Yin Koyi Da Allah Na Gaskiya
“Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.”—AFISAWA 5:1.
1. Menene wasu suka gaskata game da gaskiya, kuma me ya sa tunaninsu ba daidai ba ne?
“MENENE gaskiya?” (Yohanna 18:38) Bilatus Babunti kusan shekaru 2,000 da suka shige ya yi wannan tambayar cikin rashin gaskatawa, da yake nufi yana da wuya a biɗi gaskiya. Mutane da yawa a yau ma za su yarda haka. Ana wa gaskiya farmaki. Wataƙila ka taɓa ji ana ce kowa ke da nasa gaskiya, ko kuma gaskiya ba cikakkiya ba ce, ko kuma gaskiya sai canzawa take. Irin wannan tunanin ba daidai ba ne. Ainihin dalilin bincike da ilimi shi ne a koyi lazu, gaskiya, game da duniya da muke zama ciki. Gaskiya ba ra’ayin kan mutum ba ne. Alal misali, ko a ce kurwa ba ta mutuwa ko tana mutuwa. Ko a ce Shaiɗan yana wanzuwa ko kuma ba ya wanzuwa. Ko a ce rayuwa tana da ma’ana ko kuma babu. A kowanne, ɗaya ne kawai zai zama gaskiya. Ɗaya gaskiya ce, ɗayan kuma ƙarya; su biyun ba za su zama gaskiya ba.
2. A waɗanne hanyoyi ne Jehovah Allah na gaskiya ne, kuma waɗanne tambayoyi ne za a tattauna?
2 A cikin talifi na baya, mun yi la’akari da cewa Jehovah Allah ne na gaskiya. Ya san gaskiya game da kome. Dabam da magabcinsa mai ruɗi, Shaiɗan Iblis, Jehovah kullum mai gaskiya ne. Ballantana ma, Jehovah yana bayyana gaskiya ga wasu a yalwace. Manzo Bulus ya aririci ’yan’uwa Kiristoci: “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu.” (Afisawa 5:1) Da yake mu Shaidun Jehovah ne, ta yaya za mu yi koyi da shi a faɗin gaskiya kuma yi rayuwa ta gaskiya? Me ya sa yake da muhimmanci a yi hakan? Kuma wane tabbaci muke da shi cewa Jehovah yana amince da waɗanda suke biɗan gaskiya? Bari mu gani.
3, 4. Yaya manzanni Bulus da Bitrus suka kwatanta abin da zai faru a “kwanaki na ƙarshe”?
3 Muna zama a zamani da ake da ƙaryar addini da yawa. Kamar yadda manzo Bulus ya annabta ta wurin hurewar Allah, mutane da yawa cikin waɗannan “kwanaki na ƙarshe” suna da halin ibada amma suna saɓa wa ikonta. Wasu suna tsayayya da gaskiya, domin “ɓātattu ne cikin azancinsu.” Ban da haka, “miyagun mutane da masu-hila . . . [suna] daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” Ko da yake irin waɗannan mutane suna koyo kullum amma ba su “ruski sanin gaskiya daɗai ba.”—2 Timothawus 3:1, 5, 7, 8, 13.
4 An kuma hure manzo Bitrus ya rubuta game da kwanaki na ƙarshe. Daidai yadda ya annabta, ba kawai mutane sun ƙi gaskiya ba amma kuma sun yi wa Kalmar Allah ba’a da kuma waɗanda suke shelar gaskiyarta. “Da gangar,” masu ba’ar nan suke banza da gaskiyar cewa an yi rigyawa a kwanan Nuhu, wannan tana kafa tafarki don hukunci na nan gaba. Abin da suke wasiƙar jakinsa zai nufi bala’i gare su sa’ad da lokacin Allah ya kai ya halaka marasa ibada.—2 Bitrus 3:3-7.
Bayin Jehovah Sun San Gaskiya
5. In ji annabi Daniel, me zai faru a “kwanaki na ƙarshe,” ta yaya annabcin nan yake cika?
5 A wani kwatanci na “kwanaki na ƙarshe,” annabi Daniel ya yi annabcin wata aukuwa da ke dabam tsakanin mutanen Allah—maido da gaskiyar addini. Ya rubuta: “Mutane dayawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru.” (Daniel 12:4) Babban Mai Ruɗu bai ɗimauce ko kuma makantar da mutanen Jehovah ba. Suna kai da kawowa cikin shafofin Littafi Mai Tsarki, ta haka sun samu sani na gaskiya. A ƙarni na farko, Yesu ya wayar da almajiransa. Ya “buɗe hankalinsu, domin su fahimci littattafai.” (Luka 24:45) A zamaninmu ma, Jehovah ya yi makamancin haka. Ta wurin Kalmarsa, ruhunsa, da kuma ƙungiyarsa, ya taimaki miliyoyi a duk duniya su fahimci abin da ya riga ya sani—gaskiya.
6. Waɗanne gaskiyar Littafi Mai Tsarki mutanen Allah a yau suka fahimta?
6 Domin mu mutanen Allah ne, mun fahimta abubuwa da yawa da ba za mu taɓa sani ba. Mun san amsoshin tambayoyi da masu hikimar duniya suke ta kokawa da su na dubban shekaru. Alal misali, mun san dalilin da ya sa ake wahala, abin da ya sa mutane suke mutuwa, kuma abin da ya sa mutane ba za su iya samun salama da haɗin kan dukan duniya ba. An kuma albarkace mu da wahayin abin da nan gaba ke ɗauke da shi—Mulkin Allah, aljanna ta duniya, da kuma kamiltaccen rayuwa marar matuƙa. Mun sami sanin Jehovah, Mafifici. Mun koya game da halinsa mai kyau tare da abin da dole mu yi domin mu more albarkarsa. Sanin gaskiya ya taimake mu mu fahimci abin da ba gaskiya ba. Yin amfani da gaskiya na kāre mu daga biɗe-biɗan banza, tana taimakonmu mu samu abu mafi kyau a rayuwa, kuma tana ba mu bege mai girma na nan gaba.
7. Su wa ke iya samun gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma su wa ba sa iya samu?
7 Ka fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki kuwa? Idan haka ne, ka sami albarka mai yawa. Idan wani mawallafi ya rubuta littafi, ita ko shi yakan sa ya zama da ban sha’awa ga wasu rukunin mutane. Wasu littattafai an rubuta su domin masu ilimi sosai, wasu domin yara, har ila kuma wasu domin wata fasaha na musamman. Ko da yake yana da sauƙi kowa ya sami Littafi Mai Tsarki, an yi shi domin wani rukuni musamman su fahimta kuma su more shi. Jehovah ya yi shi domin marasa girman kai, masu tawali’u na duniya. Irin waɗannan mutanen za su iya fahimtar Littafi Mai Tsarki, ko da yaya iliminsu, al’ada, da kuma matsayi a rayuwa, ko kuma ƙabila. (1 Timothawus 2:3, 4) A wata sassa kuma, an hana waɗanda ba su da zuciyar kirki fahimtar gaskiyar Littafi Mai Tsarki, ko yaya basirarsu ko iliminsu yake. Masu kumburi, masu girman kai, ba za su iya fahimtar gaskiya mai tamani na Kalmar Allah ba. (Matta 13:11-15; Luka 10:21; Ayukan Manzanni 13:48) Allah ne kaɗai zai iya fito da irin littafin nan.
Bayin Jehovah Suna da Gaskiya
8. Me ya sa Yesu kansa gaskiya ne?
8 Kamar Jehovah, Shaidunsa amintattu suna da gaskiya. Yesu Kristi, Mashaidi na farko na Jehovah, ya tabbatar da gaskiya ta wurin abubuwan da ya koyar kuma ta yadda ya rayu kuma mutu. Ya ɗaukaka gaskiyar maganar Jehovah da alkawuransa. Haka nan kuma, Yesu kansa gaskiya ne, yadda ya faɗi.—Yohanna 14:6; Ru’ya ta Yohanna 3:14; 19:10.
9. Menene Nassosi suka ce game da faɗin gaskiya?
9 Yesu yana “cike da alheri da gaskiya” kuma “ba kuwa ƙarya a bakinsa ba.” (Yohanna 1:14; Ishaya 53:9) Kiristoci na gaskiya suna bin tafarkin da Yesu ya kafa ta yi wa mutane gaskiya. Bulus ya gargaɗar da ’yan’uwa masu bi: “Ku faɗi gaskiya kowane game da ɗan’uwansa . . . mu gaɓaɓuwa ne na junanmu.” (Afisawa 4:25) Da farko, annabi Zechariah ya rubuta: “Mutum shi faɗi gaskiya ga maƙwabcinsa.” (Zechariah 8:16) Kiristoci suna gaskiya domin suna son su faranta wa Allah zuciya. Jehovah mai gaskiya ne kuma ya san lahani da ke cikin ƙarya. Saboda haka, ya dace ya biɗi bayinsa su faɗi gaskiya.
10. Me ya sa mutane suke ƙarya, kuma da wane mummunar sakamako?
10 A wajen mutane da yawa, yin ƙarya abin da zai kawo musu wata albarka ne. Mutane suna ƙarya don kada a yi musu horo, domin su sami wani riba, ko kuma wasu su yaba musu. Duk da haka, yin ƙarya laifi ne. Ballantana ma, maƙaryaci ba zai sami tagomashin Allah ba. (Ru’ya ta Yohanna 21:8, 27; 22:15) Idan an san mu da faɗan gaskiya, wasu za su gaskata abin da muka ce; za su tabbata da mu. Amma kuma, idan aka iske mun yi ƙarya ko sau ɗaya ne, zai yi wuya wasu su gaskata duk kome da muka faɗa a nan gaba. Wata karin magana ta Afirka ta ce: “Ƙarya ɗaya takan ɓata gaskiya mai yawa.” Wata karin maganar kuma ta ce: “Ba za a gaskata da maƙaryaci ba ko ma sa’ad da ya faɗa gaskiya.”
11. A waɗanne hanyoyi ne gaskiya ya wuci faɗin gaskiya kawai?
11 Gaskiya tana nufin fiye da a faɗi gaskiya kawai. Tafarkin rayuwa ce. Tana nuna irin mutanen da muke. Mukan sa wasu su san gaskiya ba kawai ta abin da muke faɗa ba amma kuma ta abin da muke yi. “Kai . . . mai-koya ma wani, ba ka koya ma kanka ba?” in ji manzo Bulus. “Kai da ka ke yin wa’azi kada a yi sata, kana yin sata? Kai da ka ke faɗi kada a yi zina, kana yin zina?” (Romawa 2:21, 22) Idan muna koya wa wasu gaskiya, dole ne mu yi gaskiya a dukan hanyoyinmu. Sunan da muke da shi game da gaskiya da kirki zai taɓi mutane da suke sauraron abin da muke koyarwa.
12, 13. Menene wata matashiya ta rubuta game da gaskiya, kuma menene dalilinta na riƙe mizanin ɗabi’a mai girma?
12 Matasa tsakanin bayin Jehovah ma sun fahimci muhimmancin kasance da gaskiya. A wani insha’i, Jenny, wadda a lokacin shekararta 13 ta rubuta: “Yin gaskiya abu ne mai tamani da na daraja ƙwarai. Amma abin baƙin ciki ne, ba mutane da yawa suke da gaskiyar gaske a yau ba. Na shawarta cewa zan riƙa yin gaskiya kullum a rayuwata. Zan ci gaba da yin gaskiya har idan faɗin gaskiya ba zai amfane ni nan da nan ba ko kuma abokaina ba. Na tabbata abokaina waɗanda suke faɗin gaskiya ne kuma masu yin gaskiya.”
13 A magana game da wannan insha’i, malamar Jenny ta ce: “Ko da ke ƙarama ce kin gina ɗabi’a mai ƙarfi mai kyau haka. Na san za ki dage domin kina da ƙarfin ɗabi’a ƙwarai.” Menene ya sa ’yar makarantar nan take da ƙarfin ɗabi’a? A cikin gabatarwa na insha’inta, Jenny ta ambata cewa addininta “ya kafa mata mizani domin [rayuwarta.]” Shekaru bakwai sun wuce da Jenny ta rubuta wannan insha’i. Yadda malamarta ta faɗi, Jenny ta ci gaba da nuna mizanin ɗabi’a mai girma cikin rayuwarta na Mashaidiyar Jehovah.
Bayin Jehovah Suna Bayyana Gaskiya
14. Me ya sa bayin Allah musamman suke da hakki mai girma don ɗaukaka abin da ke gaskiya?
14 Ban da Shaidun Jehovah, wasu za su iya ƙoƙarin su faɗi gaskiya kuma su yi kirki. Amma, mu bayin Allah, muna da hakki mai girma musamman mu ɗaukaka abin da ke gaskiya. An ba mu gaskiyar Littafi Mai Tsarki—gaskiyar da za ta kai mutum zuwa rai na har abada. Saboda haka, muna da hakkin gaya wa wasu wannan sanin. “Dukan wanda an ba shi dayawa,” in ji Yesu, “za a nemi dayawa a gareshi.” (Luka 12:48) Hakika, “za a nemi dayawa” daga waɗanda aka albarkace su da sanin Allah.
15. Wane farin ciki kake samu a koyar wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
15 Da akwai farin ciki a koyar wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki. Kamar almajiran Yesu na ƙarni na farko, muna shelar bishara—saƙon bege mai daɗaɗa zuciya—ga waɗanda suke “watse kuma, kamar tumakin da ba su da makiyayi” da waɗanda suka makanta kuma sun ɗimauce da “koyarwar aljanu.” (Matta 9:36; 1 Timothawus 4:1) Manzo Yohanna ya rubuta: “Ba ni da wani farinciki wanda ya fi wannan, in ji labarin ’ya’yana suna tafiya cikin gaskiya.” (3 Yohanna 4) Amincin ‘ ’ya’yan’ Yohanna—wataƙila waɗanda ya koyar da su gaskiya—ya kawo masa farin ciki mai girma. Abin farin ciki ne gare mu idan muka ga mutane suna bin kuma suna godiya ga Kalmar Allah.
16, 17. (a) Me ya sa ba duka ne suke yarda da gaskiya ba? (b) Wane farin ciki kake samu sa’ad da ka yi shelar gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
16 Alhali, ba duka za su karɓi gaskiya ba. Yesu ya faɗi gaskiya game da Allah, har ma sa’ad da mutane ba sa so. Ya faɗa wa Yahudawa masu adawa: “Don me ba ku bada gaskiya gareni ba? Wanda shi ke na Allah, yana jin maganar Allah: abin da ya sa ba ku ji ke nan, domin ku ba na Allah ba ne.”—Yohanna 8:46, 47.
17 Kamar Yesu, ba ma ja da baya a gaya wa wasu gaskiya mai tamani game da Jehovah ba. Ba ma tsammanin dukan mutane su yarda da abin da muka gaya musu ba, domin ba duka suka yarda da abin da Yesu ya faɗa ba. Duk da haka, muna da farin cikin sanin cewa muna yin abin da ke daidai. Jehovah cikin alherinsa yana son a bayyana gaskiya ga ’yan Adam. Kamar waɗanda suke da gaskiya, Kiristoci sun zama masu ɗauke da haske cikin duniya mai duhu. Ta wurin yarda hasken gaskiya ya haskaka ta kalmomi da kuma ta wurin ayyukanmu, za mu taimaka wa wasu su ɗaukaka Ubanmu na samaniya. (Matta 5:14, 16) Muna sanar a fili cewa mun ƙi jabun gaskiya na Shaiɗan kuma muna ɗaukaka Kalmar Allah mai tsarki marar ɓatanci. Gaskiyar da muka sani kuma muke gaya wa mutane tana kawo ’yanci da gaske ga waɗanda suka yi na’am da ita.—Yohanna 8:32.
Ka Biɗi Tafarkin Gaskiya
18. Me ya sa kuma ta yaya Yesu ya yi wa Natanayilu alheri?
18 Yesu ya so gaskiyar kuma ya faɗe ta. A lokacin hidimarsa a duniya, ya yi tagomashi wa waɗanda suke da gaskiya. Game da Natanayilu, Yesu ya ce: “Duba, ga mutumin Isra’ila na gaske, wanda ba shi da algus!” (Yohanna 1:47) Daga baya, aka zaɓi Natanayilu, da ake kira Barthalamawus ya zama ɗaya cikin manzanni 12. (Matta 10:2-4) Wannan daraja ce!
19-21. Ta yaya aka albarkace wani makaho na dā domin faɗan gaskiya da gaba gaɗi?
19 Wata sura gabaki ɗaya cikin littafin Yohanna a Littafi Mai Tsarki ya ba da labarin wani mutum mai gaskiya da Yesu ya yi masa albarka. Ba mu san sunansa ba. Abin da muka sani shi ne cewa mutumin maroƙi ne da aka haife shi makaho. Mutane sun yi mamaki da Yesu ya mai da masa da ganin gari. Labarin wannan warkarwa ta mu’ujiza ya kai kunnen wasu Farisawa, matsanantar gaskiya, da suka ƙulla tsakaninsu cewa duk wanda ya gaskata da Yesu za a fitar da shi daga majami’ar. Domin sun san ƙullinsu, iyayen makaho na dā da sun tsorata suka yi wa Farisawa ƙarya, cewa ba su san yadda ɗansu ya sami ganin gari yanzu ba ko kuma ba su san wanda ya warkar da shi ba.—Yohanna 9:1-23.
20 Sai aka sake kiran mutumin nan da aka warkar zuwa gaban Farisawan. Ko da menene zai faru, ya yi gaba gaɗi ya faɗi gaskiya. Ya bayyana yadda aka warkar da shi kuma cewa Yesu ne ya warkar da shi. Da mamakin cewa waɗannan shahararrun kuma mutane masu ilimi ba su gaskata da cewa Yesu daga wurin Allah ya zo ba, mutumin da aka warkar ya aririce su da gaba gaɗi su amince da gaskiyar: “Da mutumin nan ba daga wurin Allah ba ne, da ba ya iya yin kome ba.” Domin ba su da abin faɗa, Farisawan suka tuhumi mutumin da rashin kunya kuma fitar da shi waje.—Yohanna 9:24-34.
21 Da Yesu ya ji wannan, ya ɗauki lokaci ya nemi mutumin. Bayan ya yi haka, ya ƙarfafa bangaskiyar makaho na dā ɗin. Yesu ya ambata masa a fili cewa shi ne Almasihu. Dubi albarkar da mutumin ya samu domin ya faɗi gaskiya! Hakika, alherin Allah na bisa waɗanda suke faɗan gaskiya.—Yohanna 9:35-37.
22. Me ya sa ya kamata mu biɗi tafarkin gaskiya?
22 Faɗin gaskiya abin da ya kamata mu ɗauka da muhimmanci ne. Tana ƙulla kuma adana dangantaka mai kyau da mutane kuma tare da Allah. A kasance da gaskiya na nufin kar mutum ya ɓoye ta, ya kasance da gaske, ana iya zuwa wurinsa, kuma tabbatacce, kuma yana samun tagomashin Jehovah. (Zabura 15:1, 2) Ƙarya kuma ita ce ruɗi, da ba a gaskata da ita, riya, da ke jawo rashin tagomashin Jehovah. (Misalai 6:16-19) Saboda haka, ka shawarta ka biɗi tafarkin gaskiya. Hakika, domin mu yi koyi da Allah mai gaskiya, dole ne mu san gaskiya, mu faɗi gaskiya, kuma rayu bisa gaskiya.
Yaya Za Ka Amsa?
• Me ya sa za mu yi godiya cewa mun san gaskiya?
• Ta yaya za mu yi koyi da Jehovah a kasance da gaskiya?
• Waɗanne fa’idodi ne ake da su don gaya wa wasu gaskiyar Littafi Mai Tsarki?
• Me ya sa yake da muhimmanci mu biɗi tafarkin gaskiya?
[Hotuna a shafi na 27]
Domin an ba su gaskiyar Littafi Mai Tsarki, Kiristoci suna gaya wa wasu cikin himma
[Hotuna a shafi na 28]
Makaho da Yesu ya warkar da shi an albarkace shi ƙwarai domin faɗin gaskiya