Biɗan Adalci Zai Kāre Mu
“Ku fara biɗan . . . adalcinsa [Allah].”—MATTA 6:33.
1, 2. Wane mataki ne wata matashiya Kirista ta ɗauka, kuma me ya sa ta ɗauki wannan matakin?
WATA Kirista matashiya a Asiya tana aikin sakatare a ofishin gwamnati. Tana mai da hankali ga aikinta, tana zuwa aiki a kan lokaci kuma ba ta wasa da aiki. Amma, aikinta ba na dindindin ba ne, jifa jifa ana iya sake ma’aikaci. Shugaban ma’aikatar ya gaya wa matashiyar cewa zai ba ta aiki na dindindin kuma zai ba ta babban matsayi, idan ta yarda ta yi lalata da shi. Ba tare da jinkiri ba ta ƙi, ko da yake ta sani za a kore ta a aiki.
2 Wannan matashiya Kirista abin da ta yi ba daidai ba ne? Hakika, tana bin kalmomin Yesu ne sau da ƙafa: “Ku fara biɗan . . . adalcinsa [Allah].” (Matta 6:33) A gare ta bin mizanai na adalci ya fi muhimmanci da samun dukiya ta wurin yin fasikanci.—1 Korinthiyawa 6:18
Muhimmancin Adalci
3. Menene adalci?
3 “Adalci” yana nufin kasancewa mai tarbiyya da kuma gaskiya. A Littafi Mai Tsarki, kalmomin Helenanci da kuma Ibrananci na adalci suna nufin “miƙeƙƙe” ko “marar nuƙu nuƙu.” Ba adalci ba ne na kai, da mutum zai riƙa gwada kansa da na shi mizani. (Luka 16:15) Adalci ne bisa mizanai na Jehobah. Adalci ne na Allah.—Romawa 1:17; 3:21.
4. Me ya sa adalci yake da muhimmanci ga Kiristoci?
4 Me ya sa adalci yake da muhimmanci? Domin Jehobah, ‘Allah mai adalci’ yana yi wa mutanensa tagomashi sa’ad da suka yi adalci. (Zabura 4:1; Misalai 2:20-22; Habakuk 1:13) Dukan wanda yake yin rashin adalci ba zai kasance kusa da Allah ba. (Misalai 15:8) Abin da ya sa ke nan Bulus ya aririci Timothawus: “Ka guje ma sha’awoyin ƙuruciya, ka yi ta bin adalci,” da kuma wasu halaye masu muhimmanci. (2 Timothawus 2:22) Abin da ya sa ke nan, da Bulus ya lissafa ɓangarori dabam dabam na makami na ruhaniya, ya haɗa da “sulke na adalci.”—Afisawa 6:14.
5. Ta yaya halittu ajizai za su biɗi adalci?
5 Hakika, babu ɗan adam da yake mai adalci ne marar aibi ko kaɗan. Dukanmu mun gaji ajizanci daga Adamu, kuma dukanmu masu zunubi ne, marasa adalci, tun daga lokacin da aka haife mu. Duk da haka, Yesu ya ce mu biɗi adalci. Ta yaya hakan zai yiwu? Domin Yesu ya ba da ransa kamiltacce fansa dominmu, idan kuma muka ba da gaskiya ga wannan hadaya, Jehobah zai gafarta mana zunubanmu. (Matta 20:28; Yohanna 3:16; Romawa 5:8, 9, 12, 18) Domin wannan, idan muka koyi mizanan adalci na Jehobah kuma muka ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu mu kiyaye su, kuma muna yin addu’a domin mu kawar da raunanarmu, Jehobah zai karɓi bautarmu. (Zabura 1:6; Romawa 7:19-25; Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Hakan yana ba da ƙarfafa!
Masu Adalci a Duniya Marar Adalci
6. Me ya sa duniya muguwar wuri ce ga Kiristoci?
6 Sa’ad da aka umurci almajiran Yesu su zama shaidunsa ‘har iyakan duniya,’ sun fuskanci yanayi mai wuya. (Ayukan Manzanni 1:8) Dukan yankinsu yana “kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Duniya tana cike da mugun hali da Shaiɗan yake yaɗawa, kuma rinjayarsa zai shafi Kiristoci. (Afisawa 2:2) Duniya muguwar wuri ce ga Kiristoci. Sai dai kawai idan suka biɗi adalcin Allah za su jimre su riƙe amincinsu. Da yawa sun jimre, amma kaɗan sun kauce daga “hanyar adalci.”—Misalai 12:28; 2 Timothawus 4:10.
7. Waɗanne yanayi ne suka bukaci Kiristoci su tsayayya wa rinjaya ta lalata?
7 Duniya ba ta da haɗari ne a yau ga Kiristoci? Da yawa kuwa! Ta ma fi muni a yau fiye da ƙarni na farko. Ƙari ga haka, an jefo da Shaiɗan zuwa duniya kuma yana yaƙi cikin fushi da Kiristoci shafaffu, “sauran zuriyanta [matar], waɗanda su ke kiyaye dokokin Allah, suna riƙe da shaidar Yesu.” (Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Shaiɗan yana kuma kai hari ga dukan wanda yake taimakon “zuriyar.” Duk da haka, Kiristoci ba za su iya ɓuya ba daga duniya. Ko da yake su ba na duniya ba ne, dole ne su rayu cikinta. (Yohanna 17:15, 16) Kuma dole ne su nemi mutane masu zukatan kirki kuma su koyar da su su zama almajiran Kristi. (Matta 24:14; 28:19, 20) Saboda haka, tun da Kiristoci ba za su iya guje wa dukan rinjaya ta lalata ta wannan duniya ba, dole ne su tsayayya mata. Bari mu bincika huɗu cikin waɗannan abubuwa.
Tarkon Lalata
8. Me ya sa Isra’ilawa suka koma ga bauta wa allolin Mowabawa?
8 A kusa da ƙarshen shekara 40 na tafiya a cikin daji, Isra’ilawa da yawa sun juya daga bin hanyar adalci. Sun ga yadda Jehobah ya cece su sau da yawa, kuma ba da daɗewa ba za su shiga Ƙasar Alkawari. Duk da haka, a wannan lokaci mai muhimmanci suka koma ga bauta wa allolin Mowabawa. Me ya sa? Sun faɗa wa “sha’awar idanu.” (1 Yohanna 2:16) Tarihi ya nuna cewa: “Mutane kuwa suka fara yin fasikanci da ’yan matan Moab.”—Litafin Lissafi 25:1.
9, 10. Wane yanayi ne a yau ya sa ya zama da muhimmanci mu riƙa tuna yadda sha’awar idanu take da ikon lalatarwa?
9 Wannan abin da ya faru ya nuna yadda sha’awa ta ido za ta iya lalata marasa kula. Ya kamata mu koya daga wannan, musamman ma da yake lalata ta sami karɓuwa a ko’ina. (1 Korinthiyawa 10:6, 8) Wani rahoto daga Amirka ya ce: “Kafin shekara ta 1970, ba a yarda da jima’i ba [tsakanin marasa aure] a dukan jihohin ƙasar Amirka. Amma yanzu abu ne na yau da kullum. Fiye da rabin dukan waɗanda suka yi auren fari sai da suka yi jima’i da junansu.” Wannan da kuma wasu ayyukan lalata ba su tsaya a ƙasa ɗaya ba kawai. Suna faruwa a dukan duniya, kuma abin baƙin ciki, wasu Kiristoci sun bi wannan hanyar, har suna hasarar matsayinsu a ikilisiya.—1 Korinthiyawa 5:11.
10 Bugu da ƙari, talla da take yaɗa lalata ta cika ko’ina. Silima da wasanni na telibijin suna nuna cewa daidai ne matasa su yi jima’i kafin su yi aure. Yin luwaɗi ba laifi ba ne. A wasanni da yawa ana jima’i. Samun hoton jima’i ba shi da wuya a Intane. Alal misali, wani marubucin jarida ya ba da rahoto cewa ɗansa ɗan shekara bakwai ya dawo gida daga makaranta da farin ciki ya gaya wa babansa cewa abokinsa a makaranta ya sami wurin da ake nuna hotunan mata tsirara suna yin jima’i. Baban ya fusata, amma yara nawa ne suka ga irin wannan wurin ba tare da gaya wa iyayensu ba? Bugu da ƙari, iyaye nawa ne suka san irin wasan bidiyon da ’ya’yansu suke yi? Wasannin bidiyo da yawa suna ɗauke da lalata, da shaiɗanci, da nuna ƙarfi.
11. Ta yaya za a kāre iyali daga lalata ta wannan duniyar?
11 Ta yaya iyali za ta guji irin wannan mugun “nishaɗi”? Ta wajen biɗan adalcin Allah, ta wajen ƙin saka hannu a dukan wani abin da yake na lalata. (2 Korinthiyawa 6:14; Afisawa 5:3) Iyaye da suke kula da ayyukan ’ya’yansu kuma suke koya wa yaransu, ƙaunar Jehobah da kuma adalcinsa suna kāre su daga hotunan batsa, fim na batsa, da kuma wasu jaraba na rashin adalci.—Kubawar Shari’a 6:4-9.a
Haɗarin Matsi na Jama’a
12. Wace matsala ce ta taso a ƙarni na farko?
12 Sa’ad da Bulus yake Listra a Asiya Ƙarama, ya warkar da mutum cikin mu’ujiza. Labarin ya ce: “Sa’anda taro suka ga abin da Bulus ya yi, suka tada muryassu, da harshen Lika’oniya suka ce, Allohi sun sauko a wurinmu da kamanin mutane. Suka ce da Barnaba, Zafsa; Bulus kuwa suka ce da shi, Harmasa, gama shi ne magabci cikin zance.” (Ayukan Manzanni 14:11, 12) Daga baya waɗannan mutanen suka yi ƙoƙari su kashe Bulus da Barnaba. (Ayukan Manzanni 14:19) A bayyane yake cewa rinjayar jama’a yana shafan waɗannan mutane. Kamar dai wasu da suka zama Kirista daga wannan yankin ba su bar camfe-camfensu ba. A wasiƙarsa zuwa Kiristoci a Kolossi, Bulus ya yi gargaɗi game da “yin sujada ga mala’iku.”—Kolossiyawa 2:18.
13. Waɗanne al’adu ne ya kamata Kirista ya guje wa, kuma a ina zai sami ƙarfin yin haka?
13 A yau, Kiristoci na gaskiya suna bukatar su guje wa al’adu da aka yi na’am da su da suka samo asalinsu daga addinan ƙarya da suka taka mizanai na Kirista. Alal misali, a wasu ƙasashe, al’adu da yawa game da biki na haihuwa da kuma na mutuwa sun samo asali ne daga ƙarya cewa muna da kurwa da take tsira bayan mun mutu. (Mai-Wa’azi 9:5, 10) Da kuma wasu ƙasashe da ake yi wa mata lahani.b Mugunta ce wannan, da ba ta dace ba da ƙauna da iyaye Kiristoci ya kamata su nuna wa ’ya’yansu ba. (Kubawar Shari’a 6:6, 7; Afisawa 6:4) Ta yaya Kiristoci za su tsayayya wa matsi na jama’a kuma su guji irin waɗannan ayyuka? Ta wajen dogara ga Jehobah. (Zabura 31:6) Allah mai adalci zai ƙarfafa kuma ya kula da waɗanda suka ce masa daga zukatansu: ‘Kai ne mafakata da marayata kuma; Allahna, a gare ka ni ke dogara.’—Zabura 91:2; Misalai 29:25.
Kada Ka Manta da Jehobah
14. Wane gargaɗi Jehobah ya yi wa Isra’ilawa kafin su shiga Ƙasar Alkawari?
14 Ba da daɗewa ba kafin Isra’ilawa su shiga Ƙasar Alkawari, Jehobah ya yi musu gargaɗi cewa kada su manta shi. Ya ce: “Ka yi lura kada ka manta da Ubangiji Allahnka, da ba za ka kiyaye dokokinsa da shari’unsa, da farillansa, waɗanda na umurce ka da su yau: kada ya zama lokacinda ka ci ka ƙoshi, ka gina gidaje na ƙwarai, ka zauna ciki; kuma sa’anda garkunanka na shanu da na tumaki sun ƙaru, azurfarka da zinariyakka sun yawaita, dukan abin da ka ke da shi kuwa ya yawaita; sa’annan zuciyarka ta kumbura, har ka manta da Ubangiji Allahnka.”—Kubawar Shari’a 8:11-14.
15. Ta yaya za mu tabbata cewa ba mu manta da Jehobah ba?
15 Irin wannan abin zai faru kuwa a yau? Hakika, idan makasudinmu ba su da kyau. Idan muka biɗi adalcin Allah, bauta ta gaskiya za ta zama aba mafi muhimmanci a rayuwarmu. Za mu yi kamar yadda Bulus ya ƙarfafa mu mu yi, mu ‘rifta zarafi’ kuma mu kasance muna tuna gaggawar hidimarmu. (Kolosiyawa 4:5; 2 Timothawus 4:2) Amma kuma idan shakatawa da nishaɗi suka fi halartar taro da kuma wa’azi muhimmanci a gare mu, to, za mu manta da Jehobah wato ta wajen ba shi wuri na biyu a rayuwarmu. Bulus ya ce a kwanaki na ƙarshe, mutane za su zama masu “son annishuwa da Allah.” (2 Timothawus 3:4) Kiristoci masu gaskiya suna bincika kansu a kai a kai domin su tabbata cewa irin wannan tunanin bai rinjaye su ba.—2 Korinthiyawa 13:5.
Ka Guje wa Halin Neman ’Yancin Kai
16. Wane hali ne marar kyau Hauwa’u da kuma wasu a zamanin Bulus suka nuna?
16 A Adnin, Shaiɗan ya yi nasara wajen rinjayar sha’awar ’yanci na Hauwa’u. Hauwa’u tana so ta yanke shawara da kanta game da abin da ke mai kyau da marar kyau. (Farawa 3:1-6) A ƙarni na farko, wasu a ikilisiyar Koranti suna da irin wannan halin neman ’yanci. Suna tsammanin cewa suna da sani fiye da Bulus, shi ya sa ya kushe su ya kira su mafifitan manzanni.—2 Korinthiyawa 11:3-5; 1 Timothawus 6:3-5.
17. Ta yaya za mu guje wa koyon halin neman ’yanci?
17 A duniya ta yau, mutane da yawa “masu-taurin kai, masu-kumbura” ne, kuma irin wannan rayuwa ta rinjayi wasu Kiristoci. Har wasu suka zama masu hamayya da gaskiya. (2 Timothawus 3:4; Filibiyawa 3:18) Idan ya zo ga bauta ta gaskiya, yana da muhimmanci mu nemi ja-gora daga Jehobah kuma mu ba da haɗin kai ga “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” da kuma dattawa na ikilisiya. Wannan hanya ce ta biɗan adalci, kuma za ta kāre mu daga koyon hali na ’yanci. (Matta 24:45-47; Zabura 25:9, 10; Ishaya 30:21) Ikilisiyar shafaffu “jigon gaskiya da ƙarfinta” ce. Jehobah ya yi tanadinta domin ta kāre kuma ta yi mana ja-gora. (1 Timothawus 3:15) Fahimtar matsayinsa mai muhimmanci zai taimake mu kada mu yi ‘kome domin girman kai’ sa’ad da muka miƙa kai ga nufin Jehobah.—Filibiyawa 2:2-4; Misalai 3:4-6.
Ka Yi Koyi da Yesu
18. A wace hanya aka ƙarfafa mu mu yi koyi da Yesu?
18 Littafi Mai Tsarki ya ce cikin annabci game da Yesu: “Ka yi ƙaunar adalci, ka ƙi mugunta.” (Zabura 45:7; Ibraniyawa 1:9) Lalle wannan halin kirki ne da ya kamata mu koya! (1 Korinthiyawa 11:1) Yesu ya san mizanan adalci na Jehobah; kuma ya ƙaunace su. Saboda haka sa’ad da Shaiɗan ya jarabe shi a cikin daji, Yesu bai yi wani jinkiri ba wajen ƙin ya kauce daga “hanyar adalci.”—Misalai 8:20; Matta 4:3-11.
19, 20. Menene albarkar biɗan adalci?
19 Hakika, muradi marar kyau na jiki zai kasance da ƙarfi. (Romawa 7:19, 20) Duk da haka, idan adalci yana da kyau a gare mu, wannan zai ƙarfafa mu wajen ƙin mugunta. (Zabura 119:165) Ƙauna mai ƙarfi ta adalci za ta kāre mu, sa’ad da muka fuskanci yin abin da ke mugu. (Misalai 4:4-6) Ka tuna, dukan lokaci da muka faɗa wa jaraba, to mun ba wa Shaiɗan nasara. Ya fi kyau mu tsayayya masa mu ba wa Jehobah nasara!—Misalai 27:11; Yaƙub 4:7, 8.
20 Domin sun biɗi adalci, Kiristoci na gaskiya an cika su da “ ’ya’yan adalci, waɗanda sun kasance zuwa darajar Allah da yabonsa ta wurin Yesu Kristi.” (Filibiyawa 1:10, 11) Sun yafa “sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afisawa 4:24) Sun kasance na Jehobah kuma suna raye domin su bauta masa, ba domin su faranta wa kansu rai ba. (Romawa 14:8; 1 Bitrus 4:2) Wannan ne yake ja-gorar tunaninsu da kuma ayyukansu. Suna faranta wa Ubansu na samaniya rai ƙwarai!—Misalai 23:24.
[Hasiya]
a Za a iya samun shawarwari masu muhimmanci ga iyaye game da yadda za su kāre iyalansu a cikin littafin nan Asirin Farinciki na Iyali, Shaidun Jehobah ne suka wallafa.
b Ana kiran shi kaciya.
Za Ka Iya Ba da Bayani?
• Me ya sa biɗan adalci yake da muhimmanci?
• Ta yaya Kirista ajizi zai biɗi adalci?
• Waɗanne abubuwa ne a duniya ya kamata Kirista ya guje musu?
• Ta yaya biɗan adalci yake kāre mu?
[Hoto a shafi na 28]
Ga mabiyan Kristi duniya muguwar wuri ce
[Hoto a shafi na 29]
Yara da aka koya musu su ƙaunaci Jehobah za su ƙarfafa wajen ƙin lalata
[Hoto a shafi na 30]
Wasu Isra’ilawa sun manta da Jehobah bayan sun sami wadata a Ƙasar Alkawari
[Hoto a shafi na 31]
Kamar Yesu, Kiristoci suna ƙin mugunta