Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 3/1 pp. 8-12
  • Jimrewa Da “Ƙaya A Cikin Jiki”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Jimrewa Da “Ƙaya A Cikin Jiki”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Yadda Za a Jimre da Ƙaya
  • Ana Bukatar Tanadodi na Jehovah
  • Yadda Wasu Suka Jimre da Kyau
  • Jimiri Yana Kawo Farin Ciki
  • Sun Jimre Da Ƙaya Cikin Jikinsu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Abin da Ya Zama Kamar ‘Kaya a Jikin’ Bulus
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
  • Kasancewa Da Ƙarfi Sa’ad Da Aka Raunana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Jehobah Zai Karfafa Ka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 3/1 pp. 8-12

Jimrewa Da “Ƙaya A Cikin Jiki”

“Alherina ya ishe ka.”—2 KORINTHIYAWA 12:9.

1, 2. (a) Me ya sa ba za mu yi mamaki ba cewa muna fuskantar gwaji da matsaloli? (b) Me ya sa za mu kasance da gaba gaɗi duk da gwaji?

“DUKAN waɗanda su ke so su yi rai mai-ibada cikin Kristi Yesu za su sha tsanani.” (2 Timothawus 3:12) Me ya kawo haka? Saboda Shaiɗan ya yi jayayyar cewa mutane na bauta wa Allah domin son kai ne kawai, kuma ya dage ya tabbatar da wannan abin da ya ce. Yesu ya taɓa yi wa manzanninsa masu aminci gargaɗi: “Shaiɗan ya roƙa ya same ku, domin shi rairaye ku kamar alkama.” (Luka 22:31) Yesu ya sani sarai cewa Allah ya ƙyale Shaiɗan ya gwada mu ta wurin matsaloli masu ban ciwo. Amma, wannan ba ya nufin cewa dukan wahalar da muke fuskanta a rayuwa Shaiɗan ne kai tsaye ko aljannunsa ke jawowa. (Mai-Wa’azi 9:11) Amma Shaiɗan yana ɗokin ya yi amfani da duk zarafin da ya samu ya lalata amincinmu.

2 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa kada mu yi mamaki game da gwajin da sun same mu. Duk abin da ya same mu, ba baƙon abu ba ne ko kuma na babu shiri. (1 Bitrus 4:12) Hakika, “ ’yan’uwan[mu] da ke cikin duniya suna shan waɗannan azabai da ku ke sha.” (1 Bitrus 5:9) A yau, Shaiɗan yana sa matsi mai tsanani a kan kowanne bawan Allah. Iblis yana jin daɗin ya ga muna shan azaba da matsaloli da yawa da suke kama da ƙaya yadda ya yiwu. Domin haka, yana amfani da zamanin nan a hanyar da yake ƙara ko kuma tsananta duk wata ‘ƙaya da ke cikin jikinmu.’ (2 Korinthiyawa 12:7) Duk da haka, bai kamata farmakin Shaiɗan ya lalata amincinmu ba. Kamar yadda Jehovah ya yi “hanyar tsira” mana don mu jimre gwajin, zai yi hakanan yayin da muka fuskanci wahala da ke kama da ƙaya cikin jikinmu.—1 Korinthiyawa 10:13.

Yadda Za a Jimre da Ƙaya

3. Yaya Jehovah ya amsa yayin da Bulus ya ce ya cire masa ƙaya daga cikin jikinsa?

3 Manzo Bulus ya roƙi Allah ya cire masa ƙaya da ke cikin jikinsa. “Na yi roƙo ga Ubangiji so uku saboda wannan, a raba ni da shi.” Menene amsar Jehovah game da roƙon da Bulus ya yi mai ƙwazo? “Alherina ya ishe ka: gama cikin kumamanci ikona ya ke cika.” (2 Korinthiyawa 12:8, 9) Bari mu bincika wannan amsar kuma mu ga yadda za ta taimake mu mu jimre wa matsaloli da suke kama da ƙaya da ke gana mana azaba.

4. A waɗanne hanyoyi ne Bulus ya amfana daga alherin Jehovah?

4 Ka lura cewa Allah ya ƙarfafa Bulus ya yi godiya don alherin da aka nuna masa ta wurin Kristi. Hakika, an albarkaci Bulus a hanyoyi dabam dabam. Jehovah ya ba shi gatar zama almajiri, ko da dama shi mai hamayya da zafin hali ne a kan mabiyan Yesu, cikin ƙauna. (Ayukan Manzanni 7:58; 8:3; 9:1-4) Daga baya, Jehovah ya ba wa Bulus ayyuka da kuma gata masu girma. Darasin dominmu a bayyane yake. Ko a cikin lokatai mafi muni, har ila muna da albarka da za mu iya godiya dominsu. Kada gwajin da muke sha ya sa mu manta da yalwar nagarta ta Jehovah.—Zabura 31:19.

5, 6. (a) Ta yaya Jehovah ya koyar da Bulus cewa ikonsa ‘cikin kumamanci ya ke cika’? (b) Ta yaya misalin Bulus ya tabbatar da Shaiɗan maƙaryaci ne?

5 A wata hanya alherin Jehovah ya isa. Ikon Allah ya isa ƙwarai ya taimake mu cikin gwajin da muke sha. (Afisawa 3:20) Jehovah ya gaya wa Bulus cewa ikonsa ‘cikin kumamanci ya ke cika.’ Ta yaya? Cikin ƙauna ya yi wa Bulus tanadin iko da yake bukata don ya iya jimre wa gwajinsa. Da haka, jimirin Bulus da dogararsa ga Jehovah ya bayyana ga kowa cewa ikon Allah yana nasara a cikin wannan mutum mai kumamanci kuma mai zunubi. Yanzu, duba sakamakonsa a kan Iblis, da yake da’awar cewa mutane suna bauta wa Allah ne kaɗai domin moriya kuma domin ba sa wahala. Amincin Bulus ya zama kamar mari a fuskar wannan ɗan tsegumi!

6 Ga shi, Bulus abokin Shaiɗan ne dā a yaƙinsa da Allah, mai tsananta wa Kiristoci, Bafarisi mai ƙwazo, hakika ya more rayuwa domin daga iyali mai arziki ya fito. A yanzu Bulus yana bauta wa Jehovah da Kristi “autan manzanni.” (1 Korinthiyawa 15:9) Domin haka, cikin sauƙin kai yana biyayya ga ikon hukumar mulki na Kiristoci na ƙarni na farko. Kuma yana jimrewa cikin aminci duk da ƙaya da yake da shi cikin jiki. Ga fushin Shaiɗan, gwajin da ya same Bulus bai sa ƙwazonsa ya ragu ba. Bulus bai bauɗe daga begensa na cewa zai yi tarayya cikin Mulkin Kristi a samaniya ba. (2 Timothawus 2:12; 4:18) Babu wata ƙaya, ko yaya zafinta da za ta iya rage ƙwazonsa. Bari ƙwazonmu mu ma ya ci gaba da ƙarfi haka! Ta wurin ba mu ƙarfi mu jimre wa gwaji, Jehovah yana daraja mu da gatar tabbatar da Shaiɗan maƙaryaci ne.—Misalai 27:11.

Ana Bukatar Tanadodi na Jehovah

7, 8. (a) Ta wurin me Jehovah yake ba bayinsa ƙarfi a yau? (b) Me ya sa karanta Littafi Mai Tsarki kullum da nazarinsa yake da muhimmanci a jimre da ƙaya a cikin jikinmu?

7 A yau, Jehovah yana ba Kiristoci masu aminci ƙarfi ta wurin ruhu mai tsarki, Kalmarsa, da kuma ’yan’uwanci na Kirista. Kamar manzo Bulus, za mu iya zuba alhininmu ga Jehovah cikin addu’a. (Zabura 55:22) Ko da yake Allah ba zai kawar da gwajinmu ba, zai ba mu hikima da za mu iya jimre da su, har ma da waɗanda suke da wuyar jimrewa. Jehovah yana iya yi mana tanadin ƙarfi—yana ba mu “mafificin girman iko”—don ya taimake mu mu jimre.—2 Korinthiyawa 4:7.

8 Ta yaya muke samun taimakon nan? Dole ne mu yi nazarin Kalmar Allah ƙwarai, domin a cikinta za mu samu ta’aziyya. (Zabura 94:19) A cikin Littafi Mai Tsarki, mun karanta game da kalmomi masu motsawa na bayin Allah da suke roƙon taimakonsa. Amsar Jehovah, wadda take haɗawa da kalmomin ta’aziyya, abin bimbini ne. Yin nazari zai ƙarfafa mu saboda “mafificin girman iko ya kasance na Allah, ba daga wurin mu da kanmu ba.” Kamar yadda muke bukatar mu ci abinci kowacce rana don lafiya da ƙarfi, haka ma dole ne mu ci daga kalmomin Allah a kai a kai. Muna yin haka kuwa? Idan muna haka, za mu ga cewa samun “mafificin girman iko” ya taimake mu mu jimre wa duk wata ƙaya da ke ba mu azaba a yanzu.

9. Ta yaya dattawa za su toƙara wa waɗanda suke jimre wa matsaloli?

9 Dattawa Kiristoci masu tsoron Allah za su iya zama “maɓoya daga iska” ta wahala, “makāri kuma daga hadarin ruwa” na matsaloli. Dattawa da suke son su yi daidai da kwatancin nan za su biɗa cikin tawali’u da gaske kuma Jehovah ya ba su “harshe na koyayyun mutane” domin su san yadda za su amsa wa waɗanda suke shan wahala da kalmomin da suka dace. Kalmomin dattawan suna iya zama kamar ruwan sama da ke kawo sanyi kuma ke ta’azantarwa a lokatan wahala ta rayuwa. Ta wurin yin magana da “ƙarfafa [ga] masu-raunanan zukata,” dattawa da gaske suna toƙara wa ’yan’uwansu na ruhaniya da ƙila suke gajiya ko kuma suke yin sanyin gwiwa saboda wasu ƙayoyi cikin jikinsu.—Ishaya 32:2; 50:4; 1 Tassalunikawa 5:14.

10, 11. Ta yaya bayin Allah za su ƙarfafa wasu da suke shan gwaji mai tsanani?

10 Dukan bayin Jehovah suna cikin iyalinsa mai haɗin kai na Kirista. Hakika, mu “gaɓaɓuwa ne na junanmu,” kuma ya “kamata mu yi ƙaunar juna.” (Romawa 12:5; 1 Yohanna 4:11) Yaya muke cika wajibin nan? In ji 1 Bitrus 3:8, muna yin haka ta nuna “juyayi, kuna yin ƙauna kamar ’yan’uwa, [kuma kasancewa] masu-tabshin zuciya” ga waɗanda su ke cikin iyalin imani. Game da waɗanda suke jimrewa da ƙaya mai zafi ƙwarai cikin jiki, ko yara ko manya, dukanmu za mu iya nuna mun damu. Ta yaya?

11 Ya kamata mu yi ƙoƙarin nuna muna jin zafin wahalarsu. Idan ba ma damuwa, ba ruwanmu, ko kuma ba mu da marmari, cikin rashin sani, za mu iya daɗa munin yanayinsu. Idan mun san gwajinsu, zai motsa mu mu mai da hankali game da abin da za mu faɗa, yadda muka faɗe shi, da kuma yadda muke aikatawa. Idan muka kasance da hali mai kyau na ban ƙarfafa zai taimaka a rage wasu azaba da ƙayar ke yi musu. Da haka za mu iya zama abin ƙarfafa gare su.—Kolossiyawa 4:11.

Yadda Wasu Suka Jimre da Kyau

12-14. (a) Menene wata Kirista ta yi don ta jimre da ciwon daji? (b) Ta yaya ’yan’uwan matar nan na ruhaniya suka toƙara kuma ƙarfafa ta?

12 Yayin da muke kusa da ƙarshen waɗannan kwanaki, “wahala” na ƙaruwa kowacce rana. (Matta 24:8) Saboda haka, kusan kowa a duniya zai sha gwaji, musamman ma bayin Jehovah masu aminci, da suke biɗan yin nufinsa. Alal misali, wata Kirista da take hidimar cikakken lokaci. An ce tana da ciwon daji kuma aka ce za a yi mata aiki a cire abin da yake kawo yau da abin da ke jiƙe jijiyoyin jiki. Lokacin da maigidanta da ita suka san tana da irin ciwon nan, nan da nan suka juya wajen Jehovah ta doguwar addu’a. Ta faɗa daga baya cewa salama da ba su tsammani ba ta sauƙo kansu. Har ila, ta jimre wa azaba ƙwarai, musamman sakamakon aikin da aka yi mata.

13 Don ta iya bi da yanayin ta, ’yar’uwar ta yi ƙoƙari sosai ta ƙara koyo game da ciwon daji. Ta je wajen likitocinta. A cikin Hasumiyar Tsaro, Awake!, da kuma wasu littattafai na Kirista ta sami labaran mutane da suka jimre a motsin rai da irin wannan ciwon. Ta kuma karanta wasu wurare cikin Littafi Mai Tsarki da ke nuna iyawar Jehovah ya taimaki mutanensa a cikin wahala, da wasu abubuwan taimako.

14 Wani talifi a kan jimre da fid da rai ya ɗauko kalmomin nan na hikima: “Wanda ya ware kansa dabam, muradin kansa ya ke biɗa.” (Misalai 18:1) Saboda haka, talifin ya ba da wannan shawarar: “Ka tsayayya wa son ware kai.”a ’Yar’uwar ta ce: “Mutane da yawa sun gaya mini suna addu’a domina; wasu suna yi mini waya. Dattawa biyu suna zuwa a kai a kai su duba ni. An aika mini furanni da katin gaisuwa da yawa. Har wasu ma suna yin abinci. Kuma, mutane da yawa sun ba da kansu su kai ni wajen jinya.”

15-17. (a) Yaya wata Kirista ta jimre da wahalar da haɗarin mota ya jawo mata? (b) Wane taimako ne waɗanda suke cikin ikilisiya suka yi?

15 Wata da ta daɗe tana baiwar Jehovah a New Mexico, U.S.A., ta kasance cikin haɗarin mota sau biyu. Wuya da kuma kafaɗarta sun yi rauni, ya daɗa azabar ciwon gaɓaɓuwarta da take fama da shi na shekaru fiye da 25. Ta ce: “Ba na iya ɗaga kaina da kuma ɗaukan wani abu mai nauyi fiye da awo biyar. Amma sahihiyar addu’a ga Jehovah ta toƙara mini ƙwarai. Haka ma talifofin da muka yi nazarinsu daga cikin Hasumiyar Tsaro. Wani ya yi zance a kan Mikah 6:8, yana bayyana cewa yin tafiya tare da Allah cikin tawali’u yana nufin sanin iyakar gwargwadon abin da mutum zai iya yi. Wannan ya taimake ni na gane cewa duk da yanayi na, bai kamata na yi sanyin gwiwa ba, ko da ma lokacin da na yi cikin hidima bai kai wanda nake so ba. Bauta masa da zuciya mai kyau shi ne mafi muhimmanci.”

16 Ta kuma ce: “Koyaushe dattawan suna yaba mini don ƙoƙarina a halartar taro da kuma fita hidimar fage. Matasa suna runguma na. Majagaban masu hidima suna haƙuri da ni kuma sau da yawa sukan canja shirinsu don ranar da ban iya fita fage ba. Idan yanayin ranar ba shi da kyau, sukan je da ni wajen koma ziyara ko kuma ce na bi su wajen nazari da ɗalibansu na Littafi Mai Tsarki. Kuma tun da yake ba na iya ɗaukan jakar littattafai, wasu masu shela sukan saka nawa littattafan cikin jakarsu yayin da nake fagen aikin wa’azi.”

17 Yi la’akari da yadda dattawan ikilisiya da ’yan’uwa masu bi suka taimaki waɗannan ’yan’uwa mata biyu su jimre da ciwonsu mai kama da ƙaya. Sun yi taimako, na alheri don ya gamsar da bukata ta ruhaniya, na jiki, da kuma a jiye-jiye. Wannan bai motsa ka ka so ka ba da taimako ga wasu ’yan’uwa maza da mata da suke da matsaloli ba? Ku matasa ma za ku iya zama abin taimako ga waɗanda suke fama da ƙaya cikin jiki da suke ikilisiyarku.—Misalai 20:29.

18. Wace ƙarfafa za mu iya samu cikin labaran rayuwa da ke cikin jaridun Hasumiyar Tsaro da Awake!?

18 Jaridar Hasumiyar Tsaro da Awake! sun fito da labaran rayuwa da labaran Shaidu da suka jimre, kuma da har ila suke jimrewa da matsalolin rayuwa. Idan kana karanta irin talifofin nan, za ka gani cewa ’yan’uwanka maza da mata na ruhaniya a dukan duniya sun jimre wa wahalar tattalin arziki, rashin waɗanda suke ƙauna cikin bala’i, da kuma mummunar yanayin yaƙi. Wasu suna rayuwa da cuta da ke naƙasawa. Mutane da yawa ba sa iya yin wasu abubuwa masu sauƙi da wasu masu lafiya suke ɗauka da rashin muhimmanci ba. Ciwon da suke yi, gwaji ne mai tsanani, musamman idan ba su iya sa hannu a ayyukan Kirista ba yadda za su so yi. Hakika kuwa suna godiya ga taimako da toƙarawa da ’yan’uwansu maza da mata, yara da manya, suke ba su!

Jimiri Yana Kawo Farin Ciki

19. Me ya sa Bulus ya iya farin ciki duk da gwajin da ya sha da kumamanci masu kama da ƙaya?

19 Bulus ya yi farin ciki a ganin yadda Allah ya ƙarfafa shi. Ya ce: “Na gwammace . . . in yi fahariya cikin kumamancina, wannan kuwa da farinciki mai-yawa, domin ƙarfin Kristi shi inuwantarda ni. Domin haka fa ina jin daɗi cikin kumamanci, da ɓatanci, da damuwa, da tsanani, da fitinu, sabili da Kristi: gama sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.” (2 Korinthiyawa 12:9, 10) Saboda abin da ya same shi, Bulus ya iya faɗi da gaba gaɗi cewa: “Ban faɗi wannan domin ina bukatan wani abu ba: gama na rigaya na koya, zaman da ni ke ciki duka, raina ya kwanta da shi. Na iya ƙasƙanta, na kuwa iya yalwata: a cikin kowace matsala, a cikin dukan abu kuma, an fayace mini in saba da ƙoshi in saba da yunwa kuma, in yalwata in yi fatara kuma. Na iya yin abu duka a cikin wannan da ya ke ƙarfafata.”—Filibbiyawa 4:11-13.

20, 21. (a) Me ya sa za mu iya samun farin ciki a yin bimbini a kan al’amura “marasa-ganuwa”? (b) Menene wasu al’amura “marasa-ganuwa” da kake begen gani cikin Aljanna a duniya?

20 Saboda haka, ta jimre wa kowacce irin ƙaya ta alama cikin jikinmu, za mu iya samun farin ciki a nuna wa kowa cewa ikon Jehovah yana cika kumamancinmu. Bulus ya rubuta: “Ba mu yi yaushi ba . . . mutumi namu na fai yana lalacewa, mutumi namu na ciki yana sabontuwa yau da gobe. Gama ƙuncinmu mai-sauƙi, wanda ke na lokaci kaɗan, yana aika dominmu nauyin daraja madawwami gaba gaba ƙwarai; muna nan . . . mu lura da al’amuran . . . marasa-ganuwa: gama al’amuran . . . da ba su ganuwa madawwama ne.”—2 Korinthiyawa 4:16-18.

21 Yawancin mutanen Jehovah a yau suna da begen rayuwa cikin Aljanna ta duniyarsa kuma su mori albarka da ya yi alkawarinta. Irin albarkar nan za mu iya ɗaukansu “marasa-ganuwa” a gare mu a yau. Amma, lokaci yana jawo kusa kusa da za mu ga waɗannan albarka da idanunmu, hakika, mu more su har abada. Ɗaya cikin albarkar nan za ta zama na samun sauƙi daga rayuwa na wata irin matsala mai kama da ƙaya! Ɗan Allah zai “halaka ayyukan Shaiɗan” kuma ya “wofinta wanda yake da ikon mutuwa.”—1 Yohanna 3:8; Ibraniyawa 2:14.

22. Wane gaba gaɗi da ƙuduri ne ya kamata mu kasance da shi?

22 Saboda haka, kowacce irin ƙaya da take gana mana azaba cikin jikinmu a yau, bari mu ci gaba da jimrewa. Kamar Bulus, za mu sami ƙarfin yin haka ta wurin Jehovah, wanda yake ba mu ƙarfi. Yayin da muke zama cikin Aljanna a duniya, za mu yabi Jehovah Allah kowacce rana domin dukan ayyukansa masu girma.—Zabura 103:2.

[Hasiya]

a Duba talifin nan “Ra’ayin Littafi Mai Tsarki: Yadda Za Ka Jimre wa Fid da Rai,” a cikin Awake! fitar 8 ga Mayu, 2000 Turanci.

Yaya Za Ka Amsa?

• Me ya sa kuma ta yaya Iblis ya yi ƙoƙarin ya lalata amincin Kirista na gaskiya?

• Ta yaya ikon Jehovah ‘ke cika cikin kumamancinmu’?

• Ta yaya dattawa da kuma wasu za su ƙarfafa waɗanda suke shan azabar matsaloli?

[Hoto a shafi na 8]

Sau uku Bulus ya yi addu’a Allah ya cire ƙaya da ke cikin jikinsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba