Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w02 7/1 pp. 5-8
  • Ka Bauta Wa Allah “Cikin Ruhu”

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Bauta Wa Allah “Cikin Ruhu”
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Bayyananniyar Koyarwar Littafi Mai Tsarki
  • Haɗari da Yake Ɓoye
  • Za a Yi Addu’a ga “Waliyai” ne ko Maryamu?
  • Ka Tsare Dangantakarka da Allah
  • Siffofi Na Addini—Tushensu na Dā
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
  • Me Ya Sa Shaidun Jehobah Ba Sa Yin Amfani Da Siffofi A Bautarsu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Ƙage Na 6: Allah Ya Amince Da Yin Amfani Da Gumaka Da Siffofi A Bauta
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ya Kamata Mu Yi Bauta wa Siffofi?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2002
w02 7/1 pp. 5-8

Ka Bauta Wa Allah “Cikin Ruhu”

“Za ku kwatanta Allah fa da wanene? Ina kama kuwa da za ku gwada ta da shi?”—ISHAYA 40:18

WATAƘILA ka gaskata cewa amfani da siffofi an yarda da shi wajen bautar Allah. Za ka ji cewa wannan yana matso da kai kusa da Mai Sauraron addu’a, wanda ba a gani kuma wanda kamar dai ba wani ba ne.

Amma muna da ’yanci ne mu zaɓi salon yadda za mu kusaci Allah? Bai kamata ba ne cewa Allah kansa yana da ikon ya faɗi abin da ya yarda da shi da kuma abin da bai yarda da shi ba? Yesu ya yi bayanin ra’ayin Allah game da wannan batun sa’ad da ya ce: “Ni ne hanya, Ni ne gaskiya, Ni ne rai: ba mai-zuwa wurin Uban sai ta wurina.” (Yohanna 14:6) Waɗannan kalmomin kawai sun kawar da amfani da siffofi ko kuma wasu abubuwa masu tsarki.

Hakika, da akwai ainihin irin bautar da Jehovah Allah yake karɓa. Mecece wannan? A wani lokaci Yesu ya yi bayani: “Sa’a tana zuwa, har ma ta yi yanzu, inda masu-yin sujjada da gaskiya za su yi ma Uba sujjada a cikin Ruhu da cikin gaskiya kuma; gama irin waɗannan Uban ya ke nema, su zama masu-yi masa sujjada. Allah ruhu ne; waɗanda su ke yi masa sujjada kuma, sai su yi sujjada cikin ruhu da cikin gaskiya kuma.”—Yohanna 4:23, 24.

Allah wanda “ruhu” ne, za a iya kwatanta shi da siffa ta zahiri ne? A’a. Ko yaya kyan wannan siffar, ba za ta taɓa kusantar darajar Allah ba. Saboda haka siffa ta Allah ba za ta taɓa yin kama da shi ba. (Romawa 1:22, 23) Shin mutum zai yi ‘bauta cikin gaskiya’ idan yana zuwa ga Allah ta wajen wata siffar da mutum ya zana?

Bayyananniyar Koyarwar Littafi Mai Tsarki

Dokar Allah ta hana a yi siffofi domin bauta. Doka ta biyu a cikin Dokoki Goma ta ce: “Ba za ka misalta wata ƙira, ko surar abin da ke cikin sama daga bisa, ko abin da ke cikin duniya daga ƙasa, ko kuwa abin da ke cikin ruwa daga ƙarƙashin ƙasa: ba za ka yi sujjada garesu ba, ba kuwa za ka bauta musu ba.” (Fitowa 20:4, 5) Hurarrun Nassosi na Kirista kuma sun ba da umurni: “Ku guje ma bautar gumaka.”—1 Korinthiyawa 10:14.

Babu shakka, mutane da yawa sun dage cewa amfani da suke yi da siffofi wajen bauta ba bautar gumaka ba ce. Alal misali, Kiristocin Orthodox, sau da yawa sun ƙi yarda cewa ainihi siffofi da suke yi wa sujjada, suke durƙusa wa, ko kuma suke yi wa addu’a ne suke bauta wa. Wani firist na Orthodox ya rubuta: “Muna daraja su domin abubuwan suna da tsarki, kuma domin muna bauta wa waɗanda siffofin suke wakilta.”

Har yanzu ba a amsa tambayar ba tukuna: Shin Allah ya yarda da yin amfani da siffofi ne domin bauta da ba ta kai tsaye ba ma? Babu inda Littafi Mai Tsarki ya ba da izini a yi waɗannan ayyuka. Sa’ad da Isra’ilawa suka yi gunkin ɗan maraƙi, da da’awar cewa domin su bauta wa Jehovah ne, ya nuna rashin yardarsa, ya ce sun yi ridda.—Fitowa 32:4-7.

Haɗari da Yake Ɓoye

Amfani da wani abu na zahiri wajen bauta aiki ne mai haɗari. Ba wuya zai jarabi mutane su bauta wa abin maimakon Allah da abin yake wakilta. Watau, siffar sai ta zama abin bauta.

Wannan ya faru da abubuwa da yawa a zamanin Isra’ilawa. Alal misali, Musa ya yi macijin jan ƙarfe bayan Fitowarsu daga ƙasar Masar. Asali, abin da macijin yake wakilta a kan gungumen domin warkarwa ne. Waɗanda aka hore su da cizon maciji za su iya kallon macijin jan ƙarfen kuma su samu taimakon Allah. Amma bayan mutanen sun zauna a Ƙasar Alkawari, kamar dai sun juya wannan gungumen ya zama gunki, kamar dai macijin jan ƙarfen yana da ikon ya warkar. Sun ƙona masa turare har ma suka ba shi suna Nehustan.—Litafin Lissafi 21:8, 9; 2 Sarakuna 18:4.

Isra’ilawa suka yi ƙoƙarin su yi amfani da sunduƙin alkawari kamar laya ga abokan gabansu, sakamakon haka ya zama da lahani. (1 Samu’ila 4:3, 4; 5:11) Kuma a zamanin Irmiya, mazaunan Urushalima sun damu da haikalin sosai, fiye ma da yadda suka yi da bautar Allah a cikinsa.—Irmiya 7:12-15.

Ra’ayin a bauta wa abubuwa maimakon Allah har wa yau yana ko’ina. Mai bincike Vitalij Ivanovich Petreko ya ce: “Siffar . . . ta zama abin bauta kuma ana cikin haɗarin bautar gumaka . . . Dole ne a yarda cewa ainihin ra’ayin, na arna ne da aka kawo cikin bautar siffa ta wajen abin da yawanci suka yi imani da shi.” Hakazalika, firist na Cocin Orthodox na Helas Demetrios Constantelos ya ce a littafinsa Understanding the Greek Orthodox Church: “Yana yiwuwa Kiristoci su mai da siffa abin bauta.”

Da’awar cewa siffofi suna taimako ne kawai wajen bauta, ba a yarda da shi ba. Me ya sa? Ba gaskiya ba ne cewa wasu siffofi na Maryamu da wasu “waliyai” za a ɗauke su sun cancanci ibada sosai fiye da wasu siffofin da suke wakiltan wasu mutane da suka mutu da daɗewa ba? Alal misali, wata siffa da take wakiltan Maryamu a Tínos, Hellas, tana da mabiyanta na Orthodox da suka saɓa da wasu masu bautar wata siffa da take wakiltar Maryamu a Soumela, a arewacin Hellas. Kowanne cikin rukuni biyun ya yi imani cewa siffarsa ce ta fi, tana yin mu’ujizoji fiye da ɗayar, ko da yake dukansu biyu suna wakiltar mutuniya ɗaya ce da ta mutu da daɗewa. Saboda haka, mutane sun yi imani cewa waɗannan siffofi suna da iko sai suka fara bauta musu.

Za a Yi Addu’a ga “Waliyai” ne ko Maryamu?

To, yaya game da bauta wa wasu, kamar su Maryamu ko kuma “waliyai”? Yesu, sa’ad da ya amsa jarabtar Shaiɗan ya yi ƙaulin Kubawar Shari’a 6:13 kuma ya ce: “Ka yi sujjada ga Ubangiji Allahnka, shi kaɗai ma za ka bauta masa.” (Matta 4:10) Kuma daga baya ya ce masu bauta ta gaskiya za su bauta wa “Uba,” shi kaɗai. (Yohanna 4:23) Da fahimtar wannan, wani mala’ika ya gargaɗi manzo Yohanna da ke ƙoƙarin ya bauta masa, yana cewa: “Kada ka yarda ka yi wannan . . . ka yi ma Allah sujjada.”—Ru’ya ta Yohanna 22:9.

Yana da kyau ne a yi wa uwar Yesu ta duniya, Maryamu, ko kuma wani “waliyi,” addu’a, a roƙe su su roƙi Allah a maimakonmu? Amsar Littafi Mai Tsarki ta kai tsaye ita ce: “Akwai Allah ɗaya, matsakanci ɗaya kuma tsakanin Allah da mutane, shi kuwa mutum ne, Kristi Yesu.”—1 Timothawus 2:5.

Ka Tsare Dangantakarka da Allah

Amfani da siffofi wajen bauta, ƙin koyarwa ce ta kai tsaye ta Littafi Mai Tsarki, ba zai taimaki mutane su samu tagomashin Allah ba kuma su samu ceto. Akasin haka, Yesu ya ce rai madawwami ya dangana ne a kan mu samu sanin Allah makaɗaici na gaskiya, sanin mutuntakarsa marar kama da kuma nufe-nufensa da yadda yake sha’ani da mutane. (Yohanna 17:3) Siffofi da ba sa gani, ba sa ji, kuma ba sa magana ba sa taimakon mutum ya san Allah kuma ya bauta masa a hanyar da ya amince da ita. (Zabura 115:4-8) Ilimi mafi muhimmanci yana a yalwace ta wajen nazarin Kalmar Allah, Littafi Mai Tsarki.

Ban da ma cewa ba su da amfani, bautar siffofi tana da haɗari ga ruhaniya. Ta yaya? Da farko, za ta iya ɓata dangantakar mutum da Jehovah. Game da Isra’ilawa, waɗanda “suka ba shi haushi da allolinsu abin ƙyama,” Allah ya ce: “Zan ɓoye fuskata a gare su.” (Kubawar Shari’a 32:16, 20, The New American Bible) Sake kyautata dangantakarsu da Allah yana nufin ‘ƙin allolinsu na zunubi.’—Ishaya 31:6, 7, NAB.

Lallai gargaɗin Nassin nan: “ ’Ya’yana ƙanƙanana, ku tsare kanku daga gumaka,” ya dace!—1 Yohanna 5:21.

[Akwati a shafi na 6]

Taimako Domin a Yi Bauta “Cikin Ruhu”

Olivera ’yar Cocin Orthodox ce mai ibada a Albaniya. Sa’ad da ƙasar ta hana addini a shekara ta 1967, Olivera ta ci gaba da ayyukanta na addini a asirce. Ta yi amfani da yawancin ɗan kuɗin fensho nata wajen sayan siffofi na zinariya da azurfa, turare, da kuma kyandirori. Sau da yawa takan ɓoye su a kan gadonta ta kwana a kan kujera domin tana tsoron kada a gansu ko kuma a sace su. Sa’ad da Shaidun Jehovah suka ziyarce ta a shekarun 1990, Olivera ta fahimci gaskiyar Littafi Mai Tsarki cikin saƙonsu. Ta fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da bauta ta gaskiya “cikin ruhu,” kuma ta koyi yadda Allah yake ji game da siffofi. (Yohanna 4:24) Mashaidiya da ta yi nazari da ita ta lura cewa siffofin suna raguwa dukan lokacin da ta ziyarci gidan Olivera. A ƙarshe, babu ko ɗaya. Bayan baftismarta, Olivera ta ce: “A yau, maimakon siffofi marasa amfani, ina da ruhu mai tsarki na Jehovah. Ina godiya ƙwarai cewa ruhunsa ba sai da siffofi ba zai samu.

Athena, daga tsibirin Lesbos a Helas, tana da ƙwazo ƙwarai a Cocin Orthodox. Tana cikin mawaƙa kuma tana bin al’adunsu sawu da ƙafa, har da yin amfani da siffofi. Shaidun Jehovah suka taimaki Athena ta fahimci cewa ba dukan abin da aka koya mata ba ne ya jitu da Littafi Mai Tsarki. Wannan ya haɗa da amfani da siffofi da kuma gicciya a wajen bauta. Athena ta dage cewa za ta yi nata bincike game da tushen waɗannan siffofi na addini. Bayan ta bincika littattafan bayani masu yawa, ta yarda cewa tushen wannan siffofi na addini ba a Kiristanci ba ne. Muradinta ta bauta wa Allah “cikin ruhu” ya kai ta ga halaka dukan siffofinta, duk da tsadarsu. Amma, Athena tana farin ciki ta yi hasarar domin ta bauta wa Allah a hanya mai tsabta ta ruhaniya da zai gamsar da shi.—Ayukan Manzanni 19:19.

[Box/Hoto a shafi na 7]

Siffofi Ayyukan Zane ne Kawai?

A shekarun baya bayan nan, siffofin Orthodox an tara su daga dukan duniya. Waɗanda suke tara su ba su ɗauke su abubuwa masu tsarki ba, amma kawai zane-zane ne da suke nuna al’adar Byzantine. Ba abin mamaki ba ne ka ga irin waɗannan siffofin an yi ado da su a gida ko kuma ofishin mutumin da yake da’awar shi bai yarda da akwai Allah ba.

Amma Kiristoci na gaskiya ba su manta da ainihin dalilin siffar ba. Siffa ce ta bauta. Ko da yake Kiristoci ba za su tuhumi ’yancin wasu su mallaki siffofin ba, su ba za su kasance sun mallaki siffofin ba, ko da kayayyakin zane ne kawai. Wannan ya yi daidai da mizanin da yake Kubawar Shari’a 7:26: “Ba kuwa za ka kawo abin ƙyama [gumaka da ake amfani da su wajen bauta] cikin gidanka ba, har ka zama haramtaccen abu kamarsa: amma za ka ƙi shi sarai, za ka yi ƙyamarsa sarai.”

[Hoto a shafi na 7]

Allah bai yarda a yi amfani da gumaka ba wajen bauta

[Hoto a shafi na 8]

Sani daga Littafi Mai Tsarki yana taimakonmu mu bauta wa Allah cikin ruhu

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2025 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba