gaba da cewa: “Masifu na mai-adalci dayawa su ke: amma Ubangiji ya kan tsamarda shi daga cikinsu duka.” (Zabura 34:19) Komi yawan wahalar da ya faɗa mana, Jehobah yana da ƙarfin cetonmu.
15, 16. (a) Wane bala’i ne Dauda ya fuskanta bayan ya rubuta Zabura ta 34? (b) Menene zai taimaka mana mu jimre gwaji?
15 Bayan ya rubuta Zabura ta 34, Dauda ya ji bala’in da ya faɗa wa mazaunan Nob, sa’ad da Saul ya yi wa yawancin firistoci da mazauna ƙasar kisan kiyashi. Ya yi baƙin ciki sosai domin ya san cewa ziyarar da ya kai Nob ce ta ba Saul haushi! (1 Samuila 22:13, 18-21) Babu shakka, Dauda ya nemi taimako daga wurin Jehobah, kuma tashin “masu-adalci” daga matattu da za a yi a nan gaba ya ƙarfafa shi.—Ayukan Manzanni 24:15.
16 A yau, begen tashin matattu na ƙarfafa mu. Mun san cewa ba abin da maƙiyanmu za su yi mana da zai jawo mana lahani na dindindin. (Matta 10:28) Dauda ya furta tabbacinsa da waɗannan kalaman: “Yana kiyaye dukan ƙasusuwansa [masu adalci], Ko ɗaya cikinsu ba ya karye ba.” (Zabura 34:20) Wannan surar ta sami cika na zahiri a Yesu. Ko da yake an yi wa Yesu mugun kisa, babu ƙashinsa da aka “karye.” (Yohanna 19:36) A wani fannin kuma, Zabura 34:20 ta tabbatar mana cewa duk gwajin da shafaffun Kiristoci da kuma “waɗansu tumaki” suka fuskanta, ba zai yi musu lahani na dindindin ba. Ba za a taɓa karye ƙasusuwansu ba a alamance.—Yohanna 10:16.
17. Wane bala’i ne yake jiran waɗanda suke gāba da mutanen Jehobah?
17 Ga miyagu kuwa, yanayin ya bambanta. Nan ba da daɗewa ba za su girbe muguntar da suka shuka. “Mugunta za ta kashe miyagu: Kuma waɗanda suna ƙin masu-adilci za a kāda su.” (Zabura 34:21) Duka waɗanda suka ci gaba da yin hamayya da mutanen Allah za su fuskanci bala’i. A lokacin da Yesu Kristi zai bayyana, “hukunci za su sha, madawamiyar hallaka.”—2 Tassalunikawa 1:9.
18. Ta yaya ne aka riga aka ceci “taro mai-girma,” kuma me za su shaida a nan gaba?
18 Zaburar Dauda ta kammala da waɗannan kalaman masu ban ƙarfafa: “Ubangiji yana pansar ran bayinsa; A cikin masu-dogara gareshi ba za a kada ko ɗaya ba.” (Zabura 34:22) A kusan ƙarshen sarautarsa ta shekara 40, Sarki Dauda ya ce: “[Allah] ya panshi raina daga cikin dukan masifa.” (1 Sarakuna 1:29) Kamar Dauda, nan ba da daɗewa ba, masu jin tsoron Jehobah za su tuna baya kuma su yi farin ciki domin sun sami ceto daga duka laifi domin zunubi, kuma sun sami ceto daga duka gwajin da suka fuskanta. Yawancin shafaffun Kiristoci sun sami ladarsu ta sama. “Taro mai-girma” daga duka al’ummai suna ta haɗa hannu da sauran ’yan’uwan Yesu wajen bauta wa Allah kuma suna more matsayi mai tsabta a gaban Jehobah. Wannan ya faru ne domin sun nuna bangaskiya ga ikon jinin da Yesu ya zubar na ceto. A lokacin Sarauta na Shekara Dubu na Kristi, za su shaida cikakkiyar amfanin hadayar fansa, wadda za ta sa su kamilta.—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14, 17; 21:3-5.
19. Menene ƙudurin “taro mai-girma”?
19 Me ya sa “taro mai-girma” ta masu bauta wa Allah za su sami duka waɗannan albarkar? Domin sun ƙudurta cewa za su ci gaba da jin tsoron Jehobah, su bauta masa da ban girma da kuma biyayya. Hakika, tsoron Jehobah na sa rayuwa ta yi daɗi a yanzu kuma yana taimaka mana mu “ruski rai wanda shi ke hakikanin rai,” wato rayuwa ta har abada a sabuwar duniya ta Allah.—1 Timothawus 6:12, 18, 19; Ru’ya ta Yohanna 15:3, 4.
Ka Tuna?
• Me ya sa ya kamata mu ji tsoron Allah, kuma menene jin tsoronsa ke nufi?
• Ta yaya ne ya kamata tsoron Allah ya shafi halinmu?
• Waɗanne sakamako ne muke samu daga jin tsoron Allah?
• Waɗanne alkawura ne suke taimaka mana mu jimre?
[Hoto a shafi na 28]
Masu jin tsoron Jehobah suna amfani da hikima sa’ad da aka hana aikinsu
[Hoto a shafi na 30]
Abu mafi kyau da za mu iya yi wa maƙwabtanmu shi ne mu gaya musu bisharar Mulki