Ka Faɗi Gaskiya Ga Maƙwabcinka
“Sai ku watsar da ƙarya, kowa ya riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa.”—AFI. 4:25, Littafi Mai Tsarki.
1, 2. Yaya mutane da yawa suke ɗaukan gaskiya?
FAƊAN gaskiya abu ne da ke kawo matsala tsakanin ’yan adam tun da daɗewa. A ƙarni na shida K.Z., wani mawaƙi Baheleni, Alcaeus ya ce: “Mashayi ba ya ƙarya.” Hakan yana nufin cewa mutum yana faɗan gaskiya bayan ya sha ya bugu kuma wataƙila ya fi jin ya yi magana. Bilatus Babunti, Gwamnan Roma na ƙarni na farko, shi ma yana da ra’ayin da bai dace ba game da gaskiya sa’ad da ya tambayi Yesu: “Menene gaskiya”?—Yoh. 18:38.
2 Ra’ayin da ya saɓa wa gaskiya yana ko’ina a zamaninmu. Mutane da yawa sun ce kalmar nan “gaskiya” tana da ma’ana dabam-dabam ko kuma gaskiya ta bambanta ga mutane. Wasu sukan faɗi gaskiya kaɗai idan ba za su shiga cikin matsala ba kuma hanya ce da za su sami wani abu. Littafin nan The Importance of Lying ya ce: “Ko da yake ana ɗaukan cewa faɗin gaskiya yana da kyau, amma ba shi da amfani sosai wajen yin rayuwa da kuma samun kwanciyar rai. Ɗan adam ba shi da zaɓi a wannan batun, dole ne ya yi ƙarya don ya rayu.”
3. Me ya sa Yesu fitaccen misali ne wajen faɗan gaskiya?
3 Almajiran Kristi ba su da irin wannan ra’ayin! Yesu ma ba shi da irin wannan ra’ayin game da gaskiya. Koyaushe yana faɗan gaskiya. Har magabtansa sun yarda da haka: “Malam, mun sani kai mai-gaskiya ne, kana kuwa koyaswar tafarkin Allah cikin gaskiya.” (Mat. 22:16) Hakanan ma a yau, Kiristoci na gaskiya suna yin koyi da misalin Yesu. Ba sa jinkirin faɗin gaskiya. Sun yarda da manzo Bulus da dukan zuciyarsu, wanda ya umurce ’yan’uwa masu bi: “Ku watsar da ƙarya, kowa ya riƙa faɗar gaskiya ga maƙwabcinsa.” (Afis. 4:25, LMT) Bari mu yi la’akari da fannoni uku na kalmomin Bulus. Na farko, wanene maƙwabcinmu? Na biyu, menene ake nufi da a faɗi gaskiya? Kuma na uku, yaya za mu yi amfani da wannan a rayuwarmu ta yau da kullum?
Wanene Maƙwabcinmu?
4. Yaya yadda Yesu ya nuna ra’ayin Jehobah game da ko wanene maƙwabcinmu ya bambanta da na shugabannin Yahudawa?
4 A ƙarni na farko, A.Z., wasu shugabannin Yahudawa sun yi tunanin cewa ’yan’uwansu Yahudawa ko kuma abokansu ne kawai ya dace a kira “maƙwabci.” Amma, Yesu ya nuna halaye da kuma tunanin Ubansa sarai. (Yoh. 14:9) Ya nuna wa almajiransa cewa Allah ba ya nuna cewa ya fi son ƙabila ko ƙasa ɗaya fiye da ɗaya. (Yoh. 4:5-26) Bugu da ƙari, ruhu mai tsarki ya bayyana wa manzo Bitrus cewa “Allah ba mai-tara ba ne: amma a cikin kowace al’umma, wanda ya ke tsoronsa, yana aika adalci kuma, abin karɓa ne gareshi.” (A. M. 10:28, 34, 35) Saboda haka, ya kamata mu ɗauki dukan mutane a matsayin maƙwabtanmu, muna nuna ƙauna har ga waɗanda suke aikata wa magabtanmu.—Mat. 5:43-45.
5. Menene ake nufi da mu faɗi gaskiya da maƙwabcinmu?
5 Duk da haka, menene Bulus yake nufi sa’ad da ya ce mu faɗi gaskiya ga maƙwabcinmu? Faɗin gaskiya ya ƙunshi faɗin ainihin abin da ya faru ba tare da ruɗu ba. Kiristoci na gaskiya ba sa murɗe magana ko kuma su faɗi abin da ba daidai ba don su yaudari mutane. Suna “ƙyamar abin da ke mugu” kuma su “lizimci abin da ke nagari.” (Rom. 12:9) Ta wajen yin koyi da “Allah na gaskiya,” ya kamata mu yi ƙoƙari mu riƙa faɗin gaskiya da kuma yin magana kai tsaye a duk sha’anonin da muke yi da mutane. (Zab. 15:1, 2; 31:5) Idan muka zaɓi kalmominmu da kyau, za mu iya yin amfani da basira mu magance yanayin da zai sa mu ji kunya ba tare da yin ƙarya ba.—Karanta Kolosiyawa 3:9, 10.
6, 7. (a) Faɗin gaskiya yana nufin cewa za mu faɗi kome dalla-dalla ga duk mutumin da ya tambaye mu ne? Ka ba da bayani. (b) Su wanene suka cancanci mu ba su cikakkiyar amsa sa’ad da muke faɗin gaskiya?
6 Faɗan gaskiya yana nufin cewa za mu faɗi dukan abin da muka sani a kan wani batu ga duk wanda ya tambaye mu? A’a. Sa’ad da yake duniya, Yesu ya nuna cewa wasu mutane ba sa bukatar a ba su amsa kai tsaye ko kuma a gaya musu wasu abubuwa. Sa’ad da shugabannin addinai masu riya suka tambaye shi ko da ikon waye yake yin alamu da mu’ujizai, Yesu ya ce: “Ni tambaye ku magana guda ɗaya, ku amsa mani, ni kuma in faɗa maku da ko wane iko ni ke yin waɗannan al’amura.” Sa’ad da marubuta da shugabannin addinai suka ƙi ba da amsa, sai Yesu ya ce masu: “Ni kuma ba ni faɗa maku da ko wane iko ni ke yin waɗannan al’amura ba.” (Mar. 11:27-33) Bai ga dalilin amsa wannan tambayar ba domin munanan ayyukansu da misalinsu na rashin aminci. (Mat. 12:10-13; 23:27, 28) Hakanan ma a yau, mutanen Jehobah suna bukatar su mai da hankali da ’yan ridda da miyagun mutane waɗanda suke amfani da wayo ko makirci don abubuwa na son kai.—Mat. 10:16; Afis. 4:14.
7 Bulus ma ya nuna cewa akwai wasu mutanen da ba su cancanci samun cikakkiyar amsa ba. Ya ce “masu-tsegumi kuma, masu-shishigi” suna “faɗin abin da ba ya kamata garesu ba.” (1 Tim. 5:13) Hakika, waɗanda suke shishigi ga batun wasu ko waɗanda ba sa iya riƙe amana za su ga cewa mutane ba za su so su gaya musu wasu abubuwa ba. Ya fi kyau a bi hurarren gargaɗin Bulus: “Ku ƙallafa ranku kuma ga yin natsuwa, kuna ta naku sha’ani.” (1 Tas. 4:11) Amma, a wasu lokatai wataƙila dattawan ikilisiya suna bukatar su yi tambayoyi game da abubuwa da suka shafe mu domin su cika hakkinsu. A wannan yanayin, muna bukatar mu ba da haɗin kai ta wajen faɗin gaskiya kuma hakan na taimakawa sosai.—1 Bit. 5:2.
Ka Faɗi Gaskiya a Batutuwa na Iyali
8. Ta yaya faɗin gaskiya ke taimakon waɗanda suke cikin iyali su kusaci juna?
8 Babu shakka, mun fi ƙulla gami na kud da kud da waɗanda suke cikin iyalinmu. Don mu ƙarfafa wannan gamin, yana da muhimmanci mu gaya wa juna gaskiya. Za a iya rage ko kuma kawar da matsaloli da yawa da rashin fahimta ta wajen faɗin zuciyarmu, faɗin gaskiya, da kuma kasancewa da halin kirki sa’ad da muke magana. Alal misali, sa’ad da muka yi kuskure, muna jinkirin gaya wa mijinmu ko matarmu, yaranmu, ko sauran waɗanda suke cikin iyalinmu cewa mun yi kuskure? Neman gafara da dukan zuciyarmu na sa a kasance da salama da haɗin kai a cikin iyali.—Karanta 1 Bitrus 3:8-10.
9. Me ya sa faɗin gaskiya ba ya nufin cewa za mu nuna rashin ladabi?
9 Faɗin gaskiya ba ya nufin faɗin abu da rashin ladabi. Rashin ladabi ba ya sa mutane su daraja gaskiya ko kuma su san amfaninsa. Bulus ya ce: “Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gareku, tare da dukan ƙeta: ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.” (Afis. 4:31, 32) Idan muka yi magana da ladabi, hakan yana ɗaukaka saƙonmu kuma yana daraja waɗanda muke yi wa magana.—Mat. 23:12.
Ka Faɗi Gaskiya a Al’amuran Ikilisiya
10. Menene dattawa Kirista za su iya koya daga misali mafi kyau da Yesu ya kafa wajen faɗin gaskiya?
10 Yesu ya yi wa almajiransa magana da hankali kuma kai tsaye. Yana ba da gargaɗi cikin ƙauna, duk da haka ba ya rage muhimmancin gargaɗinsa don kada masu sauraronsa su ji haushi. (Yoh. 15:9-12) Alal misali, sa’ad da manzaninsa suka yi gardama a kai a kai game da wanda ya fi girma a cikinsu, da gaba gaɗi amma cikin haƙuri Yesu ya taimake su su fahimci bukatar kasancewa da tawali’u. (Mar. 9:33-37; Luk 9:46-48; 22:24-27; Yoh. 13:14) Hakazalika, ko da yake suna da gaba gaɗi don adalci, dattawa Kirista a yau ba sa nuna iko a kan garken Allah. (Mar. 10:42-44) Suna yin koyi da Kristi ta wajen kasancewa da ‘nasiha zuwa ga junansu’ da kuma “tabshin zuciya” a sha’anoninsu da wasu.
11. Ya kamata nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu ya motsa mu mu yi menene a yadda muke amfani da harshenmu?
11 Ta wajen faɗin gaskiya kai tsaye ga ’yan’uwanmu amma ba yawan faɗin abu a fili ba, muna iya faɗin abin da ke zuciyarmu ba tare da ɓata musu rai ba. Hakika, ba za mu so harshenmu ya zama “aska mai-kaifi,” ta wajen yin amfani da shi mu ji musu rauni mai zafi ta yin baƙar magana. (Zab. 52:2; Mis. 12:18) Nuna ƙauna ga ’yan’uwanmu za ta motsa mu mu “kiyayadda harshen [mu] ga barin mugunta, leɓunan [mu] kuma ga barin maganar algus.” (Zab. 34:13) Ta hakan, za mu ɗaukaka Allah kuma mu sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai.
12. Wane lokaci ne ya kamata a yi wa wanda ya yi ƙarya shari’a? Ka ba da bayani.
12 Dattawa suna aiki tuƙuru don su kāre ikilisiya daga waɗanda suke muguwar ƙarya. (Karanta Yaƙub 3:14-16.) Ana muguwar ƙarya don a ɓata sunan mutum; a sa mutumin ya sha wahala a wata hanya ko kuma ya yi baƙin ciki. Ya ƙunshi fiye da yin ’yan kalamai na yaudara ko kuma zuguiguita abin da ya faru. Hakika, ba ƙaryar da take da kyau, amma ba a dukan yanayin ba ne ake bukatar a yi shari’a game da ƙarya ba. Saboda haka, dattawa suna bukatar su kasance da daidaita, sanin ya kamata, da kuma hikima sa’ad da suke bincika ko mutumin da ya yi furci da ba gaskiya ba ya saba yin muguwar ƙarya da zai bukaci a yi masa shari’a. Ko kuma gargaɗi na kai tsaye da aka yi da ƙauna daga Nassosi zai isa?
Ka Faɗi Gaskiya a Sha’anonin Kasuwanci
13, 14. (a) Yaya wasu mutane suka kasa zama masu faɗin gaskiya ga shugaban aikinsu? (b) Wane sakamako mai kyau za a iya samu don zama ma’aikaci mai aiki da kyau da kuma faɗin gaskiya?
13 Muna zama a zamanin da ake yawan ƙarya, saboda haka yana iya kasance da wuya mutum ya tsayayya wa gwajin rashin gaskiya ga shugaban aikin. Sa’ad da suke neman aiki, mutane da yawa suna ƙarya kai tsaye. Alal misali, suna zuguiguita irin aikin da suka yi ko kuma makarantar da suka je domin su samu aikin da aka fi biyan kuɗi. A wata sassa kuma, ma’aikata da yawa suna da’awa wai suna aiki yayin da kuma suna yin abubuwa na kansu ko da yake an ce kada a yi hakan a dokokin kamfanin. Suna iya karanta abubuwa da ba su shafi aikin ba, suna yin waya, suna aika saƙo ta hanyar na’ura ko tarho, ko kuma bincika wani dandali a Intane.
14 Kiristoci na gaskiya ba su da wani zaɓi game da faɗin gaskiya. (Karanta Misalai 6:16-19.) Bulus ya ce: “Muna so mu yi tasarrufin kirki cikin dukan abu.” (Ibran. 13:18) Saboda haka, Kiristoci suna yi wa shugaban aikinsu aiki na cikakkiyar rana don a biya su cikakken albashin su. Wanda yake yin aiki da kyau yana sa a yaba wa Ubanmu na samaniya. (1 Bit. 2:12) Alal misali, shugaban aikin Roberto a ƙasar Spain ya yaba masa don faɗin gaskiya da kuma yin aiki da kyau. Don halin kirki na Roberto, kamfanin sun ɗauki ƙarin Shaidu aiki. Waɗannan ma sun zama ma’aikata mafi kyau. Cikin shekaru da yawa, Roberto ya samo wa ’yan’uwa maza ashirin da uku da suka yi baftisma aiki da kuma ɗaliban Littafi Mai Tsarki guda takwas!
15. Ta yaya Kirista ɗan kasuwa zai nuna cewa yana faɗin gaskiya?
15 Idan muna aiki na kanmu, muna faɗin gaskiya a dukan sha’aninmu na kasuwanci, ko kuma wani lokaci muna ƙin faɗin gaskiya ga maƙwabcinmu? Bai kamata Kirista ɗan kasuwa ya faɗi abin da ba gaskiya ba game da wasu kaya ko kuma wani aiki domin ya sayar da sauri; kuma bai kamata ya ba da cin hanci ko kuma ya karɓi cin hanci ba. Ya kamata mu bi da mutane yadda za mu so a bi da mu.—Mis. 11:1; Luk 6:31.
Ka Faɗi Gaskiya ga Masu Mulki
16. Menene Kiristoci suke ba (a) masu mulki? (b) Jehobah?
16 Yesu ya ce: “Ku ba Kaisar abin da ke na Kaisar; Allah kuma abin da ke na Allah.” (Mat. 22:21) Wane irin ‘abu’ ne Kaisar, wato, masu mulki suke bin mu? Sa’ad da Yesu ya furta waɗannan kalaman, yana magana ne a kan haraji. Saboda haka, don su kasance da lamiri mai tsabta a gaban Allah da mutane, Kiristoci suna biyayya ga dokokin ƙasa, har da waɗanda suka shafi biyan haraji. (Rom. 13:5, 6) Amma mun fahimci cewa Jehobah ne Mafifici Mai Ikon Mallaka, Allah makaɗaici na gaskiya, wanda muke ƙauna da dukan zuciyarmu, ranmu, azancinmu, da kuma ƙarfinmu. (Mar. 12:30; R. Yoh. 4:11) Saboda haka, muna yin biyayya ga Jehobah Allah da dukan zuciyarmu.—Karanta Zabura 86:11, 12.
17. Yaya mutanen Jehobah suke ɗaukan samun taimako da ake ba jama’a?
17 Ƙasashe da yawa sun tsara ƙungiyoyi ko kuma ayyuka don su taimaka wa waɗanda suke bukatar abin biyan bukata. Babu laifi idan Kirista ya karɓi irin wannan taimako, muddin ya cancanta ya karɓa. Faɗin gaskiya ga maƙwabcinmu yana nufin cewa ba za mu faɗi ƙarya ko kuma bayani na yaudara ga masu mulki domin mu sami taimako ba.
Albarkar Faɗin Gaskiya
18-20. Waɗanne albarka muke samu ta wajen faɗin gaskiya ga maƙwabcinmu?
18 Albarka da ake samu don faɗin gaskiya tana da yawa. Muna kasancewa da lamiri mai tsabta, wanda ke sa mu samu kwanciyar hankali. (Mis. 14:30; Filib. 4:6, 7) Samun lamiri mai tsabta yana da muhimmanci sosai a gaban Allah. Sa’ad da muke faɗin gaskiya a dukan abubuwa, ba za mu ji tsoron tonon asiri ba.—1 Tim. 5:24.
19 Ka yi la’akari da wata albarka. Bulus ya ce: “Cikin kowace matsala mu koɗa kanmu masu-hidimar Allah, . . . cikin maganar gaskiya.” (2 Kor. 6:4, 7) Hakan ya zama gaskiya ga wani Mashaidi da ke zama a Britaniya. Da yake son ya sayar da motarsa, ya kwatanta duka abubuwa masu kyau game da motar da kuma matsalolinta, har da waɗanda ba za a iya gani ba. Bayan ya tuƙa motar don ya gwada ta, mutumin ya tambayi ɗan’uwan ko shi Mashaidin Jehobah ne. Me ya sa mutumin ya kammala hakan? Domin mutumin ya lura cewa ɗan’uwan ya faɗi gaskiya kuma yana da tsabta. Taɗinsu ya sa ɗan’uwan ya yi wa mutumin wa’azi da kyau.
20 Mu ma muna sa a yabi Mahaliccinmu ta wurin halinmu mai kyau kuwa? Bulus ya ce: “Mun kakkaɓe ɓoyayyun al’amura na kunya, ba mu yi tafiya cikin kirsa ba.” (2 Kor. 4:2) Saboda haka, bari mu yi iyakar ƙoƙarinmu mu riƙa faɗin gaskiya ga maƙwabcinmu. Ta yin haka za mu sa a yabi Ubanmu na samaniya da kuma mutanensa.
Yaya Za Ka Amsa?
• Wanene maƙwabcinmu?
• Menene ake nufi da mu faɗi gaskiya ga maƙwabcinmu?
• Ta yaya faɗin gaskiya yake sa a ɗaukaka Allah?
• Waɗanne albarka ake samu don faɗan gaskiya?
[Hotunan da ke shafi na 17]
Kana amincewa da ƙananan kurakurai?
[Hotunan da ke shafi na 18]
Kana faɗin gaskiya sa’ad da kake neman aiki?