Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 7/1 pp. 10-15
  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bi Tafarkin Sarakuna
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koya Kamar Sarki
  • Aiki Domin Sarakuna Kuma Domin Ka
  • Amfani Dominka da Kuma Wasu
  • Ka Inganta Yadda Kake Nazari!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
  • Karatun Littafi Mai Tsarki—Mai Amfani Kuma Mai Daɗi
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ku Yi Matuƙar Amfani Da Lokaci Don Karatu Da Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2000
  • Ka Riƙe Kalmar Allah Gam
    Ka Bauta wa Allah Maƙadaici na Gaskiya
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 7/1 pp. 10-15

Ka Bi Tafarkin Sarakuna

“Za ya sāke wannan shari’a cikin littafi, . . . za ya zauna tare da shi kuwa, za ya riƙa karantawa daga ciki dukan kwanakin ransa.”—KUBAWAR SHARI’A 17:18, 19.

1. Kamar wa Kirista zai so ya zama?

WATAƘILA ba za ka taɓa tunanin gwada kanka da sarki ko sarauniya ba. Wane Kirista mai aminci ne ko ɗalibin Littafi Mai Tsarki zai yi tsammanin yana ko tana da ikon sarauta, kamar na nagargarun sarakuna irin su Dauda, Yosiya, Hezekiya, ko Yehoshafat? Duk da haka, za ka iya kuma ya kamata ka zama kamarsu, aƙalla, a hanya guda ta musamman. Wace hanya ke nan? Kuma me ya sa ya kamata ka so zama kamarsu a wannan hanyar?

2, 3. Menene Jehovah ya hanga game da sarki taliki, kuma menene sarkin zai yi?

2 A zamanin Musa, da daɗewa kafin Allah ya yarda a naɗa sarki taliki wa Isra’ilawa, Ya hangi muradin a naɗa musu sarki zai taso a tsakanin mutanensa a nan gaba. Saboda haka, ya hure Musa ya haɗa umurnai cikin Dokar alkawarin. Umurnai ne domin sarauta, ja-gora wa sarakuna.

3 Allah ya ce: “Sa’anda ka zo cikin ƙasa wadda Ubangiji Allahnka ke ba ka, . . . ka kuwa ce, Zan naɗa sarki shi yi mulkina, kamar yadda dukan al’umman da ke kewaye da ni suke yi; lallai wanda Ubangiji Allahnka za ya zaɓa, shi ne za ka naɗa. . . . Za ya zama kuwa, sa’anda yana zaune bisa kursiyin mulkinsa, za ya sāke wannan shari’a cikin littafi, . . . za ya zauna tare da shi kuwa, za ya riƙa karantawa daga ciki dukan kwanakin ransa: domin shi koya shi ji tsoron Ubangiji Allahnsa, shi kiyaye dukan zantattukan wannan shari’a da farillan nan, domin ya aikata.”—Kubawar Shari’a 17:14-19.

4. Menene umurnin Allah ga sarakuna ya ƙunsa?

4 Hakika, sarki wanda Jehovah zai zaɓa domin masu bauta masa zai yi nasa rubutun da ke cikin Littafi Mai Tsarki naka. Kuma sarkin zai karanta shi kowacce rana, a kai a kai. Ba domin watsa ƙwaƙwalwa ba ne kawai. Nazari ne kuma manufarsa tana da amfani. Wannan sarki da zai sami tagomashin Jehovah yana bukatar ya yi irin nazarin nan kuma ya kasance da zuciyar kirki. Kuma yana bukatar ya yi nazarin waɗannan hurarrun rubutu don ya zama sarki mai nasara, mai basira.—2 Sarakuna 22:8-13; Misalai 1:1-4.

Ka Koya Kamar Sarki

5. Waɗanne sashen Littafi Mai Tsarki Dauda yake bukatar ya kofa kuma ya karanta, kuma yaya ya ji game da wannan?

5 Me kake jin wannan zai kasance wa Dauda da ya zama sarkin Isra’ila? Hakika, zai bukaci ya kofi littattafai na Pentateuch (watau, Farawa, Fitowa, Leviticus, Litafin Lissafi, Kubawar Shari’a). Ka yi tunanin yadda zai kafu a cikin zuciyar Dauda yayin da ya yi amfani da idanunsa da hannayensa domin ya sake rubuta Dokar. Mai yiwuwa ne Musa ya rubuta littafin Ayuba da kuma Zabura ta 90 da ta 91. Dauda ya kofa har da waɗannan ne? Wataƙila. Kuma, ƙila lokacin, da akwai littattafai na Joshua, Alƙalawa, da Ruth. Hakika, za ka ga cewa Sarki Dauda yana da sashe mai yawa na Littafi Mai Tsarki don karantawa da kuma yin bimbini. Kuma kana da dalilin gaskata hakan, domin za ka lura da abin da ya ce game da Kalmar Allah, da yanzu yake a Zabura 19:7-11.

6. Yaya za mu tabbata cewa Yesu kamar kakansa Dauda ya so Nassosi?

6 Dauda Mai Girma—Yesu, Ɗan Dauda—ya bi irin wannan tafarkin. Al’adar Yesu ne ya je majami’a kowanne mako. A wajen yana jin ana karanta Nassosi kuma a yi kalami a kansu. Ban da haka ma, a wasu lokatai Yesu kansa ya yi karatu daga Kalmar Allah kuma ya ba da bayaninta. (Luka 4:16-21) Yana da sauƙi ka fahimci yadda ya san Nassosi. Ka karanta labaran Lingila, kuma ka lura ko sau nawa ne Yesu ya ce “an rubuta” ko kuma ya ambaci wasu wurare cikin Nassi. Shi ya sa, cikin Hudubarsa Bisa Dutse da aka rubuta a Matta, Yesu ya ɗauko magana sau 21 daga Nassosin Ibrananci.—Matta 4:4-10; 7:29; 11:10; 21:13; 26:24, 31; Yohanna 6:31, 45; 8:17.

7. Ta yaya Yesu yake dabam daga shugabannan addini?

7 Yesu ya yi biyayya da gargaɗi da ke a Zabura 1:1-3: “Mai-albarka ne mutum wanda ba ya bi ta shawarar miyagu ba, . . . Amma marmarinsa cikin shari’a ta Ubangiji ya ke; kuma a cikin shari’arsa ya kan riƙa tunani dare da rana. . . . iyakar abin da ya ke yi za shi yi albarka.” Wannan lallai ya saɓa da shugabannan addini na zamaninsa, da suke “zaune bisa mazaunin Musa” amma sun yi banza da ‘doka ta Ubangiji’!—Matta 23:2-4.

8. Me ya sa karatu da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da shugabannan addinin Yahudawa suke yi bai kasance da amfani ba?

8 Wataƙila wasu za su yi mamakin wani sashe da za a iya fassara shi kamar dai Yesu ba ya ƙarfafa yin nazarin Littafi Mai Tsarki. A Yohanna 5:39, 40, mu karanta abin da Yesu ya faɗa game da wasu a zamaninsa: “Kuna bin cikin littattafai, domin kuna tsammani a cikinsu kuna da rai na har abada, su ne fa suna shaidata: amma ba ku yarda ku zo wurina ba, domin sami rai.” Da wannan abin da ya ce, Yesu ba hana masu sauraronsa yake su yi nazarin Nassosi ba. Maimakon haka, yana nuna rashin gaskiya da ruɗunsu ne. Sun fahimci cewa Nassosi za su iya bishe su zuwa rai madawwami, har ila yau, Nassosin da suke binciken, da ya kai su wajen Almasihu, Yesu. Duk da haka dai, sun ƙi su amince da shi. Saboda haka, nazari bai kasance da amfani ba domin ba su da gaskiya, ba sa son su koya.—Kubawar Shari’a 18:15; Luka 11:52; Yohanna 7:47, 48.

9. Wane misali mai kyau ne manzanni da annabawa na farko suka kafa?

9 Wannan ya bambanta daga almajiran Yesu har da ma manzanninsa! Sun yi nazarin “littattafai masu-tsarki, waɗanda ke da iko su hikimtadda [mutum] zuwa ceto.” (2 Timothawus 3:15) Game da haka, suna kama da annabawa na farko da suka yi “bincike kuma da himma.” Annabawan ba su ɗauki nazarin nan kawai na ɗan lokaci na watanni ko shekara guda ne ba. Manzo Bitrus ya ce “suna nema su sani,” musamman game da Kristi da daraja da ke ƙunshe a matsayinsa na ceton mutane. A cikin wasiƙarsa ta farko, sau 34 Bitrus ya yi ƙaulin littattafai goma na Littafi Mai Tsarki.—1 Bitrus 1:10, 11.

10. Me ya sa kowannenmu ya kamata ya kasance da son nazarin Littafi Mai Tsarki?

10 A bayyane yake, nazarin Kalmar Allah da kyau aiki ne ga sarakuna a Isra’ila ta dā. Yesu ya bi wannan tafarki. Kuma yin nazarinsa aiki ne ga waɗanda za su yi sarauta tare da Kristi a sama. (Luka 22:28-30; Romawa 8:17; 2 Timothawus 2:12; Ru’ya ta Yohanna 5:10; 20:6) Wannan tafarki na sarakuna ya dace ga duka a yau da suke zuba ido ga albarka ta nan gaba a duniya a ƙarƙashin Mulkin.—Matta 25:34, 46.

Aiki Domin Sarakuna Kuma Domin Ka

11. (a) Wane haɗari ne game da nazari yake akwai ga Kiristoci? (b) Waɗanne tambayoyi zai yi kyau mu yi wa kanmu?

11 A hakikance kuma da gaske za mu ce kowanne Kirista na gaskiya ya kamata ya ko ta yi ƙoƙarin bincika Littafi Mai Tsarki. Ba abin da ake bukata da farko ba ne kawai sa’ad da kake nazari da Shaidun Jehovah. Kowannenmu ya kamata ya tsai da shawarar guje zama kamar wasu a zamanin manzo Bulus da daga baya suka daina yin nazarin. Sun koyi “tussa na farkon zantattukan Allah,” su “zancen ruknai na Kristi.” Amma, ba su ci gaba da yin nazarinsu ba domin haka ba su ci gaba sun kai “isassun mutane” ba. (Ibraniyawa 5:12–6:3) Mu ma za mu iya yin tambayar nan: ‘Yaya nake ji game da nazari da kaina na Kalmar Allah, ko na daɗe ina tarayya da ikilisiyar Kirista ne ko kuma ban jima ba? Bulus ya yi addu’a cewa Kiristoci a zamaninsa su ci gaba da “ƙaruwa kuma cikin sanin Allah?” Ina nuna cewa wannan shi ne muradi na?—Kolossiyawa 1:9, 10.

12. Me ya sa ci gaba da marmarin Kalmar Allah yake da muhimmanci?

12 Muhimmin abu a iya samun hali mai kyau na yin nazari shi ne kasancewa da marmarin Kalmar Allah. Zabura 119:14-16 ta yi nuni ga yin tunani kullum a kan Kalmar Allah da ma’ana domin ta wurinsa ne kake da marmarinsa. Hakan kuma gaskiya ne ko yaya daɗewarka a zaman Kirista. A batun nan ka tuna da misalin Timothawus. Ko da yake wannan Kirista dattijo yana hidimarsa na “mayaƙin kirki na Kristi Yesu,” Bulus ya aririce shi ya yi iyakacin ƙoƙarinsa a “rarrabe kalmar gaskiya sosai.” (2 Timothawus 2:3, 15; 1 Timothawus 4:15) Hakika, yin iyakacin “ƙoƙari” ya ƙunshi kasancewa da halin kirki na yin nazari.

13. (a) Ta yaya za a samu ƙarin lokaci don nazarin Littafi Mai Tsarki? (b) Wace gyara za ka iya yi don ka samu ƙarin lokaci don nazari?

13 Mataki domin halin kirki na nazari shi ne ba da lokaci a kai a kai don yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ina ka tsaya a batun nan? Ko da menene amsarka, kana tsammanin za ka iya amfana daga ƙara lokaci don yin nazari? Kana iya jin cewa ‘Ta yaya ke nan zan iya tsara lokaci domin wannan?’ Hakika, wasu sun ƙara ingancin nazarinsu na Littafi Mai Tsarki ta wurin farkawa da asuba. Suna iya karanta Littafi Mai Tsarki na mintoci 15 ko kuma yi wani nazari dabam. Ga wani hali kuma, idan kuma ka ɗan yi gyara a tsarinka na mako fa? Alal misali, idan kana karanta jaridar labarai yawancin kwanaki ko kuma kana sauraron labarai a telibijin kowanne maraice, za ka iya shirya ka ɗauke rana guda kawai a mako daga ciki? Kana iya yin amfani da lokaci da kuma ranar don yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Idan kana ɗaukan minti 30 a maimakon sauraron labarai a rana guda don nazarinka, za ka sami awoyi 25 a shekara. Ka yi tunanin amfani na ƙarin awoyi 25 na karatu ko nazarin Littafi Mai Tsarki! Ga wata shawara kuma: A cikin mako guda, a ƙarshen kowacce rana ka maimaita abin da ka yi. Ka bincika ƙila abin da za ka iya kawar da shi ko kuma rage lokacinsa don samun ƙarin lokaci na karatun Littafi Mai Tsarki ko kuma nazarinsa.—Afisawa 5:15, 16.

14, 15. (a) Me ya sa ake bukatar makasudi idan ya zo ga nazari da kanka? (b) Waɗanne makasudai ne ake da su idan ya zo ga karatun Littafi Mai Tsarki?

14 Me zai sa yin nazari ya zama da sauƙi a gare ka, da kuma daɗi? Makasudai. Wane irin makasudi ne mai ci za ka iya kafawa na nazari? Ga mutane da yawa, makasudi na farko shi ne karance Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa. Wataƙila har yanzu, sashen Littafi Mai Tsarki kawai ka karanta kuma ka amfana daga wannan. Za ka iya ka ƙuduri aniyar karance Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa? Makasudinka na farko zai iya zama na karance Lingila huɗu ne, sai kuma na biye, kana iya karance sauran Nassosin Helenanci na Kirista. Muddin ka sami gamsuwa da kuma amfaninsa, makasudinka na biye sai ya zama fara karanta littattafan Musa da na tarihi zuwa Esther. Idan ka yi wannan, za ka ga cewa da gaske za ka iya karance Littafi Mai Tsarki. Wata mace da take ’yar shekara 65 lokacin da ta zama Kirista, ta rubuta a rufin Littafi Mai Tsarki nata kwanan wata da ta fara karatunsa zuwa kwanan wata da ta kammala shi. Yanzu kwanan wata bibbiyu da ta rubuta ya kai biyar! (Kubawar Shari’a 32:45-47) Maimakon ta yi karatun daga kwamfuta ko a kan takarda, tana karatu daga Littafi Mai Tsarki.

15 Wasu da sun riga sun gama karance Littafi Mai Tsarki gabaki ɗayansa sun ɗauki wasu matakai na samun ƙarin nazari mai gamsarwa kuma mai amfani. Hanya ɗaya ita ce ka zaɓi abin da za ka yi nazarinsa a kowanne cikin littattafai na Littafi Mai Tsarki. A cikin “All Scripture Is Inspired of God and Beneficial” da Insight on the Scriptures, za ka iya samun labarai game da wasu yanayi, salo da kuma amfani da za a iya samu daga kowanne cikin littattafan Littafi Mai Tsarki.a

16. Wane misali game da nazarin Littafi Mai Tsarki za mu guje wa?

16 A lokacin da kake nazari, ka guji irin halin da wasu da wai su manazartan Littafi Mai Tsarki suke da shi. Suna nace bisa kalmomin Littafi Mai Tsarki sai ka ce mutum ne tushensa. Wasu cikinsu suna aza cewa kowanne littattafan Littafi Mai Tsarki ga masu sauraro kaza ne ko kuma su ƙaga wani nufi da kuma ra’ayin da kowanne marubucin littafin yake da shi. Irin halin nan na talikai zai sa littattafan Littafi Mai Tsarki su zama tarihi kawai ko kuma aza cewa addini ya bayyana ne kawai. Wasu manazartan suna mai da hankali da kalmomin ne kawai kamar nazarin falsafar adabi na Littafi Mai Tsarki. Sukan dulmaya cikin nazarin kalmomi da asalinsu suna ba da ma’anarsu na Ibrananci da Helenanci maimakon manufar saƙon Allah. Kana jin irin matakin nan zai sa a samu imani mai zurfi kuma mai motsawa?—1 Tassalunikawa 2:13.

17. Me ya sa ya kamata mu ɗauki Littafi Mai Tsarki saƙo domin dukan mutane?

17 Ra’ayin manazartan daidai ne ma? Gaskiya ne cewa kowanne littafi cikin Littafi Mai Tsarki yana da manufa ɗaya ne ko kuma rukuni guda ne kawai aka rubuta shi dominsu? (1 Korinthiyawa 1:19-21) Gaskiya ita ce, littattafan Kalmar Allah suna da daraja na dindindin ga dukan tsararrakin mutane da duk inda suka fito. Ko idan a farko littafin an yi magana ga mutum guda ne, kamar ga Timothawus ko Titus, ko kuma ga wani rukuni, kamar su Galatiyawa ko Filibbiyawa, ya kamata dukanmu mu yi nazarin waɗannan littattafai. Suna da amfani a gare mu kuma littafi guda zai iya magana a kan jigo da yawa kuma ya amfani mutane da yawa. Hakika, saƙon Littafi Mai Tsarki yana da amfani ga dukan mutane, haka ya taimaka mana mu fahimci abin da ya sa aka fassara shi cikin harsunan mutane a dukan duniya.—Romawa 15:4.

Amfani Dominka da Kuma Wasu

18. Yayin da ka karanta Kalmar Allah, a kan me za ka yi bimbini?

18 Yayin da kake nazari, za ka iske shi da amfani ka biɗi fahimi na Littafi Mai Tsarki kuma ka yi ƙoƙarin bincika yadda daki-dakin suke da nasaba da juna. (Misalai 2:3-5; 4:7) Abin da Jehovah ya bayyana cikin Kalmarsa yana haɗe ƙwarai da ƙudurinsa. Saboda haka, idan kana karatu ka ga nasabarsa da gargaɗin. Kana iya tunanin yadda wani aukuwa, ra’ayi, ko kuma annabci yake da nasaba da ƙudurin Jehovah. Ka tambayi kanka: ‘Menene wannan yake gaya mini game da Jehovah? Yaya ya shafe ƙudurin Allah da zai cika cikin Mulkinsa?’ Kana kuma iya yin tunani: ‘Ta yaya zan yi amfani da wannan bayani? Zan iya yin amfani da shi a koyarwa ko ba wa wasu shawara da ke bisa Nassosi?’—Joshua 1:8.

19. Wanene yake amfana yayin da kake gaya wa wasu abin da ka koya? Ka ba da bayani.

19 Damuwa game da wasu yana da amfani ma a wata sassa. A cikin karatunka da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka koyi sababbin abubuwa kuma ka sake samun fahimi. Ka yi ƙoƙarin saka su cikin taɗi mai daraja tsakanin iyali ko kuma wasu. Idan ka yi hakan a lokatai da sun dace kuma a hanya mai kyau, taɗin lallai zai zama da albarka. Idan ka lissafa abin da ka amfana ko kuma sashen da yake da amfani ƙwarai a gare ka, zai iya zama da taimako ga wasu. Fiye da haka, zai zama da amfani a gare ka. A wace hanya? Masana sun lura cewa mutum zai iya tuna abin da ya koya na dogon lokaci idan lokacin da abin yake sabo sabo a zuciyarsa ya maimaita shi, ta wajen gaya wa wasu.b

20. Me ya sa yake da amfani a karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai?

20 Duk lokacin da ka karanta wani littafi cikin Littafi Mai Tsarki lallai za ka koyi sabon abu. Za ka yi mamakin wuraren da dā ba ka yi wani tunani a kansu ba. Za ka ga sabuwar ma’ana. Wannan ya kamata ya nuna cewa maimakon ya zama wani adabi kawai na mutane, littattafan cikin Littafi Mai Tsarki tamani ne a gare ka, domin ka yi nazarinsu a kai a kai kuma ka amfana. Ka tuna, cewa sarki Dauda, an bukaci ya “riƙa karantawa daga ciki dukan kwanakin ransa.”

21. Wace albarka za ka yi zaton samu daga ƙara nazarinka na Kalmar Allah?

21 Hakika, waɗanda suke ɗaukan lokaci su yi nazari mai zurfi na Littafi Mai Tsarki sukan amfana ƙwarai. Suna samun tamani da fahimi na ruhaniya. Dangantakarsu da Allah ta zama da ƙarfi, na kud da kud. Suna kuma zama da tamani na ƙwarai ga waɗanda suke cikin iyalinsu, ga ’yan’uwansu cikin ikilisiyar Kirista, da kuma waɗanda ba sa bauta wa Jehovah tukuna.—Romawa 10:9-14; 1 Timothawus 4:16.

[Hasiya]

a Waɗannan abubuwan yin nazari, Shaidun Jehovah ne suka buga su cikin harsuna da yawa.

b Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Agusta, 1993 (Turanci), shafuffuka 13-14.

Ka Tuna?

• Menene sarakuna a Isra’ila suke bukatar su yi?

• Wane misali Yesu da manzanni suka kafa game da nazarin Littafi Mai Tsarki?

• Wace gyara za ka yi don ka ƙara lokacinka na nazari?

• Da wane hali za ka soma nazarin Kalmar Allah?

[Akwati a shafi na 13]

“A Hannunmu”

“Idan muna son . . . jerin lafazi na Littafi Mai Tsarki, za mu same shi cikin Intane. Amma idan muna so mu karanta Littafi Mai Tsarki, mu yi nazarinsa, mu yi tunani a kansa, mu yi bimbini a kansa, ya kamata ya kasance a hannunmu, domin ta haka ne kaɗai za mu sa shi cikin azantai da kuma zukatanmu.”—Gertrude Himmelfarb, farfesa shahararriya da ta yi murabus, na City University, New York.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba