Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 3/1 pp. 24-29
  • Gaskiya Da Tamani Take A Gare Ka Kuwa?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Gaskiya Da Tamani Take A Gare Ka Kuwa?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Halin Duniya Game da Gaskiya
  • Kiristoci da Duniya
  • Jehovah Yana Kula da Mu
  • Kula da Kanmu a Ruhaniya
  • Bin Ja-Gorar Allah na Kawo Farin Ciki
  • Kiristoci Suna Bauta Cikin Ruhu Da Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • Yin Koyi Da Allah Na Gaskiya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ku Ci Gaba da “Bin Gaskiya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 3/1 pp. 24-29

Gaskiya Da Tamani Take A Gare Ka Kuwa?

“Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.”—YOHANNA 8:32.

1. Yaya yadda Bilatus ya yi amfani da kalmar “gaskiya” ya bambanta da yadda Yesu ya yi amfani da ita?

“MENENE gaskiya?” Sa’ad da Bilatus ya yi wannan tambayar, abin da yake so ya sani, yadda yake, game da gaskiya ne galibi. Yesu, a wani ɓangare kuma ba da jimawa ba, ya ce: “Domin wannan an haife ni, domin wannan kuma na zo cikin duniya, domin in bada shaida ga gaskiya.” (Yohanna 18:37, 38) Ba kamar Bilatus ba, Yesu yana maganar gaskiyar Allah da take da muhimmanci.

Halin Duniya Game da Gaskiya

2. Wane furci Yesu ya yi da ya nuna amfanin gaskiya?

2 Bulus ya ce: “Ba duka ke da imani ba.” (2 Tassalunikawa 3:2) Abu ɗaya ne ma da gaskiya. Ko ma lokacin da aka ba su zarafi su san gaskiya da ke bisa Littafi Mai Tsarki, mutane da yawa da gangan suna banza da ita. Amma tana da tamani! Yesu ya ce: “Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.”—Yohanna 8:32.

3. Wane gargaɗi ne game da koyarwa ta ruɗu ya kamata mu yi biyayya da shi?

3 Manzo Bulus ya ce ba za a samu gaskiyar cikin falsafa da al’adu na mutane ba. (Kolossiyawa 2:8) Hakika, irin wannan koyarwar ruɗu ce. Bulus ya gargaɗi Kiristocin Afisawa cewa idan sun ba da gaskiya gare su, za su zama kamar yara na ruhaniya da ake “wofadda su . . . ga kowace iskan sanarwa, ta wurin wawa[n]-idon mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.” (Afisawa 4:14) A yau, waɗanda suke hamayyar gaskiya daga Allah ne suke gabatar da ra’ayi na “wawa[n]-idon mutane.” The New Encyclopædia Britannica ya ba da ma’anar “baza ra’ayi” hanyar rinjayar imanin mutane, halaye, ko kuma ayyukansu da wayo.” Irin wannan ra’ayi da ruɗu na juya gaskiya zuwa ƙarya kuma ya gabatar da ƙarya wai gaskiya ce. Don mu samu gaskiya a irin wannan dabara na matsi, dole mu bincika Nassosi sosai.

Kiristoci da Duniya

4. Su wanene aka ba gaskiyar, menene hakkin waɗanda suka karɓe ta?

4 Da yake maganar waɗanda suka zama almajiransa, Yesu Kristi ya yi wa Jehovah addu’a: “Ka tsarkake su cikin gaskiya: maganarka ita ce gaskiya.” (Yohanna 17:17) Za a tsarkaka irin waɗannan mutane, a ware su, don su bauta wa Jehovah su sanar da sunansa da kuma Mulkinsa. (Matta 6:9, 10; 24:14) Ko da ba dukan mutane ba ke da ita, gaskiyar Jehovah kyauta ce ga dukan waɗanda suka neme ta, ko a ina ne ƙasarsu, ƙabila, ko al’adarsu. Manzo Bitrus ya ce: “Na gane Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.”—Ayukan Manzanni 10:34, 35.

5. Sau da yawa, me ya sa ake tsananta wa Kiristoci?

5 Kiristoci suna gaya wa wasu gaskiya daga Littafi Mai Tsarki amma ba ko’ina ba ne ake yi musu maraba. Yesu ya yi gargaɗi: “Za su miƙa ku ga ƙunci, za su kashe ku kuma: za ku zama abin ƙi ga dukan al’ummai sabili da sunana.” (Matta 24:9) Da yake magana a kan wannan ayar, limamin Ireland, John R. Cotter ya rubuta a shekara ta 1817: “[Kiristocinsu] suna ƙoƙari su gyara rayuwar mutane ta wa’azinsu, maimako ya sa mutane godiya, yana sa su ƙiyayya kuma su tsananta wa almajiran don suna fallasa muguntarsu.” Irin waɗannan masu tsanantawa ba sa “karɓan ƙaunar gaskiya don a cece su.” Domin wannan, “Allah yana aike musu da aikawar saɓo, har da za su gaskata ƙarya: domin a hukunta shari’a bisa dukan waɗanda ba su gaskata gaskiya ba, amma suka ji daɗin rashin adalci.”—2 Tassalunikawa 2:10-12.

6. Waɗanne sha’awoyi ya kamata Kirista ya gina?

6 Manzo Yohanna ya gargaɗi Kiristoci da suke zama a wannan duniya ta ƙiyayya: “Kada ku yi ƙaunar duniya, ko abubuwan da ke cikin duniya. . . . Dukan abin da ke cikin duniya, da kwaɗayin jiki, da sha’awar idanu, da darajar rai ta wofi, ba na Uba ba ne, amma na duniya ne.” (1 Yohanna 2:15, 16) Da ya ce “dukan,” Yohanna bai bar kome ba. Domin wannan kada mu gina sha’awar kome da duniyar nan za ta bayar da zai janye mu daga gaskiya. Yin biyayyar da gargaɗin Yohanna tasiri ne mai girma a rayuwarmu. Ta yaya?

7. Ta yaya sanin gaskiya ke motsa masu zukatan kirki?

7 A shekara ta 2001, Shaidun Jehovah a duka duniya sun gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki na gida fiye da miliyan huɗu da rabi kowane wata, suna koyar wa mutane ɗaɗɗaya da kuma a rukuni farillan Allah na rayuwa. A sakamakon haka an yi wa mutane 263,431 baftisma. Hasken gaskiya ya zama da tamani ga waɗannan sababbin almajiran, sun ƙi zama da miyagu da hanyoyin lalata da ba sa daraja Allah, da ke ko’ina a wannan duniya. Tun da sun yi baftisma, sun ci gaba da rayuwa daidai da mizanan da Jehovah ya kafa don duka Kiristoci. (Afisawa 5:5) Gaskiya tana da tamani a gare ka kuwa?

Jehovah Yana Kula da Mu

8. Ta yaya Jehovah yake amsa keɓe kanmu, me ya sa hikima ce mu ‘biɗi mulkin da farko’?

8 Duk da ajizancinmu, Jehovah da jinƙai ya karɓi keɓe kanmu, a alamance, yana sunkuyowa, ya jawo mu. A haka yana koya mana mu ɗaukaka muradinmu da sha’awoyinmu. (Zabura 113:6-8) Duk da haka, Jehovah yana barinmu mu kasance da nasaba da shi, kuma ya yi alkawari zai kula da mu idan mun ‘biɗi mulkinsa, da adalcinsa da farko.’ Idan mun yi haka kuma muka kiyaye kanmu a ruhaniya, ya yi alkawari: “Waɗannan abu duka fa za a ƙara muku su.”—Matta 6:33.

9. Wanene “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” kuma ta wajen amfani da wannan “bawan” yaya Jehovah yake kula da mu?

9 Yesu Kristi ya zaɓi manzaninsa 12 kuma ya kafa tushe na ikilisiyar shafaffu Kiristoci da aka san su da “Isra’ila na Allah.” (Galatiyawa 6:16; Ru’ya ta Yohanna 21:9, 14) Daga baya aka kwatanta wannan “ikilisiyar Allah mai-rai ke nan, jigon gaskiya da ƙarfinta.” (1 Timothawus 3:15) Yesu ya nuna waɗanda suke cikin ikilisiyar cewa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma “wakili mai-aminci, mai-azanci.” Yesu ya ce wannan bawa mai aminci ne ke da hakkin ba wa Kiristoci “abincinsu a lotonsa.” (Matta 24:3, 45-47; Luka 12:42) In ba abinci za mu mutu. Hakanan ma, in ba tare da cin abinci na ruhaniya ba, za mu raunana kuma mu mutu a ruhaniya. Saboda haka, kasancewar “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” wani tabbaci ne cewa Jehovah yana kula da mu. Bari koyaushe muna godiya ga tanadi na ruhaniya mai tamani da ake mana ta wurin wannan “bawan.”—Matta 5:3.

10. Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance a taronmu a kai a kai?

10 Cin abinci na ruhaniya ya ƙunshi nazari da kanmu. Ya kuma ƙunshi yin tarayya da wasu Kiristoci da halartar taron Kirista. Ka tuna abin da ka ci watanni shida da sun shige, ko ma makonni shida da sun shige? A’a. Har ila, ko menene ka ci zai ba ka abin da ka ke bukata don ya kiyaye ka. Kuma wataƙila ka sake cin irin abincin nan. Haka yake game da abinci na ruhaniya da ake tanadinsa a taronmu na Kirista. Wataƙila ba ma tuna da bayani dalla-dalla da muka ji a taro. Kuma an ba da irin bayanin nan fiye da sau ɗaya. Har ila, abinci na ruhaniya ne, yana da muhimmanci don zaman lafiyarmu. Taronmu koyaushe na tanadin abu mai kyau na ruhaniya da ke gyara, da ake ba da a lokaci da ya dace.

11. Wane hakki muke da shi sa’ad da muke halartar taron Kirista?

11 Halartar taron Kirista ya ɗora hakki a kanmu. An gargaɗi Kiristoci su ‘ƙarfafa juna,’ su motsa ’yan’uwa da suke ikilisiya tare zuwa “ƙauna da nagargarun ayyuka.” Shiri, halarta, da yin furci a duka taron Kirista na ƙarfafa bangaskiyarmu ɗai-ɗai kuma su ƙarfafa wasu. (Ibraniyawa 10:23-25) Kamar yara da suke zaɓan abinci, wasu ƙila za su bukaci ƙarfafa a kai a kai don su ci abinci na ruhaniya. (Afisawa 4:13) Yana da kyau a ba da ƙarfafa sa’ad da ake bukata don irin waɗannan su yi girma zuwa Kiristoci da suka manyanta, waɗanda manzo Bulus ya rubuta game da su: “Abinci mai-ƙarfi domin isassun mutane ne, watau waɗanda suna da hankulansu wasassu bisa ga aikaceya garin rabewar nagarta da mugunta.”—Ibraniyawa 5:14.

Kula da Kanmu a Ruhaniya

12. Wanene yake da hakki na musamman mu kasance cikin gaskiya? Ka ba da bayani.

12 Abokan aurenmu ko iyayenmu za su iya ƙarfafa mu a hanyar gaskiya. Hakanan ma, dattawan ikilisiya za su iya kiwon mu da yake muna cikin garken da suke kula da shi. (Ayukan Manzanni 20:28) Amma wa yake da hakki na musamman idan za mu nace a hanya ta rayuwa bisa gaskiya? Hakika, hakkin yana kan kowannenmu. Wannan haka yake, ko a yanayi mai kyau ko a lokatan wahala. Yi la’akari da labari na gaba.

13, 14. Yadda aka kwatanta da labarin ɗan rago, ta yaya za mu samu taimako na ruhaniya da ake bukata?

13 A Scotland wasu ’yan tumaki suna kiwo sai ɗaya ya fanɗare zuwa kan dutse ya faɗa cikin rami. Bai yi rauni ba, amma ya firgita kuma bai iya koma baya ba. Sai ya soma kuka. Mamarsa ta ji, ita ma ta soma kuka har sai da makiyayin ya zo ya cire ɗan ragon.

14 Ka lura da yadda abin ya faru bi da bi. Ɗan ragon ya yi kuka don taimako, mamar ta daɗa nata muryar, kuma makiyayin da ke a farke ya aikata nan da nan ya cece shi. Idan ɗan dabba da mamarsa sun gane cewa akwai haɗari kuma nan da nan suka nemi taimako, bai kamata mu yi hakan ba sa’ad da muka yi tuntuɓe a ruhaniya ko kuma muka fuskanci haɗari da ba mu yi tsammaninsa ba daga duniyar Shaiɗan? (Yaƙub 5:14, 15; 1 Bitrus 5:8) Ya kamata, musamman idan ba mu manyanta ba ko kuma domin mu sababbi ne cikin gaskiya.

Bin Ja-Gorar Allah na Kawo Farin Ciki

15. Yaya wata mata ta ji sa’ad da ta soma cuɗanya da ikilisiyar Kirista?

15 Ka yi la’akari da amfanin fahimtar Littafi Mai Tsarki da kuma kwanciyar rai da yake kawowa ga waɗanda suke bauta wa Allah na gaskiya. Wata mace mai shekara 70 da take zuwa Cocin Ingila dukan rayuwarta ta yarda Mashaidiyar Jehovah ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ita. Ba da jimawa ba ta koyi cewa sunan Allah Jehovah ne kuma ta amsa “Amin” ga addu’o’in da aka yi a Majami’ar Mulki. Da sosawar zuciya ta ce: “Maimakon nuna cewa Allah na da nisa sosai daga gare mu ’yan Adam ajizai, kuna kawo shi tsakaninmu kamar wani aboki ƙaunacacce. Abu ne da ban taɓa gani ba.” Mai yiwuwa, wannan matar ba za ta taɓa manta yadda gaskiya ta taɓa ta da farko ba. Bari mu ma, kada mu manta yadda gaskiyar take da tamani a gare mu sa’ad da muka karɓe ta da farko.

16. (a) Me zai iya faruwa idan muka sa samun kuɗi makasudinmu na farko? (b) Ta yaya za mu samu farin ciki na gaske?

16 Mutane da yawa suna jin cewa idan suna da kuɗi za su fi farin ciki. Amma, idan mun sa neman kuɗi makasudi na farko a rayuwa, za mu jawo wa kanmu “baƙinciki mai-yawa.” (1 Timothawus 6:10) Ka yi tunani mutane nawa suke sayan tikiti na caca, ƙona kuɗi a gidajen caca, ko kuma mutane da suke damun kansu da son sanin ribar da ƙungiyar kasuwanci za ta kawo, mafarkin samun sa’ar kuɗi masu yawa. Mutane kalilan ne kawai suke samun kuɗi da suka yi fatansu. Sau da yawa waɗanda suke samu ma suna gani cewa arzikinsu ba ya kawo farin ciki. Maimako, farin ciki mai daɗewa na zuwa daga yin nufin Jehovah, yin aiki da ikilisiyar Kirista da ja-gorar ruhun mai tsarki na Jehovah da taimakon mala’ikunsa. (Zabura 1:1-3; 84:4, 5; 89:15) Yayin da muka yi haka, za mu iya samun albarka da ba mu yi tsammaninsa ba. Gaskiyar tana da tamani a gare ka ta kawo irin wannan albarka cikin rayuwarka?

17. Menene zaman Bitrus da Siman majemi, ya bayyana game da halin manzon?

17 Ka yi la’akari da abin da manzo Bitrus ya fuskanta. A shekara ta 36 A.Z., ya yi tafiyar wa’azi a Filin Sharon. Ya tsaya a Ludda, inda ya warkar da Iniyasu mai shan inna sai ya ci gaba zuwa bakin teku inda jirage ke sauka a Yafa. A wurin ya tashi Dokas daga matattu. Ayukan Manzanni 9:43 ta gaya mana: “Sai ya zauna kwanaki dayawa cikin Yafa tare da wani majemi, sunansa Siman.” Wannan bincike ya nuna halin rashin wariya na Bitrus yayin da yake hidima ga mutane a wannan birnin. Ta yaya? Manazarin Littafi Mai Tsarki Frederic W. Farrar ya rubuta: “Ba mai bin Dokar Baka ta [Musa] da zai iya zama a gidan majemi. Taɓa fata da gawayen dabbobi dabam dabam da ake amfani da su a wannan kasuwanci, da kayayyaki da yake bukata, ya sa ba shi da tsarki kuma da ban ƙyama a idanun wanda ya nace wa doka.” Ko idan ma Siman da “gidansa yana bakin teku” ba ya kusa da wurin jimansa, Siman yana ‘kasuwanci da ake ƙyama da yake rage darajar duk wanda yake yin sa,’ in ji Farrar.—Ayukan Manzanni 10:6.

18, 19. (a) Me ya sa Bitrus ya yi mamakin wahayi da ya samu? (b) Wace albarka ce da Bitrus bai yi tsammaninta ba ta zo masa?

18 Bitrus da ba ya nuna wariya ya amince da halin marhabin na Siman, kuma a wurin Bitrus ya samu ja-gora daga Allah da bai yi tsammaninsa ba. Ya ga wahayi da aka umurce shi ya ci halittu da ba su da tsabta bisa ga dokar Yahudawa. Bitrus ya ƙi cewa bai “taɓa cin wani abu haram ko mai-ƙazanta ba.” Amma sau uku aka ce ya daina cewa da: “Abin da Allah ya tsarkake, kada kai ka maishe shi haram.” A bayyane, “Bitrus yana cikin dɗimuwa a ransa dayawa, yana shakkan azancin ru’ya wadda ya gani.”—Ayukan Manzanni 10:5-17; 11:7-10.

19 Bitrus bai sani ba cewa washegari a Kaisariya, nisan mil 30, ɗan Al’umma Karniliyus ya samu wahayi. Mala’ikan Jehovah ya shawarci Karniliyus ya aika bayi su nemi Bitrus a gidan Siman majemi. Karniliyus ya aiki bayinsa zuwa gidan Siman, Bitrus ya bi su zuwa Kaisariya. A wurin ya yi wa Karniliyus da danginsa da abokansa wa’azi. Sakamakon haka, suka zama na Al’umma na farko da ba a yi musu kaciya ba da suka zama masu bi suka samu ruhu mai tsarki su zama magadan Mulki. Ko da ba a yi wa mutanen kaciya ba, duka waɗanda suka saurari maganar Bitrus an yi musu baftisma. Wannan ya buɗe hanya ga mutane na dukan al’ummai, da aka ɗauka ba su da tsabta a ra’ayin Yahudawa, su zama waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista. (Ayukan Manzanni 10:1-48; 11:18) Wannan gata ce ta musamman ga Bitrus—duka domin gaskiya na da tamani a gare shi ne kuma ta sa shi ya yi biyayya ga ja-gora daga Jehovah kuma ya yi aiki cikin bangaskiya!

20. Wane taimako aka ba mu daga Allah yayin da muka saka gaskiya da farko a rayuwarmu?

20 Bulus ya yi gargaɗi: “Garin faɗin gaskiya cikin ƙauna, mu yi girma cikin abu duka zuwa cikinsa, wanda shi ne kai, watau Kristi.” (Afisawa 4:15; Tafiyar tsutsa tamu ce.) Hakika, gaskiya za ta kawo mana farin ciki yanzu idan mun saka ta na farko a rayuwarmu kuma muka bar Jehovah ta ruhunsa mai tsarki ya ja-goranci tafiyarmu. Ka tuna da goyon bayan mala’iku a aikinmu na wa’azi. (Ru’ya ta Yohanna 14:6, 7; 22:6) Gata ce muke da ita mu samu irin wannan goyon baya a aikin da Jehovah ya ce mu yi! Riƙe amincinmu zai sa mu yabi Jehovah, Allah na gaskiya, har abada. Akwai abin da zai fi wannan tamani ne?—Yohanna 17:3.

Me Muka Koya?

• Me ya sa mutane da yawa ba sa karɓan gaskiya?

• Yaya Kiristoci ya kamata su ɗauki abin duniyar Shaiɗan?

• Yaya za mu ɗauki taro, kuma me ya sa?

• Wane hakki muke da shi mu kula da kanmu a ruhaniya?

[Box/Hoto a shafi na 29]

BABBAR TEKU

FILIN SHARON

Kaisariya

Yafa

Ludda

Urushalima

[Picture]

Bitrus ya bi ja-gora daga Allah kuma ya samu albarka da bai yi tsammaninta ba

[Inda aka Dauko]

Taswira: Mountain High Maps® Copyright © 1997 Digital Wisdom, Inc.

[Hoto a shafi na 24]

Yesu ya ba da shaida ga gaskiya

[Hoto a shafi na 26]

Kamar abinci na zahiri, abinci na ruhaniya na da muhimmanci don zaman lafiyarmu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba