Sun Jimre Da Ƙaya Cikin Jikinsu
“Aka ba ni masuki cikin jikina, manzon Shaiɗan shi mammare ni.”—2 KORINTHIYAWA 12:7.
1. Waɗanne matsaloli ne mutane ke fuskanta a yau?
KANA fama ne da wani gwaji? Idan haka ne, kuna da yawa. A waɗannan “miyagun zamanu,” amintattun Kiristoci suna jure da hamayya mai tsanani, matsalolin iyali, ciwo, rashin kuɗi, damuwa ta zuciya, rashin waɗanda suke ƙauna, da wasu ƙalubale. (2 Timothawus 3:1-5) A wasu ƙasashe, mutane da yawa na cikin haɗari don karancin abinci da yaƙe-yaƙe.
2, 3. Wane hali da ba shi da kyau ne zai iya kai wa ga matsaloli masu kama da ƙaya da muke fuskanta, kuma ta yaya wannan zai iya kasancewa da haɗari?
2 Irin waɗannan matsaloli za su iya rufe mutum gabaki ɗaya, musamman ma idan matsaloli da yawa suka faɗo wa mutum a lokaci ɗaya. Ka lura da abin da Misalai 24:10 ta ce: “Idan ka yi suwu cikin ranar ƙunci, ƙarfinka kaɗanna ne.” Hakika, fid da zuciya domin gwaji da muke fuskanta zai hana mu ƙarfi da muke bukata kuma ya sanyatar da ƙudurinmu na jimrewa har ƙarshe. Ta yaya?
3 To, fid da zuciya zai iya sa mu kasa cika burinmu. Alal misali, yana da sauƙi mu zuguiguita wahalarmu kuma mu soma tausaya wa kanmu. Wasu ma za su yi wa Allah kuka, “Me ya sa ka ƙyale wannan ya faru mini?” Idan irin wannan hali da ba shi da kyau ya yi jijiya cikin zuciyar mutum, zai iya ɓata masa farin ciki da kuma tabbaci. Bawan Allah zai iya fid da rai har ba zai iya yaƙin “kirki na imani” ba.—1 Timothawus 6:12.
4, 5. A wasu lokatai, yaya Shaiɗan yake sa hannu cikin matsalarmu, duk da haka wane gaba gaɗi za mu kasance da shi?
4 Hakika Jehovah Allah ba shi ne ke haddasa gwajinmu ba. (Yaƙub 1:13) Wasu gwaji sukan zo mana domin kawai muna ƙoƙari mu kasance da aminci ne gare shi. Alhali ma, dukan waɗanda suke bauta wa Jehovah ne musamman babban magabci, Shaiɗan Iblis yake nema. A ɗan lokaci da ya rage masa, wannan mugun “allah na wannan zamani” yana ƙoƙari ya saka kowa da yake ƙaunar Jehovah ya daina yin nufinsa. (2 Korinthiyawa 4:4) Shaiɗan yana kawo wahala gwargwadon yadda zai iya a kan dukan tarayyar ’yan’uwanci a dukan duniya. (1 Bitrus 5:9) Ko da yake, ba Shaiɗan ba ne ke haddasa dukan matsalolinmu kai tsaye, zai iya amfani da matsalolin da muke fuskanta, yana nema ya ƙara raunana mu.
5 Ko yaya ƙarfin Shaiɗan ko makamansa za su zama, za mu iya cin nasara bisansa! Ta yaya za mu iya tabbatawa da wannan? Saboda Jehovah Allah yana yaƙi dominmu. Ya tabbata cewa bayinsa sun san dabarun Shaiɗan. (2 Korinthiyawa 2:11) Hakika, Kalmar Allah ta gaya mana abubuwa da yawa game da gwaji da ke wahal da Kiristoci na gaskiya. A batun manzo Bulus, Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da furcin nan ‘ƙaya a cikin jiki.’ Menene dalilin haka? Bari mu duba yadda Kalmar Allah ta yi bayani game da wannan furcin. Za mu ga cewa ba mu kaɗai ba ne muke bukatar taimakon Jehovah don mu yi nasara bisa gwaji.
Abin da Ya Sa Gwaji Suke Kama da Ƙaya
6. Menene Bulus yake nufi da ‘ƙaya cikin jiki,’ mecece wataƙila wannan ƙayar?
6 Bulus da ya sha gwaji ƙwarai, an hure shi ya rubuta: ‘Aka ba ni ƙaya cikin jikina, manzon Shaiɗan shi mammare ni, domin kada in fiye ɗaukaka.’ (2 Korinthiyawa 12:7) Menene wannan ƙaya a cikin jikin Bulus? To, ƙaya da ta nutse cikin jiki lallai akwai ta da ciwo. Saboda haka, furcin na nufin wani abin da ya ba wa Bulus azaba ne—a jiki, a zuciya, ko duka biyun. Mai yiwuwa Bulus ya sha wahalar ciwon ido ko wani rashin lafiya. Ko kuma ƙayar ta ƙunshi mutane da suke tuhumar ikon Bulus na manzanci kuma suna shakkar aikin wa’azinsa da koyarwa. (2 Korinthiyawa 10:10-12; 11:5, 6, 13) Ko menene dai, wannan ƙaya ta kasance da Bulus, ba a iya cire ta ba.
7, 8. (a) Menene furci nan “shi mammare ni” yake nufi? (b) Me ya sa yake da muhimmanci mu jure wa kowacce ƙaya da ke azabtar da mu yanzu?
7 Ka lura cewa ƙayar ta ci gaba da mammarin Bulus. Abin farin ciki, kalmar aikatau na Helenanci da Bulus ya yi amfani da ita a nan an ɗauko ne daga kalmomin nan “tafin hannu.” An yi amfani da waɗannan kalmomin a zahiri a Matta 26:67 kuma cikin alama a 1 Korinthiyawa 4:11. A waɗannan ayoyin, suna nufin dūkan mutum da dunƙulallen hannu. Saboda ƙiyayyar Shaiɗan mai tsanani ga Jehovah da bayinsa, za mu tabbata cewa Iblis ya ji daɗi cewa ƙaya ta ci gaba da marin Bulus. A yau, Shaiɗan na jin daɗi yayin da muke wahala da ƙaya cikin jiki.
8 Saboda haka, kamar Bulus muna bukatar mu san yadda za mu jure da irin wannan ƙayar. Rayuwarmu ta dangana ga yin haka! Ka tuna, Jehovah yana son mu rayu har abada a cikin sabuwar duniyarsa, inda matsaloli masu kama da ƙaya ba za su ƙara shafan mu ba. Don mu ci wannan nasara mai ban al’ajabi, Allah ya ba mu misalai da yawa cikin Kalmarsa mai tsarki, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bayinsa masu aminci sun yi nasara a jurewa da ƙaya cikin jikinsu. Su ma mutane ne ajizai, kamar yadda muke. Yin la’akari da wasu cikin waɗannan “taron shaidu” mai girma zai taimaka mana mu yi ‘tare da haƙuri kuma mu yi tseren da an sa gabanmu.’ (Ibraniyawa 12:1) Yin bimbini a kan abin da suka jimre zai gina amincinmu cewa za mu iya jimrewa da kowacce ƙaya da Shaiɗan zai yi amfani da ita a kanmu.
Ƙayoyi da Suka Azabtar da Mephibosheth
9, 10. (a) Yaya Mephibosheth ya samu ƙaya a cikin jikinsa? (b) Wane alheri Sarki Dauda ya nuna wa Mephibosheth, kuma ta yaya za mu yi koyi da Dauda?
9 Yi la’akari da Mephibosheth, ɗan Jonathan abokin Dauda. Sa’ad da Mephibosheth yake ɗan shekara biyar, labari ya zo cewa babansa Jonathan, da kakansa, Sarki Saul an kashe su. Mareniyar yaron ta tsorata. Ta “ɗauke shi . . . ya zama fa, cikin garajen gudunta, sai ya fāɗi, ya zama gurgu.” (2 Samu’ila 4:4) Wannan naƙasa ta zama ƙaya da Mephibosheth zai jure da ita yayin da yake girma.
10 Bayan wasu shekaru Sarki Dauda, domin ƙaunar Jonathan da yake yi, ya yi wa Mephibosheth alheri. Dauda ya mai da masa dukan dukiyar Saul kuma ya gaya wa bawan Saul Ziba ya kula da filayen. Dauda ya kuma gaya wa Mephibosheth: “Za ka ci abinci a [teburi] nawa kullayaumin.” (2 Samu’ila 9:6-10) Babu shakka alherin Dauda ya zama ta’aziyya ga Mephibosheth kuma ya taimake shi ya jimre wa azabar naƙasarsa. Wannan darasi ne mai kyau! Ya kamata mu ma mu yi wa waɗanda suke fama da ƙaya a cikin jiki alheri.
11. Menene Ziba ya ce game da Mephibosheth, yaya kuwa muka sani cewa abin da ya ce ƙarya ne? (Duba hasiya.)
11 Daga baya, Mephibosheth ya yi fama da wata ƙaya a cikin jikinsa kuma. Bawansa Ziba ya tsegunta shi wajen Sarki Dauda, wanda yake tserewa daga Urushalima domin tawayen ɗansa Absalom. Ziba ya ce Mephibosheth cikin rashin aminci ya zauna a Urushalima da begen zai samu sarauta.a Dauda ya gaskata tsegumin Ziba kuma ya ba wa wannan maƙaryaci dukan dukiyar Mephibosheth!—2 Samu’ila 16:1-4.
12. Menene Mephibosheth ya yi game da yanayinsa, kuma ta yaya ya zama misali mai kyau gare mu?
12 Amma, sa’ad da Mephibosheth daga baya ya sadu da Dauda, ya gaya wa sarki abin da ainihi ya faru. Yana shiri ya bi Dauda yayin da Ziba ya ruɗe shi ya ce zai je a madadinsa. Dauda ya gyara wannan laifin ne? Ɗan kaɗan. Ya raba dukiyar ga mutane biyun. Wannan wata ƙaya ce cikin jikin Mephibosheth. Ya ɓata rai ne ƙwarai? Ya ƙi hukuncin Dauda ne, yana kuka cewa ai wannan cuta ne? A’a, cikin tawali’u ya yarda da ra’ayin sarkin. Ya mai da hankali ga fanni mai kyau, yana murna cewa sarkin Isra’ila wanda ya dace ya dawo lafiya. Mephibosheth da gaske ya kafa misali mafi kyau na jimre wa naƙasa, tsegumi, da ɓacin rai.—2 Samu’ila 19:24-30.
Nehemiah Ya Jure wa Gwajinsa
13, 14. Waɗanne ƙayoyi Nehemiah ya jimre musu yayin da ya dawo ya sake gina garun Urushalima?
13 Ka yi tunanin ƙayoyi na alama da Nehemiah ya jure wa sa’ad da ya dawo birnin Urushalima da ba shi da garu a ƙarni na biyar K.Z. Ya iske birnin a zahiri ba shi da kāriya, kuma Yahudawa da aka komar da su ba a shirye suke ba, sun yi sanyin gwiwa, ba su da tsabta a gaban Jehovah. Ko da Sarki Artaxerxes ne ya ba da umurni a sake gina garun Urushalima, ba da jimawa ba Nehemiah ya fahimci cewa gwamnoni na kusa da ƙasar ba sa son aikin. “Ya ɓāta musu zuciya ƙwarai, da shi ke wani ya zo mai-biɗan lafiya ’ya’yan Isra’ila.”—Nehemiah 2:10.
14 Waɗannan baƙi ’yan hamayya sun yi iyakar ƙoƙarinsu don su hana Nehemiah yin aikinsa. Burgansu, ƙaryace-ƙaryacensu, tsegumi, barazanarsu—haɗe da aika da ’yan leƙen asiri su sa shi ya yi sanyin gwiwa—lallai suna kama da ƙaya mai ci gaba a cikin jikinsa. Ya faɗa wa dabarun waɗannan magabta ne? A’a! Ya saka cikakkiyar dogara ga Allah, bai raunana ba. Da haka, sa’ad da a ƙarshe aka sake gina garun Urushalima, ya ba da shaidar dindindin ta tallafawa na Jehovah cikin ƙauna ga Nehemiah.—Nehemiah 4:1-12; 6:1-19.
15. Waɗanne matsaloli tsakanin Yahudawa ya dami Nehemiah ƙwarai?
15 Da yake shi gwamna ne, Nehemiah ya yi fama da matsaloli da yawa tsakanin mutanen Allah. Waɗannan wahaloli suna kama da ƙaya da ke damunsa sosai domin suna shafan dangantakar mutanen da Jehovah. Masu arziki suna neman riba mai yawa, kuma don su biya bashi da kuma haraji na ’yan Persiya, suna sayar da filayensu da kuma yaransu zuwa bauta. (Nehemiah 5:1-10) Yahudawa da yawa suna karya dokar Asabar kuma kasa tallafa wa Lawiyawa da kuma haikalin. Wasu kuma sun auri “Matan Ashdod, da na Ammon, da na Moab.” Wannan ya sa Nehemiah baƙin ciki ƙwarai! Amma babu wata cikin waɗannan ƙayoyi da ta sa shi ya daina aikin. A kai a kai ya mazakuta kansa mai ɗaukaka dokokin Allah na adalci da himma. Kamar Nehemiah, bari mu ƙi halin rashin aminci na wasu ya rinjaye mu daga hidimar aminci ga Jehovah.—Nehemiah 13:10-13, 23-27.
Wasu Masu Aminci da Yawa Sun Jure
16-18. Ta yaya jayayya ta iyali ta shafi Ishaƙu, Rifkatu, Hannatu, Dauda, da Hosea?
16 Littafi Mai Tsarki na ɗauke da misalai da yawa na mutane da suka jure da yanayi na wahala da ke kama da ƙaya. Tushe ɗaya na irin wannan ƙaya shi ne matsaloli na iyali. Mata biyu na Isuwa “su kuwa suka zama abin ɓāta rai ga Ishaƙu da Rifkatu,” iyayen Isuwa. Rifkatu ta ma ce ta gaji da ranta saboda matan nan. (Farawa 26:34, 35; 27:46) Ka kuma yi tunanin Hannatu da kishiyarta, Peninnah, ta “riƙa ba ta haushi” domin Hannatu bakararriya ce. Wataƙila Hannatu ta sha wannan azabar a kai a kai a cikin gidansu. Peninnah kuma ta sha ba ta haushi a fili—hakika a gaban dangi da abokai—yayin da iyalin suke halartan biki a Shiloh. Wannan na kamar tura ƙayar ne sosai cikin jikin Hannatu.—1 Samu’ila 1:4-7.
17 Yi la’akari da abin da Dauda ya jimre wa domin kishin surukinsa, Sarki Saul. Don ya tsira, an tilasta wa Dauda ya zauna a cikin kogo a dajin En-gedi, inda ya hau duwatsu masu tsawo cike da haɗari. Rashin adalcin abin ba da haushi ne, domin bai yi wa Saul kome ba. Duk da haka, Dauda yana ta gudu—duka wannan domin kishin Saul.—1 Samu’ila 24:14, 15; Misalai 27:4.
18 Ka yi tunanin jayayya ta iyali da ta dami annabi Hosea. Matarsa ta zama mazinaciya. Lalatarta ta zama kamar ƙaya da ke cikin zuciyarsa. Ya ƙara baƙin ciki sa’ad da ta haifi yara biyu shegu daga faskancinta!—Hosea 1:2-9.
19. Wace tsanantawa ce ta same annabi Mikaiah?
19 Wata ƙaya cikin jiki ita ce tsanantawa. Ka yi la’akari da labarin annabi Mikaiah. Yana ganin mugun Sarki Ahab ya gewaye kansa da annabawan ƙarya kuma Ahab ya yarda da ƙaryarsu ya dami ran Mikaiah mai adalci. Sa’ad da Mikaiah ya gaya wa Ahab cewa duka waɗannan annabawa suna magana ta “maƙaryacin ruhu” ne, menene shugaban waɗannan masu maƙirci ya yi? Duba, ya “mari Mikaiah a kumatu”! Mafi muni ma abin da Ahab ya yi ne game da gargaɗin Jehovah cewa maido da Ramoth-gilead ba zai yi nasara ba. Ahab ya umurta cewa a jefa Mikaiah cikin kurkuku kuma a rage abincinsa. (1 Sarakuna 22:6, 9, 15-17, 23-28) Ka tuna kuma da yadda masu tsananta wa Irmiya suka bi da shi.—Irmiya 20:1-9.
20. Waɗanne ƙayoyi Naomi ta bukaci ta jimre, kuma yaya aka albarkace ta?
20 Rashin waɗanda muke ƙauna wani yanayi ne da ke iya zama kamar ƙaya a cikin jiki. Naomi ta jimre da rashin mijinta da ’ya’yanta biyu maza. Duk da irin matsalar nan ta dawo Bai’talami. Ta gaya wa ƙawayenta su kira ta, Mara, ba Naomi kuma ba domin sunan yana nufin wahalar da ta sha. Amma a ƙarshe, Jehovah ya albarkaci jimirinta da jika da ya zama daga layin Almasihu.—Ruth 1:3-5, 19-21; 4:13-17; Matta 1:1, 5.
21, 22. Yaya ne Ayuba ya sha hasara, kuma me ya yi?
21 Ka yi tunanin yadda Ayuba ya firgita da ya ji labarin mutuwar ’ya’yansa goma da yake ƙauna, ban da hasarar dukan dabbobi da bayinsa. Farat ɗaya, kamar duniya ta juya ne! Sai kuma, yayin da Ayuba yake kan makoki game da waɗannan, Shaiɗan ya harbe shi da ciwo. Wataƙila Ayuba ya yi tunanin cewa wannan mugun ciwo zai kashe shi. Azabar ta yi tsanani da har ya ga mutuwa samun sauƙi ne.—Ayuba 1:13-20; 2:7, 8.
22 Kamar dai wannan bai isa ba, matarsa, cikin baƙin ciki da azaba, ta zo wajensa kuma ce masa: “Ka la’anta Allah ka mutu!” Lalle wannan ƙaya ce cikin jikinsa da ke ciwo! Ban da haka, abokan Ayuba uku, maimakon su yi masa ta’aziyya, suka hukunta shi, suna tuhumarsa da yin zunubi a asirce da kuma ganin shi ke da alhakin masifar da ta same shi. Wannan hukunci na kuskure da suka yi masa, ya daɗa tura ƙayar ciki cikin jikinsa. Ka kuma tuna cewa, Ayuba bai san dalilin waɗannan masifu da suke faɗo masa ba; ba kuwa ya san ko za a ceci ransa ba. Amma, “a cikin wannan duka Ayuba ba ya yi zunubi ba, ba ya kuwa saɓi Allah ba.” (Ayuba 1:22; 2:9, 10; 3:3; 14:13; 30:17) Ko da yake ƙayoyi sun same shi bi da bi, bai fid da rai ba cikin tafarkinsa na aminci. Lalle yana da ban ƙarfafa!
23. Menene dalilin da ya sa amintattu da muka tattauna game da su suka iya jimre wa ƙayoyi dabam dabam cikin jikinsu?
23 Misalai da suke bayan nan babu shakka ba su ke nan kawai ba. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ƙarinsu. Dukan waɗannan bayi masu aminci suna bukatar su yi fama da nasu ƙaya ta alama. Kuma lalle suna da matsaloli dabam dabam da suke fuskanta! Duk da haka suna da abu iri ɗaya. Babu ɗaya cikinsu da ya daina bauta wa Jehovah. Duk da wahalarsu, sun yi nasara bisa Shaiɗan ta wurin ikon da Jehovah ya ba su. Ta yaya? Talifi na gaba zai amsa wannan tambayar kuma ya nuna mana yadda mu ma za mu iya jimre wa duk wani abin da ke kama da ƙaya cikin jikinmu.
[Hasiya]
a Irin wannan ƙulli na dogon buri ba za a zace shi daga mai godiya, mai tawali’u kamar Mephibosheth ba. Babu shakka ya san tarihi na aminci da babansa, Jonathan ya kafa. Ko da yake Jonathan ɗan Sarkin Saul ne, cikin tawali’u ya gane cewa Dauda ne Jehovah ya zaɓa ya zama sarki bisa Isra’ila. (1 Samu’ila 20:12-17) Da yake shi mahaifi ne mai jin tsoron Allah kuma abokin Dauda na ƙwarai, Jonathan ba zai koya wa ɗansa ya biɗa ikon sarauta ba.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa matsaloli da muke fuskanta za a kamanta su da ƙaya a cikin jiki?
• Waɗanne ne wasu ƙayoyi da Mephibosheth da Nehemiah suka jimre musu?
• Cikin misalai na Nassosi na maza da mata da suka jimre wa ƙayoyi dabam dabam cikin jiki, wanne ne ya motsa ka musamman, kuma me ya sa?
[Hotuna a shafi na 5]
Mephibosheth ya jimre wa naƙasarsa, tsegumin da aka yi masa, da kuma rashin cika alkawari
[Hoto a shafi na 6]
An ceci Nehemiah duk da hamayya