Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 6/1 pp. 21-26
  • Ka Yi Murna Cikin Adalcin Jehovah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Murna Cikin Adalcin Jehovah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Neman Mizani na Adalci
  • Adalci da Ceto
  • Waɗanda Allah ke Ɗauka Masu Adalci
  • Murna Cikin Adalcin Jehovah
  • Ka Yi Ƙaunar Adalci Da Dukan Zuciyarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Ka Ci Gaba Da Biɗan “Adalcinsa” Da Farko
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Biɗan Adalci Zai Kāre Mu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2006
  • Bayin Jehobah Suna Son Adalci
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2022
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 6/1 pp. 21-26

Ka Yi Murna Cikin Adalcin Jehovah

“Waɗanda su ke jin daɗin gaskiyata bari su yi sowa domin farinciki, su yi murna kuma.”—ZABURA 35:27.

1. Waɗanne hanyoyi ne na mutane a yau ya kai ga sakamako na bala’i?

“AKWAI wata hanya wadda ta ke da alamar kirki ga mutum, amma matuƙatta tafarkun mutuwa ce.” (Misalai 16:25) Wannan karin magana na Littafi Mai Tsarki ya kwatanta daidai rayuwar yawancin mutane a yau! Galibi, mutane suna damuwa ne kawai da yin abin da ke daidai a nasu ra’ayi, suna ƙyale har bukatun rayuwa na wasu. (Misalai 21:2) Suna da’awa ce kawai game da dokoki da mizanai na ƙasa amma suna neman hanyoyi su guje hani da doka ta kafa ba tare da karya ta ba. Sakamakon haka, jama’a ce da ta rabu, kuma ta rikice.—2 Timothawus 3:1-5.

2. Menene ake bukata da gaggawa don amfanin ’yan Adam?

2 Don amfaninmu—da salama da kwanciyar hankali na dukan ’yan Adam—muna bukatar doka ko mizani na adalci, wanda dukan mutane za su amince da shi da yardar rai kuma su yi biyayya da shi. Hakika, babu doka ko mizani da mutum ya kafa, ko yaya hikima da gaskiyar wannan mutumin da zai biya wannan bukata. (Irmiya 10:23; Romawa 3:10, 23) Idan irin wannan mizani ya kasance, ina za a samu kuma yaya kamarsa? Wataƙila tambaya da ta fi muhimmanci ita ce, idan irin wannan mizani ya kasance, za ka karɓe shi ba tare da wani musu ba?

Neman Mizani na Adalci

3. Waye ya fi cancanta ya ba da mizani da dukan mutane za su amince da shi kuma su amfana, kuma me ya sa?

3 Don mu nemi mizani da kowa zai amince da shi kuma ya amfana, za mu je wurin wanda ya fi dukan ƙabila, al’ada, da siyasa da wanda rashin fahimi da kasawa na mutane ba za su hana shi ba. Babu shakka, wanda ya cancanta sosai Mahalicci maɗaukaki, Jehovah Allah ne wanda ya ce: “Kamar yadda sammai suna da nisa da duniya, hakanan kuma al’amurana sun fi naku tsawo, tunanina kuma sun fi naku.” (Ishaya 55:9) Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya kwatanta Jehovah “Allah mai-aminci ne, mara-mugunta, kuma, mai-adalci ne shi mai-gaskiya.” (Kubawar Shari’a 32:4) A duk cikin Littafi Mai Tsarki, mun samu furcin nan “Ubangiji mai-adalci ne.” (2 Labarbaru 12:6; Zabura 11:7; 129:4; Makoki 1:18) Hakika, za mu iya zuba wa Jehovah ido don mizanai domin shi mai aminci ne, mai gaskiya, da adalci.

4. Mecece kalmar nan ‘adali’ take nufi?

4 Hakika, kalmar nan ‘adali’ ba a yawar son ta a yau. Yawancin mutane suna ƙi, har ma suna baƙar magana game da mutane da suke ji sun fi wasu adalci ko tsarki. Amma, in ji wani ƙamus, ‘adali’ tana nufin “mai gaskiya, halin kirki; marar laifi, marar zunubi; bin ƙa’idodi na dokar Allah ko mizanai na tarbiyya da aka amince da shi; aika daidai.” Ba za ka yi murna da doka ko mizani da ya ƙunshi irin wannan halaye masu kyau ba?

5. Ka kwatanta hali na adalci da aka nuna cikin Littafi Mai Tsarki.

5 Game da hali na adalci, Encyclopaedia Judaica ya lura: “Adalci ba ra’ayi da ba a ganewa ba ne amma ya ƙunshi yin abin da ke da kyau, abin da yake daidai a dukan dangantaka.” Alal misali, adalcin Allah ba kawai hali na ciki ba ko na kansa da yake da shi kamarsu kasancewarsa da tsarki. Maimakon haka, nuna mutuntakarsa ne a hanyoyi da ke daidai da adalci. Ana iya faɗi cewa domin Jehovah yana da tsarki, kome da yake yi da kome da ke fitowa daga wurinsa nagari ne. Yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa, “Ubangiji mai-adalci ne cikin dukan tasarrufinsa, mai-alheri ne cikin dukan ayyukansa.”—Zabura 145:17.

6. Menene Bulus ya faɗa game da wasu Yahudawa na zamaninsa da su marasa bi ne, kuma me ya sa?

6 Manzo Bulus ya nanata wannan a wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci a Roma. Game da wasu Yahudawa marasa bi, ya rubuta: “Gama yayinda suka rasa sanin adalcin Allah, suna kuwa biɗa su kafa na kansu, ba su yi biyayya da adalcin Allah ba.” (Romawa 10:3) Me ya sa Bulus ya ce waɗannan sun “rasa sanin adalcin Allah”? Ba a koyar da su cikin Doka, mizanan Allah na adalci ba ne? Hakika an koyar da su. Amma, yawancinsu suna ɗaukar adalci halin kirki ne na mutum, da za a cim ma ta wajen azabtar da kai, wajen kiyaye dokokin addinai masu wuya, maimakon bin mizani na adalci da zai yi musu ja-gora a yadda suke bi da mutane. Kamar shugabannan addinai na zamanin Yesu, ba su fahimci ainihin ma’anar shari’a da adalci ba.—Matta 23:23-28.

7. Ta yaya Jehovah ya nuna adalci?

7 Da bambanci kuwa, adalcin Jehovah yana bayyana kuma ana gani sarai cikin duk sha’aninsa. Ko da yake adalcinsa bai bukaci ya ƙyale zunubai na masu zunubi da gangan ba, wannan bai sa ya zama Allah marar juyayi, mai neman laifi ba, da za a ji tsoronsa a ƙi kusantarsa. Akasarin haka, ayyukansa na adalci ya yi tanadin tushe da mutane za su iya kusantar shi kuma a cece su daga sakamakon zunubi. Saboda haka ya dace da aka kwatanta Jehovah “Allah mai-adalci mai-ceto.”—Ishaya 45:21.

Adalci da Ceto

8, 9. A waɗanne hanyoyi ne Doka ke nuna adalcin Allah?

8 Don mu fahimci nasaba da ke tsakanin adalcin Allah da ayyukansa na ceto, yi la’akari da Doka da ya ba al’ummar Isra’ila ta bakin Musa. Babu shakka cewa Dokar tana da adalci. A kalmominsa na ƙarshe, Musa ya tuna wa Isra’ilawa: “Ina kuma al’umma mai-girma wadda ta ke da farillai da shari’u masu-adalci haka kamar dukan wannan shari’a, wadda na sanya a gabanku yau?” (Kubawar Shari’a 4:8) Ƙarnuka bayan haka, Sarki Dauda na Isra’ila ya ce: “Hukuntai na Ubangiji masu-gaskiya ne, masu-adalci ne dukansu.”—Zabura 19:9.

9 Ta wurin Dokar, Jehovah ya bayyana cikakken mizanansa na nagarta da mugunta. Dokar ta bayyana dalla-dalla yadda Isra’ilawa za su bi da kansu ba kawai a batutuwan addini ba amma har da sha’anin kasuwanci, aure, abinci, tsabta da kuma hukunci. Dokar ta ƙunshi abin da za a yi wa masu karya ta, har da hukuncin kisa a wasu yanayi.a Amma farillan Allah na adalci yadda yake cikin Doka, nauyaya ce mai wuya mai gajiyar da mutane, tana hana su ’yancinsu da farin ciki, yadda mutane da yawa a yau suke da’awa?

10. Yaya waɗanda suke ƙaunar Jehovah suke ji game da dokokinsa?

10 Waɗanda suke ƙaunar Jehovah sun samu farin ciki mai yawa a dokokinsa da umurnai na adalci. Alal misali, Sarki Dauda ba kawai ya yarda cewa hukunci na Jehovah gaskiya ne kuma masu adalci ba, yadda muka gani, amma yana sonsa kuma yana yin godiya daga zuciyarsa game da su. Game da dokoki da hukuntai na Jehovah, ya rubuta: “Abin marmari ne gaba da zinariya, i, gaba da yawan zinariya mai-kyau: sun fi zuma zaƙi da kuma saƙar zuma. Kuma ta wurinsu a kan hori bawanka; kuma cikin kiyaye su da lada mai-girma.”—Zabura 19:7, 10, 11.

11. Ta yaya Dokar ta zama “mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi”?

11 Ƙarnuka bayan haka, Bulus ya nuna amfanin Dokar da ya fi girma. A wasiƙarsa zuwa ga Galatiyawa, ya rubuta: “[Dokar] ta zama mai-tsaronmu shi kai mu ga Kristi, domin a baratadda mu ta wurin bangaskiya.” (Galatiyawa 3:24) A zamanin Bulus, mai koyarwa (malami, Kingdom Interlinear) bara ko kuma bawa ne a babban iyali. Aikinsa ne ya tsare yaran kuma ya raka su zuwa makaranta. Hakanan, Dokar ta tsare Isra’ilawa daga lalatattun ɗabi’a da ayyuka na addini na al’ummai da suke kewaye su. (Kubawar Shari’a 18:9-13; Galatiyawa 3:23) Ƙari ga haka, Dokar ta sa Isra’ilawa suka san yanayinsu na zunubi da bukatar da suke da ita na gafara da ceto. (Galatiyawa 3:19) Sharuɗa na hadaya ya nuna cewa suna bukatar hadayar fansa kuma ya yi tanadin gurbi na annabci da za a gane Almasihu na gaskiya. (Ibraniyawa 10:1, 11, 12) Da haka, yayin da Jehovah ya nuna adalcinsa ta Dokar, ya yi haka cikin la’akari da lafiyar mutanen da cetonsu na madawwama.

Waɗanda Allah ke Ɗauka Masu Adalci

12. Da menene Isra’ilawa za su samu ta kiyaye Dokar?

12 Tun da Dokar da Jehovah ya bayar tana da adalci a kowacce hanya, ta yin biyayya da ita, da Isra’ilawan za su samu tsayawa mai kyau a gaban Allah. Musa ya tuna wa Isra’ilawa da suke so su shiga Ƙasar Alkawari: “Za ya zama adalci garemu kuma, idan mun kiyaye dukan wannan umurni garin mu aikata a gaban Ubangiji Allahnmu, kamar yadda ya umurce mu.” (Kubawar Shari’a 6:25) Ƙari ga haka, Jehovah ya yi alkawari: “Za ku fa kiyaye farillaina, da shari’una: waɗanda idan mutum ya yi su, za ya rayu ta wurinsu: ni ne Ubangiji.”—Leviticus 18:5; Romawa 10:5.

13. Rashin adalci ne da Jehovah ya bukaci mutanensa su kiyaye Doka mai adalci? Ka yi bayani.

13 Abin baƙin ciki, al’ummar Isra’ilawa suka kasa “kiyaye dukan wannan umurni . . . a gaban Ubangiji.” Sun kasa kiyaye dukan umurnin Allah domin Dokar Allah cikakkiya ce amma su ba cikakku ba ne. Wannan yana nufin cewa Allah marar adalci ne? Hakika babu. Bulus ya rubuta: “Me za mu ce fa? Da rashin adalci tare da Allah? Daɗai!” (Romawa 9:14) Gaskiyar ita ce, wasu mutane, kafin da bayan da aka ba da Dokar, Allah ya ɗauka su masu adalci ko da su ajizai ne da masu zunubi. Jerin irin wannan mutane masu tsoron Allah sun haɗa da Nuhu, Ibrahim, Ayuba, Rahab, da Daniel. (Farawa 7:1; 15:6; Ayuba 1:1; Ezekiel 14:14; Yaƙub 2:25) To, tambayar ita ce: Bisa menene Allah ya lissafa waɗannan mutane masu adalci?

14. Menene Littafi Mai Tsarki yake nufi yayin da ya ce “mutum mai-adalci”?

14 Sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya yi maganar mutane masu “adalci,” ba ya nufin cewa su ba masu zunubi ba ko kamiltattu. Maimako, yana nufin mutum ya cika wajibansa ne a gaban Allah da mutane. Alal misali, an kira Nuhu “mutum mai-adalci” da “mara-aibi ne cikin tsararakinsa” domin “ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.” (Farawa 6:9, 22; Malachi 3:18) Zakariya da Alisabatu, iyayen Yohanna Mai Baftisma “masu-adalci ne a gaban Allah, suna tafiya cikin dokokin Ubangiji da farillansa duka ba laifi.” (Luka 1:6) Wani da ba Ba’isra’ile ba ne, soja na Italiya mai suna Karniliyus, an kwatanta shi da “mutum mai-adalci, mai-tsoron Allah.”—Ayukan Manzanni 10:22.

15. Da menene adalci yake da nasaba?

15 Bugu da ƙari, adalci cikin mutane yana da nasaba sosai da abin da yake zuciyar mutum—bangaskiya, godiya da ƙauna ga Jehovah da alkawarinsa—ba kawai mutum ya yi abin da Allah ke bukata ba. Nassosi ya ce Ibrahim “Ya fa bada gaskiya ga Ubangiji; shi kuma ya lissafa wannan adalci ne gareshi.” (Farawa 15:6) Ibrahim ya ba da gaskiya ba kaɗai cewa Allah yana wanzuwa ba amma kuma ga alkawarinsa game da “zuriya.” (Farawa 3:15; 12:2; 15:5; 22:18) Bisa irin wannan bangaskiya da ayyuka cikin jituwa da bangaskiyar, Jehovah ya yi sha’ani da mutane kuma ya albarkaci Ibrahim da wasu masu aminci ko da yake ajizai ne.—Zabura 36:10; Romawa 4:20-22.

16. Menene ba da gaskiya cikin fansa ya kawo?

16 A ƙarshe, adalci cikin mutane ya dangana a kan bangaskiya ga hadayar fansa na Yesu Kristi. Game da Kiristoci a ƙarni na farko, Bulus ya rubuta: “Bisa ga alherin [Allah] an barata a yalwace ta wurin fansa da ke cikin Yesu Kristi.” (Romawa 3:24) Bulus a wurin yana magana ne game da waɗanda aka zaɓa su zama magāda da Kristi a Mulkin samaniya. Amma hadayar fansa na Yesu ya buɗe wa wasu miliyoyi zarafin samu tsayawa na adalci a gaban Allah. Manzo Yohanna ya ga a wahayi “taro mai-girma, wanda ba mai-ƙirgawa, . . . suna tsaye gaban kursiyin da gaban Ɗan ragon, suna yafe da fararen riguna.” Fararen riguna na alamta cewa suna da tsabta da adalci a gaban Allah domin sun “wanke rigunansu, suka faranta su cikin jinin Ɗan ragon kuma.”—Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14.

Murna Cikin Adalcin Jehovah

17. Waɗanne matakai dole ne a ɗauka in za a biɗi adalci?

17 Yayin da Jehovah cikin ƙauna ya ba da Ɗansa, Yesu Kristi, hanyar da mutane za su samu tsayawa na adalci a gabansa, sakamako na tsayawa na adalci ba haka kawai ba. Dole ne mutum ya ba da gaskiya a fansar, ya kawo rayuwarsa cikin jituwa da nufin Allah, ya keɓe kansa ga Jehovah, ya nuna alamar ta baftisma cikin ruwa. Sa’annan, mutum zai ci gaba da biɗan adalci, da wasu halaye na ruhaniya. Bulus ya gargaɗi Timothawus, Kirista da ya yi baftisma da an kira shi zuwa sama: “Ka bi adalci, ibada, bangaskiya, ƙauna, haƙuri, tawali’u.” (1 Timothawus 6:11; 2 Timothawus 2:22) Yesu kuma ya nanata bukatar mu ci gaba da ƙoƙari yayin da ya ce: “Ku [ci gaba da] biɗan mulkinsa, da adalcinsa.” Za mu yi aiki tuƙuru mu nemi albarka na Mulkin Allah, amma muna kuma aiki tuƙuru mu biɗi hanyoyin adalci na Jehovah?—Matta 6:33.

18. (a) Me ya sa ba shi da sauƙi a biɗi adalci? (b) Menene za mu koya daga misalin Lutu?

18 Babu shakka, ba shi da sauƙi a biɗi adalci. Wannan domin dukanmu ajizai ne kuma halinmu game da rashin adalci ne. (Ishaya 64:6) Bugu da ƙari, mutane da ba ruwansu da hanyoyin adalci na Jehovah ne suka kewaye mu. Yanayinmu na kama da na Lutu, wanda yake da zama cikin mugun birni da aka sani na Saduma. Manzo Bitrus ya yi bayanin abin da ya sa Jehovah ya ga ya dace ya ceci Lutu daga halaka mai zuwa. Bitrus ya ce: “Wannan mai-adalci da ya ke zaune a tsakiyarsu, yana gani yana ji, yau da gobe ya azabatadda ransa mai-adalci domin ayyukansu marasa-shari’a.” (2 Bitrus 2:7, 8) Saboda da haka, zai yi kyau kowannenmu ya tambayi kansa ko kanta, ‘Ina so a cikin zuciyata ayyukan lalata da muke gani kewaye da mu? Ina ganin nishaɗi ko wasanni da ke ko’ina kawai cewa ba su da kyau? Ko kuma ayyukan nan marasa adalci suna damu na yadda suka yi wa Lutu?’

19. Wace albarka ce za mu samu idan muka yi murna cikin adalcin Allah?

19 A wannan kwanaki na haɗari da rashin tabbaci, yin murna cikin adalcin Jehovah shi ne tushen kwanciyar rai da kāriya. Ga tambayar nan: “Ya Ubangiji, wa za ya sauka cikin [tanti] naka? Wanene za ya zauna cikin tudunka mai-tsarki?” Sarki Dauda ya amsa: “Shi wanda ke tafiya sosai, yana aika adalci.” (Zabura 15:1, 2) Ta biɗan adalcin Allah da yin murna a ciki, za mu riƙe dangantaka mai kyau da shi kuma mu ci gaba da moran alherinsa da albarka. Da haka, rayuwarmu za ta zama na wadar zuci, mutunci da kwanciyar rai. Kalmar Allah ta ce, “wanda ya bi adalci da jinƙai rai ya ke samu, da adalci, da girma.” (Misalai 21:21) Bugu da ƙari, yin iyakar ƙoƙarinmu mu yi abin da ke gaskiya da daidai zai kawo dangantaka ta farin ciki da kyautata ingancin rayuwa—a ɗabi’a da ruhaniya. Mai Zabura ya ce: “[Masu-farin ciki] ne su waɗanda ke tsaron shari’a, da shi wanda ya kan aika adalci kullayaumi.”—Zabura 106:3.

[Hasiya]

a Don ƙarin bayani game da faɗin Dokar Musa, ka duba talifi “Some Features of the Law Covenant,” a shafofi 214-220 a littafi na 2 na Insight on the Scriptures da Shaidun Jehovah suka buga.

Za Ka Iya Bayyanawa?

• Menene adalci?

• Ta yaya ceto yake da nasaba da adalcin Allah?

• Bisa menene Allah yake lissafa mutane cikin masu adalci?

• Ta yaya za mu yi murna cikin adalcin Jehovah?

[Hotuna a shafi na 23]

Sarki Dauda ya furta son dokokin Allah daga zuciya

[Hotuna a shafi na 24]

Nuhu, Ibrahim, Zakariya da Alisabatu, da Karniliyus Allah ya lissafa su masu adalci. Ka san abin da ya sa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba