Siffofi Na Addini—Tushensu na Dā
“Siffofi hanyar haɗa mu ne da nagarta da kuma tsarkakar Allah da na Waliyansa.”—GREEK ORTHODOX ARCHDIOCESE NA AUSTRALIA.
AWANNAN rana mai zafi ta Agusta, rana ta buga matakala ta siminti da take kai wa gidan ’yan zaman zuhudu na “Uwar Allah Mafi Tsarki,” a tsibirin Tínos, a Tekun Aegean. Wannan zafi mai ƙuna bai rage niyyar ’yan ziyarar bauta 25,000 na Greek Orthodox waɗanda suke tafiya a hankali suna ƙoƙarin su kai ga siffar uwar Yesu wadda aka yi wa ado.
Wata ’yar yarinya, gurguwa, hakika tana cikin azaba tana rarrafe da gwiwoyinta da suke jini. Kusa da ita, wata mace da ta yi tafiya daga wani ɓangaren ƙasar, tana ƙoƙari ta ci gaba da tafiya. Wani mutum ya yi gumi jigib yayin da yake ƙoƙarin ya ƙusa kai zuwa wajen jama’ar. Burinsu su yi wa siffar Maryamu sumba kuma su yi sujjada a gabanta.
Waɗannan mutane masu tsarin addini babu shakka da gaske suna da muradin su bauta wa Allah. Amma nawa ne tsakaninsu suka sani cewa ibada ga siffofin addinin sun samo asalinsu ne ƙarnuka kafin ma zuwan Kiristanci?
Yaɗuwar Siffofi
A ƙasashen Orthodox, siffofi suna ko’ina. A gine-gine na coci, siffofin Yesu, na Maryamu, da wasu “waliyai” suna wajaje masu muhimmanci. Mabiya sau da yawa suna daraja waɗannan siffofin da sumbace-sumbace, da turare, da kuma kunna kyandirori. Bugu da ƙari, kusan dukan gidajen ’yan Orthodox suna da nasu wajen ajiye siffa, wajen da ake yin addu’o’i. Ba abin mamaki ba ne Kiristoci ’yan Orthodox su ce sa’ad da suka bauta wa siffa suna matsawa kusa ne da Allah. Sun yi imani cewa siffofi suna da albarkar Allah da kuma iko na mu’ujiza.
Waɗannan masu bi wataƙila su yi mamaki idan suka fahimci cewa Kiristoci na ƙarni na farko ba su yarda da yin amfani da siffa ba wajen bauta. Littafin nan Byzantium ya ce: “Kiristoci na farko, sun gāji ƙyamar gumaka daga addinin Yahudawa, kuma ba sa son ɗaukaka hotuna na mutane masu tsarki.” Wannan littafin ya lura cewa: “Daga Ƙarni na Biyar zuwa gaba, siffofi ko kuma gumaka . . . suka fara yawa a bauta tsakanin jama’a ko kuma na kaɗaita.” Idan ba daga Kiristanci na ƙarni na farko ba, daga ina ne amfani da siffofi na addini ya samo asalinsa?
Bincika Tushensu
Mai bincike Vitalij Ivanovich Petrenko ya rubuta: “Amfani da gumaka da kuma al’adarta sun kasance da daɗewa kafin zamanin Kirista kuma ‘tushensu daga arnanci ne.’ ” ’Yan tarihi da yawa sun yarda, suna cewa tushen bauta wa siffofi an samo su daga addinan Babila ta dā, Masar, da kuma Hellas. Alal misali, a Hellas ta dā, siffofin addini suna da surar halittu da aka ƙaga. An yi imani cewa an ba waɗannan iko na Allah. Mutane suna tsammanin cewa wasu cikin waɗannan gumaka ba a yi su da hannu ba amma sun faɗo ne daga sama. Lokacin bukukuwa na musamman, irin waɗannan gumaka na bauta ana ɗaukansu a zagaya birni da su, a yi musu hadaya. “Wannan siffa ta bautar, masu tsarin addinin suna ɗaukansu Allah ne kansa, . . . ko da yake an yi ƙoƙarin a bambanta tsakanin Allah da siffar,” in ji Petrenko.
Ta yaya wannan ra’ayi da ayyuka suka shigo cikin Kiristanci? Wannan mai bincike ya lura cewa, ƙarnuka bayan mutuwar manzannin Kristi, musamman a ƙasar Masar, “Imani na Kiristoci ya fuskanci ‘damawar imanin arna’—da aka ƙago shi daga ayyuka da kuma imani na Masarawa, Helenawa, Yahudawa, mutanen Asiya da kuma Romawa da ake yinsu tare da ayyuka da imani na Kiristoci.” Saboda haka, “Kiristoci masu fasaha suka karɓi [salo na arna] kuma suka yi amfani da siffofinsu, suka ba su sababbin sunaye, ko da yake ba su tsarkaka su ba daga dukan rinjaya na arna.”
Ba da daɗewa ba jama’a da kuma mutane ɗai-ɗai suka mai da hankali ga siffofi. A cikin littafin nan The Age of Faith, ɗan tarihi Will Durant ya kwatanta yadda wannan abin ya faru, yana cewa: “Sa’ad da adadin waliyai da ake bauta musu ya ƙaru, sai bukatar a bambance su kuma a tuna da su ya samu; aka fito da hotunansu da na Maryamu da yawa; kuma game da Kristi ba siffarsa ba kawai amma har da gicciyarsa ya zama abin bauta—har, wa jahilai, suka zama abin sihiri. ’Yancin tunani tsakanin mutanen ya sa abubuwa masu tsarki, hotuna, gumaka suka zama abin ado; mutane suna yi musu sujjada, suna yi musu sumba, suna ƙona kyandirori da kuma turare a gabansu, suna tara musu furanni, kuma suna neman mu’ujiza daga wurin su. . . . Fada da kuma hukumar Coci suka riƙa nanata cewa wannan gumaka ba alloli ba ne, amma suna abubuwan tuna da allolin ne; amma mutane ba su damu ba su bambanta su.”
A yau, mutane da yawa da suke amfani da siffofi za su musanta cewa siffofi ba abubuwan bauta ba ne, daraja kawai ake ba su—ba bauta ba. Za su yi da’awar cewa zane-zane na addini daidai ne—abin da ba za a iya yasarwa ba—abubuwan taimako ne wajen bautar Allah. Wataƙila kai ma haka kake gani. Amma tambayar ita ce, Yaya Allah yake ɗaukan wannan? Zai yiwu ne cewa daraja siffofi daidai yake da bauta masa? Shin irin waɗannan ayyukan za su iya haddasa haɗari?
[Box/Hoto a shafi na 4]
Mecece Siffa?
Ba kamar gumaka ba da ake yawan amfani da su wajen bauta a Cocin Roman Katolika, siffofin Kristi, Maryamu, “waliyai,” mala’iku, mutanen dā ko kuma aukuwa na Littafi Mai Tsarki ne, ko kuma na tarihin Cocin Orthodox. Ana zana su ne a kan allo na katako.
In ji Cocin Orthodox, “a siffofin Waliyai, hoton ba daidai yake ba da na mutane masu jini da tsoka.” Har ila, game da siffofin, “suna faɗaɗawa yayin da mutum ya yi nisa da su”—hoton ba ya ƙanƙancewa yayin da aka yi nisa da shi. “Ba su da inuwa, ko kuma yadda za a nuna dare ko rana.” Kuma an yi imanin cewa katako ko kuma fantin siffa za su iya “cika da bayyanuwar Allah.”
[Hoto a shafi na 4]
Yin amfani da siffofi tushensu daga ayyukan arna ne
[Inda Aka Ɗauko Hoto da ke shafi na 3]
© AFP/CORBIS