Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 6/1 pp. 5-8
  • Bincika Wasu Ƙage-Ƙage Game da Mutuwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Bincika Wasu Ƙage-Ƙage Game da Mutuwa
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ’Yanci Daga Tsoro
  • Me Zai Taimaka Mini Na Daina Tsoron Mutuwa?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Ina Matattu Suke?
    Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
  • Me Ke Faruwa Sa’ad da Muka Mutu?
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!​—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 6/1 pp. 5-8

Bincika Wasu Ƙage-Ƙage Game da Mutuwa

DUK cikin tarihi, mutane sun yi mamaki kuma sun ji tsoron tabbacin mutuwa. Ban da haka ma, tsoron mutuwa ya ci gaba domin ra’ayoyin addinan ƙarya, al’adu da ke ko’ina da kuma imani. Matsala da ke tattare da tsoron mutuwa ita ce cewa za ta iya hana mutum more rayuwa kuma a ɓata tabbacin mutum cewa akwai ma’ana a rayuwa.

Addini ne musamman yake gabatar da ƙage-ƙage da aka yarda da su game da mutuwa. Ta wajen bincika wasu cikin waɗannan da taimakon gaskiyar Littafi Mai Tsarki, za ka gani ko za a gyara ra’ayinka game da mutuwa.

Ƙage na 1: Mutuwa ƙarshen rai ce.

“Mutuwa . . . ɓangare ne na rayuwarmu,” in ji littafin nan Death—The Final Stage of Growth. Furci kamar haka na nuna cewa mutuwa daidai take, ƙarshen duk wani abu mai rai ne. Saboda haka, irin wannan imani yana ƙarfafa falsafa da halin yin amfani da zarafi yadda bai dace ba da mutane da yawa suke yi a yau.

Amma da gaske mutuwa ita ce ƙarshen rai? Ba duka masu bincike ba ne suka gaskata hakan. Alal misali, Calvin Harvey masanin ƙwayoyin halitta wanda yake nazarin tsufan ’yan Adam, a wata ganawa ya ce, bai gaskata ba cewa “an tsara mutane don su mutu.” Masanin garƙuwar jiki William Clark ya lura cewa: “Mutuwa bai kamata ta kasance ɓangaren ma’anar rai ba.” Kuma Seymour Benzer, na California Institute of Technology ya faɗi cewa “Zai fi kyau a kwatanta tsufa ba da lokaci ba amma da yanayi, da za mu iya gyarawa.”

Sa’ad da masana kimiyya suka yi nazarin tsarin jikin mutane, sun yi mamaki. Sun gano cewa an yi mana arziki da iyawar da suka fi bukatu na rayuwarmu na shekara 70 zuwa 80. Alal misali, masana kimiyya sun gano cewa ƙwaƙwalwar mutum na da iyawa mai girma na riƙe abubuwa da yawa. Wani mai bincike ya kimanta cewa ƙwaƙwalwarmu za ta iya riƙe bayani da “zai cika littattafai miliyan ashirin, daidai da laburare mafi girma na duniya.” Wasu masana jijiyoyin jiki sun gaskata cewa lokacin matsakaiciyar rayuwa, mutum yana amfani da ɗan mitsitsi ne na iyawar ƙwaƙwalwarsa. Ya dace a yi tambaya, ‘Me ya sa muke da ƙwaƙwalwa da irin wannan iyawa mai girma sa’ad da muke amfani da kaɗan kawai a matsakaiciyar rayuwa?’

Yi la’akari kuma da yadda mutane suke ji game da mutuwa! Ga yawancin mutane, mutuwar mata, miji, ko ɗa ya fi sa su baƙin ciki a rayuwa. Mutane sau da yawa na rikicewa na dogon lokaci bayan mutuwar wanda suke ƙauna ƙwarai. Har ma waɗanda suke da’awa cewa mutane an yi su suna mutuwa, suna iske shi da wuya su yarda da ra’ayin cewa nasu mutuwa za ta nufi ƙarshen rayuwarsu. Jaridar nan British Medical Journal ta yi maganar “wani gwani da ya gaskata cewa kowa yana son ya rayu muddin zai yiwu.”

Saboda yadda mutum yake ji game da mutuwa, iyawarsa mai ban mamaki na tuna abu da kuma koyo, da son ya rayu har abada, ba a bayyane yake ba cewa an yi mutum ya dawwama? Hakika, Allah ya halicce mutane, ba don su mutu ba ne a ƙarshe, amma don su rayu har abada. Ka lura da abin da Allah ya kafa don rayuwa na nan gaba na mutane biyu na farko: “Ku yalwata da ’ya’ya, ku riɓu, ku mamaye duniya, ku mallake ta; ku yi mulkin kifaye na teku, da tsuntsaye na sarari, da kowane abu mai-rai wanda ke rarrafe a ƙasa.” (Farawa 1:28) Lallai, wannan dawwama ce mai ban al’ajabi matuƙa!

Ƙage na 2: Allah yana ɗaukan mutane ta wajen mutuwa su kasance tare da shi.

Wata uwa ’yar shekara 27 da za ta mutu ta bar ’ya’yanta uku ta gaya wa wata mai zaman zuhudu na Katolika: “Kada ki shigo ki gaya mini cewa nufin Allah ne a gare ni. . . . Ba na son wani ya gaya mini wannan.” Duk da haka, abin da addinai da yawa suke koyarwa ke nan game da mutuwa—cewa Allah na ɗaukan mutane su zauna kusa da shi.

Mahalicci azzalumi ne da zai sa mu mutu ba tare da tausayi ba, bayan ya sani cewa wannan zai baƙanta mana rai? A’a, ba Allah na Littafi Mai Tsarki ba. In ji 1 Yohanna 4:8, “Allah ƙauna ne.” Ka lura cewa bai ce Allah yana da ƙauna ko Allah yana ƙauna ba, amma ya ce Allah ƙauna ne. Ƙaunar Allah tana da zurfi, tana da tsarki, cikakkiya ce, ta kasance a mutuntakarsa da ayyukansa sosai da ya dace a ce shi ne ƙauna. Ba Allah ba ne da ke ɗaukan mutane a mutuwa su kasance kusa da shi.

Addinin ƙarya ya sa mutane da yawa su rikice game da wuri da kuma yanayin matattu. Sama, jahannama, gidan azaba, Limbo—waɗannan da wasu wurare da ba za a iya fahimtarsu ba na da ban tsoro. Littafi Mai Tsarki, a wani ɓangare kuma ya gaya mana cewa matattu ba su san kome ba; suna cikin yanayi ne kamar na mai barci. (Mai-Wa’azi 9:5, 10; Yohanna 11:11-14) Da haka, ba ma bukatar mu damu game da abin da zai faru da mu bayan mun mutu, yadda ba ma damuwa yayin da mun ga mutum yana barci mai zurfi. Yesu ya yi maganar lokacin da “dukan waɗanda suna cikin kabarbaru” za su “fito” zuwa sabuwar rayuwa a cikin aljanna ta duniya.—Yohanna 5:28, 29; Luka 23:43.

Ƙage na 3: Allah yana ɗaukan yara ƙanana su zama mala’iku.

Elisabeth Kübler-Ross, wadda ta yi nazarin mutane masu ciwon ajali, ta yi nuni ga wani ra’ayi tsakanin mutane masu addini. Da take kwatanta abin da ya faru, ta ce “ba shi da kyau a gaya wa ƙaramar yarinya da ƙaninta ya mutu cewa Allah yana son yara sosai shi ya sa ya ɗauki Johnny zuwa sama.” Irin wannan furci na kwatanta Allah a hanyar da ba ta dace ba kuma ba ya nuna mutuntakarsa da halinsa. Likita Kübler-Ross ta ci gaba ta ce: “Sa’ad da wannan yarinya ta yi girma ta zama mace ba ta daina yi wa Allah fushi ba, hakan ya sa ta motsu sa’ad da ɗanta ya mutu shekara talatin bayan haka.”

Me ya sa Allah zai kwaci yaro don ya samu wani mala’ika—sai ka ce Allah yana bukatar yaro fiye da iyayen yaron? Idan da gaske ne cewa Allah yana ɗaukan yara, wannan ba zai sa ya kasance marar ƙauna ba, Mahalicci mai son kai? Akasarin irin wannan ra’ayi, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙauna ta Allah ce.” (1 Yohanna 4:7) Allah mai ƙauna zai sa a yi hasara da mutane ma masu tunani ba za su amince da shi ba?

To, me ya sa yara suke mutuwa? Ɓangaren amsar Littafi Mai Tsarki yana rubuce a Mai-Wa’azi 9:11: “Dukansu lokacinsu da zarafinsu su kan zo.” Kuma Zabura 51:5 ta gaya mana cewa dukanmu ajizai ne, masu zunubi, daga lokacin haihuwarmu, kuma yanzu mutane sukan mutu daga abubuwa dabam dabam da yawa. Wani lokaci mutuwa ta kan zo kafin a haifi mutum, tana sa a yi ɓari. A wani lokaci, yara sukan mutu don yanayi na bala’i ko su yi haɗari su mutu. Ba Allah ba ne ke haddasa irin waɗannan abubuwa.

Ƙage na 4: Wasu mutane suna shan azaba bayan mutuwa.

Addinai da yawa suna koyar da cewa miyagu za su je wutar jahannama su sha azaba har abada. Wannan koyarwar gaskiya ne kuma daga Nassi? Rayuwar ’yan Adam shekaru 70 ne ko 80. Ko da mutum yana da laifin mugunta duk rayuwarsa, madawwamiyar azaba za ta kasance horo ta adalci kuwa? A’a. Ba zai kasance adalci ba a azabtar da mutum har abada don zunubi da ya yi a gajeruwar rayuwarsa.

Allah ne kaɗai zai iya bayyana abin da yake faruwa bayan mutum ya mutu, kuma ya yi hakan cikin rubutacciyar Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yadda [dabba] ke mutuwa, hakanan kuma [mutum]; i, lumfashi ɗaya ke garesu duka . . . Duk wuri ɗaya za su; duk na turɓaya ne, turɓaya kuma za su koma.” (Mai-Wa’azi 3:19, 20) Ba a ambaci wutar jahannama ba a nan. Mutane suna komawa turɓaya—rashin wanzuwa—yayin da suka mutu.

Don mutum ya sha azaba, zai kasance da rai. Matattu sun san abu ne? Har yanzu Littafi Mai Tsarki ya ba da amsa: “Masu-rai sun san za su mutu: amma matattu ba su san kome ba, ba su kuwa da sauran lada; gama ba a ƙara tuna da su ba.” (Mai-Wa’azi 9:5) Ba zai yiwu ba matattu, da “ba su san kome ba,” su sha azaba a ko’ina.

Ƙage na 5: Mutuwa na nufin ƙarshen wanzuwarmu har abada.

Muna daina wanzuwa yayin da muka mutu, amma wannan ba ya nufin cewa kome ya ƙare. Ayuba mutum mai aminci ya san zai je cikin kabari, Sheol, lokacin da ya mutu. Amma ka ji addu’arsa ga Allah: “Da fa za ka yarda ka ɓoye ni cikin Lahira, ka ɓoye ni har lokacinda fushinka ya wuce, ka sanya mini rana, sa’annan ka tuna da ni! Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa? . . . Za ka yi kira, ni ma in amsa maka.”—Ayuba 14:13-15.

Ayuba ya gaskata cewa idan ya kasance da aminci har abada, Allah zai tuna da shi ya tashe shi. Wannan ne imanin duka bayin Allah na lokacin dā. Yesu kansa ya tabbatar da wannan begen ya nuna cewa Allah zai yi amfani da shi ya ta da matattu. Kalmomin Kristi sun ba mu wannan tabbacin: “Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryar [Yesu], su fito kuma: waɗanda sun yi nagarta, su fito zuwa tashi na rai; waɗanda sun yi mugunta, zuwa tashi na shari’a.”—Yohanna 5:28, 29.

Jim kaɗan Allah zai cire dukan mugunta kuma ya kafa sabuwar duniya a ƙarƙashin mulkin samaniya. (Zabura 37:10, 11; Daniel 2:44; Ru’ya ta Yohanna 16:14, 16) Sakamakon zai zama aljanna bisa dukan duniya, da mutane da suke bauta wa Allah za su zauna. Cikin Littafi Mai Tsarki mun karanta: “Na ji babbar murya kuwa daga cikin kursiyin, ta ce, Duba, mazaunin Allah yana wurin mutane, za ya zauna tare da su kuma, za su zama al’ummai nasa, Allah kuma da kansa za ya zauna tare da su, ya zama Allahnsu: Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙinzuciya, ko kuka, ko azaba: al’amura na fari sun shuɗe.”—Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4.

’Yanci Daga Tsoro

Sanin begen tashin matattu da sanin Wanda shi ne tushen wannan tanadi zai ƙarfafa ka. Yesu ya yi alkawari: “Ku a san gaskiya kuma, gaskiya kuwa za ta yantadda ku.” (Yohanna 8:32) Wannan ya haɗa da ’yantar da mu daga tsoron mutuwa. Jehovah ne kaɗai zai iya canja tsarin tsufa da mutuwa kuma ya ba mu rai madawwami. Za ka iya gaskatawa da alkawuran Allah? I, za ka iya, domin Kalmar Allah tana da tabbaci. (Ishaya 55:11) Muna ƙarfafa ka ka ƙara koyo game da nufe-nufen Allah don mutane. Shaidun Jehovah za su yi murna su taimake ka.

[Bayanin da ke shafi na 6]

Matsalar tsoron mutuwa ita ce cewa za ta iya hana mutum ya more rayuwa

[Taswira a shafi na 7]

WASU ƘAGE GAME DA MUTUWA MENENE NASSOSI SUKA CE?

● Mutuwa ƙarshen rai ce Farawa 1:28; 2:17; Romawa 5:12

● Allah na ɗaukan mutane Ayuba 34:15 Zabura 37:11, 29;

su zauna da shi in sun 115:16

mutu

● Allah na ɗaukan yara su Zabura 51:5; 104:1, 4;

zama mala’iku Ibraniyawa 1:7, 14 1:7, 14

● Ana azabtar da wasu Zabura 146:4; Mai-Wa’azi 9:5, 10;

mutane bayan mutuwa Romawa 6:23

● Mutuwa tana nufin ƙarshen Ayuba 14:14, 15; Yohanna 3:16; 17:3;

wanzuwarmu har abada Ayukan Manzanni 24:15

[Hoto a shafi na 8]

Sanin gaskiya game da mutuwa yana ’yantar da mu daga tsoro

[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 5]

Barrators—Giampolo/The Doré Illustrations For Dante’s Divine Comedy/Dover Publications Inc.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba