Dokokin Allah Don Amfaninmu Ne
“Ina ƙaunar [dokarka] ba misali!”—ZABURA 119:97.
1. Wane hali ne ke ko’ina game da biyayya ga dokokin Allah?
YIN biyayya ga dokokin Allah ba abin da aka yarda da ita ba ne a yau. Ga mutane da yawa, daraja wani iko mai girma marar ganuwa ba shi da amfani. Muna rayuwa ne a zamani na ra’ayin cewa ɗabi’a ta dangana ga mutane da rukuni da ke riƙe da su, iyaka ta rabe tsakanin nagarta da mugunta, da yanayi da ba shi da sauƙi a ba da ma’anarsa cewa nagari ne ko mugunta. (Misalai 17:15; Ishaya 5:20) Nuna hanyar tunani da ke ko’ina a jam’iyyoyi da yawa, a ƙirge da aka yi kwanakin baya an lura cewa “yawancin ’yan Amirka suna so su tsai da shawarar kansu a kan abin da ke daidai, yake nagari mai ma’ana.” Sun fi son “Allah mai rangwame. Ba sa son dokoki masu tsanani. Ba sa son shugabanni masu ƙarfi da tabbatacciyar ɗabi’a ko wani tabbaci.” Mai bincike a kan zaman mutane ya lura cewa a yau “ana bukatar mutane su shawarta wa kansu abin da yake nufi a yi rayuwa mai kyau da na ɗabi’a.” Ya ci gaba: “Kowane irin iko mai girma ya kamata ya daidaita dokokinsa ga bukatun mutane.”
2. Ta yaya yadda aka ambata doka da farko cikin Littafi Mai Tsarki ke da alaƙa da albarkar Allah da amincewarsa?
2 Tun da mutane da yawa suna shakkar amfanin dokokin Jehovah, muna bukatar mu ƙarfafa tabbacinmu cewa mizanan Allah don amfaninmu ne. Yana da kyau a bincika tarihin inda aka ambata doka ta farko cikin Littafi Mai Tsarki. A Farawa 26:5, mun karanta kalmomin Allah: “Ibrahim . . . ya kiyaye umurnina, da dokokina, da farillaina, da shari’una.” An furta waɗannan kalmomi ƙarnuka da yawa kafin Jehovah ya ba ’ya’yan Ibrahim dokar Musa. Ta yaya Allah ya saka wa Ibrahim don biyayyarsa, haɗe da biyayya ga dokokinsa? Jehovah Allah ya yi masa alkawari: “Cikin zuriyarka kuma dukan al’umman duniya za su sami albarka.” (Farawa 22:18) Da haka biyayya ga dokokin Allah na da alaƙa da albarkar Allah da amincewarsa.
3. (a) Yaya wani mai Zabura ya furta yadda yake ji game da dokar Jehovah? (b) Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu mai da hankali a kansu?
3 Ɗaya cikin masu Zabura—mai yiwuwa ɗan sarki na Yahuda kuma sarki ne na nan gaba—ya furta motsin ransa da ba kullum yake da nasaba da doka ba. Ya ce wa Allah: “Ina ƙaunar [dokarka] ba misali!” (Zabura 119:97; Tafiyar tsutsa tamu ce.) Wannan ba kawai furta sosawar zuciya ba ce. Furci ne na ƙaunar nufin Allah yadda yake a dokarsa. Yesu Kristi, kamiltaccen Ɗan Allah, shi ma ya ji haka. A hanyar annabci an kwatanta Yesu yana cewa: “Murna ni ke yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, [dokarka] tana cikin zuciyata.” (Zabura 40:8; Ibraniyawa 10:9) Mu kuma fa? Muna murna wajen yin nufin Allah? Mun tabbata cewa dokokin Jehovah na da amfani? Wane wuri ne biyayya ga dokokin Allah yake da shi a bautarmu, a rayuwarmu ta yau da kullum, a tsai da shawara da muke yi, da cikin dangantakarmu da wasu? Domin mu ƙaunaci dokar Allah, yana da kyau mu fahimci abin da ya sa Allah yake da iko ya kafa kuma ya ƙarfafa dokoki.
Jehovah—Mai Ba da Doka da Ya Dace
4. Me ya sa Jehovah ne Mai Ba da Doka Mafi Girma da ya dace?
4 Da yake shi Mahalicci ne, Jehovah ne Mai Ba da Doka da ya dace a sararin samaniya. (Ru’ya ta Yohanna 4:11) Annabi Ishaya ya ce: ‘Ubangiji shi ne mai ba da doka.’ (Ishaya 33:22) Ya kafa dokoki na zahiri da ke ja-gorar halitta masu rai da marasa rai. (Ayuba 38:4-38; 39:1-12; Zabura 104:5-19) Halittar Allah, mutum yana yin biyayya ga dokokin Jehovah na zahiri. Ko da mutum yana da ’yancin kai, yana da iyawar ya yi tunani na kansa, yana farin ciki lokacin da ya miƙa kansa ga dokokin Allah na ɗabi’a da na ruhaniya.—Romawa 12:1; 1 Korinthiyawa 2:14-16.
5. Ta yaya ƙa’ida da ke Galatiyawa 6:7 ta kasance gaskiya game da dokokin Allah?
5 Kamar yadda muka sani, ba a karya dokokin Jehovah na zahiri. (Irmiya 33:20, 21) Idan mutum bai bi wasu dokoki ba na zahiri, kamar su dokar ƙarfin maganaɗiso, zai fuskanci sakamakon haka. Hakanan ma, ba a canja dokokin Allah na ɗabi’a kuma ba a guje ko karya su babu horo. An ƙarfafa su sosai yadda aka yi da dokokinsa na halitta, ko da yake sakamakonsa ba nan da nan ba ne. “Ba a yi ma Allah ba’a ba: gama iyakar abin da mutum ya shuka, shi za ya girbe.”—Galatiyawa 6:7; 1 Timothawus 5:24.
Faɗin Dokar Jehovah
6. Yaya faɗin dokokin Allah yake?
6 Nuni na musamman na dokar Allah Dokar Musa ne. (Romawa 7:12) Da shigewar lokaci, Jehovah Allah ya sake Dokar Musa da “[dokar] Kristi.”a (Galatiyawa 6:2; 1 Korinthiyawa 9:21) Mu Kiristoci da ke ƙarƙashin ‘cikakkiyar [doka] ta ’yanci,’ mun fahimci cewa ja-gorar Allah ba ga wasu fasalolin rayuwarmu ba ne kawai, irin su imani na addini ko kuma bukukuwa. Mizanansa ya rufe dukan fasalolin rayuwa, haɗe da harkokin iyali, sha’anin kasuwanci, hali game da kishiyar jinsi, halaye game da ’yan’uwa Kiristoci, da sa hannu a bauta ta gaskiya.—Yaƙub 1:25, 27
7. Ka ba da misalan dokokin Allah masu muhimmanci.
7 Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-fasikanci, da masu-bautan gumaka, da mazinata, da baran mata, da masu-kwana da maza, da ɓarayi, da masu-ƙyashi, da masu-maye, da masu-alfasha, da masu-ƙwace, ba za su gāji mulkin Allah ba.” (1 Korinthiyawa 6:9, 10) Hakika, zina da fasikanci ba kawai “harkokin soyayya” ba ne. Luwaɗi ba kawai “wani yayin rayuwa ba ne.” Waɗannan karkarya dokar Jehovah ce. Haka ma yake ga abubuwa kamar su, sata, ƙarya, da tsegumi. (Zabura 101:5; Kolossiyawa 3:9; 1 Bitrus 4:15) Yaƙub ya haramta fahariya, yayin da Bulus ya yi mana gargaɗi mu guji zancen banza, da alfasha. (Afisawa 5:4; Yaƙub 4:16) Ga Kiristoci, duka waɗannan dokoki game da hali, bangaren cikakkiyar doka ce ta Allah.—Zabura 19:7.
8.(a) Dokar Jehovah ta ƙunshi menene? (b) Mecece ainihin ma’anar kalmar Ibrananci ta ‘ “doka”?
8 Irin waɗannan sharuɗa na musamman na Kalmar Jehovah sun bayyana cewa dokarsa ba kawai manne wa jerin dokoki ba ne. Sun kafa tushen daidaitaciyar rayuwa mai ma’ana, da ta amfani dukan fasalolin halaye. Dokar Allah na ginawa, tana da kyau, tana koyarwa kuma. (Zabura 119:72, NW ) Kalmar nan “doka” yadda mai Zabura ya yi amfani da ita an fassara ta daga kalmar Ibrananci ce toh·rahʹ. Wani manazarcin Littafi Mai Tsarki ya ce: “An samo wannan kalmar ce daga kalmar aikatau da take nufin a nuna, a yi ja-gora, a yi nufi, a yi gaba. Saboda haka, ma’anarta za ta zama ƙa’idar hali.” Ga mai Zabura dokar kyauta ce daga Allah. Bai kamata mu ɗauke ta hakanan ba, muna bari ta gyara mana salon rayuwa?
9, 10. (a) Me ya sa muke bukatar ja-gora da za mu dogara a kanta? (b) Ta yaya kawai za mu yi rayuwa na farin ciki da nasara?
9 Dukan halitta suna bukatar ja-gora da za su dogara kuma su amince da shi. Haka gaskiya ce da Yesu da wasu mala’iku, da suka fi mutane ɗaukaka. (Zabura 8:5; Yohanna 5:30; 6:38; Ibraniyawa 2:7; Ru’ya ta Yohanna 22:8, 9) Idan waɗannan kamiltattun halittu sun iya amfana daga ja-gorar Allah, ballantana mu da ajizai ne! Tarihi na ’yan Adam da abin da muka gani ya tabbatar da gaskiyar abin da annabi Irmiya ya lura: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.
10 Idan muna son mu yi rayuwa ta farin ciki da nasara, dole mu nemi ja-gorar Allah. Sarki Sulemanu ya fahimci haɗarin yin rayuwa daidai da mizanai na kanmu, ’yancin kai daga ja-gorar Allah: “Akwai hanya wadda ta ke sosai bisa ga ganin mutum, amma matuƙarta tafarkun mutuwa ne.”—Misalai 14:12.
Dalilan Daraja Dokar Jehovah
11. Me ya sa ya kamata mu so mu fahimci dokar Allah?
11 Yana da kyau mu gina muradi mai zurfi mu fahimci dokar Jehovah sosai. Mai Zabura ya furta irin wannan muradi yayin da ya ce: “Ka buɗe mini idanuna, domin in duba al’ajibai daga cikin [dokarka].” (Zabura 119:18) Idan mun ƙara sanin Allah da hanyoyinsa, za mu ƙara fahimtar gaskiyar kalmomin Ishaya sosai: “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya ke koya maka zuwa amfaninka, wanda yana bishe ka ta hanyar da za ka bi. Da ma ka yi sauraro ga dokokina!” (Ishaya 48:17, 18) Son Jehovah ne mutanensa su guji masifa kuma su more rayuwa ta wurin sauraron dokokinsa. Bari mu binciki wasu dalilai na musamman da ya sa za mu daraja dokar Allah.
12. Ta yaya saninmu da Jehovah yake da shi ya sa ya zama Mai Ba da Doka da ya fi kyau?
12 Dokar Allah ta zo daga Wanda ya fi saninmu. Tun da yake Jehovah ne Mahaliccinmu, daidai ne cewa zai san ’yan Adam sosai. (Zabura 139:1, 2; Ayukan Manzanni 17:24-28) Abokai na kusa, dangi, har ma iyaye ba za su iya sanin mu da kyau yadda Jehovah ya san mu ba. Hakika, Allah ya san mu da kyau fiye da ma muka san kanmu! Mahaliccinmu yana da sani da babu na biyunsa game da bukatunmu na ruhaniya, na motsin rai, azanci, da na zahiri. Yayin da yake mai da hankali wajenmu, yana nuna ya fahimci yadda muke sosai, sha’awoyinmu, da burinmu. Jehovah ya fahimta iyakarmu, amma ya kuma san za mu iya yin abin da yake nagari. Mai Zabura ya ce: “Ya san tabi’ammu; ya kan tuna mu turɓaya ne.” (Zabura 103:14) Da haka, za mu kasance da kwanciyar rai ta ruhaniya yayin da muke nema mu yi tafiya cikin dokarsa, da yardan rai muna miƙa kanmu ga ja-gorar Allah.—Misalai 3:19-26.
13. Me ya sa za mu kasance da gaba gaɗi cewa Jehovah yana damuwa da abin da zai fi kyau dominmu?
13 Dokar Allah ta zo daga Wanda yake ƙaunarmu. Allah yana damuwa sosai game da madawwamiyar lafiyarmu. Ba shi ba ne ta azabtar wa kansa ya ba da Ɗansa “abin fansar mutane dayawa”? (Matta 20:28) Jehovah bai yi alkawari ba cewa ‘ba zai bari a jaraba mu yadda ta fi ƙarfinmu ba’? (1 Korinthiyawa 10:13) Ba Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa ‘yana kula da mu ba’? (1 Bitrus 5:7) Ba wanda yake son yin tanadin ja-goran da zai amfani halittar mutane fiye da Jehovah. Ya san abin da yake da kyau dominmu kuma ya san iyaka tsakanin abin da zai kawo mana farin ciki da baƙin ciki. Ko da mu ajizai ne kuma muna yin kuskure, idan mun biɗi adalci, yana nuna mana ƙaunarsa a hanyoyi da zai kawo rai da albarka.—Ezekiel 33:11.
14. A wace hanya ce mai muhimmanci dokar Allah ta bambanta daga ra’ayoyin mutane?
14 Dokar Allah ba ta canjawa. A wannan lokacin wahala da muke zama, Jehovah ne dutse mai ƙarfi, ba shi da farko ba shi da ƙarshe. (Zabura 90:2) Ya ce game da kansa: “Ni Ubangiji ba mai-[canjawa] ba ne.” (Malachi 3:6) Mizanan Allah yadda suke rubuce cikin Littafi Mai Tsarki, tabbatattu ne sarai—ba kamar ƙasa na ra’ayoyin mutane da ke canjawa koyaushe ba. (Yaƙub 1:17) Alal misali, shekaru da yawa masu koyon halin mutane sun gabatar da halin kome daidai a renon yara, amma daga baya wasu sun canja ra’ayinsu kuma suka ce shawararsu kuskure ne. Mizanan duniya da ja-gora a kan wannan batun na jujjuyawa kamar iska ke hura su. Amma, Kalmar Jehovah ba ta jijjiga. Ƙarnuka da yawa Littafi Mai Tsarki ya yi tanadin shawara a yadda za a yi renon yara da ƙauna. Manzo Bulus ya rubuta: “Ubanni kuma, kada ku yi ma ’ya’yanku cakuna har su yi fushi: amma ku goye su cikin horon Ubangiji da gargaɗinsa.” (Afisawa 6:4) Lallai abin ƙarfafa ne a sani cewa za mu iya dogara da mizanan Jehovah; ba za su canja ba!
Albarka ga Waɗanda Suke Biyayya ga Dokokin Allah
15, 16. (a) Idan muka yi amfani da mizanan Jehovah, menene zai zama sakamakon haka? (b) Ta yaya dokokin Allah za su zama ja-gora mai kyau ga aure?
15 Ta annabi Ishaya, Allah ya ce: “Maganata, wadda ta ke fitowa daga cikin bakina . . . za ta yi albarka.” (Ishaya 55:11) Babu shakka, idan mun yi ƙoƙari sosai mu bi mizanai da ke cikin Kalmarsa, za mu samu nasara, cim ma abubuwa masu kyau, kuma mu samu farin ciki.
16 Yi la’akari da yadda dokokin Allah ke ja-gora mai kyau ga aure mai nasara. “Aure shi zama abin darajantuwa a wajen dukan mutane,” in ji Bulus, “gado kuma shi kasance mara-ƙazanta: gama da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (Ibraniyawa 13:4) Abokan aure za su daraja kuma su ƙaunaci juna: “Kowane ɗayanku shi yi ƙaunar matatasa kamar kansa; matan kuma ta ga ƙwarjinin mijinta.” (Afisawa 5:33) Irin ƙauna da ake bukata an kwatanta a 1 Korinthiyawa 13:4-8: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi; ƙauna ba ta yin fahariya, ba ta yin kumbura, ba ta yin rashin hankali, ba ta biɗa ma kanta, ba ta jin cakuna, ba ta yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin adalci, amma tana murna da gaskiya; tana jimrewa da abu duka, tana gaskata abu duka, tana kafa bege ga abu duka, tana daurewa da abu duka. Ƙauna ba ta ƙarewa daɗai.” Aure da ke bisa irin wannan ƙaunar ba zai lalace ba.
17. Waɗanne fa’idodi suke zuwa daga yin amfani da mizanan Jehovah a kan shan giya?
17 Wani tabbaci cewa mizanan Jehovah na da amfani shi ne cewa ya haramta yin maye. Ya ma haramta, mutum ‘ya zama mai zarin shan ruwan anab.’ (1 Timothawus 3:3, 8; Romawa 13:13) Mutane da yawa da suka ƙyale mizanan Allah a kan wannan batun sun yi ciwo da shan giya mai yawa ke kawowa. Yin banza da gargaɗin Littafi Mai Tsarki a kan yin abu daidai wa daida, wasu sun shiga cikin halin shan giya mai yawa don ya “taimake su hutawa.” Matsaloli da shan giya mai yawa ke kawowa yana da yawa, ya haɗa da rashin daraja, lalata dangantakar iyali ko iyalai su rabu, ɓata kuɗi, da rashin aiki. (Misalai 23:19-21, 29-35) Mizanan Jehovah game da shan giya ba kāriya ba ce?
18. Dokokin Allah suna da amfani ne a batutuwan kuɗi? Ka ba da bayani.
18 Mizanan Allah ma na da amfani a batutuwan kuɗi. Littafi Mai Tsarki ya aririce Kiristoci su riƙa yin gaskiya da ƙwazo. (Luka 16:10; Afisawa 4:28; Kolossiyawa 3:23) Domin suna bin wannan gargaɗin, an ƙara wa Kiristoci da yawa matsayi ko sun ci gaba da aikinsu yayin da aka kori wasu. Amfanin kuɗi na zuwa yayin da mutum ya guje wa halaye da ba na nassi ba irin su caca, shan taba, da shan miyagun ƙwayoyi. Babu shakka za ka iya tunanin wasu misalai na fa’idodin mizanan Allah.
19, 20. Me ya sa tafarkin hikima ne mu amince kuma mu riƙe dokokin Allah?
19 Yana da sauƙi mutane ajizai su fanɗare daga dokokin Allah da mizanansa. Ka tuna da Isra’ilawa a Dutsen Sinai. Allah ya ce musu: “Idan lallai za ku yi biyayya da maganata, ku kiyaye wa’adina kuma, sa’annan za ku zama keɓaɓiyar taska a gareni daga cikin dukan al’umman duniya.” Suka ce: “Abin da Ubangiji ya faɗi duka mu a yi.” (Fitowa 19:5, 8; Zabura 106:12-43) Duk da haka, suka zaɓa su bi wani tafarki! (Fitowa 19:5, 8; Zabura 106:12-43) Akasin haka, bari mu amince kuma mu riƙe mizanan Allah.
20 Tafarkin hikima ne kuma yana kawo farin ciki mu manne wa dokokin da ba za a gwada shi da wani ba da Jehovah ya yi tanadinsa ya yi ja-gora a rayuwarmu. (Zabura 19:7-11) Don mu yi nasara a wannan, muna bukatar mu fahimci amfanin ƙa’idodin Allah kuma mu daraja su. Wannan ne jigo na talifi na gaba.
[Hasiya]
a Don bayani dalla-dalla a kan “[Dokar] Kristi,” dubi Hasumiyar Tsaro, 1 ga Satumba, 1996 shafofi 21-31.
Ka Tuna?
• Me ya sa za mu dogara da cewa dokokin Allah don amfaninmu ne?
• Don waɗanne dalilai za mu daraja dokar Jehovah?
• A waɗanne hanyoyi ne dokokin Allah ke da amfani?
[Hoto a shafi na 3]
An albarkaci Ibrahim sosai don yin biyayya ga dokar Jehovah
[Hotuna a shafi na 5]
Ɗawainiyar rayuwar yau ta janye hankalin mutane da yawa daga dokar Allah
[Hoto a shafi na 7]
Kamar gidan wuta a kan dutse, dokar Allah na daɗewa kuma ba ta canjawa