Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w08 6/15 pp. 3-5
  • Kasancewa Da Ƙarfi Sa’ad Da Aka Raunana

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kasancewa Da Ƙarfi Sa’ad Da Aka Raunana
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Masuki Cikin Jiki’
  • Kasawa da ba a Sani Ba
  • Tabbaci Cewa Jehobah Zai yi Taimako
  • Taimako Don Magance Kasawa da ba a Sani Ba
  • Jimrewa Da “Ƙaya A Cikin Jiki”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Sa’ad da Ba Ni da Karfi Ne Nake da Karfi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Dattawa—Ku Ci-gaba da Yin Koyi da Manzo Bulus
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
  • Abin da Ya Zama Kamar ‘Kaya a Jikin’ Bulus
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
w08 6/15 pp. 3-5

Kasancewa Da Ƙarfi Sa’ad Da Aka Raunana

KASAWARKA za su iya su sha ƙarfinka. Za su manne maka kamar matsattsaku. Za ka ga kamar ba za ka taɓa magance wannan matsalar ba, ko ka ji kamar ka kasa, hakan zai sa ka gwada kanka da wasu ka ga kamar ba ka cancanta ba. Wataƙila kana fama da wata cuta da take shanye maka ƙarfi kuma tana hana ka jin daɗin rayuwa. Ko menene dalilin, za ka ji kamar babu hanyar magance matsalar. Za ka ji kamar Ayuba, sa’ad da ya ce wa Allah: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira, ka ɓoye ni har lokacinda fushinka ya wuce, ka sanya mini rana, sa’annan ka tuna da ni!”—Ayu. 14:13.

Yaya za ka magance wannan matsalar? Ko da yake hakan ba zai yi sauƙi ba, amma zai yi kyau ka daina tunanin matsalolinka na ɗan lokaci. Alal misali, ka yi la’akari da tambayar da Jehobah ya yi wa amintaccen bawansa Ayuba:“ “Ina ka ke sa’anda na sanya tussan duniya? Shaida dai, idan kana da fahimi. Wanene ya aiyana iyakarta, ko ka sani? Wanene ya miƙa igiyar aunawa a kanta?” (Ayu. 38:4, 5) Idan muka yi tunanin muhimmancin wannan tambayar, za mu fahimci mafificin hikima da kuma ikon Jehobah. Ya ƙyale yanayin wannan duniya ta ci gaba don dalili mai kyau.

‘Masuki Cikin Jiki’

Wani amintaccen bawa ya roƙi Jehobah ya cire masa ‘masuki a cikin jiki,’ wata cuta da ta ci gaba damunsa. Manzo Bulus ya roƙi Allah sau uku don ya cire masa wannan cutar. Ko ma wace irin cuta ce mai kama da masuki, ta hana Bulus farin ciki a hidimarsa ga Jehobah. Bulus ya kwatanta ta da mari da ake yi wa mutum koyaushe. Amsar Jehobah ita ce: “Alherina ya ishe ka: gama cikin kumamanci ikona ya ke cika.” Jehobah bai cire masa wannan cutar ba. Dole ne Bulus ya jimre cutar, amma ya ce: “Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.” (2 Kor. 12:7-10) Me yake nufi?

Matsalar Bulus ba ta ƙare nan da nan ba. Amma, ba ta hana shi cim ma abubuwa masu ban al’ajabi a hidimar Jehobah ba. Bulus ya dogara ga Jehobah don ya taimake shi kuma a koyaushe yana roƙon taimako. (Filib. 4:6, 7) A kusan ƙarshen rayuwarsa a duniya, Bulus ya ce: “Na yi yaƙi mai-kyau, na kure fagen, na kiyaye imani.”—2 Tim. 4:7.

Jehobah ya yi amfani da mutane ajizai don ya cim ma nufinsa duk da kasawarsu da matsalolinsu kuma ɗaukakar ta sa ce. Zai iya yi musu ja-gora da hikima don su jimre matsalolinsu kuma su ci gaba da yin farin ciki a hidimarsa. Hakika, yana iya yin amfani da mutane ajizai su yi aiki mai girma duk da kasawarsu.

Bulus ya faɗi abin da ya sa Allah bai cire masa masukin ba: “Domin kada in fiye ɗaukaka.” (2 Kor. 12:7) ‘Masukin’ Bulus ya tuna masa da kasawarsa kuma ya taimake shi ya ci gaba da kasancewa da tawali’u. Hakan ya yi daidai da abin da Yesu ya koyar: “Dukan wanda za ya ɗaukaka kansa za ya ƙasƙanta; dukan wanda ya ƙasƙantadda kansa kuwa za ya ɗaukaka.” (Mat. 23:12) Gwaji zai iya sa bayin Allah su zama masu tawali’u kuma ya taimake su su fahimci cewa suna bukatar su dogara ga Jehobah don su kasance da aminci. Kamar manzon, za su iya yin “fahariya cikin Ubangiji.”—1 Kor. 1:31.

Kasawa da ba a Sani Ba

Waɗansu suna da kasawa da ba su sani ba ko kuma sun ƙi su amince da su. Alal misali, mutum yana iya kasancewa da yawan gaba gaɗi, ya dogara da iyawarsa. (1 Kor. 10:12) Wani kasawa da mutane ajizai suke da shi, shi ne son a ɗauke su da muhimmanci.

Joab, wanda ya zama janar ɗin sojojin Sarki Dauda, mutumi ne mai gaba gaɗi, mai ɗaukan mataki, kuma yana iya magance matsaloli. Duk da haka, Joab ya yi wasu abubuwa da suka nuna cewa yana da girman kai kuma yana nuna son iko. Ya kashe janarori guda biyu. Na farko, ya ɗauki fansa ta wajen kashe Abner. Bayan haka, Joab ya yi kamar yana son ya gai da ɗan kawunsa Amasa, ya riƙe gemunsa da hannun dama kamar zai yi masa sumba sai ya kashe shi da takobi da ke hannun hagunsa. (2 Sam. 17:25; 20:8-10) Amasa ne ya maye gurbin Joab a matsayin janar shi ya sa ya yi amfani da zarafin ya kashe shi, wataƙila yana zaton cewa za a mai da shi ya zama janar. Ka ga cewa Joab bai iya kame kansa ba, har da burinsa na son kai. Ya aikata mugunta kuma bai yi nadama ba. A ƙarshen rayuwarsa Sarki Dauda ya umurci ɗansa Sulemanu ya tabbata cewa an kashe Joab don muguntarsa.—1 Sar. 2:5, 6, 29-35.

Kada mu yarda mugun tunani ya shiga zuciyarmu; za mu iya magance rauninmu. Da farko dole ne mu san kasawarmu kuma mu amince da su. Sai mu yi ƙoƙari don mu sha kansu. Za mu iya yin addu’a ga Jehobah kullum, mu roƙe shi ya taimake mu mu sha kan kasawarmu, kuma mu yi nazarin Kalmarsa, sa’ad da muke neman hanyoyin da za mu magance waɗannan kasawa. (Ibran. 4:12) Muna bukatar mu ci gaba da ƙoƙari don mu magance kasawarmu kuma kada mu yi sanyin gwiwa. Za mu ci gaba da wannan yaƙin don mu ajizai ne. Bulus ya amince da hakan game da kansa sa’ad da ya rubuta: “Abin da ni ke aikawa, ba shi ni ke nufin yi ba; amma abin da ni ke ƙinsa, shi ni ke aikawa.” Kamar yadda ka sani, Bulus bai faɗa wa kasawarsa ba, kamar yanayin ya fi ƙarfin sa. Maimakon haka, ya ci gaba da ƙoƙari don ya magance kasawarsa, ya dogara ga taimakon Allah ta wurin Yesu Kristi. (Rom. 7:15-25) Bulus ya kuma ce: “Ina dandaƙin jikina, ina kai shi cikin bauta: domin kada ya zama bayanda na yi ma waɗansu wa’azi, ni da kaina a yashe ni.”—1 Kor. 9:27.

Wasu mutane sukan nemi hujjar kasawarsu. Za mu iya kawar da hakan ta wajen kasancewa da ra’ayin Jehobah, kamar yadda Bulus ya aririce Kiristoci: “Ku yi ƙyamar abin da ke mugu; ku lizimci abin da ke nagari.” (Rom. 12:9) A ƙoƙarin da muke yi na sha kan kasawarmu, dole ne mu zama mutane masu gaskiya, masu nacewa, kuma mu yi wa kanmu horo. Dauda ya roƙi Jehobah: “Ka auna cikina da zuciyata.” (Zab. 26:2) Ya san cewa Allah zai iya sanin zuciyarmu kuma ya taimake mu a lokacin da muke bukata. Idan muka bi umurnin Jehobah da ke Kalmarsa da kuma ruhu mai tsarki, za mu iya ci gaba da samun nasara bisa kasawarmu.

Wasu suna damuwa da matsalolin da suke ganin ba za su iya magance su ba. Dattawan ikilisiya za su iya ba da taimako da kuma ƙarfafa. (Isha. 32:1, 2) Amma yana da kyau ka amince da wasu matsaloli. Saboda wasu matsaloli ba su da magani a wannan zamanin. Duk da haka, mutane da yawa sun koyi yadda za su jimre, kuma hakan ya taimake su su yi rayuwa mai gamsarwa.

Tabbaci Cewa Jehobah Zai yi Taimako

Kowace irin matsala ce muke fuskanta a wannan zamani mai wuya, mu tabbata cewa Jehobah zai kāre mu kuma ya kiyaye mu. Littafi Mai Tsarki ya aririce mu: “Ku ƙasƙantarda kanku fa ƙarƙashin hannu mai-iko na Allah, domin shi ɗaukaka ku loton da ya zama daidai; kuna zuba dukan alhininku a bisansa, domin yana kula da ku.”—1 Bit. 5:6, 7.

Sa’ad da Kathy, wadda take hidima a Bethel shekaru da yawa ta ji cewa maigidanta ya kamu da cutar Alzheimer, ba ta yi tsammanin cewa za ta iya jimre wahalar da wannan cutar take kawowa ba. Yin addu’a ga Jehobah don hikima da ƙarfin zuciya ya zama bukata na koyaushe. Sa’ad da yanayin maigidanta ya yi tsanani, ’yan’uwa maza sun bada lokacinsu su ilimantar da kansu game da yadda za a jimre da irin wannan cuta kuma ’yan’uwa mata sun ba da taimako. Waɗannan Kiristoci suna cikin waɗanda Jehobah ya yi amfani da su don ya ba da taimako na ƙarfafawa, kuma Kathy ta sami ƙarfin kula da maigidanta har ya mutu bayan shekara 11. Ta ce: “Na yi godiya sosai ga Jehobah don taimakonsa; ya sa na ci gaba da rayuwa. Ban yi zaton zan iya ci gaba da yin abubuwan da ake bukata a gare ni na dogon lokaci ba bayan da na raunana!”

Taimako Don Magance Kasawa da ba a Sani Ba

Sa’ad da mutane suka ji kamar ba su cancanta ba, sai su ga kamar Jehobah ba zai saurare su ba a lokacin da suke cikin matsala. Ya dace a yi la’akari da abin da Dauda ya ce sa’ad da ya yi nadama domin zunubin da ya yi da Bath-sheba: “Karyayyar zuciya mai-tuba ba za ka rena ta ba, ya Allah.” (Zab. 51:17) Dauda ya tuba da gaske, ya tabbata cewa zai iya yin addu’a kuma Allah zai gafarta masa. Yesu ma ya kasance da irin halin kula na Jehobah. Marubucin Linjila, Matta ya yi amfani da kalaman Ishaya ga Yesu: “Rarraunan kara ba za ya karye shi ba, lagwami mai-hayaƙi ba za ya ɓice shi ba.” (Mat. 12:20; Isha. 42:3) Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi juyayi ga naƙassasu da kuma tsiyayyu. Bai ƙarasa ran mutum da ke kama da lagwanin fitila da ya kusa ƙarewa ba. Maimakon haka, yana kula da naƙassasu, yana ba su ƙarfin jiki. Haka ya yi sa’ad da yake duniya. Ka gaskata cewa haka Yesu yake har yanzu kuma zai iya yin juyayi don kasawarka? Ka lura cewa Ibraniyawa 4:15 ta nuna cewa shi ne wanda yake “taɓuwa da tarayyar kumamancinmu.”

Sa’ad da yake rubutawa game da wannan “masuki cikin jiki,” Bulus ya lura cewa ƙarfin Kristi yana kama da ‘inuwa’ bisa kansa. (2 Kor. 12:7-9) Ya ji kāriyar Allah ta wurin Kristi, kamar yadda mutumin da yake cikin inuwa yake ji a lokacin da rana ta buɗe. Kamar Bulus, kada mu yi sanyin gwiwa don kasawarmu da matsalolin da muke fuskanta. Don mu ƙarfafa a ruhaniya, muna iya yin amfani da dukan abubuwan da Jehobah ya yi tanadin su ta wurin ikilisiyarsa ta duniya. Za mu iya yin iya ƙoƙarinmu kuma mu dogara ga Jehobah da tabbacin cewa zai ja-gorance mu. Fahimtar yadda Allah yake taimakonmu bisa kasawarmu, za mu iya cewa kamar Bulus: “Sa’anda ina rashin ƙarfi, sa’annan mai-ƙarfi ni ke.”—2 Kor. 12:10.

[Hoto a shafi na 3]

Bulus ya ci gaba da yin addu’a ga Jehobah ya taimake shi don ya cim ma hidimarsa

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba